Author : Hassana Abdulaziz Yakasai Category : A Books
Abdul Maleek anty Deenah, ni wallahi nayi tunanin ma wani abun ne ya faru wai ashe hira kawai suke.
A cinyar Hajiya naje na d'ora Affan na wuce d'akin Hajiya ban d'akin ta na shiga nayi wanka na fito na shirya cikin riga da sket 'yan kanti har lokacin suna hira kaina tsaye wajen Yaya Ali na nufa dan duk bala'in sa yafi sauran yan uwana yimin abinda nake so.
"Ya Ali dan Allah kabani dubu d'aya da d'ari biyar kaji"na fad'a a marairace, ya aiko min da wani mugun kallo yace "kiyi uban me dashi?"
"Gidan anty Zainab zanje daga nan na biya gidan anty Khady zan amso sak'o" bai tanka minba saima ya Ibrahim ne yace "an hana dan uwarki"
Harara na galla masa nace "to na kulaka ne kuma wallahi badai Hajiya ba" yi yayi kamar zai taso na daka tsalle na d'ane ya Ali dan shi yafi kusa dani"kaga karka sake ka tab'a autarmu ya Ali ya fad'a yana zaro kud'in ya mik'o min dad'i ya kamani harda kwaso shoki.
Inda NAWAN yake ban kallaba har na wuce gidan anty zee baiwar Allahn nan tana shan wahala wajen mijin nan nata dan Wallahi duk yan gidanmu basa k'aunar mijin anty zee saboda mugun halinsa, gashi Allah ya d'iga mata mugun sonsa ranta har b'aci yake idan aka kushe shi mugun gashi abu kad'an zai had'a su zai hau mata horon yunwa idan zasuyi wata suna gaba to zaiyi wata bai bata abinci ba
MAMAN ISLAM
NAMIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 24
Sanin halin Ma'ruf mijin'yar uwata yasa a hanya na siyi kayan wainar fulawa na siya mata d'anyen kifi na d'ari biyar dake nima kud'ina da nake tarawa duka na had'a dasu saboda nasan zuwa gidan anty zee kashe kud'i ne.
Tundaga k'ofar gida nake jiyo hayaniyar ma'aruf yana surfa bala'i bansan sanda na saki wani mugun tsaki ba na afka cikin gidan a raina nake fad'in wallahi yau sainaci ubanka ma'aruf muddun ka sake ka zagi Hajiya da Alhaji.
Yana ganina kuwa yayi muk'us na watsa masa wani mugun kallo na saki tsaki na shige d'akin ai ina shiga anty zee ta d'auke fuskata da Mari "dan ubanki Abban Annur sa'anki ne da zaki masa tsaki" mamaki kusan kasheni yayi na kafeta da ido ina mamakin yadda anty zee take fifita ma'aruf akan yan uwanta shiyasa yawancin su suka k'yale ta take shan bak'ar wahala.
Bak'in ciki ne yasa na durk'ushe a wajen na fashe da kukan bak'in ciki yayin da anty zee ta koma tana bawa ma'aruf hak'uri waini yarinya ce innalillahi ganin yadda ma'aruf ya d'auke anty zee da mari wai ai dama dukanmu bamu da tarbiyya,wannan magana ta mummunan tafarfasa min zuciya tun ina yar yarinyata na tsani wulak'anci bana jurar sa yana d'aya daga abinda yake masifar k'untata min d'ago idon da zanyi kawai ya sauka akan wani dutsen wuta guda biyu mai d'an girma da kuma k'arami nasan aikin Annur ne da sauri na d'auka ma'aruf dake ta zagin iyayenmu cikin tsantsar wulak'anci da cin mutunci sai jiyai na sauke masa dutsen da yasa jiri ya wulwulashi da k'asa, kafin anty zee tayi wani abu itama na sauke mata nata kuma na had'a da fad'in "Kuma Allah ya isana muguwa kawai azzaluma ki zauna ya kasheki a banza ba kowa yayi asaraba sai 'ya'yanki dan bayan ni akwai anty Khady da anty Deenah kuma kinwa kanki abinda na kawo dagashi bazan baki ko sisina ba wahalalliya" daga haka na d'iba da gudu na bar mata gidanta ina kukan bak'in ciki da mamakin abinda yau anty zee tamin akan wannan tsinannen ma'aruf d'in.
Yadda anty Khady ta ganni wurjanjan ido jazur yasa ta rud'e tana tambayana abinda ya faru ban b'oye mata duk abinda ya faruba na fad'a mata, itama ranta yai masifar b'aci ta rik'a zagin anty zee ni kuwa cewa tayi nayi daidai.
A takaice sai bayan sallar isha Sulaiman mijin anty zee ya kawomu muna sa kai falon mukai ido hud'u da anty zee yaya Abdul Maleek sai zaginta suke tana kuka.
"Ga munafukar nan ai sai ki shigo ki kwance k'ullin da kikaje gidan mace kika had'a tsakanin ta da mijinta" inji ya Ibrahim, kafin ma nace wani abu anty Khady tace"dallah malam dakata karka takura mata ni abinda tayi yamin daidai ta burgeni wallahi, ke kuma baiwar soyayya saikije yaci gaba bautar dake kamar jaka"
Ta fad'a tana fincikar hannuna mukayi ciki
MAMAN ISLAM
NAMIJI K'UDAN ZUMA
By
MAMAN ISLAM
☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️
Page 25
Gaban ya Ibrahim ta tunkud'ani "gatanan kashe ta, kasheta nace dan ubanka akan me wannan shashashar zata zauna wannan banzan yana azabtar dake da alama wannan dukane kika sha"
Ta fad'a tana nuna gefen kanta inda na jefeta da dutse ya fashe shi ya Ibrahim duk bak'ar zuciyarsa shiru yayi yana kallon ta yau tunda yaga tana zuba ruwan bala'i yasan da akwai dalili.
Ni kam banyi mamakin ganin anty zee a gidaba dan ma'aruf bashi da aiki sai korarta gida abu kad'an zatayi ya koreta idan tazo kuma maimakon ta tsaya a karb'ar mata hak'k'in ta sai tak'i tayi ta damunsa da waya ba dole yayita wulak'anta taba.
Gaban Hajiya da tayi zaune tanajin duk yadda anty Khady ke fad'a kamar zata ari baki amma bata kulaba dan Khadija bata iya fushi ba.
"Fad'a musu abinda ya faru SUHANA" kafin ince komai saida na dubi Hajiya nace "nida gidan anty zee har abada kawai dan ma'aruf yana zaginta nayi tsaki shine ta gauramin mari tana zagina ma'aruf d'in yana tayata wai harda cewa bakiyi mana tarbiyya ba wai duk haka muke sakaka ba kwab'a ni kuwa nayi musu ruwan dutsina ita da ma'aruf d'in na gudu"
"Kinmin daidai autarmu ni dama na tsani wannan mijin na zainab dan dai kawai ta nace masa ne kamar wanda yake bata wani abu ni daga yau kada a k'ara cewa na bada kud'ina ayi mata wani abun tunda bata san ciwon kanta ba"
Take falon ya kauraye da hayaniya aka hau zagin ma'aruf ana tsine masa saboda tsabar haushin sa da sukeji gashi da d'an banzan bak'in hali ita kuwa anty zee kuka tasa ta shige d'aki dama hakace take faruwa ta tsani a zagi ma'aruf da azageshi gwara a zagi Alhajinmu.
Wai ashe bayan na taho harda duka ma'aruf yaiwa anty zee sannan ya korota amma baiwar Allahn nan kwana biyu banzan ya lallab'a ta muka nemeta muka rasa ta koma gidanta.
Irin hakane yake faruwa duk lokacin da akaso k'watar mata hak'k'in ta bata bada damar hakan shiyasa ma'aruf yake masifar gana mata azabar wahala
*********
Rayuwa taja sosai yanzun mun shiga js 3 aji uku na lokacin kuma wani yayan yazeeda mai kirkin gaske ya dawo daga k'asar waje karatu ba d'an k'aramin kirkine da bawan Allahn nan ba cikin k'ank'ann lokaci mukayi wata irin shak'uwa dashi wanda yake haddasa mana yawan fad'a da NAWAN saboda d'an banzan kishin sa dan zuwa lokacin ya jima da sanar dani irin son da yakemin kuma nima ina tsananin sonsa wannan Kennan.
Zaune muke nida yaya Marwan muna hira NAWAN yazo wucewa Marwan yana masa magana ya saki wani mugun tsaki ya wuce kawai Marwan ya saki baki ya bishi da kallo kafin ya maida kallonsa kaina "ikon Allah SUHANA kodai Abdul Samad baida lafiya ne kinga ina masa magana yak'i kulani"
"Uhmm nima bansan me yake damunsa ba" na fad'a muryata na rawa matsalata kenan da raina ya baci sai muryata ya kama rawa "Allah ya kyauta" cewar Marwan na amsa da "amen daga haka nayi masa sallama na wuce gida.
A soro na tadda NAWAN cikin fushi yace "ban hanaki kula wannan mutumin ba?"
"Idan aurena kake to daga yau ka fasa na fad'a tareda shigewa cikin gida ai kuwa ba k'aramin fusata yayi ba ya wuce gidansu cikin d'acin rai.
A k'alla saida muka shafe kusan wata guda bama magana kafin mu shirya dan gaskiya bawan Allahn nan yana mugun zuciya ga masifaffen kishi tunda ya nuna yana sona ban isa kula koda abokiba.
Cikin wata gudan da mukayi bama magana da NAWAN wani irin shak'uwa mukayi da Marwan wanda har mutane da yawa suke tunanin soyayya muke nan kuwa yace yana sona na fad'a masa gaskiyar magana tsakanina da Abdul Samad.
"Hadiza wannan ciwon zuciyar da ya kamani ba sanadin komai bane sai Abdul Samad wanda na lura yana tsananin son SUHANA ni kuma bazan iya jurewa ganin Hajiya da Alhaji a cikin wani haliba yasa nake b'oye musu duk lokacin da ya motsamin nake jinya b'oye"
Cak na dakata da shiga d'akin namu jin wannan batun mai kama da almara mamaki ne ya kusa kasheni yar uwata tana son saurayin danake tsananin so kamar raina kai innalillahi wainnailahi raji'un
MAMAN ISLAM CE