Author : Ummu Maheer Miss Green Category : Thnovels
Shiru nayi kamar me tunani na ce" Amira me zai hana muje gidan DEEN MARSHAL gidan da
muke aiki nida Umma muje su taimaka mana da kuɗin aikinta ko na rabin wata ne kinga ya isa
mu bayar asallame ta".
"kin kawo shawara Anti Humaira, sai dai kinsan ba suda mutunci wallahi, kada mutun yaje su
nemi su wulaƙantasa".
Kafin ta kammala maganarta na tuno da abinda ya faru abaya, sanda Umma na laulayi naje
domin su bata kuɗin watanta sai da suka silleni sil sannan suka watsomin afuskata, ina kuka na
ƙwashe kuɗin na dawo gida Umma sarkin haƙuri bata ko nuna min komi ba, ire iren wulaƙanci
da nuna ƙyama duk suna mata saboda wani lokacin idan za'ayi sha'ani agidan ina zuwa in taya
Umma aiki abiyani, amma tun da naga suna wulaƙantata sai na daina zuwa sam.
wani tunani ya faɗomin.
Na ce" Amira me xai hana muje wajen Baba Sadi, ina ganin kamar ba zai hanamu dubu ashirin
ba dai tunda kinga ƴar uwarsa ce".
"eh to bazan ce komi ba Anti, amma sai dai ke kije domin bazan lamunci wulaƙancin matarsa ba
ehe, domin tana yimin zan fito mata a asalin kala ta".
Inaji ina gani na goya Anisa abayana, domin bata fiya yarda da kowa ba Amira kumw dukanta
take shiyasa bata yarda da ita.
Na kama hanya na tafi, da yake can Hotoro GRA yake nayi sa'a yana gida ba kowa, da yake
yaransa biyu ne kuma duk suna makaranta matarsa kuma ma'aikaciya ce, shi kuma ɗan
kasuwa ne amma ba kullum ya ke fita kasuwar ba.
A farfajiyar gidansa na hangosa, yana shan iska na ƙarasa da fara'ata yana karanta jaridar
Aminiya, na ƙarasa na gaidashi saɓanin da yake amsawa da ƙer yanzu cike da gwanintar iya
dariya yake yaƙe haƙora, har yana tambayata mahaifiyata da Babanmu.
Na ce" lafiya lau Kawu, inasu Fadil da Amrah da Maman Fadil"?.
ya amsa yana shafa gemunsa gamida ƙaremun wani irin kallo me cike da fassarori da dama,
sai dai ni ban gane kallon ba ina tunanin ko dom yaga na rame ne yanzu oho?.
na sunkuyar da kaina, hawaye suka shiga ƙwaronyomin na fara irgo baya nan sala sala.
"dama Ummanmu ce ba lafiya Kawu, tana asibiti yau ta haihu da safe ƴan biyu amma Baba
babu kuɗin da za'a biya mata na asibiti kuma gashi suna son sallamarta".
yaɗan shafa gemunsa cike da tausayina ya ce" yi haƙuri kinji daina kuka, zo muje daga ciki sai
in ɗakko miki kuɗin".
jikina asanyaye na tashi na bishi, ina godewa Allah domin kuwa nasan kukana ya ƙare tunda
yaji tausayina ya ce zai bayar, duk da Kawu Sadi aƙwaisa da masifar son kuɗin tsiya ko
matarsa sai ta yi da gaske take ɓanɓarar rabonta abinda dai ya sani shi ne kawai ya ɓoye
abinsa, shi ba da sadaka ba balle zakkah.
Babban falon gidan ya ce in zauna, Anisa taji sanyin AC sai tayi barci ni kuwa sai kallon falon
nake, wai ace ɗan uwan mahaifiyata ne yake da wannan kuɗin? amma ni har yau har gobe ya
kasa samun damar taimakawa Ummanmu ko da jari ne.
can ya fito daga shi sai jallabiya, ya ƙaraso da fara'arsa yana ce wa" kinga ma alwala
nayo an shiga sallah, bari inyi sallar sai na dawo in baki saƙon har da kuɗin mota, ki shiga
wannan ɗakin kije ki ɗauro alwalar".
na tashi ina masa godiya, na sauke Anisa akan kafet ɗin ɗakin ahankali saboda kada ta tashi ni
kuma na shiga ɗakin domin ɗauro alwalar.
ɗaki kamar me saboda tsaruwarsa da kyawunsa, kuma daga gani bama nasu bane wataƙil na
Fadil ne domin ayanzu saurayi ne sa'a na ne ma.
Ƙofar ban ɗakin naji an turo, da sauri na juyo ina shirin ɗaura ɗanƙwalina sai dai me??????
tsoro da firgici suka sanyani kurma wani uban ihu ina firfito da idanuwa..............
INA GODIYA MASOYANA, AƘARA BADA HIMMA WAJEN TAYANI YAƊA WANNAN LITTAFIN
DOMIN KOWA YA ƘARU DA ABINDA KE CIKINSA.
*MRS GREEN GRAPHICS*
MUNA KOYARDA KALOLIN GRAPHICS MASU KYAU DA TSARI KAMAR SU.
Invitation card
Logo
3d mockup
3d render
Cover book
Banner
da dai sauransu, idan kina buƙatar koya kiyimun magana ta lambata kamar haka
07068606171
UMMU MAHER.
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN): *_ƊAN HALAK_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
*Danna wanna link ɗin kai tsaye xaka samu 3k daga tsarin palmpay amma waɗanda basu taɓa
buɗewa ba, kisa lambar wayarki zai kai ki inda zaki ɗakko application ɗinsu, idan baki gane ba
ki tuntuɓe ni ta lambata 07068606171*
Hey, I use the PalmPay app for free transfers and to get cashback on every transaction. Use my
link or my code "SUQD6653" to join and get ₦1000 welcome bonus.
https://link.palmpay.com/34vPB
3
_________Ganin yanayin dana shiga yasa Baba Sadi saurin tura ƙofar banɗakin da yake glass
ce, na waje ma ba zai hango duk abinda ya ke faruwa ba.
Ya sanya babban ɗan yatsansa dai dai laɓɓansa, sannan ya ce"shitttttttt!".
yana me zaro manyan idanuwansa waje, jikinsa sai rawa yake yana wani irin smilling na rainin
wayo, sannan ya lashe harshensa tamkar yadda asalin ƙwartaye suke idan suka samu cafka. ni
kuwa ina rakuɓe sai tafiya nake da baya baya har Allah yasa ya taddani har zuwa inda nake,
tuni hawaye suka cika idona ga uwar majinar dana ke ja tamkar an buɗe kogin tafkin maliya.
yana wani banzan murmushi irin na basawa muryarsa tana rawa tamkar rawani ya kunce akan
basarake ya ce" inaso ki bani dama in nuna miki zallar abinda yake raina, tun kina ƙaramarki
kike burgeni sosai saboda Allah ya yi miki halitta, ga kyau, ga fari, ga kyawun diri, wallahi
Humaira ina matuƙar sonki da sha'awarki inaso ki bani dama in dinga ɗaukarki ina kaiko hotel
duk abinda kikeso zan miki shi ko menene sh..........."
tun kafin ya ƙarasa nayi wani kukan kura na bangajeshi yayi taga-taga ya faɗa kan jakuxi,
na'urar wanka sannan na samu damar buɗe ƙofa ban san ba har na faɗi naji ciwo agoshi na, na
yi saurin ɗaukar Anisa dake barcinta hankali ƙwance sai naji dama in dawo Anisa domin ita ɗin
bata san komi ba, rayuwarta take cike da kula da jin daɗi bata san wata damuwa ba, ni kuwa
ashekara 18 danayi arayuwata na fuskanci ƙalubale da dama, domin duk namijin daya kalleni
sai ya kuma kallona, kai hatta jinsina na mata basu daina furta kalmar ina burgesu ba har zuwa
kamar rana ta yau basi daina ambaton kalmar burgewa ba.
Gudu nake sosai har na isa bakin titi, gashi ba nida kuɗin mota gashi na haɗa wani irin uban
gumi tamkar an tsamoni aruwan sama, sai wulƙita ido nake tamkar wacce ta samu kyautar
tsabar sisin naira.
Anisa sai kuka take na goyata ina rarrashinta, na dinga tunani azuciyata ko dai bara zan fara yi
ne? domin abincin da xamuci yazu yana nema ya gagaremu dama mahaifiyarmu ke wanke
wanke da shara agidan 'DEEN MARSHAL' saboda haka duk wata ake bata kuɗi dubu talatin har
da biyar, saboda wanke wanken gidan kamar na buki haka yake ga uwar harabar gidansu duk
faɗinta ita ce take sharewa har tausayinta nake ji.
Kuka nake har nazo gida, amma ina shiga gidan na goge hawayena saboda ƙanwata Amira
nasan zan sanyata cikin wani hali, saboda haka sai na wayance har da dariyata kamar na samo
wani abin arziƙi, nan kuwa babu abin arziƙi sai na tsiya domin kuwa ban samo komi ba sai bara
abulayi bara akufai. Amira tayi saurin miƙewa ta ce" ya dai!? an samu kuɗin kuwa"?.
na zauna yaraf dani kamar kayan wanki, sannan na ce" uhum naje baya gida ma amma yanzu
ya zamuyi Amira"?.
"Anti meye agoshin ki"?.
na shafa ina ɗan wayancewa na ce" uhum faɗuwa nayi ne"?.
ta nuna damuwarta har da miƙomin ruwa me sanyi a aranda, Amira tana matuƙar sona da kuma
jin tausayina da tana da hali da ko ƙuda ba zai hau kai na ba.
ta ce" uhum ni ina ganin muje gidan da Umma take aiki kamar yadda na kawo shawara abaya,
ita ce dai shawarar da ta rage mana tunda Baba Sadi baya nan wa zamu samu a ƴan uwan
Umma? tunda dama sun tsani Baba kinga kuwa babu me taimaka mata, kuma dama kullum
suna ƙorafin ta fiya haihuwa". Ummi tayi caraf ta ce" oho dai dole ayo da ita ai, kullum Umma cikin haihuwa tamkar wata
kaz......."
Duka Amira ta kai mata, ta kauce tana ƙunƙuni.
$$$$$$
Ammi ta rintse idonta ta ce"Zaki kazo inason ganinka gobe".
da yake sunan da take kiran Haidar dashi shi ne ZAKI.
ya ɗanyi jim, sannan ya ce" ok in sha Allahu zanzo".
Daga haka bai ƙara magana ba, itama ta kashe wayar ba tare da ta ce komi ba, domin tasan
miskilancinsa ba magana zai yi ba sannan daga jin muryarsa yana cike da damuwa sosai.
Ammi tana ajje wayar Mimi ƙanwar Haidar ta ce" Ammi wai me yasa wasu ƴaƴan basa son
ganin farin cikin iyayensu ne?".
Ammi ta gane inda maganarta ta dosa amma sai ta nuna bata gane ba ta ce" Mimi ban gane
maganar ki ba? waye baya son farin cikin iyayensa? indai ƊAN HALAK, ne ai dole yayi
biyayya".
"Ammi gaskiya na tsani bro Haidar, wallahi baya son farin cikinki yanzu ga irinta nan, kullum sai
ciwonki ya tashi ni na lura ma so yake ki mutu yayi mun biyu babu tunda ni Abbana ya rasu shi
kuma dama baisan zafin uba b............"
cikin zafin nama Ammi ta kai mata bugu, tun kafin ta ƙarasa maganar da taso yi ɗin Ammi ta
nuna ta da yatsanta ta ce" ni zaki faɗawa wannan maganar Mimi? ban faɗa miki banason
wannan mugun furucin naki ba? ke da ɗan uwanki amma kina nuna masa tsana? akan abinda
bai da laifi aciki, har kina kiransa da wannan muguwar maganar? uban waye ya ce miko baisan
zafin uba ba? to don ubanki arziƙin ubansa kike ci ayanzu".
Sosai Mimi ta fashe da kuka, ta tsugunna gaban Ammi gamida riƙe kunnenta cike da yarinta ta
ce" ki yafemin Ammi rai na ne ya ɓaci amma na tuba bazan sake ba".
Ammi ta ɗago ta, ta sanya lallausan hannunta tana goge mata hawaye ta rungumeta a ƙirjinta
tana rarrashinta tamkar ƴar Baby, sannan ta ce" ko wani bawa da kike ganinsa da kalar
ƙaddararsa, bawa baya iya kaucewa ƙaddara saboda haka baki ɗaya rayuwar Zaki rayuwa ce
ta jin daɗi abayyana amma abaɗini ba haka bane sam baya jin daɗin rayuwarsa shiyasa ya zaɓi
yin rayuwa shi kaɗai, wai don ma yana da kuɗi da babu me kulasa nasan Haidar cikinsa da
wajensa yana da matuƙar haƙuri yana son yayi aure amma hakan ya faskara, saboda rikitattan
al'amarin daya faru abaya wanda ni nasan shi ɗin ƊAN HALAK ne, amma mutane da dama sun
ɗauka ba ɗan halak bane".
Mimi tayi saurin gogewa Ammj hawaye, tana maƙale a ƙirjinta ta ce"Ammi duk nasan da hakan
amma banason inga ranki yana ɓaci Silar ɗan uwana, bazan so ace ɗan uwana yana yawan
ɓata miki ba domin bana son fushinki ya tabbata akansa domin ko da bakice komi ba Allah yaga
zuciyarki kuma abin zai dinga bibiyarsa".
Ammi ta janyo hannun Mimi ta fara nuna mata hotunan wasu mata kyawawa, waɗanda suka
amsa sunansu a mata kuma kana ganinsu ka ga ƴaƴan manya.
"Ammi waɗannan hotunan fa"?.
tayi ƴar dariya ta ce" Zaki zan nunawa su ko Allah zaisa adace yayi aure nima ko zan samu jin
daɗi domin bana jin daɗin halin da yake ciki kusan shekara arba'in amma ba mata".
"taɓ, ai kuwa Ammi dama bakiyi wannan wahalar ba, domin kuwa nasan ko kallon arziƙi ba zai
musu ba saboda kinsan halinsa".
"hakan dai zan nuna masa, sannan in nuna masa ɓacin raina indai har bai zaɓi ɗaya daga
cikinsu ba saboda idan na sanya masa ido haka za ayi tayi, sannan iyayen waɗannan yaran
sun san komi na rayuwar ZAKI bana tunanin zasu juya masa baya".
badon Mimi ta so ba ta biyewa Ammi, amma sam bata son ɓacin ran ɗan uwanta domin tasan
wannan haɗin maimakon yayi masa daɗi sai ma sanyasa damuwa da za tayi.
***
"Anty Salima wallahi ki ƙara tunani, amma bai kamata daga an faɗa miki abu ki hau kai ki zauna
ba, domin ni na tabbatar wannan batun na Anti Tahira zancan ƙanzon kurege ne saboda tana
baƙin ciki kin samu miji ita bata samu ba, tsakani da Allah da yaya ma kika samu zuciyar Haidar,
kinsha wuya sosai har Allah yasa ya fara kulaki yana damuwa da lamuranki, amma don me zaki
ce masa wai shi ba ƊAN HALAK bane yo ko ba hakan bane ma menene? Tunda kina sonsa
yana sonki menene to? yanzu ke zaki iya cire sonsa acikin zuciyarki"?.
shiru Salima tayi, hawaye masu zafi suka fara zubo mata ta ce" Hanan, wallahi ina cikin matsala
wallahi tunda na faɗa masa wannan maganar nake jin ba daɗi har cikin raina wallahi amma na
kasa jurewa ne har sai dana faɗa masa, amma yanzu kuma ina cike da nadama me tsanani
akan hakan".
"My freind indai har kin yarda ga wayarki danna ki kirashi yanzu, ki tabbatar masa da lallai kinyi
laifi ya yafe miki".
Salima taji kamar idan tayi hakan ta zubar da mutuncinta na mace, ga ta matsayin ƴar sarauta
kuma gimbiya Salima taya zata sakko nan da nan ta bawa namiji haƙuri.
"daman nasan baza ki iya ba, biyo bayan girman kanki Allah Salima ki daina wannan girman
kan domin zai cutar dake anan gaba, abinda kake so ai baka yi masa wargi". Salima ta tashi
tana gyara alkyabbarta da yake yau zata kasance wajen mahaifinta domin neman da yayi mata
na gaggawa.
tana fita Hanan tayi saurin ɗaukar wayar Salima, nan da nan ta ƙwashr lambar Haidar tana ta
wani mugun murmushi domin Allah ya sani wannan damar ta daɗe tana jira, sai yau da ƙawar ta
ta buɗe wayar agabanta taga pin ɗin wayar.
tayi wani shu'umin murmushi sannan ta adana wayarta ta cigaba da binciken wayar Salima,
tana yi tana cige leɓe tamkar zata fasa leɓen saboda ita kaɗai tasan irin tashin hankalin da take
ciki tun daga ranar da ƙawarta ta sanar mata da wanda take soyayya taci alwashin mallakarsa
ta ko'ina, da ta ɗauka zata sha wahala ta ɓangaren Salima amma ayanzu ta tabbatar Salima
sokuwa ce ita da kanta zata taimaka mata wajen cika burinta na mallakar namijin maza ZAKI
Aliyu Haidar.
*UMMU MAHER CE*
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN): *_D'AN HALAK_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
*_UMMU MAHER BUSINESS CENTER_*
*koyon sana'o'i 5 kamarsu*
1 MAYAFI NA BEAD WORK
2 MAYAFI NA STONE WORK
3 HULUNA
4 COVER BOOK
5 INVITION CARD
dukkaninsu zaki koya akan 500 ƊARI BIYAR KACAL.
*KIBI WANNAN LINK ƊIM DOMIN SAMUN DAMAR GARAƁARSA SHIGA GROUP
ƊINMU*
https://chat.whatsapp.com/CMlWt3cUVvkDAXPthThNQx
4
_________Hanan tayi wani murmushin yaudara sannan ta fita daga masarautarsu Salima tana
wata irin dariya me cike da fassarori da dama.
tana ganin ta fito ta duba bayanta ko wani ya biyo ta, tayi maza ta fito da wayarta ta dannawa
wata lamba kira.
Can aka ɗaga, taɗan sanyaya muryarta kamar wata marainiya me neman taimako ta fara
magana" assalamu alaikum, nasan baka sanni ba Alhaji Haidar amma don Allah inason ka
saurare ni wallahi ina cikin wata matsala ne kuma Allah ne zai fitar dani sai kuma kai, wallahi
kamar yadda rayuwata ta zama abin tausayi haka taka take duk kuwa da irin tarin ni'imomin da
jalla wa'ala yayi maka, kafin ƙarfin komi arayuwa amma kuma kana cikin ƙaddarar rayuwa mafi
muni duk wanda ya rasa abokin rayuwa ai ya rasa babbar madafa arayuwarsa, duk da yana da
ni'imomi da dama da yayi masa kamar yadda ka rasa abokiyar rayuwa nima haka na rasa,
ahalin yanzu miji ya gagareni samu duk wanda yazo sai ya tafi, saboda ana min kallon ba ƳAR
HALAK bace, ada can baya ina addu'ar Allah ya kawomin wanda zanyi shawara dashi
agameda abinda yake damuna, sai gashi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Allah yasa ya kawomin kai
cikin rayuwata, don Allah ka ceci rayuwata kada kace zaka ƙi karɓar tayin soyayyata wallahi ni
kaɗai nasan abinda nake ji sai kuma Allah sai wanda yasan irin ƙaddarar da Allah ya jehomin
ma'ana me irin ƙaddarata kamar kai ɗinnan".
Shiru Haidar yayi, yana tunanin irin amsar da zai bata, gashi kuma Allah ya hanasa kashe
wayar domin zuciyarsa tuƙuƙi take tana wani haƙilo gamida amon tafashshiyar wuta na masifa,
abin mamaki ma yake basa wato tsabar ya zama tasi no gareji ta yaya za'ace wai mace ta
kirasa tana faɗa masa wai itama irin ƙaddararsu ɗaya? wato kowa ma yanzu yasan shi ba ƊAN
HALAK bane, ɗan shege ne shi? kai wannan baƙin ciki da yawa yake, shiyasa akullum sai yayi
kuka akan wannan mummunar ƙaddarar tasa wacce tun yana ƙarami take bibiyarsa har yanzu,
wacce yaci ace yanzu tuni an manta da wani rashin asalinsa, amma tun yana da ƙananan
shekaru yake fuskantarsu har zuwa yanzu da yake da kusan shekara 38.
ya goge wata ƙwalla me masifar zafi.
Jin yayi shiru kamar ruwa ya cinyesa yasa Hanan tasha jinin jikinta, da sauri ta katse shirun da
ce wa" Allah ya huci zuciyarka yallaɓai, nasan daman ba lallai ne ka karɓi tayina ba, saboda ba
nida asali wallahi yallaɓai banyi hakan domin ɓata maka ba, nayi hakan ne saboda na duba
gabas da yamma babu wanda na dace dashi sama da kai.........."
Jin ɗib tayi, tun kafin ta ƙarasa ya kashe wayarsa yana jan numfashi me masifar zafi yana ajje
wayar akan tamfatsetsen gadonsa ya fashe da wani irin