Author : Ummu Maheer Miss Green Category : Thnovels
Tamkar raƙumi da akala haka na buɗe, na fara cin karo da hotunan kyawawan y'ammata,
waÉ—anda suka amsa sunan su kuma daga ganinsu ma yaran masu shuni da hannu ne domin ko
kusa babu É—igon talauci ajikinsu.
Tun ban gama ba na ce" Ammi wannan kuma fa"?....
Tun kafin in ƙarasa ta ce "cigaba da dubawa dai ina ganin akwai wacce zata yi maka cikinsu".
Wani mugun malolon baƙin ciki ne ya tsaya min, wato har na kai lokacin da za a dinga min
tallan mata? Raina ya ɓaci amma saboda mahaifiyata ce babu yadda zanyi.
Na tashi tsaye, gami da zuba hannuna cikin aljihu na juya bayana sannan na ce" Ammi shi
aure da mutuwa lokaci ne, banason auren macen da banaso, domin shi aure ba a yiwa É—aya
tilas kiyi haƙuri Ammi amma babu wacce tayimin a cikinsu".
Ban ƙara tsayawa ba na fito kai tsaye direbana ya buɗe min mota na shiga zuciyata na yimin
wani irin tururi yanzu har lokacin tallah na agari yayi? Wata ƙila ma Ammi ce ta bawa wacce ta
kirani jiya lamabata, sam zuciyata ba daÉ—i asalin Haidar É—ina ya bayyana sak a fuskata..........
$$$$$$
Tare muka tafi Ni da Amira gidan da Umma take aiki, da ƙer me gadin gidan ya bar mu muka
shiga kai tsaye muka wuce wajen masu aikin gidan.
Iya Abu muka tarar tana girki akicin, muka gaisheta sai ƙara kallon gidan nake saboda tsabar
kyawunsa da tsaruwarsa abin sai wanda ya gani, kicin kamar aljannar duniya.
Bayan mun gaisa take tambayar mu mahaifiyarmu ta haihu kuwa?.
Muka bata amsa da eh ta haihu, amma tana asibiti babu kuÉ—in sallama.
Jikinta yayi sanyi ta ce" kai Allah ya tsinewa wasu mazajen wallahi, sam ba suda tausayi bare
imani, yanzu ace matarka tana asibiti amma saboda tsabar salalan tsiya ka kasa biya mata
kuÉ—in asibiti? Kai Allah dai ya gyara wallahi, shiyasa na kashe auren nayo nan saboda mutanen
gidan nan akwai kirki wallahi ba dai ka nemi abu ka rasa ba, yanzu dai bari inje in faÉ—awa
Hajiyar nasan za a dace in Sha Allah".
Tana shiga cikin gidan muka fito daga babban kicin É—in wanda yake manne da babban falonsu.
Muna fitowa Amira ta shiga kallon gidan, tana riƙe da haɓarta tana santi na dungureta ta dawo
hayyacinta da sauri.
Ta ce" ayyah anty wallahi gidan nan kullum kamar ana ƙara masa kyau, dubi fa yadda aka
canja masa wani hamshaƙin fenti tamkar gidan y'an katun"?.
Muna haka Iya Abu ta fito jikinta duk asanyaye, Ni kuwa cikina sai kaÉ—awa yake saboda
bansan me ya faru ba.???
_IYA ABU_
Kai tsaye wajen Hajiya babba tayi, saboda Hajiya ƙarama bata nan itace amarya kuma tana da
kirki sosai saɓanin Hajiya babba, sam bata san darajar mutane ba da ita da yaranta ba suda
mutunci yadda suke murza talaka tamkar lokacin murza bayi..........
*Ayi haƙuri jina shiru, na canja wayane sai danayi settling ɗin komi*
UMMU MAHER CE
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN)í ¼í½ƒ: *_ÆŠAN HALAK_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MISS GREEN)í ¼í½ƒ_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATIONí ½í³š_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
*~Wattpad~*
D'AN HALAK
https://www.wattpad.com/story/368199708?utm_medium=link&utm_source=android&utm_conte
nt=story_info
8
________ Tasleem ce a falon Iya Abu sai sallama take amma ta maishe ta banza, abun ya
ƙuntata ran iya har batasan lokacin da ta ce" Haba Tasleem ko baki sanni ba ai kya amsa
sallama ta ko? tunda na fito daga tsatson musulunci........"
Tun kafin ta ƙarasa kalaminta tayi saurin miƙewa, da wayarta tankamemiya a hannu ta yiwa Iya
wani kallo sannan ta watsar ta ce" ke har kin isa in amsa sallamarki? ke wacece? me kika taka
aduniya da har kika isa ni Tasleem Marshal in amsa sallamae baiwa ƙasƙantacciya irinki?, To
idan ma mafarki kike ki farka domin ni da kike ganina nafi ƙarfin banza kiyashi ƙaramar alhaki in
amsa sallamarki, kiriminal kawai ƴar ƙauye kuma zan tambayi momi zaman uban mi kike
agidanmu da kike ganinmu É—aya dake".
Iya Abu ta sunkuyar da kanta, ta kusa daskarewa awajen saboda tsabar tashin hankali, tunda
take aduniyarta babu wani mahaluƙin daya taɓa yi mata wannan mummunan zagin irinta, tunda
take ba'a taɓa faɗa mata maganar da ta kusa tarwatsa ƙwanyarta irin maganar da Tasleem ta
faɗa mata ba'a taɓa faɗa mata kamar wannan ba, gaskiyar hausa da suka ce me ƙwaɗayi shi
yasan gidan me rowa, banda haka ina Tasleem ina zaginta da batazo gidansu da sunan aiki ba
da bata zage taba.
Dai dai nan Hajiya Babba ta fito, cikin shirinta tsaf na tafiya aiki da yake alƙaliya ce, taci uban
gashin atach tamkar wata asalin baturiyar ingila, da yake gashin ba me kalar baƙi bane irin me
haske ne ja kamar na turawa.
gashi taci uban glass me kalar fari kamar ruwa, ƴar ƙaramar jakarta a hannunta yadda kasan
wata budurwa ƴar shekara 18 saboda tsabar son zuciyarta ko takalmin ƙafarta ya isheka gane
budurwar zuciya ce da ita.
Ganin autarta Tasleem a wani yanayi yasa ta cire gilashin fuskarta, tana wani firfito da idanuwa
tamkar taga abin tsoro domin arayuwarta ta tsani ganin yanayin Tasleem ya canja, ko da kuwa
ciwo take to fa sai kaga hankalinta duk yabi ya tashi saboda tana masifar sonta cikin yaranta.
"Babyna me ya faru? Uban waye ya ɓata miki rai"?.
Tasleem ta dallawa Iya Abu harara, sannan ta ya mutsa fuska ta ce" Momi wai uban waye ya
bawa wannan matar damar aiki agidan nan"?.
da wani irin sauri Iya Abu ta kama hanya zata arce, domin Allah ya sani tana masifar son
aikinta bata son abinda zai taɓa aikinta.
Wani kallo ta yi mata sannan ta dakawa tsohuwar wata gigitacciyar tsawa.
"Ke!!!!!!!!!".
da mugun sauri ta dawo, yadda hanjin cikinta ya kaÉ—a tuni taji gudawa na neman zubo mata, ta
rikice tayi saurin tsugunnawa sannan ta ce" Allah yaja da ranki ayimin afuwa, wallahi sallama
nayi bata amsa ba nayi mata magana to fa shi ne ranta ya ɓaci, amma don Allah don annabi
domin sonki dana iyayenki ki yafemin kada ki koreni daga aiki".
Wani banzan wulaƙantaccen kallo ta bita dashi, sannan ta ce" wallahi yau ɗinnan zaki bar
gidan nan uban wa ya faɗa miki ana ɓatawa autata rai? Yar uban wacece ke da zaki takurawa
ƴata? saboda waccan mahaukaciyar kucakar matar ta ɗaukeki aiki shi ne zaki zomin ɓangare ki
dameni? To bari uwar Æ´an karanbanin ta dawo, zan faÉ—awa Alhaji komi idan yaso ta zauna
babu me aikin, Haba wannan masifa da yawa take an auromin mata tunda jajayen sahuna ba'a
barni ba, tsinanniya masu shiga su fita da asirinsu na buzaye".
Haka dai tayi ta yin maganganunta, har daga bisani ta sanya Iya Abu bawa Tasleem haƙuri.
taƙi haƙura wai har sai ta dafa ƙafafuwanta sannan zata haƙura, iya tana kuka ta dafa ƙafarta
tana bata haƙuri sa'ar jikokinta amma take dafa ƙafarta tana bata haƙuri saboda ita talakace su
kuma masu kuÉ—i.
ahaka ta tashi jiki ba nauyi, tana share hawayenta da gefen zaninta, domin cin mutuncin ya kai
cin mutunci amma duk da haka cewa take sai ta wulaƙantata sai ta kore ta daga aiki.
_HUMAIRA_
Tsananin fushi da aman wutar da take cin zuciyata Allah kaÉ—ai yasani, saboda labarin da Iya
Abu ta bamu yanzu na ci mata mutunci da sukayi, sosai raina ya ɓaci har na gaza ɓoyewa na
ce" amma waÉ—annan mutanen bazasu ga annabi ba, ace don suna da kuÉ—i su dinga murza
mutane son ransu Allah ya wadaran naka ya lalace, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu".
Suka amsa da amin.
Saboda tsabar ɓacin rai Ameera bata gama saurararmu ba ta fice fuuu, daman nasan duk
zuciyata ta dameni da ita da Ummi zuciyarsu har mamaki take bani domin ita idan zuciyarta ta
motsa bata iya gane waye agabanta waye abayanta, sannan idan Amira ta saka ƙafar wando
É—aya da kai ko magana baka isa tayi maka ba.
Hayaniya naji muka fito da sauri.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN".
Ganin Ameera nayi tsaye a bakin babban falonsu wanda zai sadaka da mutanen gidan, ta riƙe
ƙugu tana ta ruwan ashar da bala'i tana masifa idanuwanta arufe bata ganin na gabanta dana
bayanta.
Jikina amatuƙar zafafe na ƙarasa kusa da ita ina riƙe ta, amma ina sai da ta sada kanta har
cikin babban falon da yake irin me gilas É—in nan ce,nan da nan ta buÉ—e da kanta ta shige tana
ihu tana zage zage.
Ni dai da Allah zaisa in kama Ameera sai na naÉ—a mata na jaki, domin naga alamar so take ta
janyo mana masifa tunda gashi tana son taɓa masu hannu da shuni, waɗanda ubansu idan
baizo na farko a masu kuÉ—in nigeria ba zai iya zuwa na biyu.
Hajiya babba tana tsaye inda Iya Abu ta barta, tana rarrashin autarta Tasleem. kamar daga
sama suka hango Ameera tamkar mahaukaciya, dukkansu sunyi matuƙar mamakin ganinta
gamida tsorata, saboda harga Allah sun É—auka mahaukaciya ce ashe me hankali ce abu É—aya
ya ɓata mata rai yadda suka wulaƙanta Iya Abu, domin ko kai waye indai Ameera tana kusa ka
wulaƙanta wani musamman ma talaka to fa sai inda ƙarfinta ya ƙare.
"wacece Hajiya babba acikinku"?.
ta hau nuna su da yatsanta, ni kuwa sai janta nake ina rufe mata baki, tana yarfar da hannuna
saboda dama ta fini jikin girma ni yadda kasan a hure ni haka nake.
Tasleem ce ta matso sosai tana mata kallon mahaukaciya ta ce" hey! who are u? are u mad"?.
wani dallelen mari Ameera ta bata sannan ta ce" hey! criminal, ba dake nake ba alamu sun
nuna ba ke bace waccan guzumar ce".
ta nuna Hajiya babba wacce ta tsorata sosai da marin da aka yiwa Æ´arta, idanuwanta suka
firfito za tayi rashin mutunci ta tunkaro Ameera gadan gadan tana wani irin huci tamkar farar
wuta..........
_HANAN_
Sosai ta ƙurawa hoton Haidar ido, har tana mamakin yadda zuciyarta take tsananin bugawa
idan tana kallonsa, lallai sai yanzu ta gasgata rashin hankalin Saleema da ta kasa gane irin
baiwar da Allah ya yiwa Haidar, namiji acikin maza namijin daya haÉ—a komi uwa uba kuÉ—i,
gaskiya dole ma ta ƙwacewa Saleema Haidar ko anaso ko ba aso dole ma ta ƙwace mata shi,
domin idan ta bari akayi wannan auren mutuwa za tayi, domin Allah ya sani ahalin yanzu ta
tsani buÉ—e ido taga Saleema ita da Saleemar ma zata mutu da kowa ya huta.
ƙarar buɗe ɗakinta taji, da sauri ta mayar da wayarta ta ƙwanta harda jan minshari domin
tasan ba kowa bane wanda ya wuce mahaifiyarta domin bataji shigowarta ba kuma bata faÉ—a
mata ta dawo ba, tunda tasan dama ba nisa tayi ba bazata wuce wajen Saleema ba tunda duk
gisa É—aya suke gidan sarauta, amma sai ka É—auka unguwarsu ma dabance amma duk agida
ɗaya ne, banbancin dai shi ne su sun fita dabanne agidan tun bayan da wani ɓoyayyan al'amari
ya faru.
tana jin wucewarta tayi saurin É—akko wayarta, ta danna lambar Saleema sai da ta kirata sau
wajen uku sannan ta É—aga.
Alamar tasha kuka ta gaji, jin muryarta yasa Hanan yin kalar tausayi tamkar dai tana gabanta ta
ce"haba Saleema kar dai kice min haryanzu kukan nan kike? Ni banason ganinki cikin damuwa
don Allah, damuwarki tana hanani sukuni ki gane ki daina don Allah".
daga can taja ajiyar zuciya sannan ta ce" ayya! Hanan bazaki gane irin son da nakewa Haidar
ba, inason with all my heart sona tsakani sa Allah, wallahi idan har ban auresa ba komai zai iya
faruwa dani".
"ki mutu mana".
Cewar Hanan azuciyarta, domin idan har ta mutun sai tafi kowa murnar hakan, ada dai tana
tsananin son aminiyartata amma ahalin yanzu kiÉ—a ya canja ya koma tsana sanadin gadanga
ƙusar yaƙi Aliyu Haidar.
da ƙer ta saita kanta sannan ta ce" Hanan kenan, ai ke kika rusa damarki ke da kanki da kikayi
bincike kin gano cewa babu kalmar da Haidar ya tsana sama da ace masa É—an shege, amma
saboda kinason ki ƙuntata masa kika faɗa masa kalmar da tafi masa zafi fiye da kowacce".
Saleema ta rushe da kuka, ta ce" Hanan idan ba damuwa gobe da safe kizo, inaso inje har
gida in bawa Haidar haƙuri saboda ni kaɗai nasan halinda nake ciki gashi me martaba ya
matsamin in fito da miji".
Hanan taɗan taɓe baki, sannan ta ce" haba Saleema wai me yasa kikeson aikata abinda zai
xama laifi ne? ina ke ina zuwa gidansu Haidar? Idan Memartaba yaji me zakice? Kinsan fa
bayason fita ba tare da an sanar dashi ba".
Shiru tayi tana tunani, sannan ta ce" to naji Hanan, yanzu me kike so ayi? Ni kaina ya kulle
wallahi, ga son Haidar na neman kaini lahira".
"ki bari gobe idan nazo aƙwai maganar da zamuyi dake me muhimmanci, kuma cikin sauƙi zai
yarda ya yafe miki laifin da kika yi masa".
bayan sunyi sallama, mahaifiyar Saleema uwae gidan sarki Abdussalam ta shigo.
Sosai ta ƙare mata kallo sannan ta ce" Saleema, wai me yake damunki ne? ƙwana biyun nan
bakya zama kan dining sam ko a falo bana ganinki, anya kuwa lafiya"?.
Kuka ta fashe dashi duk da dauriyar da take arowa, ta dinga yinsa babu kama ƙafar yaro
Fulani ta barta tayi kukanta me isarta sannan ta ce" Fulani, wallahi Haidar ne ya kasa gane
abinda nake nufi bisa binciken da Memartaba yayi akansa ya gano ba shida uba, ni kuma
wallahi inasonsa tsakani da Allah"........
Tun kafin ta ƙarasa ta galla mata wani irin kallon banza sannan ta ce" amma Saleema kin bani
mamaki, yanzu ke saboda rashin hankali É—an shegen kike son aura?.....................
*_WELCOME TO UMMU MAHER BUSINESS CENTER_*
_____¥¥¥¥¥¥¥
*TIME TABLE NA KOYON SANA'A*
CLASS 1í ½í±‡í ¼í¿»
____________
*KOYON MAYAFI NA BEAD WORK BEAD WORK*
*MAYAFI NA STONE WORK*
*HULUNA*
*RIGUNA*
*FANTIS*
*WANDO JEANS*
í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»
~Naira~ 800
CLASS 2í ½í±‡í ¼í¿»
______________
*INVITION CARD*
*3d logo*
*3d mockup*
*3d render*
*Cover book*
í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»
~Naira~ 800
CLASS 3
_________
*Turaren wuta*
*Humrah*
*Gyaran jiki*
í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»í ½í±‡í ¼í¿»
~Naira~ 1k
a tuntuÉ“i ummu maher ta lambartaí ½í±‡í ¼í¿»
07068606171
*DOMIN SHIGA WHATSAPP GRP ÆŠINMUí ½í±‡í ¼í¿»*
https://chat.whatsapp.com/CMlWt3cUVvkDAXPthThNQx
*UMMU MAHER*
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN)í ¼í½ƒ: *_ÆŠAN HALAK_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MISS GREEN)í ¼í½ƒ_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATIONí ½í³š_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
~*Wattpad*~
D'AN HALAK
https://www.wattpad.com/story/368199708?utm_medium=link&utm_source=android&utm_conte
nt=story_info
9
_______da sauri Saleema ta kalli Fulani mahaifiyarta, sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa
tabbas taji zafin maganar da ta faɗa akan Haidar, domin tabbas da wanine da sai inda ƙarfinta
ya ƙare, domin babu abinda ta tsana nab gidan duniya wanda ya wuce cin mutuncin burin
zuciyarta kuma sahibinta Haidar.
"ba dake nake magana bane? saboda an taɓo miki inda yake miki ƙaiƙayi dolenki kiyi shiru ai,
to ki buÉ—e kunnuwanki ki jini indai har ina raye baki isa ki auri wannan shegen yaron ba, ni ina
ruwana da kuÉ—insu? kuÉ—in da ba'a ginashi ta hanyar halal ba? ai daman ance can yawon
banzanta ta sameshi, saboda haka mu zuri'armu ba'a haÉ—a haram da halal yaje can ya samu
Æ´ar uwarsu shegiya amma ba Æ´ata ba, domin ke É—innan matar Æ´an gidan mutunci ce waÉ—anda
sukasan mutuncin mutane da kuma girma, amma ba Æ´aÆ´an terere Æ´aÆ´an kwalta ba".
Fashewa da kuka tayi, sannan ta ƙarasa gaban Fulani ta durƙusa gwiwarta duk a ƙasa ta dafa
ƙafarta ta ce"Mama Fulani don Allah don annabi kiyimin rai, ki ceceni don Allah ki taimaka ki
barni da Haidar, wallahi nayi muku alƙawarin kare mutuncin wannan masarautar, don Allah ki
taimakawa rayuwata rasa Haidar yana nufin rasa rayuwata ne baki É—aya, don Allah ki taimaka ki
barni dashi".
ta haɗa hannayenta waje ɗaya alamar ban haƙuri, amma ko kallo bata isheta ba daga bisani
ma ta hankaÉ—ata gefe tayi wucewarta.
sosai take kuka har batasan iya adadin hawayen da ta zubar ba, gani take tamkar ba Fulani ce
ta tsugunna ta haifeta ba, domin kuwa ayadda takeson Haidar ya kamata su gane halin da take
ciki.
da sauri ta É—akko wayarta tamkar mahaukaciya tana neman hotunan Haidar, ada can baya ma
hotonsa ne akan wayarta amma ayanzu ta ciresa ne saboda abubuwan da suka dinga faruwa
marasa daÉ—i.
ya subhanalillah, baki É—aya taji zuciyarta na tsinkewa gamida bugawa acikin lokacin da bai fi
sakan guda ba, jikinta yahau rawa saboda ganin hoton Haidar wanda yake ƙara mata wutar
mikin sonsa acikin ɓargon zuciyarta da ruhinta.
sai da tasha kukanta ta ƙoshi, domin babu wani mahaluƙin da zata faɗawa abinda yake
damunta sama ga sarki buwayi gagara misali, tunda uwar dama ta haifeta ta nuna bata santa
ballantana kuma wani?. tunda duk son da wani ko wata xai nuna mata bai ka ga na mahaifiyarta
ba.
ta ɗauro alwala tayi sallah raka'a biyu ta ɗaga hannayenta sama tana addu'ar neman zaɓin
ubangiji, domin ayanzu ta gane ba zaɓin mutum ne alheri ba, zaɓin Allah shi ne alherin ba zaɓin
mutum ba.
*******
ganin haka yasa tun kafin ma Hajiya babbar ta ƙaraso ita da kanta ta rage mata aiki ta ƙaraso,
tana wani cika tana batsewa ta nuna Ameera da yatsanta ta ce.
"ke Æ´ar uban waye da zaki shigomin gida