'DAN HALAK Book Complete (By ummu maher)miss green.pdf

Author :  Ummu Maheer Miss Green Category :  Thnovels

Chapter   4 / 13

9K to 12K   out of 37.7K words



*TIME TABLE NA KOYON SANA'A*

CLASS 1👇🏻
____________

*KOYON MAYAFI NA BEAD WORK BEAD WORK*
*MAYAFI NA STONE WORK*

*HULUNA*
*RIGUNA*
*FANTIS*
*WANDO JEANS*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800

CLASS 2👇🏻
______________
*INVITION CARD*
*3d logo*
*3d mockup*
*3d render*
*Cover book*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800

CLASS 3
_________
*Turaren wuta*
*Humrah*
*Gyaran jiki*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 1k

a tuntuɓi ummu maher ta lambarta👇🏻
07068606171

*DOMIN SHIGA WHATSAPP GRP ƊINMU👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/CMlWt3cUVvkDAXPthThNQx

6
________da sauri na kalli wanda ya shigo, na haɗe rai jikina har ɓari yake saboda ruwan
masifa idanuwana suka canja kala asalin Haidar É—ina ya bayyana baki É—aya.

"Mu'azzam anya kana da hankali kuwa? wannan fa shi ne wanda naga an rataye hotonsa a
wajen folis shi ne wanda ya sanya ka wannan jinyar alhali bakaji ba baka gani ba? To yanzu
kuma meye ya kawosa wajen nan? ai kuwa yau aƙwai Inda ba ƙasa"..............

maimakon naga ransa ya ɓaci sai ma naga yayi murmushi mai ma'anoni da dama, ya ƙaraso
kusa dani ya ce" Bro Haidar, ka daina kumfar baki domin shi wanda na yiwa abun ya daÉ—e da
yafemun, wallahi ban taɓa ganin bawa me masifar haƙuri irin Mu'azzam ba, bawan Allah ne
wanda bai damu da kowa ba, ban taɓa yin tunani akan duk abubuwan dana ke aikatawa ba,

ban taɓa tunanin zanyi abun yazo ya dameni ba Mu'azzam ya yafemun yanzu kai kaɗai ya rage
Haidar, domin Mu'azzam ya nunamin muhimmancinka arayuwarsa, ya faÉ—amin tamkar Hassan
da Usaini kuke, jini É—aya ciki É—aya don Allah ka taimaka ka yafemun".

HaÉ—a hannayensa waje É—aya yayi yana neman yafiyata, sai naji duk masifar dana tattaro ta
koma na samu waje na zauna, ko dama ni can hukuma ne sai da rarrashi inada zuciya sosai
wacce idan ina cikinta bana iya gane hagu balle kuma dama, haka nake rayuwata ni kaÉ—ai ba
nida wani aboki wanda zance ina iya gayawa sirrina, ko ayanzu danake jin Mu'azzam tamkar
jinina ba komi ya sani na sirrin rayuwata ba, saboda ni mutum ne me masifar zurfin ciki, da
wuya kaji cikina in har ba laɓewa kayi kaji saƙon zuciyata ba, ko kuma akayi wani abun
agabanka to shi ne zaka É—orar da wani abun.

na kalli Mu'azzam yana zaune akan gado, yayi wata irin muguwar rama tamkar wanda ya daÉ—e
yana jinya, abin tausayi dai sai naji dama in koma me irin zuciyarsa saboda nasan mutum ne
shi me masifar haƙuri da sanin ya kamata, babu ruwansa da rayuwa balle ƙele ƙelenta. nasan
kome zanyi bazan taɓa komawa irin zuciyarsa ba saboda dama ni can mutum ne me masifar
zuciya balle lokaci É—aya in canja ta nasan ba abune me yiyuwa ba, sai dai in zama me yafiya ko
iya wannan ma na tsaya na daki wani makami na siraÉ—in rayuwa wajen hayewa da tsani me
kyau.

na buÉ—e bakina tamkar me ciwon baki na ce" ba komi na yafe maka, tunda wanda aka yiwa
laifin ya yafe, kaga ni ƙarashe ne nawa saboda haka na yafe maka Allah ubangiji ya yafe mana
baki É—aya".

Sosai naga farin ciki akan kyakkyawar fuskar Mu'azzam, abun ya bani mamaki sai ya shiga bani
tausayi kuma, saboda nasan duk inda me haƙuri ya kai to Mu'azzam ya kai kuwa.

abinda yake min yawo bai wuce abinda ya janyo wannan yaƙaddamar ba, tunda ni nasan shi ba
mutum ne me faÉ—a ko neman masifa ba, da dai nine sai ince zan aikata tunda nasan yadda na
iya fitina da tada zaune tsaye, domin É—an abu kaÉ—an zaka yimin in tada zaune tsaye.

"ina son jin abinda ya kawo wannan taƙaddamar"?.

É—an murmushi duka sukayi, Mu'azzam ya ce" ni ne da laifi Haidar ni na shiga gonarsa domin bai
sakoni a harkarsa ba ni na shiga nayi kane kane, duk abinda babu ruwanka daÉ—in ji gareshi ban
zama me kauda kai akan ɓarna ba, daman ni can haka nake in har za'ayi abinda ba dai dai ba
agabana zan faÉ—i gaskiya, amma ta cikin nutsuwa da neman maslaha nake komi, amma inason
ya faɗa maka komi da bakinsa kada na faɗa ba dai dai ba kasan na fara jin sauƙi kada na
karkace in faɗo ƙarya".

dukkansu sukayi Æ´ar dariya.

"Sunana Hammud Mai Nasara, mahaifina yana da kuÉ—i sosai ta inda baka tunani amma halin

rayuwa yasa yanzu ya samu karayar arziƙi, ina ɗaya daga cikin masu safarar miyagun ƙwayoyi
daga wata ƙasar zuwa Nigeria, na tara kuɗi sosai ta wannan harkar bana tsoron kowa harkar
gabana kawai nake, mahaifina yayi yayi in daina wannan harkar naƙi na daina, alhali ni kaɗai ne
ɗansa namiji wanda yake tunƙaho dashi gashi ina karatu wanda daga baya na daina karatun
ma baki É—aya, abinda ya kawoni na daina sa sai shashanci da kule kulen Æ´ammata, babu
ruwana da karatun da mahaifina ya ƙwallafa rai akansa ayanzu haka silar abinda nake ya
sanyawa mahaifiyata mummunan hawan jini, Mu'azzam shi ne mutum na farko daya karyamin
alƙadarina saboda babu wanda yake iya kallon cikin idona ya faɗi laifina sai shi, depertment
É—inmu É—aya dashi ganin bana karatu yasa ya ke janyonu ajiki tare da nunamin abinda nake bai
kyautu yinsa ba, amma na rufe kunnuwana na sanya musu toka na daina ganin kowa da jin
komi, ahaka har na daina zuwa makaranta jin na daina zuwa yasa Mu'azzam bibiyata yaji ina
nake zuwa? babu inda bai tambaya ba kowa yace baisan inda nake ba, har aka samo wani ya
faɗa masa amma ya nemi daya ɓoye sunansa domin kowa tsorona ya keji, ahaka yazo ya
sameni ya dinga yimin nasiha, ko É—aya ban É—auki nasiharsa ba sai ma niyyar fansa danaso
ɗauko akansa, saboda sanin inda nake da yayi zai iya tonamin asiri domin wannan ƙasar ba irin
ƙasarmu Nigeria ba ce, duk harka da manya da kake idan har kayi laifi ko kai waye sai an ɗauki
mataki akanka, daga nanne na sanya aka É—akkominshi nayi ta azabtar dashi, amma da yake
Allah ba azzalumin bawansa bane sai gashi ya shiryenu cikin gaggawa, aÉ—an zaman danayi
dashi haka ya cigaba da yimin nasiha duk da ina azabtar dashi ta ko'ina amma bai gajiya wajen
daina yimin nasiha ba, cikin nasihar tasa yana yawan faÉ—amin.

_KAJI TSORON ALLAH HAMMUD, KA SANI ITA DUNIYA BA WAJEN ZAMA BACE WAJEN
ARO CE DOMIN SHI KANSA RAN ARO AKA BAMU, BA DON ARO AKA BAMU BA DA TUNI
BABU MUTUWA TUNDA RAN NAMU NE, SANNAN DUK ABINDA KAKE KA TUNA DA CE WA
ALLAH YANA GANINKA, KAJI TSORON ALLAH KA GYARA MU'AMALARKA DA KOWA DUK
DA WANI KO GOYASA ZA KAYI VA ZAI DAINA JIN ZAFINKA BA TUNDA DAMA KOWA YANA
DA MAƘIYI, TUNDA MANZON TSIRA YAYI MAƘIYA DOLE KOWA MA YAYI SU SHI DA ALLAH
YA WANKE BAI TAÆA LAIFI BA, KAJI TSORON ALLAH KA TUNA RANAR MUTUWA. RANAR
DA ZA A ÆŠAUKEKA BA KADA BAKI BA KADA IDO BA KADA HANNUN AIKATA LAIFUKA
IDAN KAYI AIKI NE KYAU KAYITA KUKA KANA CEWA KADA SU KAIKA, IDAN KUMA KAI
ÆŠAN ALJANNA NE KAYI TA MURNA ZA A KAIKA INDA ZAKA HUTA DA FITIN TUNU DA
WAHALAR RAYUWA....._

ire iren waɗannan nasihun yake mun, bai taɓa gajiyawa ba har Allah yasa ayanzu na gane komi
ina kuma roƙon Allah ya shiryi dukkanin masu hali irin nawa, Allah kuma ya daɗo irin masu halin
Mu'azzam domin da ana samun irinsu da munafunce munafunce baiyi yawa ba".

Tun daga wannan ranar muka zama abokai, duk da bayan lokacin sai da Hammud ya shiga
hannun hukuma tunda ba irin ƙasarmu Nigeria bace, ko da kaida kayi report ka yafe to suma
suna da hakki, idan baka haÉ—a da addu'ah bama har gidan yari zaka tafi tunda su can laifin
gidan yari ba wahala ne dashi ba.
Bayan an gama shari'ah bisa addu'ar da muka dingayi Allah ya taimakesa da kansa sukace ta

tafi.

Mun haÉ—e kanmu tsintsiya É—aya maÉ—aurinki É—aya, saboda haka a makaranta aka sanya mana
suna TRIPLET Æ´an uku kenan, kowa da haka ya sanmu duk dani halinmu ya banbanta dasu
domin su suna da haba haba da jama'ah, ni kuma sam ba nida fuska kullum fuskata aÉ—aure,
sannan ba nida sakin jiki da kowa idan ba da triplet É—ina ba, bana shawara da kowa sai su
Mu'azzam yana ƙara mana karatu sosai cikin ikon Allah sai gashi har mun haddace ƙur'ani
azaman shekara 6 da mukayi tare.

cikin abinda na ɓoye musu shi ne asalina, ban taɓa nuna musu ni ba ƊAN HALAK bane, duk
wanda yake hirar mahaifinsa sai dai ni inyi shiru saboda ba nida abinda zance sai dai damuwa
ce fal araina domin nasan ina cikin rayuwa mafi tsanani.

Domin acikin babbar ƙaddara ta rayuwa rashin fitowa ta hanya tsarkakkiya ita ce babba, domin
kowacce ƙaddara ta biyo bayan wannan domin su iyayen da suka aikata ɓarnan basa jin daɗi
da kuma rashin ƙwanciyar hankali, sannan uwa uba shi yaron daya zo ta wannan hanyar
rayuwarsa na lalacewa ne tamkar dai yadda abinci yake lalacewa idan yayi wasu ƙwanaki.
asannu duk zurfin cikina suka gano komi, sun tayani alhini kuma sun shiga cikin tashin hankali
fiye da yadda nake ciki, saboda suna É—aya daga cikin manya manyan masoyana.

mun gama makaranta lafiya, kowa yana ta murna amma mu muna cikin tashin hankali na
rabuwa da juna, har gwara ni da Hammud saboda muna ƙasa ɗaya state ɗaya, shi kuma
Mu'azzam yana wata ƙasar daban duk da muna kusan maƙota da Niger, har tsokanarmu akayi
tayi.
*BAYAN RABUWA*

Haka kowa ya dawo gida, sakamakonmu yayi kyau sosai tunda dukkanin bama saka wasa
adukkanin harkokinmu, Mu'azzam yana yawan ziyartarmu akoda yaushe har na bashi shawara
ko zan bashi manaja a kamfanina, tunda ni da kaina inada kamfanin da bansan adadinsu ba a
ƙalla zasu kai ɗari ko ma sama da haka domin ina da dukiyar da nima ban san ta yadda aka
samota ba, tasowa nayi na sameta na cigaba da kula da ita ban fara tsorata da rayuwa sai
bayan dawowa ta daga ƙasar Italy, rayuwata ta zama abar farauta domin duk waɗanda Ammi ta
ɗora kan kasuwancina macuta ne ta yadda suka dinga aikata ɓarna babu ruwansu, domin sai
yadda sukayi da Ammi kuma ko sisi basa kawo mata, domin ita bata ma damu da kuÉ—in ba
tunda tana dasu har ta rasa ma yadda za tayi dasu.

Ganin wannan ɓarnar yasa duk na koresu na ɗauki aminai na Mu'azzam da Hammud suka
zama masu kula da komi sai dai ni inzo kawai in duba, sannan ina kula da hada hadar
kasuwancina na ƙasashen waje...............

*SHARE🥰*

*$HAIDAR*
*$MU'AZZAM*

ÆŠAN HALAK GRP LINK
https://chat.whatsapp.com/LcnDvlFNqL0Enq7llnpAVe




*UMMU MAHER*
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN)🍃: *_�ƊAN HALAK�_*



MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MISS GREEN)🍃_*

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION📚_*

~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159


7
_______Mu'azzam da Hammud suna iya bakin kokarin su wajen gina wannan rusassun
kamfanonin da aka lalata, nan da nan sai gashi an samu tsabar zunzurutun kudaden da ba'a
taɓa samu ba, hankalina ya kwanta da aikinsu, saboda sam basa nuna min mugunta suna
zaune dani tsakani da Allah.
A wata ranar juma'ar da bazan taɓa mantawa da ita ba, ina zaune a babban ofis ɗina na ƙasar
Faransa sai naga kira daga wata lambar da bansan ko waye ba?.

Mutum uku ne suke da lambata ta ƙasar waje, Mu'azzam da Hammud sai kuma Ammi wacce
itama bata daɗe da sanin lambata ba, domin sai da Mu'azzam yayi yaƙi dani Sannan na bawa
Ammi lambata.

"Hhhhhhh".


Dariyar dana ji ce ta bani mamaki sosai, sai naji gaba kid'aya kasalar dana keji ta ƙaru sosai, na
buÉ—e baki da niyyar yin magana sai naji Muryar wani mutumi wanda tabbas nasanta amma
halin mantuwa na manta inda na sansa baki É—aya.

"Haidar"....

Jin sunana yasa naja wani numfashi me cike da jin daÉ—in kiran sunana, sai daga baya ne
kunnuwana suka jiyomin wani mummunan lamari, wanda yasa na tashi amatsanan mugun
bugawar zuciya, wanda ta sanya gangar jiki da ruhi acikin wani mummunan yanayi.

"dama na kira ka ne da babban murya, Haidar wannan sanya idon naka yayi yawa kai da
amininka Mu'azzam ina ƙara faɗa maka kayi a hankali kayi a sannu kuma domin ayanzu haka
ka haÉ—a ruwa da wuta awaje É—aya, wanda sai nan gaba ne zaka gane dukkanin abinda ake nufi,
amma ahalin yanzu dab Mu'azzam yake da bankwana da duniya, domin wannan wutar da ka
haɗa shi da ita ta kusa cinyesa baki ɗaya har ƙashin ɓargonsa"..............


Tun kafin ya ƙarasa na gaza haƙuri zan hau masa ka, da sauri ya kashe wayar kaina ya ruɗe
baki É—aya, na rasa wani irin tunani zanyi ne? To me wannan mutumin yake nufi? Matsalar dana
shiga abaya ita ce zata dawo yanzu? Duk wanda na É—ora a kamfanoni na mutane masu amana
sai kaga sai wani mugun abu ya faru dasu, ko dai a kashe su ko kuma a lahantasu, Misali akwai
waÉ—anda da dama sukayi hauka, wasu kuma ciwon laka wasu ciwon wuya.

Wani irin ɓacin rai ne ya ziyarce Ni acikin daƙiƙun da basu fi uku zuwa huɗu ba, na samu waje
na zauna ina tuno tunatar War Mu'azzam a kaina akan duk damuwar dana ke ciki in miƙa
lamurana ga sarki Allah, sannan inyi ta maimaita Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un.

Kalmar danayi ta ambatawa kenan har Allah yasa naji nutsuwar zuciya.



*Bayan wasu awanni*

A mugun kiÉ—eme na fito nayi hanyar gidana dake cikin kasar Farisa, ko gabana bana gani sam
baki É—aya naji zuciyata tayi min zafi tamkar tafasasshiyar wutar gashin tsire.


Mutuwar Mu'azzam ta tarwatsa dukkanin wasu notikan kaina, adaren nayi bisa na dawo ƙasata
ta haihuwa Nigeria tare da É—imbin tashin hankalin daya gaza wassafuwa azuciyata da gangar
jikina, lokaci É—aya na fita daga hayyacina na rame sosai.


Abirkice na shigo kamfanin yayinda na sameshi cike da mutune, ana ta tayani baƙin ciki a
fuska, Hammud na hango zaune ya haÉ—a uban tagumi sai haÉ—iyar zuciya yake babu ma ruwan
hqwayen sai kukan zuci da wasi wasi.

Yana ganina ya taso da mugun sauri yayo kaina, dukkaninmu muka saki wani irin kuka me ban
tausayi, sai da muka yi ne isarmu sannan muka yi shiru.


Ko gawar Mu'azzam ba a gani ba, domin a inda yayi hatsari motar ta kama da wuta sai toka
aka É—iba aka yiwa addu'ah.

Na shiga tashin hankali sosai, Hammud ma ya shiga damuwa mu biyu muka haÉ—u muka ta
bawa juna haƙuri har Allah yasa muka rage damuwar.

Hammud ya shiga tashin hankali bayan ya koma aiki, saboda ya saba sosai da Mu'azzam sai
ya zamanto komi yayi baya harkar cinikayyar ta ja baya, saboda shi wanda yake kula da
dukkanin al'amuran ya zama abin a tausaya wa.

Su kura masu jiran Nama, su Alhaji Hadi aka cigaba da tafiyar da harkoki cikin almundahana
da aikata ɓarna da kuɗin da ko kusa ba suda gadonsa.

Da ƙer na fara dawowa hayyacina, har Allah yasa na samu nutsuwar zuciya nayi tafiya zuwa
Niger bisa kwatanta Mu'azzam wanda ya bani wasiyya tun kafin ya rasu.

Nayi tafiya na dawo lafiya bayan na cika mahaifinsa da abin arziki domin tun kafin in taho
sunsan da rasuwar Mu'azzam É—in. Bayin Allahn sun bani tausayi sosai mahaifinsa da Æ´an
uwansa mata waÉ—anda suke ciki É—aya, domin sun shiga damuwa sosai.
Mahaifinsa har na taho bai daina kuka ba, domin shi kaÉ—ai ne É—ansa namiji wanda yake
matuƙar so da ƙauna.


*Cigaban labari*


______da mugun sauri na farka daga nannauyan tunanin dana daɗe ina yi, jikina har ɓari yake
nayi wankan na fito.


Wajen Ammi na fara zuwa saboda dama ta ce tana nema na.


A babban falonta na same ta, ita da wata mata ban wani tsaya ba na wuce zuwa saman bene,
saboda yana yin tunanin danayi É—azu ya dawo mun da komi daya wuce, mutuwar Mu'azzam ta
dawo sabuwa fil azuciyata.

Abakin rantsatstsan gadonta na zauna, duk jikina asanyaye saboda Ni mutun Ni ne masifar

saka damuwa araina.

Ta ɗan daɗe kaɗan a kaina, tana nazarina sannan ta ƙaraso cike da kuzari ta zauna kusa dani,
uwa kenan ita kaɗai ce take gane yanayin damuwar zuci da ta fuska, sai da ta ƙaremin kallo
sannan ta ce

"Haidar
Wani abu na damun ka ne"?.


"Babu komi Ammi".

Daga nan ban ƙara magana ba, itama taja bakinta tayi shiru domin kuwa tasan ba lallai ne in
ƙara magana ba.

"Haidar don Allah inason ka rage damuwar da take damunka, duk fa bawan da ka gani a gidan
duniya da irin ƙaddararsa kuma haka yake amsar ta ayadda tazo masa hannu bibbiyu, amma
sam Haidar baka cikin bayin da suke da yarda da ƙaddara, ka zama me yarda da ƙaddara me
kyau ko mara kyau idan kaga rayuwar wani sai ka tausaya masa, saboda ƙaddararsa ta
munana amma ahaka ya karɓe ta saboda ya samu ya tsira kuma ya dace, yarda da ƙaddara
yana É—aya daga cikin shika shikan musulunci, bawa baya cika na kwarai har sai ya kasance me
yarda da ƙaddara, Haidar ban taɓa zama na baka labarina ba shiyasa bakasan wahalar
danasha a rayuwata ba, amma lokaci da zai zo da zan bayyana maka asalin Ni wacece sannan
kaima kasan Asalinka".


Har lokacin bance mata komi ba, taja nunfashi alamar tanason yimin magana domin duk lokacin
da kaga Ammi taja nunfashi akwai Magana me muhimmanci da take son yimin.

Wasu hotuna ta ɗakko kamar diary, ta miƙomin gami da ce wa" karɓi ka buɗe ka gani".

4 / 13