Author : Ummu Maheer Miss Green Category : Thnovels
gami da ce wa"shegiya ki mutu ma kowa ya huta gayyar tsiya, bara gurbi
kawai".
Kuka Mimi ta fara mai sauti, ga wani irin azabar da hannunta yake mata, abin ka da farar fata
nan da nan sai ta yi jawur tamkar ɗanyan nama. tasowarta har zuwa yanzu basu taɓa sonta ko
na second ba, ko da yaushe tsakaninta dasu sai hantara da zagi tamkar dai ba mahaifinsu ɗaya
ba. Kalmar da tafi ɓata mata rai ita ce uwarki ma ta ajje ɗan shege, sosai take jinta aranta ita
ma taji hakan? Ina ga yaya Haidar?. Innalillahi wa inna laihi raji'un, abin da ta dinga nanatawa
kenan ta tashi da ƙyar tana hawaye ga hannun har ya fara kumbura.
juyawar da za ta yi, sai ta yi saurin yin baya saboda tsoron ganin shi da tayi ta ƙwalalo idanuwa
waje tamkar za ta saki fitsari.....
MISS GREEN CE
SHARE
COMMENTS
07068606171
CHART NO CALL
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN): *_ƊAN HALAK_*
MALLAKAR
*UMMU MAHER(MISS GREEN)*
_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_
_AREWABOOK_
https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
_WATTPAD_
https://www.wattpad.com/story/368199708?utm_medium=link&utm_source=android&utm_conte
nt=story_info
Ina masu son shiga adashe Amma kuna fargabayar uwa ki tsarkake zuciyan ki kizo kiyi
adashe cikin aminci da kwanciyan hankali insha Allah Babu rigima ko tashin hankali kwanciyan
hankali zaki Yi adashen ki Kuma mu gama lfyh da yardan Allah..
30k weekly parking 300k
1)Haj Maryam✅
2)Ada umar/hafsat yahya✅
3)Usman
4) barrister hauwa'u
5)shafa bello/baby daura
6)
7)
8)
9)
10)
Akama slot
https://chat.whatsapp.com/HAkm8rINu8a0ouQsRmuDuL
*AYI HAƘURI, AN SAMU MATSALAR EDITING NE A WASU PAGES, AMMA YANZU AN
GYARA MUSAMMAN WAƊANDA SUKE KARATU A WATTPAD SAI DAI SU YI HAƘURI SU
CIGABA DA KARANTAWA HAKA.* NA GODE MASOYANA.
14
_MIMI_
________Ta faɗa da ɗan ƙarfi Ruhi me kake yi anan kuma?!".
Sosai yake kallon hannunta ganin ya kumbura ya ce"my baby me ya faru dake haka a
hannunki"?. Kallon hannun ta yi tana zubar da ƙwalla ta ce"su Nasreen ne da Tasleem wai akan
na zo kiran Hajiya". Ranshi ya ɓaci sosai kana hango hakan a idon shi har ma da fuskarshi,
danne ɓacin ran ya yi amma sam zuciyar shi babu daɗi, ya rasa wani irin so yake wa yarinyar
duk dama ta kasance ƙanwar amininshi dole dama ya so ta, amma duk da haka son da yake wa
Mimi ya yi yawa. Ba kunya ya janyo ta jikin shi yana ce wa "sannu my baby, dama naje sashen
Ammi ne shi ne tace min kina nan sai na biyo ki, sannu fatan baza ki faɗawa Ammi ba ko"?. Ta
fara kuka tamkar yarinyar goye tana ce wa"Allah Ruhi sun tsane ni, na rasa me na yi musu
wallahi kullum cikin yi min mugunta suke musamman ma Tasleem ta tsaneni, nasha kulle ɗaki
na yi kuka saboda cin kashin da suke mana ni da Ammi ya Haidar, musamman ma mummunar
kalmar da suke faɗa akanshi, ina ji kamar na shaƙesu saboda haushi amma don rainin hankali
idan a gaban shi ne basa faɗa mishi sai a bayan idon shi". Ta faɗi hakan tana kuka, saboda
raɗaɗin da take ji a hannun ta.
Wani ɗan sanda ne ya kira Hajiya babba, tana fitowa da niyyar zuwa wajen Alhaji Marshal sai ta
koma kai tsaye gida, ta ɗakko mayafinta suka fice ita da Tasleem.
Tana fitowa Munir ya kirata, yana tambayar me taje yi folis ɗazu? Yanzun haka yana cikin
station ɗin.
Ƙala bata ce ba kai tsaye ta wuce da motarta, sai dai abin da ya bata mamaki bai wuce ganin
ɗanta Munir a wajen ba.
*MAMA SALAMATU*
_______Mama Salamatu ta biyo bayan Umma tana ta sababi, Umma dai tuni tayi gaba abinda
ke gabanta kawai take tunawa yaranta har guda uku a folistashon.
"Allah ya wadaran ahalinku marasa mutunci waɗanda basusan annabi ya faku ba".
Baba ne yake faɗin hakan yana shigewa ɗakin Baba kande, ita kuma sai zugashi take domin
daman shi bai ƙi zuga ba ɗan abu kaɗan zai sa yahau kamar ƙwaɓin fanke.
****
"Ai waɗannan yaran yau sai sun san sun taɓoni, wallahi tallahi na rantse da wanda raina yake
hannunsa sai sunyi gidan yari waɗannan yaran, marasa kunya iyalan malam audu me dattin
hula ƴaƴan talakawa waɗanda suka ɗaurewa talauci gaba".
" ni fa babu wacce nafi tsana irin waccan yayar tasu, me take da suna ma? Humaira ko
umaimah?".
Cewar Tasleem wacce take ta harararsu tana musu gwalo, su kuma suna cikin sell suna shan
azabar zafi domin sell ɗin irin ɗan ƙaramin nanne, wanda numfashinka ma da ƙer zaka dinga
shaƙa.
"Anti Humaira wallahi bana nadamar zuwana wajen nan, tunda naga alamar ba suda mutunci
kuma har yanzu basu ɗauki talaka abakin komi ba".
Cewar Ameera wacce ta haɗa zufa sosai.
Ummi ta yamutsa fuska ta ce" uhum ni tunani na ɗaya ne Umma, domin kuwa nasan yanzu
tana can cikin wani hali, ga matsalata da Baba kande kan wancan Alhajin ga kuma wannan
matsalar, abin zaiwa Umma yawa gashi ba tada wanda zai ƙwantar mata da hankali".
"Akwai Allah ai, sannan nasan duk inda take yanzu tana kan hanyar zuwa gidansu, sannan
mama Salamatu baza ta taɓa barinta haka ba za ta dinga ƙwantar mata da hankali".
Cewar Humaira baiwar Allah, wacce idanuwanta suka jiƙe da ruwan ƙwalla domin duk cikinsu
ita kaɗai ce tayi kuka, domin ni ina da raunin zuciya su kuma ba suda shi yadda kasan masu
zuciyar maza haka suke.
wani ɗan sanda ya kallemu sosai, sai naga ya ƙaraso inda muke ai kuwa nan da nan Hajiya
Babba ta ƙaraso inda muke har tana haɗawa da tumtuɓe Tasleem tana binta tamkar zata karye
saboda sirantaka.
"ƴan mata me kuka yi aka kawo ku nan"?.
Da sauri Ummi ta ce" saboda zalunci mana, babu abinda mukayi har gida wata tazo ta sanyamu
agaba mu duka uku aka kawomu nan".
Ɗan sandan yayi shiru, Hajiya Babba ta gallama mana harara sannan ta ce" mara kunya, yaran
talakawa in sha Allahu rayuwarku a birsin zata ƙare".
Ameera za ta yi magana na riƙe mata hannu alamar ka da ta ce komi, shirun kuwa tayi tunda
dukkansu babu wani me ƙin bin umarnina, idan na tsawatar musu tamkar Umma ta tsawatar ne.
"Da ki yi magana mana, ƴar talakawa jikan talaka......."
Cewar Hajiya Babba, wacce take ta faman hura hanci tana ɗagawa.
Da sauri ɗan sandan nan ya dakatar da ita ta hanyar ce wa" haba Hajiya bai kamata kina kula
waɗannan yaran ba, tunda kin yi jikoki dasu sannan bai kamata anan kina ɗagawa mutane
hankali ba".
ƙwarjinin da yayi mata shi ne yasa tayi shiru, amma sam bata so ya hanata ba taso ne taci
mana mutunci tunda mu mun zama marasa gata.
*******
Munir ya ce" haba Hajiya me kuma ya haɗaki da yara? da zaki je ki kaisu wajen ƴan sanda?
sannan yara ƴan mata har guda uku kuma duk yaran mutum ɗaya? haba Hajiya bai kamata ba
wallahi".
"to sannu mara mutunci, wanda baisan darajar uwa ba yanzu har kai ne zaka zo kana faɗar
haka? agaban mutane saboda kaci min mutunci? to bari kaji tunda kai bakasan mutuncina ba ai
yarana mata sunsan mutunci na".
Munir yayi shiru, yana kallon tsala tsalan ƴammatan waɗanda aka rabosu da iyayensu aka
kawosu nan, saboda kawai tana tutiyar tana da kuɗi ya rasa me yasa Hajiyar take wulaƙanta
talaka, alhali ita da kanta ƴar talakawan ce jikar talaka amma ahaka mahaifinsu ya aure ta kuma
ya sakar mata komi sai yadda tayi dashi, ko ƴan uwansa basu isa suce ga yadda za'ayi ba
amma ita tana ce wa ayi kaza sai kaga anyi.
wayarsa ya ɗakko ya kira Hajiya ƙarama kishiyar Mamansa, nan da nan ta ɗaga ta ce" ɗan
arziƙi lafiya kuwa ɗazu naje ɓangarenka ban same ka ba, nayi ta kiranka nan ma ban same ka
ba?".
"Mami ke dai bari, wallahi Hajiyarmu ce ta haɗosu da wasu yara ƴammata, to fa shi ne ta
kawosu wajen ƴan sanda yanzu haka ma ina can".
Jikinta yayi sanyi sosai, ranta kuma ya ɓaci sosai wato ita Hajiya har yanzu batasan annabi ya
faku ba? ace wai kina da yara har guda uku amma ace wai bakisan darajar yara mata ba har
kina kaisu wajen ƴan sanda saboda aci musu mutunci, zato zunubi ne ko da ya kasance
gaskiya amma ta tabbatar Hajiya ce ta tsokani waɗannan yaran, domin tasan halinta sama da
shekara ashirin take tare da ita tafi kowa sanin mugun halinta.
ta samu kanta amai kira Munir, yana ɗagawa ta ce "zanzo wajen yanzu ka ƙwatantamin"?.
Jikinsa a matuƙar sanyaye ya faɗa mata wajen sannan ya kashe wayar, domin yasan in har
Hajiya Babba ta samu labarin shiya faɗawa kishiyarta wannan maganar sai ta kusa yi masa
baki, domin akaf duniya yasan babu wanda ta tsana irin Hajiya ƙarama kishiyarta, ya rasa me
yasa? domin yasan kishiya ai ƴar uwa ce idan da mutunci.
Tun daga nesa Hajiya Babba take kallonta, ranta amatuƙar ɓace tuni fuskarta ta koma tamkar ta
shanu saboda tsabar haushi, tun da jajayen sahu ta tsani Aisha, sam bata sonta ko kaɗan tun
lokacin da mijinta ya auro ta tayi ƙaura da farin ciki.
Aisha macece kyakkyawar gaske, fara sol ga ta da kyaun jiki da kuma kyawun sura. Aisha tana
ƴar shekara 15 aka auro ta mahaifinta hamshaƙin me kuɗi ne wanda ya amsa sunansa, gidajen
radio da talabijin ko ina ka zaga aikin alkhairinsa ake yaɗawa saboda shi mutum ne me
taimakon talaka, shi kuma Alhaji Mashahud yaronsa ne, wanda ayanzu haka ya koma Alhaji
Marshal saboda sunansa dana Aisha dake haɗe saboda soyayyarsu.
Babu haukar da Hajiya babba batayi ba, wato Hajiya Habiba uwar gidan Marshal akan ta tsani
auren Aisha da mijinta, amma da yake Allah yayi Aishar matar Marshal ɗin ce dolenta ta
haƙura, tunda babu yadda za tayi domin ita da kanta Aishar ba son Marshal ɗin take ba,
mahaifinta ta yiwa biyayya ta auresa wanda alokacin tsaf Marshal zai haifi kamarta tunda yana
da kusan 38 ya aure ta.
Sam Hajiya babba bata san da Hajiya ƙarama ta ƙaraso ba, har sai sa ta ƙaraso inda take ta
wannan mayen ƙamshin da take amfani dashi ya daki hancinta, ai kuwa fitgigit ta farka daga
mummunar duniyar hassadar ta, sannan ta ce" ke kuma meye ya kawo ki nan? anzo munafurci
da iyayi da karuwanci ko"?.
da sauri Aisha ta kalle ta sannan ta kawar da kanta, har ga Allah taji haushi sosai amma ba
tada yadda za tayi dolenta kome ta ce mata ta amshesa hannu bibbiyu, saboda ayanzu haka ita
ta kawo kanta kome ta faɗa mata ma ba laifinta bane, sannan bai kamata ma sam ta biye mata
ba saboda haka kai tsaye ta wuce ofishin babbansu saboda taji matsalar.
ko da tazo wucewa gabanta ne ya tsananta faɗuwa, ta ƙaraso da sauri saboda ta gane Humaira
sosai domin sanda mahaifiyarta tana aiki agidan tana yawan ganin yarinyar, saboda haka ta
ƙaraso da sauri ta ce" daman kune Hajiya babba ta kulle? me kuka yi mata haka"?.
cikin kuka na fara yi mata bayanin komi, domin nasan matar dama kuma kaf mutanen gidan
bayan ita da megidan sune masu mutunci amma daga Hajiya babba har yaranta duk kanwar ja
ce.
Shiru tayi, sai naga ta goge ƙwallar idonta sannan ta ce" babu komi kada ku damu zaku fita yau
ɗinnan in sha Allah".
Muka amsa da "Amin".
ita kuma ta shiga daga ciki wajen folis ɗin.
"yallaɓai kunfa san aikinku sarai, saboda me zaku dinga biyewa irin waɗannan masu kuɗin da
babu abinda suka sani sai cutar yaran jama'ah? domin sunsan ko me zasuyi musu gwamnati ba
magana za tayi ba, tunda sunsan ba suda shi saboda haka ni dai da muryar adalci nazo ba wai
zan bada kuɗi domin asakesu bane, ayi musu adalci a komar dasu gidan iyayensu".
DPO ya gyara zamansa akan kyakkyawar kujerarsa me juyawa, sannan ya ce" ba komi Hajiya
Aisha Marshal in sha Allahu ayau ba gobe ba zasu bar wajen nan, domin nima da kaina nayi
bincike sosai kuma na gane gaskiyar komi, sai dai zamuja musu kunne akan su daina zagin
babba ko da shi babban ne ya yada girmansa, kuma zasu bata haƙuri domin amatsayinta na
babba bai kamata su zage taba".
"naji na kuma yarda DPO nasan sunyi laifi amma ayi musu uzirin ƙuruciya, domin yaran suna da
mutunci da mutuntawa kuma sunsan mutunci".
haka dai yayi ɗan rubuce rubucensa sannan ya ce" ki kirawomin sajen awaje ya shigo dasu
sannan sai ayi abinda za'ayi su koma gidajensu".
Hakan kuwa akayi, aka fito dasu Humaira ganin an fito dasu Hajiya babba ta wani wurgo daka
kan kujerar da take, yadda kasan zata daki sajen ɗin ta ƙaraso da faɗanta da hargagi tana son
zaginsa.
wani kallo ya wurga mata sannan ya ce" Hajiya ki kiyayi bakinki idan kuwa ba haka ba xa'ayi
ƙaiƙayi koma kan masheƙiya su sun fito ke kuma kin koma inda suka fito, domin naga alama da
irin wajen nan kika dace".
Haba wa, wannan maganar daya faɗa ai sai ta harzuƙa hajiya ta inda take shiga ba tanan take
fita ba tana wani irin zagi wanda kana jinsa kasan cin mutunci ne ɗanyensa.
Munir sai haƙuri yake bata amma ko kallonsa bata yi ba, baisan shima haushinsa take jiba
domin tasan babu wanda zai faɗawa Aisha sai shi, shi da Aisha aƙwai amana saboda rabin
rayuwarsa a ɓangarenta yayi.....................
*$HAJIYA ƘARAMA*
*$ HUMAIRA*
*$ UMMI*
*$ AMIRA*
*$ HAJIYA BABBA*
UMMU MAHER.
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN): *_ƊAN HALAK_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MISS GREEN)_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
~*Wattpad*~
D'AN HALAK
https://www.wattpad.com/story/368199708?utm_medium=link&utm_source=android&utm_conte
nt=story_info
MAHER'S COLLECTION
https://chat.whatsapp.com/C3tsX4CqiEp939DhYvJ3SZ
Ina masu son shiga adashe Amma kuna fargabayar uwa ki tsarkake zuciyan ki kizo kiyi
adashe cikin aminci da kwanciyan hankali insha Allah Babu rigima ko tashin hankali kwanciyan
hankali zaki Yi adashen ki Kuma mu gama lfyh da yardan Allah..
30k weekly parking 300k
1)Haj Maryam✅
2)Ada umar/hafsat yahya✅
3)Usman
4) barrister hauwa'u
5)shafa bello/baby daura
6)
7)
8)
9)
10)
Akama slot
https://chat.whatsapp.com/HAkm8rINu8a0ouQsRmuDuL
15
_______Tun tana hana shi zuwa ɓangaren Aisha har ta dena, domin shi yaro idan jininsa ya
haɗu da abu da wuya kace zaka cire masa shi lokaci ɗaya, akwai sanda suka yi rigima da Aisha
baki ɗaya Munir Hajiya babba ta tirsasawa mahaifinsa da ya kaishi bodin, da yake duk abin da
take so yana so nan da nan aka kaishi karatu ƙasar waje lokacin yana ɗan shekara 13, anan ya
cigaba da rayuwarsa har ya yi shekara 27 sannan ya dawo, bayan ya kammala digiri ɗinsa
aƙasar Tunusia.
Ɗan sandan yayi rubutu, sannan ya bada odar fito damu, idanuwanmu sun yi jawur saboda
kuka musamman idan muka tuno da halin da Umma za ta iya shiga, domin duk inda take yanzu
hankalinta idan ya yi dubu ya tashi.
Ya ce" ina son ku bawa baiwar Allahn nan haƙuri musamman akan rashin kunyar da ku ka yi
mata, sai asanya hannu kubar wajen nan baki ɗaya, domin ganin dacewar hakan yasa muka
yanke wannan shawarar, sannan abu na biyu sel ɗinmu ya cika da mutane bama buƙatar
yawan jama'a domin tun ɗazu aka kawo wasu gasu can a zaune, kunga da kun bar ɗakin sai su
shiga".
Tunda ya fara maganar Hajiya babba ta saki salati, sannan ta ce " Ni awa zasu bani haƙuri? Ai
waɗannan ƴaƴan ƙwaltan ba iya bani haƙuri za suyi ba, ko da ma sun bani haƙurin ai sun cuce
ni saboda sun ci mutuncina, ni kuma wallahi basu bama duk wani me ji da rashin mutuncinsa na
fisa iyawa, saboda haka su riƙe haƙurinsu kawai idan ma ba zaku ƙwatar min haƙƙina ba nasan
ni inda zan kai, kuma wallahi duk sai kun yi nadamar abin da ku ka yi".
Ganin tana ta masifa kowa yayi shiru yana jinta, domin babu wanda zai kulata ganin ayanayin
yadda take faɗan idan ka kulata jarabar tata gaba za tayi ba baya ba, domin kome za'a faɗa
mata ba yarda dashi za tayi ba, kawai gani za tayi ai anbi bayanmu.
Bayan mun fito Munir ya biyomu da sauri, Hajiyarsa ta daka masa wata uwar tsawa tamkar
tsawar dake rugugi acikin samaniya, ko kuma tsawar amon wuta me tafe da sauti sosai.
Abin da zai baka mamaki yadda Munir ya maze ya yi wucewarsa, ya buɗewa Hajiya ƙarama
gaban motarta sannan shima ya shiga, ya bamu umarnin shiga cikin motar jikinmu duk
amatuƙar sanyaye, domin ni na tabbatar ayanzu haka Umma tana cikin tashin hankali mara
misaltuwa.
Har ƙofar gida suka kawomu, bisa jagorancinmu Munir ya fito da sauri ya buɗe murfin ƙofar da
take ɓangarena. Yadda kasan zai ƙwanta na taka bayansa na wuce, haka ya yi min domin har
rausayar da kansa yake saboda tsabar jin tausayina.
Har cikin gidanmu Hajiya ƙarama ta biyomu, jikinta duk yayi sanyi a yanayin da ta same mu
amma sai ta daure bata nuna hakan ba, amma jikinta duk ya yi matuƙar sanyi zaka fuskanci
hakan ayanayin kuzarinta. Domin duk wani karsashinta ya ragu sosai, kai talauci bai yi ba
domin annabi ma da kansa ya nemi tsarinsa, (S.A.W) domin talauci wani babban kataɓus ne
arayuwa da zai hanaka gaba balle baya ya Allah muna roƙonka ka fitar damu daga ƙangin
talaucin da muke fama da shi Amin.
Baba ne atsakar gida, yana hangota yayi saurin tashi da fara'arsa kamar dai daman can ya