Author : Hassana Abdulaziz Yakasai Category : A Books
da kwanciya a k'asan kafet d'in falon ina birgima, da wani irin mugun mamaki yake kallona kafin ya kamo tattausan hannuna ya jawoni gefensa ya kwantar da kaina gefen kafad'arshi yana fad'in
"Haba TAWAN dan Allah dama har yanzu baki daina wannan shirmen ba shekaran ki sha d'aya fa kina aji shida a primary gaki hazuk'a haddar izu talatin gareki shine kike irin wannan kamar wata karamar yarinya?"
Harara na galla masa na mik'e zan bar wajen yayi saurin rik'o hannuna yace 'ina zaki zo muci abincin Mana?"
Baki na tura nace "na fasa ci kuma idan alhaji ya dawo saina fad'a masa nace ba'a bani abinci a gidan nan"
Hajiya ta fusata dajin abinda nace tace "dan ubanki idan ya dawo karki fasa fad'a masa shi kuma idan kin fad'a masa kar ya barni da rai?"
Hajiya ta rik'a fad'a sosai yayin da Abdul Samad yayi ta bata hak'uri yace ta rik'a hak'uri dani kuruciya ce, ita kuma tace babu wani kuruciya iskanci ne"
Bayan Hajiya ta gama sababin ta tabar wajen sai ya kama rarrashina nayi bala'in had'e rai, babu yadda baiyi dani naci abincin ba nace na k'oshi dan dole ya hak'ura yaci abincin sa shi kad'ai.
Abdul Samad shima d'aya ne daga cikin yaran dake shiga gidanmu aboki ne ga ya Usman d'an Hajiya na hud'u hakanan d'ane ga mak'ocin mu malam Ibrahim wanda ya kasance malamin makaranta, a jama'ar BUK ta shi kad'ai ne dan daya rage musu a rayuwa amma kafinshi alh. Ibrahim yana da yara hud'u wanda Allah yayiwa rasuwa sakamakon gobara tare da mahaifiyar su shine ya auro mahaifiyar Abdul Samad Haj Aina'u mace mai tsananin kirki da hak'urin gaske dan zan iya cewama tafi Hajiyata hak'urin sannan aminai ne su na k'ud da k'ud baka tab'a jin kansu.
Ana gaisuwar mutunci da girmamawa tsakanin alhaji Aminu da alh. Ibrahim amma sanadin abotar Yaya Usman da Abdul Samad alak'ar su ta soma k'arfi har sukayi wata irin shak'uwa har ya kasance idan d'aya zai aiwatar da wani abu sai ya nemi shawarar d'an uwansa.
Abotar Yaya Usman da Abdul Samad ya samo asaline tun daga nussery har zuwa yanzun sunyi wata irin shak'uwa mai ban mamaki.
Tun sanda aka haifoni Allah ya d'igawa Abdul Samad wani irin k'auna ta duk da kasancewar suna makarantar kwana nane shida Yaya Usman amma duk sanda akayi hutu yana mak'ale dani saboda ni Abdul Samad ya dawo gidanmu da zama duk da k'ulafucinsa da iyayensa sukeyi kasancewar sa shi shi kad'ai hardai suka hak'ura.
Haka nataso da d'an banzan kiwa babu wanda nake yarda dashi sai NAWAN shine asalin sunan da ya koyar dani na rik'a kiransa shi kuma yace dani TAWAN kama har yau danake da shekara goma sha d'aya a duniya bamu daina kiran juna da hakaba wanda har yan gidanmu sun saba da hakan.
MAMAN ISLAM CE
NAMIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 16
D'aki na koma abincin ma na fasa ci babu irin rarrashin da NAWAN baimin ba ya hak'ura k'arshe shima fasa cin abincin yayi duk da cewa Hajiya tasan za'ayi hakan shima sai ta rufeshi da fad'a ta inda ta shiga batanan take fitaba "eh tunda na tab'a JININ JIKINKA ai dole kace bakacin abincin tunda tayi masa yaji itama to dan Allah daganan har a busa k'aho kar ka k'ara ci" da dai yaga abin bana K'are bane shima ya lallab'a ya gudu dan Hajiya badai lafiyar mitaba.
Ina fita gidan mommy na nufa, ina nufin Babar su NAWAN tana ganina ta hau fad'in "a a kaga sark' mai rikicin gangan daga ina haka naga kina ta wani cin maganin?"
Kawai sai na fashe mata da kukan tab'ara nace "ba Hajiya bace take tamin masifa kuma ta hanani abinci" hannuna ta kamo tace "zonan yar lelena kinga yau danbun naman kaza nayiwa su Usman, muje ciki sauranki zasuci" aifa inajin abinda tace na k'wace hannuna ina bubbuga k'afa nace "wallahi mommy babu ruwana daku daga ke har Hajiyan fisabilillahi ace su yaya zasu dawo shine kuka barni natafi makaranta?"
Dariya mommy tayi tasan rikici na yanzun sai na d'aga mata hankali dan haka ta rik'a lallab'a ni tana rarrashi tajani har falonta yadda ta gyara falon yana ta k'amshi yaja hankalina sai na samu waje na zauna ta kawo min k'atuwar samiran da ta zuba dambun naman a ciki taf ta cika kuma nasan an kaiwa Hajiya kuma nasan k'ulli na daban, murmushi nayi nace "mommy yau me kika dafa?"
Kaina ta shafa tana murmushi tace "ai mutuniyarki na dafa shinkafa da miya da salad da kayan had'i" cikin jin dad'i nace "yauwa mommyna zubo min amma ni da manja da yaji nake so" mommy ta d'an had'e rai tace"waike SUHANA dan Allah mai yasa duk kinfi kauri wajen kwad'ayi ne?"
Sanin halin Mommy yasa na rik'e ciki nace "wayyo Allah cikina ya k'ulle yunwa zata kasheni" ai kafin nakai k'arshe mommy ta tafi kawomin abincin, ni kuma na ciro leda daga jakar makaranta na dake goye a bayana na d'ebi danbun naman da yawa na maida jakata, ta kawo min abincin had'e da mai da kayan had'i, nace ta maida yajinta ina dashi a jakana tace"hakafa tsabar d'aurewa k'arya gindi harda guzurin yaji" ta bar wajen tana mita.
Nidai ban tanka ba na zuba abincin dan gaske yunwar nake ji shiyasa ina gama zubawa NAWAN ya shigo "a a kice nan kika gudo kika barni da fad'an Hajiya" yana zama a kusa dani tare da jan flat d'in dana zuba abincin yasa hannu yana juya abincin yana fad'in "dole ki gudo wajen mommy tunda tana miki yadda kike so" harara na galla masa zan bar wajen yayi saurin rik'o hannuna yace "haba TAWAN karkiyi min haka mana idan kika horamin kanki da yunwa bazan tab'a yafewa kainaba"
"Ni daga yau bataka bace tunda har zaka iya gama makaranta ka dawo baka sanar min ba" marairace fuska yayi gabansa na fad'uwa yana matuk'ar tsoron fushin SUHANA dan bata da dad'i.
Shiru yayi yana kallonta jafin yayi wani kalar tausayi ya mai da kansa yana kallon kafet d'in idanunsa suka d'an surka kad'an da sauri na k'araso kusa dashi na zauna ina kallon shi a rayuwata bana k'aunar ganin canjin yanayi a tattare da NAWAN hakan ne ma yasa na dawo na d'an lek'a fuskar sa har ta fara ja abunka da farin mutum ihu na fashe dashi tare da yunk'urawa zanbar wajen, a matuk'ar rud'e ya rik'o hannuna yana kallona yace "tunda kin fison d'aga min hankali shikenan kije kiyi abinda kikeso"
"To ba kaine ka dawo baka fad'a minba ka barni na tafi makaranta" yasan za'ayi haka mitace zai shata danhaka yace "bari kawai na koma sai a maidani baya idan yaso randa zamu sabunta jarrabawa sai in sanar miki" ya k'arasa fad'a yana k'ok'arin tashi "ni bance ka koma ba idan ba hakaba yasin na daina kulaka" murmushi yayi tare da lakuce min hanci yace "ina matuk'ar k'aunar ki TAWAN" nima murmushi nayi nace "ai dai nafi sonka kuma nafika dauriya kai da wata rana da bani da lafiya ina kallonka kana matsar hawaye" na fad'a ina kwatanta yadda yakeyi a lokacin.
Murmushi yayi tare da dungure min kai yace "wai yarinyar nan dan Allah me yasa baki mantuwa?"
Dariya nayi nace "ai yasin bazan mantaba Kato dakai kanamin kuka ni haushi ma ka bani a lokacin"
"Dan bakisan tsantsar k'aunar danake miki bane shi yasa kikemin d'an biki.
Haka mukayi ta hira yana bani abincin a baki shima yanaci har muka kammala, dan koda mommy tazo taganmu tab'e baki tayi tabar wajen domin tasan halina yanzun zata ganmu muna abin arzik'i yanzun kuma zataga mun hau sama mun dawo.
Mik'ewa yayi nace "ina kuma zaka"?
"D'akina zanje na gyara mommy batasan da zuwana ba bare tasa a gyaramin"
"To bari nazo na tayaka" hummmm"kidai tayani hira banda haka me kika iya" harara na galla masa na juya a fusace zan fita yayi saurin rik'o hannuna yace "haba TAWAN meye na d'aukar zafi ke da wata ranama duka wata d'awainiya ta ma ke zaki d'auka" fusge hannuna nayi zan fita yayi saurin rungumoni jikinsa take kuma yayi saurin sakina yana d'ago kaina muryan shi na d'an rawa rawa yace"kinaso nayi miki kuka?"
Duk da hakan da yayi min ba wai sabon abu bane a wajena amma cikin yan kwanakin nan hajiya na yawan fad'a min indai ina barin na miji yana tab'a ni zan iya d'aukar ciki kuma har ga Allah na amince da wannan batun hakanne yasa naji gabana yayi wata masifar fad'uwa" na juya da gudu na fita tare da fashewa da wani fitinannen kuka.
Mommy na tsakar gida taga wucewa ta, ta hau kwalamin kira sam ban saurareta ba ta yunk'ura da nufin zuwa tambayar abinda ya had'o mu dan nata tab'a ganin wannan fusatar a tare daniba sai taga shima ya fito a mugun kid'ime zai fita tace "kai Abdul lafiya?" dake haka take kiransa dashi"ina zuwa mommy kingafa fushi tayi take kuka dan kawai na rungumeta har dacemin d'an iska" jin abinda yace sai mommy taji dad'i a ranta kenan SUHANA tana d'aukar hud'ubar su tunda gashi har ta nunawa Abdul b'acin ranta akan abinda yayi Mata.
Shikam bai saurari me mommy zatace ba ya fita da sauri.
A falo na sami Hajiya harda anty Deenah ma ta dawo a makaranta wucesu nayi ina kuka tare da fad'in wallahi idan nayi ciki bazan yardaba Allah kuwa sai nayi shari'a dakai.
Jin abinda nake fad'a Hajiya da Deenah suka kalli juna sannan suka kalleni Hajiya tace"me yafaru dake kkje wannan maganar banzan" fashewa na sakeyi da kuka nace ba NAWAN bane kawai ya rungumeni dan nayi fushi zan bar gidan tsabar iskanci kuma kince duk wanda ya tab'ani zanyi ciki"
Kafin Hajiya tace wani abu sai gashi ai da gudu na afka d'akin mu da anty Deenah na b'amo k'ofar bugun duniya da magiya nayi masa banza Ina cigaba da kukana cikin tashin hankali
MAMAN ISLAM
NAMIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 17
Cigaba yayi da bugun k'ofar cikin wata rarraunar muryan da saida naji jikina yayi sanyi to amma kuma abin kunyar da zai jaminfa ni yanzun idan aka ganni da ciki me zance da mutane dama gashi Hajiya tace duk sanda yaro zai aikata wani abu ko babu wanda ya ganshi tofa su iyaye suna gani an rubuta a goshinsa, wayyo Allah wallahi daga yau kai ba NAWAN bane na tsaneka tunda kakeso ka lalata min suna nima k'awayena su tsaneni haka na rik'a wani irin kuka mai cin rai.
A kad'an Abdul Samad yakai mintuna hamsin a bakin k'ofar yana bugu kafin Hajiya tazo da k'yar tajashi sukabar wajen tace "kai kuwa me ya had'o ka da mutuniyar taka take wannan uban kukan, kai kuma gaka hankali a tashe saikace wanda akace yau alki'yamarsa zata tsaya?"
Tayi masa tambayar duk da cewa ta d'an hasaso wani abin a zantukan da SUHANA takeyi hakan kuma ba k'aramin farin ciki ya sanyata ba kenan tsoratarwar da takewa SUHANA yana shiga kunnen ta kuma tana aiki dashi.
"Idan tayi fushi dani ai alk'iyamar tawace ta tsaya Hajiya dan Allah ki lallab'a min ita wai daga na rungumeta shine take ta wannan tashin hankalin"
Murmushi Hajiya tayi tace"kai da TAKAN wa ya isa shiga tsakanin ku ai kai da ka b'ata kaine zakaje ka gyara abinka da kanka indai SUHANA ce duk wanda ya shiga lamarinku shine zaiji kunya"
"Dan Allah Hajiya kada kice haka b'acin ran SUHANA rashin kwanciyar hankalana ne domin ita d'in duniya tace" da mamakin furucin sa take dubansa tabbas Abdul ya zauce akan SUHANA duk kunya irin tashi yake iya fad'a mata haka, wani irin sassanyar murmushi tayi tare da fatan tabbatuwar hasashen ta akan Abdul Samad da SUHANA.
Azahiri kuwa had'e rai tayi tace "lallai Abdul wato SUHANA duniyar kace kuma kake fad'a min saboda baka da kunya"
Shifa sam yama manta da wata aba wai kunya fatansa kawai kada SUHANA ta d'auki wannan muguwar gabar tata dashi dan hakan yana nufin tashin hankali ga rayuwar sa "Hajiya"""""""jeka Abdul zan mata magana Hajiya ta katseshi dan ya k'yaleta ta lura bayan karatun bussiness da yayi harda naci ya koyo abinda ba halinsa ba ko kuma tace ya koya a wajen Usman dan shi kamar marok'i yake wajen iya naci.
Sala lau sala lau haka ya mik'e ya fice Deenah ta bishi da wani irin kallo zuciyar ta na wani irin azababben bugu (off kumin afuwa nayi mantuwa wajen ce muku Abdul Samad da Usman candy sukayi a a NCE zance so kumin afuwa d'an Adam ajizine)
Fatanta kada Allah ya tabbatar da abinda take zargi tsakanin ya Abdul da SUHANA idan kuwa har hakan ya tabbata to kuwa tana da yak'inin cewa rayuwar ta tana cikin garari.(to Deenah me kike nufi da hakan? To bari dai mugani)
Yarda yabar mommy haka ya tadda ta zaune tana kallon labaran yamman a tashar NTA yanayin da ya shigo ya bata dariya da tausayi amma sai ta d'auke kai tana kallo ya zauna ya dafe kansa, sai kawai ta tashi tabar masa wajen
Tun ranan da mukayi haka da NAWAN ban k'ara yarda mun had'u dashi ba haka kuma hakanan naji na tsane shi domin a ganina ai yana sane ya rungumeni dan kawai ya cuce ni.
Haka har muka shafe kusan sati guda bai fasa zuwa ya bugamin k'ofa ba haka ban daina gudunsa ba bil hak'k'i da iya gaskiyata, idan zan tafi makaranta nakan yi wuf na riga anty Deenah fita sai dai ta taddani acen hakama idan mundawo ta baya nake biyowa.
Yau dai ban rufe kaina kamar yadda na sababa muna ta shawagin mu nida Marwa kunsan dai fad'an yara yanzun ne za'ayi yanzu kuma an shirya hakan take nida Marwa saidai kuma tana mugun tsorona saboda nafi k'arfin ta mugun duka nake mata.
Mun gama gararanbar mu a unguwar saboda wasu mutane da suke tarewa yau a kusa da gianamu hardamu ake shige da ficen saboda naga suna da yaran dabasu fimuba nida Marwa sai murna nake mun samu k'arin k'awaye
MAMAN ISLAM CE
NAMIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 18
K'ishin ruwane ya kamani nayi saurin shigewa gida dama gidan jikin gidanmu yake.
Turus nayi ganinshi zaune kusa da anty Deenah tanayi masa magana k'asa k'asa duk da bansan me take ce masaba saida naji wani irin ba dad'i araina, nayi bala'in d'aure fuska ina k'arasa shiga gabana yana fad'uwa.
Daf da zan giftasu ya d'ago muka had'a ido ya wani irin kafeni da ido nima kallonsa nake ido cikin ido araina nike ayyana ko rashin lafiya yayine yayi wannan masifar ramar?
Ganin da gaske wucesu zanyi yayi saurin tashi yasha gabana yana kallona sai naji wani irin abu yana tsargamin saboda yadda ya wani tsareni da kaifafan idanunsa sai nayi k'asa da kaina zan wuce yayi saurin rik'o hannuna "haba TAWAN dan Allah ya kikeso nayi da raina yayi maganar da rawar murya ga mamakina kuma har kamar kwalla na gani ta cika masa idanu zo kiji dan Allah" ya fad'a yana jana batareda yajira cewata ba nan Deenah tabimu da wani fitinannen kallo zuciyar ta na tsananta bugu.
A soro muka tsaya ya kafeni da idanu yana bina da wani irin kallo idanunsa har sun canja launi"wai TAWAN me nayi mikine da zafi kike azabtar dani da fushin ki?"
Harara na galla masa nace"daga yau ni ba taka bace na tsaneka tunda na gane jikina kakeso" idanu ya k'walalo gaba d'aya ya kafeni dasu nace "li'ilafi k'urraishi wallahi kurwata tafi k'arfin ka, daka wani tsareni da mayun idanunka babu abinda zaisameni" da ace ba a cikin wannan k'adamin suke ba babu abinda zai hana ya kwashe da dariya yadda tayi maganar tana wani marmar idanunta to amma sanin halin SUHANA ba'a biyo mata ta sauk'i yasa yace" nayi laifi amma ni kisani ni bada wata manufa na rungumeki ba amma zan kiyaye kiyi hak'uri ki daina wannan fushin dani zuciyata bazata d'auka ba" ya fad'a yana kai hannuna saitin zuciyar sa irin yadda naji tana bugawa da k'arfi abin ya matuk'ar bani tsoro wallahi ai tuni na manta da maganar wani fushi dan maganar gaskiya shak'uwa ta da NAWAN ya wuce tunanin duk wani mai tunani, cikind tsantsar amuwa nace"me yasameka NAWAN shine baka fad'a minba?"
Na fad'a da rawar murya idanuna suna cikowa da kwalla ai ganin har sun fara zirara sai hankalinsa yai masifar tashi har zai rungumeni sai ya tuna ya fasa yayi saurin rik'o hannuna yace "dan girman Allah ki taimakeni kada kiyimin asarar wad'annan tsadaddun hawayen naki"
Yayi maganar ne cikin tsantsar damuwa, sainaji ya bala'in bani tausayi bazan iya cigaba da fushi dashiba dalilin kenan dayasa nak'i amincewa mu had'u nasan cikin k'aramin lokacin zaisha kaina mu shirya, cikin muryan shagwab'a nace "ni k'ishin ruwane ya kawoni gidan" murmushi yayi yace?
"da kina ina?"
"Ina waje kasan yau mak'otanmu suke dawowa muna can nida Marwa muna tayasu aiki kaga babarsu kuma wallahi mai kirki ba'azo da yaran ba amma matar tace tana da yara kamar ni" murmushi yayi yaja hannuna zuwa cikin gidan har falon Hajiya sanda muka shiga anty Deenah tabar wajen hakan yamin dad'i dan haka nan naji kishin yar uwar tawa.
Roban ruwan ya Ali ya d'auko nayi saurin rik'o hannunsa nace "kai rufamin asiri namu ya K'are kaga akwai pirewater a bani murmushi yayi shida kanshi yana shakkar Yaya Ali dan bashi da fara'a
NAMIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 19
A kad'an na kwashe kusan awa guda a bayan gida wannan ka'ida tane matuk'ar cikin yayyena akwai mai uzuri kuma yaga zan shigar masa bayan gida take suke korana suce karma na soma.
Yanzuma hakan ne yafaru saida na kwashi cikakken minti talatin saman Masai kuma ma banyi kashin ba kawai tsigunon ne na jaraba da aka saba.
Bayan na fito a wankan ma sai da na gama wasa da tsalle tsallena a gaban merrow d'akin Hajiya kafin na kimtsa na fito falon, bawan Allah yana nan yana jirana haka muka wuce muka tafi, a kuwa nasha lce cream kamar ba gobe sannan na dage saida mukaje wajen wasanni nanma mun jima kafin muka biya wata super market ya siyomin su alawoyi da buscuet kala kala masu mugun dad'i da tsada.
Sanda muka dawo gida ana kiran magriba hakan yasa babu kowa a tsakar gidan sai anty Deenah tana alwala da sauri ya fita shima bayan ya ajiyemin ledar da muka