Namiji Kudan Zuma Book by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt

Author :  Hassana Abdulaziz Yakasai Category :  A Books

Chapter   6 / 7

15K to 18K   out of 19.4K words

shigo dashi.


Tun anan naga anty Deenah tana binsa da wani irin fitinannen kallo bandai tankaba amma k'eyarta yasha harara, da haka nima nayi alwala na wuce d'akin mu lokacin har anty Deenah ta idar.


Wata irin rayuwa muka shimfid'a da Yaya ABDUL SAMAD (NAWAN) tunda karancin shekaru na ya tabbatar min da yana sona zai aureni tun inajin haushin tsadaddun kalamansa har na dawo suna min dad'i tun inajin kunya har na dawo inajin kewa a duk ranan da wani abu ya gifta bamu zauna ya bani labarin yadda nake a zuciyar sa ba, duk kuwa da ya tabbatar min da cewa nice duniyarsa nice jin dad'in duniyarsa sannan babu wani babban uzuri da ya zartani a rayuwar sa.


Ina matuk'ar jin dad'in hira da NAWAN ina matuk'ar k'aunar kasancewa dashi ya iya zantuka masu matuk'ar sanyi da sanya nutsuwa Ina da tabbacin duk ranan da na rasa NAWAN tabbas nima na rasa kaina domin shine farin cikina duniyata inaga dama da k'aunar juna aka halicce mu.


A b'angaren tsokana da fitina kuwa harga Allah babu abinda na fasa musamman ma yanzu da su yazeeda mak'otanmu suka tare wayyo aiki ya dad'a lalacewa dan Hajiya da Babar su yazeeda kullum cikin bada hak'uri suke gashi muyi tabin gidajen tsofaffin unguwarmu muna kid'e kid'e da rawa Marwa har tafimu gashi bamu da wajen zama sai gefen wata bola dake bakin layinmu kuma duk sanda wani ya ganmu a cikin yan gidanmu ko gidansu yazeeda ko Marwa wallahi dukan mutuwa suke mana amma bamu fasaba ga Marwa da shegen kwalliyar aljanu a wani jagira asa eyeshadow eyelaner dama duk ciki nice bana wannan shafe shafen idan akaga nasa hodama to unguwa zamu fita da Hajiya.


A gida kuwa halina yasa kullum kafin mu kwanta sai mun tik'i d'an banzan dambe da anty Deenah dan ta gaji da halina ta fara biyemin duk dacewa ni na iya fad'an yan China hakan yasa bata wani nasara akaina.


Yau da dare muna tareda yazeeda dama Marwa ita wannan rik'on matar ubane ba'a damu da duk inda zataba in zatakai d'ayan dare babu mai cewa daga ina take kasancewar itace yar fari ga mahaifinta kuma matar babanta irin shashashun matan nanne da nasuma basu damu dasuba bare kuma d'an wani.


Yanzu haka muna js 2 nida Marwa wacce tundaga primary har yanzun tare muke tafiya kuma ajinmu guda yazeeda dai kam ta wucemu kuma da alama ta girmemu halinne kawai yazo d'aya ake d'iga fitina.


A gaskiyar magana ba d'an k'aramin hak'uri anty Deenah keyi damuba muna mata abu iri iri tun tana kirb'armu har tagaji ta daina saidai idan munyi mata wani abun tace Allah ka shiryamin wannan yaran


Yau da dare muka shirya zamuje duba alhaji bawa mak'ocin mune shima bashi da lafiya aka kwantar dashi a asbitin malam Aminu Kano da farko Hajiya tace baza'a damuba mukace wallahi koda k'afa ne sai munje sanin cewa da gasken sai munje yasa tace NAWAN ya d'auko motar daddy yakaimu


MAMAN ISLAM CE




NAMIJI K'UDAN ZUMA


By


MAMAN ISLAM


☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️


Page 20


Duk mukayi wanka muka shirya anty Deenah sai hararan mu take nace "na rantse da Allah idan kika k'ara hararana bazaki shigar mana mota ba saidai ya Ali ko ya habu sukaiki a motarsu"


Sanin halina yasa ta daina hararanmu amma tayi wani kicin kicin da rai har zamu fita anty Deenah ta dubi Hajiya tace "Hajiya kijawa yaranki kunne muje lafiya mu dawo lafiya kada su ja mana wata fitinar" ai kafin ta k'arasa nayi kanta da hargagi da hayaniya nace kece fitinanniya wallahi au da marasa ji kika d'auke mu wallahi yau sai an banbance tsakanin nidake waye fitinannen" sanin zan iya kamata da kokawa yasa Hajiya ta rik'o hannuna tace haba autana akwai fitinanne irinta karki wani biye mata ai nasan yarana masu hankali ne" da wannan Hajiya ta lallab'a ni muka wuce muka tafi duba alhaji bawa.


A mota NAWAN yana ta jana da hira ni kuma ina tunanin ta yadda idan munje zamu zame mutafi mutuware dan ganin shin da gaskene akwai gawa mai tafiya ko kuwa k'arya Nana ce d'iyar wata mak'otanmu ce daga ita har uwar idan suka shirga maka wata k'aryar yasin saika zuba da gudu tsabar kid'imewa.


Muna zuwa muka duba alhaji bawa mun d'an kwaahi mintuna kusan sha biyar a wajen kafin mu mik'e ya Abdul yace mu rakashi ya duba wani abokinsa kafin mu wuce rad'a yazeeda tayi mana nida Marwa muka kuwa shek'e da dariya muka tafa da sauri anty Deenah da NAWAN suka juyo sai kuwa na had'e rai dan karma su tambayi dariyan da kukeyi ganin yadda nai da fuskar yasa anty Deenah ta juya shima kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya sukaci gaba da tafi mu kuma muka zame mukayi wata lungu da yazeeda tace mana ta hanyar ne mutuware yake.


Ba d'an k'aramin nisane tsakanin inda muka baro zuwa mutuwaren ba wallahi gagarumar tafiyace sannan kuma hanyar babu mutane sosai sai tsilli tsilli ga hanyar ya d'anyi duhu dan ba ko ina akasa kwaiba amma tsabar fitina irin namu haka muka doshi wajen.


Muna zuwa mukaga ana fito da wata gawa, sai mukayi saurin komawa baya muka lab'e ganin bayan likitocin harda yan sanda araina nace ko gawar waye wannan oho saida suka sa gawar a motar asbitin sukabawa mai gadi kud'i suka tafi sannan muka fito.


"Sannu baba" nace bayan mun k'arasa wajen mai gadin munyi sallama ya amsa had'a baki mukayi muka gaidashi kamar wasu yan makaranta ya amsa yana kallonmu da mamaki a ransa kuwa yana d'ar d'ar anya ba fatalwowi bane dan wani zubin ana firgita shi amma ba muraran irin haka ba saidai daga nesa.


Katse masa tunanin nayi ta hanyar fad'in "baba dan Allah munzo ganin mutuware ne"
Jin abinda mukace ya sauke b'oyayyar ajiyar zuciya yace "aiata kungani sai ku wuce ku tafi kafin gawar d'aukar fansa ta mik'e ta fara ta kanku, ya fad'i hakanne dan yasamu ya koresu.


Wallahi gabana ya fad'i amma tsabar fitina nace "dan Allah baba nuna mana ita munason ganinta".
"Gawar d'aukar fansan?"
Ya fad'a yana zaro ido da mamakin rashin tsorona.


In takaice muku labarin duk ta inda baba mai gadin mutuware ya b'ullo muce ba hakaba ya d'auke wani katon katako ya bimu da gudu muka arce


MAMAN ISLAM








NAMIJI K'UDAN ZUMA


By


MAMAN ISLAM


☀️ FIRST CLASS WRTERS ASSOCIATION☀️


Page 21


"Nifa bazan tab'a barin wajen nan ba saina shiga mutuwaren nan" na fad'a ina kallon Marwa tace"nima gaskiya ina son gani, ta fad'a cikin d'ar d'ar dan har ga Allah tsoron SUHANA ne ya hanata nuna zahirin tsoronta a fili dan SUHANA muguwar fitinanniya ce wallahi.


Ta bayan d'akin muka zagayo saiga wani window da alama ma ba'a bud'e shi dan duk yayi funfuna kalle kalle na farayi ko zan hango wani abun takawar idanuna ya sauka kan wani benci can k'ark'ashin wata bishi ga d'an irin abin treder d'in nan da alama wani ke saide saide a wajen da sauri na nufi wajen Marwa tayi saurin bin bayana ita kuma yazeeda ta tsaya tana d'an dudduba ta inda zamu samu sauk'in haurawa.


Bencin Marwa ta tayani muka d'auko da k'yar dan yana da nauyi wallahi daidai window muka ajiye na taka sai dai ko kad'an ban ga alamar na doshi hanyar isa kusa da window ba dan yana da tsayi sosai.


NAWAN kuwa bayan sun fitone suka nememu sama ko k'asa suka rasa da da farko sunyi tunanin wajen mota mukaje mu jira amma ganin bama wajen hankalin NAWAN yai masifar tashi a matuk'ar gigice ya dubi anty Deenah yace.


"Yanzu fisabilillahi Deenah ina kike tunanin TAWAN zataje, ko kuma kinji suna hiran zasu duba wani anan d'in, ko akwai wanda suka sani sani a quarters d'in asbitin nan?"


Yadda ya wani gigice ya rud'e yana faman jera mata tambayoyi sai taji wani irin mugun kishin kanwar tata dan haka cikin d'an zafi zafi tace "ajiyansu kabani bare ka isheni da tambaya kasan hali ai ka taho dasu"


Da mamaki yabi bayanta da kallo to shi kuma me yayi mata take masa tsawa haka? lallai ma yarinyar nan, ransa ya d'an baci da abin da Deedah tayi masa saidai bai sa abin yayi nisaba may be wani abun SUHANA tayi mata shine ita kuma ta huce akansa.


Saida muka samo bencina uku harda turmi wanda mu kanmu saida mukayi mamakin ganin sa acan wani d'an lungu turmin fa k'atone wallahi.


Saida muka gama daidaitawa sannan rigima ya balle tsakanin ni da yazeeda tana ita zata fara hawa ina nice k'arshe dai Marwa tace tunda yazeeda doguwace sosai ko bata taka turmin ba tsayin ta zaikai kawai muhau tare haka kuwa muka hau tare ai kuwa hawan yazeeda yayi amfani domin k'ofar a rik'e yake k'am k'am munaja munajin kamar anaja daga ciki amma tsabar naci bamu hak'ura ba gashi duk gumi ya jik'amu "anya k'ofar nan zai bud'u kuwa?


Na fad'a ina kallon yazeeda tace "ai wallahi duk bala'in sa munfishi ko ana muzuru ana shaho sai mun lek'a wajennan yau" ita dai Marwa tana daga gefe tana jinmu jira kawai take taga daga daga ta arce.


"Kinga mu had'a k'arfin mu waje d'aya muja k'ofar nan da mugun k'arfi zai bud'e" na fad'a wa yazeeda haka kuwa mukayi muka had'a k'arfinmu mukaja da k'arfi maimakon k'ofar ya bud'e sai mune muka fad'o dukanmu ai kuwa mun bugu a mazaunen mu mun d'an jima a zaunen muna tunanin yadda zamuyi saijin wani k'ak'arfan sauti mukayi k'a k'a k'a k'a k'a yif muka kai dubanmu jikin tagar dan muna tunanin jan da mukai ta bud'e.


Nida yazeeda muka kalli juna muka tafa nace "ashema k'ofar me sufurun ce kingama ta bud'e kanta"
Yazeeda tace"wallahi kuwa May be da zamu fad'o ne muka danna wajen budewar" Marwa ce da tagama rudewa ta hau duba jikin windown taga dai babu wani madanni ajiki tace.


Akwai matsalafa 'yan uwa wannan k'ofar babu wani madanni ajikinshi kila dai wani fatalwar ne ya bud'e" hararan ta nayi nace "dalla can matsoraciyar banza fatalwar lafiya ana zaune k'alau" nayi maganar ne hankalina akan k'afana danaji yana d'an min zafi kad'an a inda na buge.


Ita kuwa Marwa idanunta k'ur akan k'ofar da ya bud'e kanshi tabbas tasan dole wani abin zai faru ilai kuwa tana kuma kai kanta santar k'ofar sai ganin hannu tayi dogo yana fitowa ta tagar gashi duk ya huda likafanin jiki "innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA shine abinda Marwa ta fad'a da azabar k'arfi kafin ta d'iba da mugun gudu.


Ni kuma na d'ago naga ihun da Marwa take min kawai idanuna suka sauka akan abinda na tabbatar da cewa shi ya tsorata Marwa gawace tsaye agaban mu nida yazeeda idan ba gizo idanuna keminba kamar murmushi take mana tana mik'o mana hannunta da gashi ya huda likafanin "yazeeda fatalwar ce ashe" na fad'a a haukace tareda daka wani mugun tsalle na fita da azababben gudu tuni na manta da batun zafin da k'afana kemin ai atake yazeeda ma ta rufamin baya.


MAMAN ISLAM CE




NAMIJI K'UDAN ZUMA


By


MAMAN ISLAM


☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️


Page 22


Duk da cewa Marwace ta fara tserewa amma fit nazo na wuceta kamar aljana idan ba idonane yakemin gizo ba sai nake ganin kamar dani kad'ai fatalwar ta jeru tana sakin wani mugun huci hakanne yasa na k'arfin guduna danaga abin bana K'are bane sai kawai na rufe idona naci gaba da gudun a half.


"SUHANA" naji muryan NAWAN ya kwalla min kira inda naji muryan ya fito na nufa da gudu ina haki kuma har lokacin bandaina jin hucin koma meye yake bina ba, jinai an rik'e ni nayi tunanin NAWAN ne sai kawai na bud'e ido wani irin razannen ihu na saki lokacin da naganni kwance a jikinta take numfashi na ya d'auke na sume a wajen.


Da gudu yazeeda da Marwa suka k'araso kusa dashi suka rirrik'eshi suna haki "mugudu Yaya Abdul fatalwace" Marwa ta fad'a cikin tashin hankali kafin ta yanke jiki itama ta fad'i a sume.


Wani irin kuka Deenah ta fashe dashi tana kallon yazeeda dake tsaye tana makyarkyata fitsarin tsoro nabin k'afafun ta sai Deenah ta k'ara rikicewa dan tayi yak'inin ba d'an k'ananun abubuwane suke saurin firgita SUHANA ba bare kuma yazeeda ta dame SUHANA ta shanye a tak'adiranci "ina kukaje?"
Deenah ta tambayi yazeeda da rawan murya tana kuka, cikin rawan murya yazeedan tace "MUTUWARE mukaje shine fatalwa ya biyomu" "fatalwar me kuma?" Deenah da Abdul Samad suka had'a baki wajen tambaya" wallahi anty Deenah a gabanmu ya tsaya nida SUHANA ita Marwa ta rigamu guduwa" ran Abdul Samad yai masifar b'aci yace "inba masifa ba uban me ya kaiku mutuware ai gashinan zakuje ku kashe kanku abanza da hofi" daga haka ya d'auki SUHANA yace yazeeda ta taimakawa Deenah su kamo Marwa.


Daddy da Alhaji suna waje sunacin abincin dare wanda suka makara wajen ci saboda fitan da suka d'an yi, suka hango Abdul Samad d'auke da SUHANA yayin da yazeeda da Deenah suka d'auko Marwa "lafiya Alhaji ya tambaya a kid'ime ganin an rik'o shalelensa kamar gawa "MUTUWARE sukaje wai fatalwa ya biyosu"
"Mutuware?" Alhaji da Daddy suka had'a baki wajen fad'a suna bin Abdul Samad dayai ciki da SUHANA yama kasa magana tsabar b'acin rai.


Haka Hajiya ma ta rud'e jin abinda akace ya faru ta rik'a salati tana sallalami tace "banda fitina irin nasu mai zai kaisu ma'adanar gawa matattarar aljanu da daren nan ai dole a firgita su.


Da k'yar aka samu Marwa ta farfad'o dan ta kanta aka fara saboda ta wuce gida gudun kada a nemeta duk da cewa sunsan zai wuya matar babanta ta neme ta muddun ba ubanne ya dawoba.


Ni kuwa da gayya Yaya Ali ya watsa min ruwan roba dake hannunsa mai uban sanyi na kwalla wani razannen ihu nace "NAWAN fatalwa fatalwa zata kasheni wayyo Hajiya da Alhajina ku taimakamin shike nan na kai kaina makabarta"


Fashewa Hajiya tayi da kuka tana fad'in"innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA shikenan tayi gamo wallahi mai ya kaiki mutuware idan ba masifa ba na shiga ukuna ni Hansatu"
"Wallahi Hajiya duk ku kuka lalata yarinyar nan ke da Alhaji badama tayi laifi ayi mata fad'a sai ku d'aure mata gindi" fad'a sosai Ali ya kamayi babu wanda ya tanka masa ganin irin zaburar danakeyi duk suka rufu akaina suna yimin addu'a intakaice muku dai a wannan dare saida Hajiya ta had'a da karb'o min taimako kafin na samu bacci ya d'auke Ni.


NAWAN kuwa ranan a gidan ya kwana d'akin Abdul Maleek sabida yasan ko yaje gida bazai iya runtsawa ba ina cikin wannan halin


Washegari ragal na tashi karad'ina nema ya tashi sauran yayyena Yaya Ali yana fitowa kuwa ya zubamin wani mugun rankwashi yace " shegiyar yarinya fitinanniya sai na karya wannan k'afar yawon" ihun dana zunduma ne yasa Alhaji aanya gudu dama ya fara sakowa daga samansa zaije masallaci "mamana kedawa haka nakejin ihunki?"
"Ba Yaya Ali bane ya rankwasheni" na fad'a ina Sosa wajen dan da zafi wallahi Alhaji yace "haba Ali haba Ali dan Allah yanzu bazaka tausayawa yarinyar nan halin data shiga jiyaba shine zakazo kana cin zalinta banason mugunta Wallahi" ganin Alhaji zai fara sababin nasa na fama akan antaba yar gwal Ali yayi saurin ficewa batare da ya tankaba.


Gari na gama wayewa saiga Marwa ta shigo dake yau lahadi ce babu makaranta sai muka samu waje muka zauna muna maida abinda ya faru jiya nace"wai jiya ninaga bala'in dayafi k'arfina ashe dai Nana da gaske take akwai fatalwa ni wallahi na d'auka sai a shirin film ake ganinta" Deedah ta shek'e da dariya tace "maganin marasa jin magana kenan" na galla mata harara nace "to ina ruwanki damu?" Marwa tace"uhmm ni kam na daina binki muddun asbitine dan nasan halinki duk da wannan abun kina iya cewa baki gani sosai ba sai kin koma"


Hararan ta nayi nace "banza matsoraciyar banza ke wallahi kin shiga uku da tsoro"
"Eh shiyasa naga saidana sha rubutu na farfad'o daga suman danayi"


"Wallahi kika kawomin iskanci yanzu zanci ubanki ai gwandani nayi jarumta keda tun kafin fatalwam ya diro gabanmu kin kwasa da gudu banza matsoraciyar banza" nanfa muka fara raba halin dama wani lokacin idan Marwa tagaji da halina na masifa biyamin take muyi tayi muna cikin haka babban Yaya ya iso da d'an sa a fad'a da gudu na nufi wajensa na d'auki yaron nayi hanyar waje


MAMAN ISLAM CE




NAMIJI K'UDAN ZUMA


By


MAMAN ISLAM


☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️


Page 23


A k'ofar gida muka had'u da yazeeda muka kalli juna muka tuntsire da dariya yazeeda tana dariyan tace "shegiya SUHANA dama akwai abinda zai firgitaki irin haka?"


Nima dariyan nayi nace "kedai bari yazeeda ai ban tab'a ganin bala'i irin najiyaba tsabar masifa duk ta wuce ku ta jeru dani saboda ni kad'ai ta gani, Allah nefa ya taimaka ban had'iye zuciya jiyan nan ba"na fad'a ina cigaba da dariya


Nan muka shantake da yazeeda a k'ofar gida tunda yau mun tab'a halin da Marwa nasan bak'in ran ya motsa ko na mata magana bazata kulani ba.


Muna haka NAWAN ya fito a gidansu muna had'a ido ya galla min harara zai shiga gida nayi saurin tare k'ofar nima ina hararan sa dan bazan bari yaci bulus ba na lura tun jiya yakemin wani kallon raini.


"Me na maka malam dazaka wani sani a gaba da kallon banza ko mutum na kashe maka ai sai haka" na fad'a ina murgud'a baki shi kam bina kawai yake da kallo yana mamakin yadda bandamu da zaman lafiyata ba Allah wallahi jiya saura kad'an zuciyarsa ya buga saboda halin data shiga amma ji yanzu tazo tana masa rashin kunya.


Hannu yasa ya janye ni a hanya batareda yace min k'ala ba dan yadda yakejin sannan zai iya mammakeni kuma yajawa kansa wata fitinar daban.


Ni kuwa yadda yayimin ba d'an k'aramin haushin hakan nayiba a take anan nasha alwashin babu ni babu shi tunda bashi da mutunci matsalar yarinta kenan abu kad'an ne yake zama laifi a wajen yaro.


Mun jima da yazeeda saidai yanzun munbar hiran muna zaune ne kawai tunda NAWAN ya b'ata min rai ban k'ara maganar da mukeyi ba itama yazeeda sai taja bakinta ta tsuke dan tasan idan ta takuramin yanzun zamu damben bala'i.


Can na sunkuci Affan nace wa yazeeda mu had'u anjima idan antaso a islamiyya, ta amsa da to tabar k'ofar gidanmu nima na shige ciki.


Falon Hajiya na samesu duka suna hira abin ya bani mamaki ya Abubakar ya Umar Usman ya Ali ya

6 / 7