Namiji Kudan Zuma Book by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt

Author :  Hassana Abdulaziz Yakasai Category :  A Books

Chapter   4 / 7

9K to 12K   out of 19.4K words

kiyi kuka kuma nima saida na masa wannan tambayar yace min ba fad'an ne me muhimmanci ba ayi mata maganin ta warke shine mai muhimmanci kuma yace duk sanda muka shirya aje da ita"


"Yanzu zamuje Abdul Maleek"
"To bari na fad'a masa" ya fad'a yana zaro wayarsa daga aljihu.


Inda tabarta nan ta sameta har tagama shan tea ta d'an ka shingid'a idanunta a lumshe"ki shirya SUHANA zamu fita" idanun ta bud'e akan Hajiya ta d'an kalleta kamar tace babu inda zata sai kuma ta fasa ta maida idanun ta rufe kamar bazata tanka ba dan har Hajiyan ta sare sai kuma tace "ina kuma zama yanzu da dare haka?"
Idan munje kya gani" Hajiyan ta bata amsa tana shigewa d'akinta


"Allah yasa dai ba cutar dani za'a je ayi ba" ta fad'a da d'an d'aga murya yadda Hajiyan zataji, sai da Hajiyan ta d'an yi jim kafin ta saki murmushi mai ciwo ta shige ciki "kiyi hak'uri Hajiya insha Allah komai zai wuce Abdul Maleek ya fad'a yana duban Hajiyan da yanayin ta ya sauya.


Batayi tunanin zata shirya ba Amman sai suka taddota tsab sanye da lafaya purple ta yane jikinta tsab haka suka wuce Abdul Maleek yana ta janta da hira tak'i tanka masa saboda haushin abokinsa kuma mijin yayarta da take ji.


Lokacin da sukaje k'ofar gidan malam Tijjanin hakanan SUHANA taji gabanta yayi mummanan fad'uwa tayi masifar had'e rai tana dubansu "inane nan kuka kawoni Hajiya"


"Mu shiga mana SUHANA"Hajiya ta fad'a tana kamo hannun ta"wallahi bazan shigaba ji muguwar mata ni zaki munafurta ki kawo nan?"


Da matuk'ar mamakin gaske Hajiya ke duban SUHANA "nice munafukar SUHANA?"
"Inba munafurci ba meye had'ina da gidan nan da zaki wani kawoni to wallahi banga wanda ya isa ya shigar daniba""""” saini ba" kamilar muryan malam Tijjanin ya daki kunnuwan su, shammtarsu SUHANA tayi zata d'iba da gudu Abdul Maleek yayi saurin fisgota ashe yana ankare da ita.


Ta bayanta malam ya zagayo yace"muje"bata iya kallon idanun malam ba tace "dan Allah malam kayimin sassauci nine na kwanaki wanda"""''''ban buk'aci magana anan ba"
"Dan""""""kai bana son zancen banza wuce muje" malam ya buga mata tsawa sum sum ta wuce tana hawaye.


Tofa me yake shirin faruwa ne muje zuwa dai


MAMAN ISLAM CE




NA MIJI K'UDAN ZUMA


By


MAMAN ISLAM


☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️


Page 12


Sum sum ta wuce tana hawaye suna zuwa bakin k'ofar ma saida ta tsaya ta kuma cewa "dan soyayyar dakakewa Annabi MUHAMMAD sallallahu alaihi wasalam malam ka tausaya min"


"Ita an tausaya matane? malam ya fad'a a zafafe kunbar yar mutane tana walagigi a unguwa cikakken maida hankali waje guda batayi kullum ita kenan a gantale ga zargi da akasa tsakanin ta da kowa?"


"Wallahi zan barta malam har abada"
"To mu shiga muje"malam ya fad'a tareda nuna mata hanya da hannunsa.


K'arshe dai ta k'arfin bala'i Abdul Maleek ya tura SUHANA wannan d'akin, suna shiga kuma kai tsaye ta nufi gaban buzun ta zauna ta tankwashe k'afa sai kawai ta kama kuka tun k'arfin ta.


"Ku shiga muje dole idan abin yak'i sai an rik'eta saboda ga dukkan alamu wannan abin na kanta yana da k'arfin gaske"


Jikin Hajiya a mugun sanyaye tabi bayan malam Tijjani da Abdul Maleek wanda sukayi gaba.


Lallai kam Hajiya tasha kallon gwagwarmayar tsakanin malam da wannan iska da ya tabbatar da cewa turoshi akayi jikinta kuma saida akayi aikin gaske wajen rabata da ainihin na jikinta wanda suka kasance kariya ga SUHANA wanda a hannunsu aka haifeta duk kuwa da kasancewar wajen da aka haifeta ba wajene na aljanun kirkiba wajene na shed'anun aljanu wato toilet to amma kasancewar da addu'a Hajiya ta shiga sai suka kauce na kwarai suka amshi haihuwar SUHANA wanda suna suke d'an tab'ata take zuba fitina da rashin ji tun tana 'yar ficiciyar ta.


Babu yarda malam baiyiba akan su fad'i wacce ta turosu da farko yak'i fad'a amma da yaga ruwan azaba yace zai fad'a amma sai Hajiya da Abdul Maleek sun bar wajen dan akwai Amana tsakanin su da uwar gijiyar tasu domin tana musu yadda suke so sai maganar k'in amsar abin hannun Hajiya shima sune suke sata dan gudun kada ta bata abinda zai rabasu da ita.


Saida aka kai ruwa rana kafin yace zai bar jikinta saboda malam Tijjanin ya gane me mugun taurin kaine dan haka malam ya rik'e wuta wajen yi masa yadda bazai tab'a shi'awar dawowa inda take ba, ya kuwa yi alk'awarin zai barta amma yasan da cewa uwar gijiyar su zata kuma d'aukar wani matakin akan hakan dan ba k'aramin k'ullawa RAYUWAR SUHANA tayi, malam yace "wannan kuma ba damuwar ka bane kaidai shaida ne akan abinda zan iya dan haka idan akwai wanda yafika taurin kaima yazo zan iya dashi" bayan d'aukar alk'awarin bazai kuma tukaro SUHANA ba idan kuma ba hakaba ya amince malam yayi masa mafi munin hukunci sannan ta saki atishawa tareda kifewa a wajen.


Magunguna malam Tijjani ya had'awa Hajiya wanda zata rik'a yiwa SUHANA amfani dashi sannan ya tabbatar mata zataga SUHANA ta daina wannan d'an banzan yawon mara dalili sannan kuma zata daina gayawa Hajiya magana dama bayin kanta bane, amma fa rashin jinta wannan a jininta yake.


Bayan kwana biyu kuwa Hajiya taga matuk'ar sauyi tattare da SUHANA hakanan kuma ta daina wasu abubuwan sannan sai Hajiyan tagama kamar tafi da nutsuwa sai dai tana bata mamakin wani irin mugun miskilanci wanda kwata kwata bata san SUHANA dashi ba amma dai tana cigaba dayi mata addu'a dan Allah ma yasani kaf 'ya'yan babu ya SUHANA tanayi mata wani irin fitinannen so wanda duk abinda zatayi bata ganin laifinta sai dai takanyi k'ok'arin danne hakan har ta daure tayi mata fad'a idan rigima ta had'o ta da 'yan uwanta
Wannan kenan


Asalin labarin


MAMAN ISLAM CE






NA MIJI K'UDAN ZUMA


By


MAMAN ISLAM


☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️


Page 13


Malam Garba wanda akafi sani da malam garbu shine kakan SUHANA mahaifi kenan ga alhaji Aminu mahaifin SUHANA asalinsu mutanen katsina ne a wani k'auye washi gurbin b'aure dukanin wasu dangi na malam garba sun rarrabu wasu suna zaune anan gurbin wasu suna cikin jibya yayin da wasu ke cikin katsina wasu kuwa sun tsallaka jamhuriyar Niger.


Malam garba shi kad'aine a wajen mahaifinsa wanda akafi sani da Abdul Basi shi kuma Abdul Basi su goma sha d'aya ne a wajen mahaifinsu wato malam Muhammadu wanda asalinsu su mutanen yaman ne ta jihar Niger saidai suma basu gama girma da mahaifin nasuba duk cikin suma babu wanda yakai malam Abdul Basi sanin sa domin shine d'ansa na farko bayan shi sai mai bi masa Hajiya Rahane da Hajiya Gwaggo da Hajiya Fatima da Hajiya Inna sai da Hajiya Hadiza sai Hasan da Usain da Gambonsu dukansu maza sai kuma autar su Hafsu sai mata guda biyu da suka mutu tun suna yara.


Duk da kasancewar malam Abdul Basi baiyi wani tsohon rai ba amma ya gina zuri'ar tasu abisa doron zumuncin wanda har yanzu da baya Raye zumuncin yananan yana gudana kamar yadda yake fata tun da rayuwar sa.


Malam Abdul Basi ya rasune tun ba'a san da cikin malam Aminu ba wanda sai daga baya aka lura da hakan wanda ba k'aramin murna yan uwan sa sukayi ba dan da farko sunyi tunanin ya tafine batare da ya bar musu wani irin da zasu rik'a gani suna tunawa dashi ba.


Bayan a haifi malam Aminu da shekara guda itama maihafiyarsa ta rasu sakamakon hatsarin mota wanda a lokacin tabar malam Aminu ne a wajen mahaifiyar ta taje gidan biki.


Kafin auren malam Abdul Basi da Inna Shatu ta tab'a aure harda d'iyar ta Hadiza wacce sanda mahaifiyar su ta rasuma tuni ta isa aure dan haka aka aurar da ita a wani k'auye dake cikin Niger wanda su asalinsu yan wani k'auye ne washi duhun bara duk a yankin Niger yake amma yafi kusa da gurbin b'aure.


Wannan dalilin ne yasa dangin malam Aminu suke da mugun yawa na ban mamaki dan sun tara zuri'a mai yawan gaske a yanzu haka maganar da nake muku mutum uku ne kacal suka rage a cikin wannan zuri'a Hafsu gambo da kuma malam Abdul wahab wanda yake zaune anan jibya yayin da Hafsu gambo su suna can gurbin da tasu zuri'ar.


Mafarin zuwan babana kano ankawo shi karatu ne wanda shine asalin zamanshi anan d'in da farko a unguwar fagge ya fara zama har ya auri mahaiyata wato Hajiya Sadiya wacce mahaifin tane ya kaisu makka dukkan yayansu maza da mata babu wanda baikai makka ya mallakawa gidaba kasancewar sa babban attajiri a wancen lokacin.


Kasancewar malam Aminu hayace ya Kama a faggen sai Hajiyan su Sadiya ta bata shawarar kawai su dawo gidanta da zama wannan shine asalin dawowar mu unguwar yakasai kuma duk anan aka haife mu banda mace d'aya wato nana Khdija.


Mu goma sha biyu Hajiya ta haifa wanda wani irin zamane tayi da alhajin mu na tsantsar kawaici da hak'uri kasancewar malam Aminu fad'aci na gasken gaske hakan ne yasa wasu daga cikin yayyena sukan shaida irin wahalar da Hajiyan mu tasha da mahaifin mu.


Saidai kuma mahaifin mu yana da wani rauni shine na tsantsar sonmu da Allah ya d'ora masa ko kallon banza babu wanda ya isa yayi mana babu kamar ni SUHANA Allah ya d'orawa alhaji tsantsar k'auna ta bayason ganin koda fushi nane bare kuma akai ga hawaye na hakan yasa sun sha samun matsala da Hajiya akaina wannan shine asalin rashin jituwana da yaya Abdul Maleek wanda ya kasance d'a na uku ga mahaifimu.


Kamar yadda na fad'a da farko mu goma sha biyu cif Hajiya Sadiya ta haifo a cikin babbar yayarmu sunan ta aisha wacce sam ni bansanta ba kuma shine sunan da aka maidamun bayan an haife ni.


Daga kanta saida Hajiya ta haifi Abubakar Umar Usman da Ali sannan Yaya Abdul Maleek sai yan biyu anty Khadija da Zainab sai Gambonsu wacce taci sunan Hajiya Hafsu hakan yasa yan gidanmu suke kiranta da gambo saboda kara wa k'anwar kakanmu sai aka haifi Ibrahim da Fatima wacce ta kasance sunan mahaifiyar Hajiya wato anty Deenah wacce kuma ana goyonta ne yayarmu wato wacce naci sunan ta Aisha ta rasu lokacin baifi saura yan kwanaki ayi bikin taba ba shekara biyu ko uku ne tsakani na da anty Deenah ba shekara d'ai d'ai ne har guda bakwai kafin a haifoni a wannan duniyar acikin band'akin gidanmu wanda Hajiya ta tabbatar min bata tab'a haihuwar sadaka irin tawaba domin jitai kawai tanajin bayan gida ta shiga toilet saidai kuma labarin ya sauya ashe ni Aishatul SUHANA nice zan duro doron duniya a cikin bayan gida.


MAMAN ISLAM CE






NA MIJI K'UDAN ZUMA


By


MAMAN ISLAM


☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️


Page 14


Hajiya tace bata tab'a fitinannen goyo irin nawa ba gani yar ficiciyar gaske sai fitinar tsiya gashi kuma duk abinda nace zanyi ko za a kasheni sai na aikata ga Hajiya da alhaji basa k'aunar a tab'a ni wannan ne yasa kaf ''yan uwana suka tsane ni banda Adda Deenah da Allah yasa mata tsananin k'auna ta kuma bata ganin laifina ko kad'an duk kuwa da cewa nafi takura mata fiye da kowa a cikin gidan baridai mubi labarin daki daki yadda zaku fahimci inda na dosa.


Alhaji Aminu d'an kasuwa ne maisai da kayan masarufi da na aune aune yana da kusan shaguna guda uku na kanshi a cikin sunga sannan yana da kamfanin da ake sarrafa masa shinkafa hakanne yasa muke rayuwa cikin sukuni babu abinda muka nema muka rasa najin dad'in rayuwa harma da irin mutanan da suke rab'armu wato irin abokan su yayyanmu su Yaya Ali suna da yawan abokai wanda yawancin rayuwar su duk a cikin gidanmu sukeyin ta domin hakane ma alhaji ya samowa Hajiya masu tayata aiki har mutun uku saboda ana dafa abincin da ya fi k'arfin ta saboda yawan jama'ar dake shige da fice a gidan sannan kuma akayi sa'a daga Hajiya har alhaji mutane ne masu hannun kyauta basu da rowa ko kad'an.


Bani da wayo sanda akayi bikin su anty zee wanda a yanzu haka suna da yara ita zee yaranta biyu yayin da anty Khadija ke da guda uku domin haihuwar ta ta farko yan biyu ta haifa hakanan tsransu kwanaki uku ne kacal wajen haihuwar farin saidai a ta biyun anty zee ta riga anty Khadija da kusan shekara biyu kasancewar kwanika tayi to masu karatu ku biyoni cikin gidanmu domin ganin irin yadda na gudanar da rayuwata tare da anty na wato Deenah.


"Hajiya dan Allah kibar abincin nan kawai ki bani d'ari biyar nasai buscuet da lemo" babu musu Hajiya ta kama hannun zanin ta kunto kafin ta mik'omin anty Deenah tayi saurin karb'ewa tana hararana tace"wallahi Hajiya ki daina bawa SUHANA kud'i yaran mutane take tarawa tayi ta rankwashi ko gabzawa mutum mari tana bashi biyar ko goma"


Baki Hajiya ta kama tace"hakane mamana?" Hajiya ta tambaya tana kallona nayi kicin kicin da rai ina hararan anty Deenah kafin na takarkare na saki uban ihun da duka hankalin yan wajen ya dawo kaina ashe dodona yana nan bak'in mugu maci zalina wato yaya Ali duk bala'i na ina masifar tsoron sa shine Hajiya ta sakawa duka ba ha'inci lallai duk ranan da Yaya Ali ya damk'eni sai nayi jinya saboda bana son duka ko kad'an.


Ina can ina masifar d'aga murya da haniya wa anty Deenah saboda ta hana Hajiya tabani kud'i sai jinai Hajiya ta finciko ni tana fad'in "kada ka sake ka tab'a ta sokake kajamin asara yan kud'ad'e batareda na shiryawa hakan ba" ni sai lokacin ma na kula da shi hakan ne yasa na masifar maiaraice fuska ina hawaye saboda takaici duk da cewa Yaya Ali yayi mugun jin haushin abinda Hajiya tayi na hanashi fallawa SUHANA mari amma saida ya ta bambayi abinda yake faruwa babu musu SUHANA ta kwashe yadda akayi ta fad'a masa wannan dalilin ne yasa yake k'aunar SUHANA saboda ko za'a kashe ta bata k'arya.


Sai da ya tallewa Deenah k'eya kafin ya ciro sababbin 'yan hamsi na d'ari biyar yabawa SUHANA yace "maza wuce ki tafi kuma wallahi kika sake na fito na sameki a waje sai na tattakaki.


Duk da cewa raina baiso fita batare da na karb'i na wajen Hajiya ba ina nufin kud'in hakanan na fice inayiwa anty Deenah hararan gefe tareda tsatsare ta da idanuna


Ina fita kuwa nayi karo da Marwa d'iyar malam sambo dama da safe tasa yayanta ya mareni akan kawai tayi kwanikan tab'o na rusa, tana gani na ta juya zata koma gida da gudu nayi saurin sa mata k'afa na maka da k'asa sannan na murje mata baki da takalmin k'afata, ta saki wani irin kuka kafin kice me b'at na b'ace kamar walk'iya dan Allah yayini da d'an karen gudu.


Haka dana isa bakin makaranta naci karo da Balaraba 'yar kusa da ajinmu ce itama tak'ark'arewa nayi na d'urma mata dundu (k'ulli) agadon baya ashe shegiyar a taci yayi mata karo sai gashi ta kama kuza uban amai da sauri na shige cikin makaranta saboda hango malam Yahya wato duka ba ha'inci dan mugune na gaske danma har makarantar alhaji yazo yace kar malam Yahya ya sake ya K'ara dukana wannan kenan.


A aji babu malamin da baisan da zaman Aisha Aminu ba akwai k'ok'ari akwai fitina wasu sukan lallab'a ni wasu kuwa sumin mugun duka wanda kuma hakan baya hanani abinda nayi niyya sannan bana fasa dukan duk d'an wanda tsautsayi yasa ya shiga hanyana hakanne yasa koda yaushe Hajiya cikin ganin 'yan kai k'ara take wuni take bada hak'uri


MAMAN ISLAM CE






NAMIJI K'UDAN ZUMA


By


MAMAN ISLAM


☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️


Page 15


Ina ta zuba ido naga malam Yahya dan nayi tunanin Balaraba zata fad'a masa abinda nayi mata sai dai har aka tashi banga alamunsa ba ranan ma ko ajin namu bai shiga ba duk da cewa zai karb'i hadda dake mu duk sanda akayi mana k'ari anayi ne yadda ko kwakwalwar dusane dakai zaka d'auka sai kuma ace kaje gida gobe kazo da hadda.


Na godewa Allah da irin baiwan da yayimin ta yadda indai aka biyamin karatu duk wahalar shi muddun za'a tusamin sau biyu ya zauna kenan akaina har abada.


Bayan mun tashi na hango Balaraba ita da wata k'awarta suna tafiya haka kawai na tsargi kaina na kwalla mata kira, aifa tanajin murya na jikinta ya hau tsuma ta k'araso kusa dani harara na galla mata nace "shine kikaje kika had'a ni da malam Yahya ko?"
K'irji ta dafe tace "lah wallahi babu abinda na fad'a masa ko barima banyi ya ganni ba dan kar ya tambayeni" kwafa nayi tare da k'ara mata hararan dayafi na farko nace "Allah ya ceceki yarinya da yau sai nasakaki aman mage"


Daga haka ban k'ara bi takanta ba hankali na ya kwanta tunda bata had'a ni da malam zalimu ba.


"Salamu'alaikum Hajiya ina abincina wallahi yunwa nakeji"
"Jimun yarinya ina kud'in da Ali ya baki kikace zaki sai wani abun a hanya?"
"Humum lallai wallahi bazan iya kashe wannan sababbin kud'ad'en ba dan haka zan had'a"""""""""maganar ya katse sakamakon ido hud'u da mukayi da Abdul Samad na kwasa da gudu na zube a gabansa tare da rik'o hannayen sa duka biyun nace"lah YAYANA yaushe ka dawo shine ko ka kirani a wayar Hajiya"


Hannun nawa yakai bakinsa ya sumbata yace"haba TAWAN idan nace zan fad'a miki ai bazakiyi d'okin dawowane ba ko?"
Ya fad'a yana d'age min gira, had'e rai nayi "nace shikenan babu ruwana da kai tunda haka kace" na fad'a tareda tashi zan bar wajen yayi saurin rik'o hannuna yace "haba TAWAN karkiyi min haka mana ina ta murna zanzo naga tauraruwata kuma sai tayi fushi ai sai kisa zuciyata ta buga"
Murmushi nayi na koma na zauna tareda janyo kwanon gabanshi na bud'e ido hud'u mukayi da mutumina wato farfesun kayan ciki saida na had'iyi yawu dan ina masifar son kayan ciki d'aya kwanon na bud'e lafiyayyen tuwon shinkafa ne wanda ko ba'a fad'a min ba nasan miyar d'anyen kub'ewa ne ko zogale dan sune miyar da Hajiya da alhaji suka fiso.


Zama na gyara a gabansa da nufin muci abincin tare Hajiya ta bugamin tsawar da ya gigitani na mik'e a zabure tace "wai dan Allah SUHANA meyasa baki da hankali ne bazaki jira na zubo miki nakiba zaki wani zo ki jagwal gwala masa abincin, kuma nasan ba tuwon zakici ba naman zaki tsince ki tashi dan bacin tuwo kike ba" wani irin fitinannen ihu na zunduma tare

4 / 7