'DAN HALAK Book Complete (By ummu maher)miss green.pdf

Author :  Ummu Maheer Miss Green Category :  Thnovels

Chapter   6 / 13

15K to 18K   out of 37.7K words

kizo har falona kice zaki cimin mutunci"?.

"Ameera tayi wani gyatsine gamida gyara tsayuwarta, sannan ta ce" ni ba Æ´ar kowa bace amma
ina da Allah domin shiya halicceni kuma yake sona, kinga kuwa ina sa babbar katangar da babu

wanda ya isa ya wulaƙantani duk kuɗinsa kuwa".

tana tsananin huci ta É—aga hannu da niyyar kaiwa Ameera mari, da muguwar azama Ameera ta
riƙe hannunta abinka da jikin yarinta sai ga hannun Hajiya babba agefe, Ameera ta nuna ta da
yatsanta ta ce" talaka suna ya tara kada ki É—auka ina É—aya daga cikin waÉ—anda kika saba
wulaƙantawa rayuwa, na faɗa miki baki isa ki wulaƙantani ba tunda dai ina da Allah, sannan
inason faɗa miki gaskiya ruwanki ki ɗauka ruwanki kiƙi ɗauka domin ba matsala ta bace,
matsalarki ce kuma nan gaba ke zata dama ba Ameera ba.



"kinga wannan Æ´ar ta ki"?.


ta nuna Tasleem wacce take tsaye, tanaji kamar ta shaƙo Ameera ta zauna kanta amma ko da
me kurna tafi magarya zaƙi domin whtsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa Ameera ta fita komi, jiki
tsayi yanayin ƙarfi da kuma manyan gaɓɓai na ƙira, saboda haka yasa ta ɗaga mata ƙafa banda
haka da tuni ta dilmiya kanta ƙasa domin ba zata ɗauki wannan rashin mutuncin data zo dashi
ba.


"ki tabbatar kin koya mata tarbiyya kafin ta shiga É—akin miji, domin wallahi ko nice na miji bazan
taɓa auren lalataciyyar yarinya irin taki ba, domin kowanne namiji da kika gansa yana son
yarinya me hankali, ba mara mutunci ba wacce batasan darajar kowa ba".

tana faÉ—ar hakan ta janyo hannuna, tamkar Æ´a da uwa ni kuma na bita muka tafi nayi saurin
juyowa don inga halin dasu Hajiya babba suke, suna tsaye sai huci suke suna wani irin kallo
tamkar zasu haɗiyi maita ita kuma Iya Abu tana raɓe a gefe tana zubar da ƙwallah.

Kai tsaye gida muka nufa, babu wanda ya cewa ɗan uwansa ƙala saboda kowa da tunanin da
yake acikin ma'ajiyar sirrinsa wato zuciya.


Acan gidanmu kuma ƙofar gidanmu ne cike da mutane, wanda ya sanyamu saurin ƙarasawa
domin ganin abinda ya faru.?????


Baba Kande ce da kishiyar Ummanmu, sai kuma Ummi wacce naga tana wani irin kallo tamkar
zata ari bakin kare ga rigarta tun daga sama har ƙasa a yage kana hango zararan cinyoyinta
farare ƙal, dama duk sun fini haske ni ce ma ba wata fara ba.

da sauri muka ƙarasa, Ummi tana ganinmu ta ƙaraso da gudu ta rungumeni, sannan ta fashe
da kuka tana manne dani tamkar za'a ƙwaceni daga jikinta.

tausayinta ya kamani, duk da bansan me ya faru ba? amma hankalina yayi matuƙar tashi sosai
domin ina matuƙar son Ummi domin yarinyar tafi Ameera sauƙin kai, sai dai fa itama ba tada
haƙuri ko kaɗan kamar jira take ka taɓata yanzu kaji maganganu masu dukan zuciya.


ɗan dukan bayanta na hau yi ina bata haƙuri bakida lallashi nake bata saboda naga yadda take
haÉ—iyar zuciya, ta shiga bani labarin abinda ya faru tana kuka.




_BABA KANDE_


Ummi ce ta shigo gidan da jakar islamiyya akafaÉ—arta, tana shigowa ta ajje jakarta sai taga
bama nan ta fito tsakar gida domin haɗa kan ƙannai na su tafi nemanmu, dama kuma duk inda
mukaje nida Ameera in har mu biyu muka tafi to duk inda muke sai sun nemomu har sun saba
da hakan ma.
wani yaro ne ya shigo ya ce" wai ana sallama da wadda ta shigo yanzu".

Baba kande tana ƙofar ɗakinta tayi saurin ce wa" kai yaro zo, waye ɗin yake sallama da
wannan ƙwailar wacce batafi shekara goma sha shida ba?".

Yaron ya ce" wanine yana ƙofar gida cikin wata babbar mota, me kuɗi ne sosai nima ɗari biyar
ya bani yanzu wai in kira masa yarinyar da ta shigo gidan nan yanzu".

wata uwar ashar ta mulmulo sannan ta ce" to uban me zai ci da wannan fugigiyar yarinyar me
irin jikin uwarta? kace masa ba nan gidan take ba........."

Ummi ta ce" je kace ina zuwa, ai ba zaman wani nake ba zaman uwata nake da Æ´an uwana
sabofa haka babu wanda ya isa ya hanani fita ai inda ba ƙasa nan ake gaddamar kokawa".

tayi saurin É—aukar figigin mayafinta ta fira sai huci take, domin dama takeso ta dama da ita ta
samu lokacin zane Baba Kande kan shisshigin da take mata, batasan daman haushinta take ba
dangane da ƙuntatawa mahaifiyarta da akeyi agidan.



tana fitowa ta hangosa cikin motarsa, kyakkyawane sosai amma ba fari bane amma yana da
sikin me mugun ɗaukar hankali da kuma sheƙi, kana ganinsa ba sai an faɗa maka ba kasan
dukiya ta samu gindin zama awajen, sannan ba wai yaro bane a ƙalla zai yi 45 a ƙiyasi.

haka kawai gaban Ummi ya yanke ya faÉ—i, sai take hango wata kama a idaniyarsa amma sam
ta manta wacce kamar ce, sannan kama da wanda take tunanin ta sansa na kusa da ita ne idan
ta É—auro ma tana ganinsa kullum amma Allah baisa ta tuna waye É—in ba.

Ganin ta kasa ƙarasowa ya ce" ƴammata ƙaraso mana".

daga can Ummi ta tsaya, kunyarsa ta cika mata ciki amma saboda tana ganin cika mata idon
da yayi ta kasa ƙarasawa ta fara tafiya ahankali har ta ƙarasa bakin motar duk jikinta asanyaye.

Yayi murmushi sannan ya ce" in fito ko? nasan abinda yasa kike tsorona ganina acikin mota to
bari in ƙaraso".

ya fito kansa tsaye idonsa akan Ummi, yarinyar da ta sace zuciyarsa cikin mintunan sa basufi
É—aya ko biyu ba, daga zuwa super market na bakin titi siyayua yaga Ummi zata tsallaka titi,
shikkenan yaji ta ƙwanta masa ya biyo ta, duk da Ummi sa'ar ƴarsa ce ta fari amma babu yadda
zaiyi tunda haka Allah ya ɗora masa, kuma bawa baya kaucewa ƙaddararsa banda haka da tun
kallon farko ya haƙura da ita tunda ƴar cikinsa ce, amma ya kasa haƙura har sai daya zo inda
take yaga gudansu, kuma baiso ya fara magana da ita ba har sai ya nemi izinin mahaifinta
amma yana ganin bazai iya haƙura ba tare da sake sanyata a idonsa ba har sai wani bayan
lokaci wanda shi ayanzu so yayi masa mugun kamu.


kallon yarinyar yake tamkar zai kamota ta zama tasa alokacin, amma babu yadda zai yi domin
shi gani yake ba lallai ne ma yarinyar ta auresa ba.......

*_WELCOME TO UMMU MAHER BUSINESS CENTER_*
_____¥¥¥¥¥¥¥

*TIME TABLE NA KOYON SANA'A*

CLASS 1👇🏻
____________

*KOYON MAYAFI NA BEAD WORK BEAD WORK*
*MAYAFI NA STONE WORK*
*HULUNA*
*RIGUNA*
*FANTIS*
*WANDO JEANS*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800

CLASS 2👇🏻
______________
*INVITION CARD*
*3d logo*
*3d mockup*
*3d render*
*Cover book*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800

CLASS 3
_________
*Turaren wuta*
*Humrah*
*Gyaran jiki*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 1k

a tuntuɓi ummu maher ta lambarta👇🏻
07068606171

*DOMIN SHIGA WHATSAPP GRP ƊINMU👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/CMlWt3cUVvkDAXPthThNQx
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN)🍃: *_�ƊAN HALAK�_*



MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MISS GREEN)🍃_*

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION📚_*

~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159

~*Wattpad*~
D'AN HALAK
https://www.wattpad.com/story/368199708?utm_medium=link&utm_source=android&utm_conte
nt=story_info

10

_____"nasan baki sanni ba ƴammata, amma kiyi haƙuri ki yafemin idan har na shigar miki
lokacinki babu yadda zanyi ne, shiyasa har hakan ta faru dafatan abin bai sosa ranki ba"?.

ÆŠaga kai tayi, lokaci É—aya kunyar bawan Allahn da ganin girmansa suka shige ta, sai ta jiyo
muryarsa yana ce wa" Æ´ammata nazo wajenki ne akan wani lamari duk da bana tunanin
ƙwaƙwalwarki zata iya ɗaukar darasina, amma da sannu yaro ke rarrafe har ya fara tafiya kuma
da sannu ƙaramar bishiya ke girma har ta kai ga cika waje, ban sanki ba ban taɓa ganinki ba
amma Allah ya ɗora jarabar sonki cikin lokaci ƙanƙani".

suna cikin maganar ne Baba Kande ta leƙo tana sababi, har tana tsinewa Ummi wai ta zama
karuwa tana janyo maza.daga nan ta fara dukanta har tana yaga mata riga. mutumin yana bata
haƙuri amma taƙi haƙura ta dinga zaginsa har sai da ta koresa ya tafi domin tana son haɗa
masa wani sharrin, shi kuwa ya wuce da sauri ba don yaso ba, domin har ya tafi bai daina
kallom Ummi ba kana ganin fuskarsa kasan tausayinta yake ji.


*Cigaban labari*

na ƙara rungume Ummi sosai ajikina, yadda take kukan bilhaƙƙi haka zuciyata ma take bugawa
da gaske, domin da gaske bana son duk wani abinda zai taɓa ƙannai na, yadda nake sonsu
bana son kai na haka.

Baba kande tana ta maganganunta na ɓacin rai, babu wanda ya kulata domin har Ameera ta
shiga gida abinta domin daman da wata aƙasa, biyo bayan abinda ya fari tsakaninta da Hajiya
Ƙarama, wanda agefen zuciyata nima ya maƙale yaƙi fita domin nasan ba zasu yarda ba, kuma
aikin Iya Abu nasan ya lalace haka zalika aikin Ummanmu ma ya lalace asara goma da ashirin.

Allah ya taimakemu Babanmu baya nan, saboda haka yanzu shawara muka cigaba da yi ta
yadda za'ayi mu biya kuÉ—in asibiti.

Ihun Fahad ne ya katsemu daga shawarar da mukeyi, duka atsorace muka kallesa ya ƙaraso
da gudunsa kan cinyata ya miƙomin ƴan bandir ɗim kuɗi.

Na waro ido waje domin sanin wanda ya basa, da ido nayi masa tambayar wa ya basa?.

"Antinmu wani ne ya bani, ya ce wai in bawa Anti wai ince mata wanda yazo É—azu ne".

Da sauri Ummi ta kallesa har tana haÉ—e harshe wajen ce wa.

"me....me.... wanda..yazo É—azu dai"?.

Yaron ya É—aga kai.

Godiyq muka shiga yiwa Allah, daya sa aka samu zunzurutun kuɗi haka wanda aƙalla za su kai
dubu ashirin ko su É—anfi ma.

Sai alokacin ne Amira tayi magana, cike da fara'a ta ce" oh Allah mungode maka Ummi ke me
sa'a ce wallahi yanzu kinga mun samu kuÉ—in da zamu kai asibiti a sallamo mana Ummanmu".

Tashi mukayi mu dukanmu muka shirya ƙannenmu muka ɗunguma zuwa asibiti, muka samu
adaidaita sahu har asibitin murna fal zuciyata domin da bamu samu wannan kuÉ—in ba da yaya
za'ayi kenan?.


muna zuwa kai tsaye na wuce wajen da aka tanada domin biyan kuÉ—i, na cake dubu ashirin na
bayar dubu biyar kuma na ajje a gefen zanina dama kuɗin da muka ƙirgasu dubu ashirin ne da
biyar.
Dama kuma kuÉ—in asibitin dubu ashirin ne.

Sosai su Ummi suke murna, saboda ganin mahaifiyarmu cikin ƙoshin lafiya ga ƴan biyunta duk
maza farare ƙal ƙal kamar Ameera domin ita duk ta fimu fari.

Umma ta tsuramin ido tana kallona, hankalina ya tashi sosai na ƙarasa kusa da ita domin jin
laifin da nayi mata, ko domin na daÉ—e ne dana fita? ko kuma wani abun ne dai?.

na durƙusa gabanta, gamida riƙo ɗan yatsanta babba na ce" Ummanmu lafiya kuwa? ko dai
wani laifin nayi ne ban sani ba? idan ma laifin nayi Umma ayafemun domin darajar Æ´an biyu
masu farar fuska".

Dariya mukayi mu dukanmu, sai Umma ta ce" to na haƙura Humaira h amma a ina kika samo
kuÉ—in da kika biyamin kuÉ—in asibiti"?.

Caraf Ameerah ta ce" Umma wani ne ya bada kuÉ—in, wai yaga Ummi yana sonta to akan hakan
nema akayi faÉ—a da Baba kande har ta yagawa Ummi riga, bayan mun dawo gida shi ne ya aiko
da waÉ—annan kuÉ—aÉ—en, dama kuma muna ta neman hanyar da zamu samu kuÉ—in mun rasa to
sai yanzu Allah yasa aka samu, don har gidan DEEN MARSHAL munje amma bamu samu
kuÉ—in ba, harma mukayi faÉ—a da Hajiya Babba".

Da sauri Umma ta kalli Ameerah ta ce" me yasa kuka je gidan? kunsan wacece Hajiya babba
kuwa? kunsan ƙarfin ikonta agidan? to ko uwar me gidan ce tace akora za'a kore ta, sannan ni
ayanzu haka ma nasan ba barinmu za tayi ba, dalili da meyasa bakyason zaman lafiya
Ameerah? ina yawan faɗa miki rayuwa bata yiyuwa sai da haƙuri, kayi haƙurinma ya ka ƙare

ballantana akasin haka? sannan ga wannan abin da ya faru na Ummi".

ta kalli Ummi wacce kanta yake asunkuye dom kunya ta ce" Ummi shin kinsan mutumin ne?
kuma tun yaushe kuka haÉ—u"?.

"Umma wallahi ni bansanshi ba, kuma sau ɗaya na taɓa ganinsa yau kenan amma ban taɓa
ganinsa ba amma dai yana yimin kama da wata fuska wacce na santa amma na rasa fuskar
waye"?.

Umma ta É—aga kai, sannan ta ce" to duk sanda ya ganki ya tsayar dake kice yazo ya samu
mahaifinki kinji"?.

ta É—aga kai alamar taji.

Ameerah ta ce", uhum Umma wallahi kina da haƙuri yanzu duk abinda Babanmu yake miki
bakya gani? har kike son wani yazo ya gansa daganan ya lalata lamari duk da Ummi yarinya ce
amma ai ana aurar da yara ashekara 15, tunda babu wanda zai ce hakan saɓon Allah ne, ko
don ƴan baƙin ciki ai dole a yardar masa ya turo kawai ayi, muma Allah ya zaɓa mana abinda
yafi alkhairi".


"Ameerah koma dai meye mahaifinku ne, sai haƙuri kuma ba'a hannuna neman aurenku yake
ba a hannunsa yake saboda haka ko inaso ko bana dole ne a nemi auranku a wajensa, uba
ubane koda kuwa a turu aka cirosa".



Ameerah dai don haushi bata ce komi ba, ni ce ma na ce" hakane Umma Allah ubangiji ya
ganar da Baba".

Duka suka amsa da amin.


Bayan an sallamo Umma, mun fito da taxi muka hango ƙofar gidanmu cike da mutane
damƙam...............


$$$$$$

Haidar ya É—aga wayar tamkar bazaiyi magana ba sai kuma ya amsa.

"ina jinki"?.

Hanan taÉ—an daidaita muryarta sannan ta ce" ka kuwa gane ni?".

Ya basar ya cigaba da aikinsa saboda sam bayason yin waya da kowa ayanzu saboda shi
kaÉ—ai yasan halinda yake ciki, wanda kuÉ—i ko mulki ba zai iya bayarwa ba domin ayanzu haka
aƙwance yake yana fama da ciwon cikin dake azalzalarsa wanda yake motsa masa duk bayan
wani lokaci, wanda likitoci suka tabbatar masa rashin aure ne ya janyo masa.

Hanan taÉ—an dakata da magana, saboda taji kamar yana cikin wani yanayi ne saboda haka ta
ce" kayi haƙuri bansan kana cikin wani yanayi ba, ko zan iya taimaka maka da wani abun?".

bai katse kiran ba, kuma bai ce mata ƙala ba saboda haka har Hanan ta gama maganarta bai
san abinda take cewa ba.

Da ƙer ya lalubo lambar Hammud, bugu ɗaya ya ɗaga yana jin yanayin aminin nasa hankalinsa
ya tashi sosai da sauri ya sanya jallabiyyarsa ya fito daga ƙerarran gidansa wanda ya gamasa
ƙwanannan.



***
Yana zaune gaban likita, yayi shiru yana jin dukkanin bayanansa har ya kai ƙarshe Yana kallon
yadda hankalin Hammud ya tashi sosai.

"likita yanzu meye mafita?".

Cewar Hammud wanda baki É—aya hankalinsa yake atashe.



likitan ya gyara farin gilashinsa sannan ya ce" solution dai É—aya ne yayi aure domin wannan
matsalar tasa babu wani magani ko tablet da zamu basa yayi masa magani kawai dai gwara
yayi haƙuri ya daure yayi auren shi ne magani, sannan kada ya daɗe ahaka ba tare da yayi
auren ba komi zai iya faruwa".
Hammud ya kalleni, na rintse idona inajin wani irin suya araina.


Hammud ne ya kamani muka fito, dai dai wani ɗan desk naso faɗuwa yayi saurin ruƙoni yana
ce wa" sannu Haidar kayi ahankali".

Hammud wannan wata irin ƙaddara ce? anya kuwa zan iya jure wannan ƙaddarar? ace ina da
lafiya ta da komi Allah ya horemin komi na rayuwa amma Allah bai sanya nayi aure ba, saboda

wani dalili wanda aka shafamin kashin kaji, idan ma laifina dana zo duniya ne ai ba ni na aikata
laifin ba, sannan Allah ne yaso inzo ta wannan hanyar"!!.

na faɗi maganar tawa cikin ƙaraji.

Hammud ya ce" kash! Aminina bai kamata adingajin wannan kalaman masu muni daga
bakinka ba, kamata yayi ace ka mayarda komi ba komi ba ka cigaba da addu'ah komi yayi farko
yana da ƙarshe kuma in sha Allah komi zai zama kamar ba ayiba, kuma auren ma ƙwanannan
zaka yisa in sha Allah".
Haka dai ya dinga rarrashina har muka dawo gida, allurar da suka yimin ta fara ratsa ƙwanyata,
barci me nauyi yayi awon gaba dani.





_HANAN_


wani malolon baƙin cikine ya kusa kasheta atsaye, wannan wani irin ɗan rainin hankalin namiji
ne? ace da ranta da lafiyarta namiji yana wahalar da ita? gaskiya doleta ta samowa kanta
mafita, tun kafin gari ya waye mata.

Yayarta Asabe ta kira, kirab farko ta É—aga tayi mata bayanin komi.

Yaya Asabe ta ce" aikin banza aikin hofi au dan ɗan wannan ƙaramin alhakin shi ne kika tada
hankalinki?"............................


*_WELCOME TO UMMU MAHER BUSINESS CENTER_*
_____¥¥¥¥¥¥¥

*TIME TABLE NA KOYON SANA'A*

CLASS 1👇🏻
____________

*KOYON MAYAFI NA BEAD WORK BEAD WORK*
*MAYAFI NA STONE WORK*
*HULUNA*
*RIGUNA*
*FANTIS*

*WANDO JEANS*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800

CLASS 2👇🏻
______________
*INVITION CARD*
*3d logo*
*3d mockup*
*3d render*
*Cover book*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800

CLASS 3
_________
*Turaren wuta*
*Humrah*
*Gyaran jiki*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 1k

a tuntuɓi ummu maher ta lambarta👇🏻
07068606171

*DOMIN SHIGA WHATSAPP GRP ƊINMU👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/CMlWt3cUVvkDAXPthThNQx

UMMU MAHER
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN)🍃: *_�ƊAN HALAK�_*



MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MISS GREEN)🍃_*

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION📚_*

~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159

~*Wattpad*~
D'AN

6 / 13