Author : Ummu Maheer Miss Green Category : Thnovels
wahaltaccen kuka, duk kuwa da zafin
zuciyarsa bai hanashi yin kuka ba, abune mafi wahala wanda zai sanya gadanga ƙusar yaƙi
kuka, amma yau sai da yayi me isarsa sannan yayi shiru.
Shi da kansa ya bawa kansa haƙuri, domin yana so yaje wajen Ammi bisa bin umarnin da tayi
masa, ta ce kome yake yau yazo.
ya ɓata lokaci da dama yana wanka, yana saƙe saƙe azuciyarsa daga tunani me kyau sai ta
koma masa akasin haka, wanda kowacce zuciya idan tunani yayi mata yawa xa kaga tun tana
tunani me kyau sai ta koma mara kyau.
yana cikin komin wanka, wanda ruwan har ya taɓa dai dai wuyansa ruwan wankan kalar filawar
dake cikin ruwan wato kalar yellow, sai ƙamshi ruwan yake gashi da ɗan ɗumi ɗumi daɗin
ruwan yana ratsa dukkanin ɓargo da jikinsa, yana ɗan lumshe idonsa yana buɗewa.
ga tamfatsetsiyar tv wacce take manne jikin bangon haɗaɗɗan banɗakin, wacce yake kallon
labaran bbc cikin harshen hausa, yana matuƙar son yarensa Hausa shiyasa aduk tsahon
shekara goman da yayi a Italiya bai taɓa barin yarensa ba, saboda shi mutane da dama sun iya
yaren hausa, domin duk rashin son maganarsa baya hanashi koyawa turawa yarensa na hausa,
duk da shi ba duka bane hausa mahaifiyarsa ita sam bama ƴar nigeria bace, ƴar ƙasar Mali,
amma ayadda Amminsa ta faɗa masa mahaifinsa Bahaushe ne abinda ta kasa faɗa masa shi
ne asalin waye Baban na sa, wanda akullum wannan shi ne tunanin da yake hanasa barci da
sukuni.
abu biyu ne ya kasa fita daga zuciyarsa, na farko wannan baƙin tabon na rayuwarsa, na biyu
mutuwar amininsa wanda bai da kamarsa sai Hammud wanda da ayanzu haka suke tare, Triple
ake kiransu saboda yadda suka shaƙu da juna, kuma duk a ƙasae Italy sukayi karatu.
MU'AZZAM.
Amini na gari me son ganin wani yayi farin ciki, aminin da baya tonawa amininsa asiri, ga ilimi
ga addini, mutum ne wanda ya samu tarbiyyar uwa da mahaifi babansa ɗan asalin Niger ne
garin maraɗi, babban malami ne wanda ake ce masa Malam Mousa Ali shahararran malami ne
wanda yake da ilimi me yawan gaske, sannan yana da faɗi aji agarin Maraɗi har ma da Niger
ɗin baki ɗaya, ɗansa ɗaya namiji aduniya wato Mu'azzam sai ƙannen Mu'azzam ɗin biyu mata
sai yayarsa guda ɗaya.
Alokacin da suka haɗu a Italy da faɗa suka fara, domin shi Haidar mutunne marar haƙuri
wanda baka isa ka nuna masa yatsa ba, komi girmanka idan ka nemi ka takasa sai kun ƙwasa
dashi.
Mu'azzam kuwa mutum ne me masifar haƙuri, yakana, sanin ya kamata, addini da hankali duk
babu wanda bai haɗa ba.
yana shigowa makarantar da lafceciyar motarsa me tsari da kyau, baƙa ƙirar jip yayo hanya
samɓel yana tafiya yana bin waƙar daya saka ta wizkid me taken ilove u.
Mu'azam yayi gefe, Haidar ya ƙara yin hanyar da yake ya canja wata ma nan ma bata canza
zani ba, daga ƙarshe saura ƙiris ya bugesa Allah ya taimakesa yayi gefe da gudun gaske ya
faɗa kan wasu green grass waɗanda suke shimfiɗe acikin gefen makarantar waɗanda suka
daɗa mata kyau.
cike da mugun fushi ya fito daga motar, alokacin Haidar yana cike da yarinta da kuma rashin
sanin darajar ɗan adam domin giyar kuɗi na ɗibarsa.
Bawan Allah yana rakuɓe agefe yana duba yadda duk jikinsa ya kurje, silar faɗawarsa cikin
wannan ciyayin tunda tsalle yayi ya faɗa cikinsu.
ya cire gilashin idonsa, ya ƙare masa kallon ƙasa da sama kana ganin Mu'azzam kasan ya
cika dukkanin kamalarsa amma kana ganinsa yanayin shigarsa kasan ba ɗan wani bane, hatta
agogon dake manne a hannunsa kana ganinsa kasan ba me kuɗi bane.
"wani irin mahaukaci ne kai? so kake na bugeka in baka kuɗin rigistration na makaranta ko?".
Cikin turanci yake masa maganar, yana wani gimtse fuska yana wani ya mutsa ta wai shi me
kuɗi.
Mu'azzam bai ce masa komi ba ya karkaɗe jikinsa, ya ƙaraso gar gaban Haidar ya haɗa
hannayensa biyu waje ɗaya, gamida maƙale jakarsa a hammatarsa ya ce" yallaɓai kayi haƙuri,
ni ba kowa bane kuma ba ɗan kowa ba kuma ni nayi maka laifi kayi haƙuri don Allah".
duk ƙwamdor masifar daya so sauke masa sai da jikinsa yayi sanyi, yana ji yana gani
Mu'azzam ya wuce ba tare daya ce masa komi ba.
sai daya daɗe atsaye sannan ya shiga motarsa ya tayar, jikinsa asanyaye yana tuƙi yana tuna
abinda ya faru ranar bai je lakca ɗin bama ya koma ƙerarran gidansa wanda ke cikin birnin Italy.
ko rufe ido yayi sai yaga Mu'azzam yake gani, sanyin halinsa da nutsuwarsa sai yaji ya
ƙwanta acikin zuciyarsa. tun dama can shi mutun ne me son mutum me sauƙin kai da son
mutane amma fa shi halinsa ba haka bane, domin kuwa ko shiga mutane bai son yi shiyasa ko
hostel bai nema ba ya siya ƙaton gidansa me matuƙar kyau da tsaruwa.
Washe gari a inda suka haɗu ya tsaya, sai dai duk zaman da yayi bai ko ga ƙurarsa ba,
jikinsa yayu matuƙar yin sanyi addu'arsa ɗaya Allah yasa ya gansa.
sai da yayi ƙwana biyu yana zuwa amma bai gansa ba, daga baya sai ya canja shawara ya
koma cikin makaranta yana ɗan duddubawa.
Can ya hangosa gindin wata bishiyar filawa me cike da ni'ima yana zaune irin kan kujerun nan
na makaranta waɗanda aka ginasu da dutse.
ƙur'aninsa izu sittin a hannunsa yana tilawa, ya yi matuƙar nutsuwa da abinda yake yana cike
da ƙanƙan da kai tamkar yana gaban ubangiji.
ya ƙarasa cike da nutsuwa kusa da Mu'azzam wanda ya gama nutsuwa, kamala ta haɗu da
ƙwarjini.
Mu'azzam ya ɗago ahankali, domin yaga daɗewar da Haidar yayi atsaye saboda bayason katse
sa.
da fara'arsa ya ce"sannunku bawan Allah, kamar kaine wanda muka samu kuskuren fahimta
rannan ko"?.
Haidar ya ɗan faɗaɗa fara'arsa ya ce" eh ni ne, nasha wahalar nemanka tun ranar amma sai
yau Allah yayi".
ya faɗi maganar agajarce, kuma dama can shi ba irin mutanen nan ne masu yawan magana ba,
ko jan magana.
ya matsa masa ya zauna, fuskarsa ɗauke da fara'a Haidar yana ta kallonsa al'amarin bawan
Allahn yana burgesa saboda yana da masifar haƙuri.
Haidar ya ce" amma anan kake karatu"?.
"eh anan nake, yanzu shekarata ɗaya da fara zuwa wannan makarantar, ni ɗan asalin Niger ne
duka iyaye na ƴan can ne amma mahaifiyata ƴar asalin ƙasar Mali ce".
"oh, nima mahaifiyata ƴar asalin ƙasar mali ce".
"mahaifinka fa"?.
Sosai kansa yayi nauyi kansa ya fara juyawa saboda jin tambayarsa............
*SHARE*
*$HAIDAR*
*$MU'AZZAM*
*UMMU MAHER*.
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN): _D'AN HALAK_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
*_UMMU MAHER BUSINESS CENTER_*
*koyon sana'o'i 5 kamarsu*
1 MAYAFI NA BEAD WORK
2 MAYAFI NA STONE WORK
3 HULUNA
4 COVER BOOK
5 INVITION CARD
dukkaninsu zaki koya akan 800 ƊARI BIYAR KACAL.
*KIBI WANNAN LINK ƊIM DOMIN SAMUN DAMAR GARAƁARSA SHIGA GROUP
ƊINMU*
https://chat.whatsapp.com/CMlWt3cUVvkDAXPthThNQx
5
_________ganin kamar ran Haidar ya ɓaci game da tambayarsa yasa ya juya hirar da ce wa"
wanni course kake karanta"?.
ya ɗan ja wani wahallan yawu sannan ya faɗa masa course ɗin, amma har lokacin jikinsa baki
ɗaya yayi sanyi indai har za a masa maganar mahaifi sai yaji duk duniya komi ya sare masa, sai
yaji tamkar ya shaƙe kansa saboda haushi, mutane da dama suna masa kallon wanda bai da
galihu saboda rashin uba, bai san awata duniya mahaifinsa yake ba? ko sunan mahaifin nasa
ma bai sani ba, domin Ammi ko sunan mahaifin nasa bata bari ya sani ba, akullum dai
tunaninsa bai wuce ace ta yaya zata ɓoye masa mahaifinsa alhali kuma tasha faɗa masa shi
ɗin ƊAN HALAK ne, ɗan sunnah tamkar ko wani ɗa?.
Mu'azzam yana ta yimin hira amma ni ban ma san yanayi ba, hankalina da nutsuwata baki ɗaya
yana can kan tunanin halin dana ke ciki, duk kuwa da gata na da komi nawa na rayuwa.
ɗan taɓani yayi, firgigit na dawo hayyacina na kalleshi cikin nutsuwata yana kallona ya ce"
bawan Allah ka daina wannan tunanin, domin ita ƙaddara babu yadda zamuyi da ita domin ita
ce mahaɗin rayuwarmu, kuma duk wanda kaga Allah ya jarabcesa da wata lalura ko ƙaddara
haƙuri da addu'ah ce kaɗai zata fitar da bawa daga dukkanin ƙaddarar daya faɗa, mafi
akasarinmu abinda yasa muke samun matsala arayuwa shi ne rashin cinye ƙaddara domin ita
ƙaddara abuce me wahalar gaske, idan ka daure kayi haƙuri sai kaga ka cinye ta".
Haka ya dinga yimin nasiha.
tun daga ranar muka ƙulla abota da Mu'azzam, anan na gane rayuwa bata yiyuwa sai da haƙuri,
duk rashin haƙurinka ka sabawarka kanka haƙuri da juriya koda ƙanƙani ne. domin abu na farko
daya sanya alaƙarmu yin ƙarfi shi ne haƙuri, domin ni kamar zawo nake sam ba nida haƙuri ko
da kaɗan kuwa, amma ahankali sanadiyyarsa ya koyamin halinsa na haƙuri da juriya da yakana
da sanin ya kamata.
Tunda nazo karatu ƙasar Italy na daina kiran Ammi, duk wata kafa danasan zata neme ni na
toshe ta, domin Allah ya sani na tsani ƙwane-ƙwanen da take min musamman nacin da nake
mata na son gaskiyar lamarin ni waye? wanene ubana? A'ina yake? Yana cikin ƙoshin lafiya ko
akasin haka? yana raye ko ya mutu?.
Aƙwai wani bature wanda suka saba harkar business da Ammi, dama ita shahararriyar ƴar
kasuwa ce wacce ta saba kai kaya daga ƙetare zuwa ƙasata.
babu yadda bai yi ba wajen nemana, amma bai samu damar hakan ba saboda duk wata kafa
da zata bashi damar sanin inda nake na rufeta babu damar hakan.
ni aganina ana fushi da uwa azauna lafiya, rannan muna zaune da Mu'azzam yana ƙara min
karatun islamiyya littafin ahlari, wayata tayi ƙara kamar bazan ɗauka ba sai na ɗauka ɗin.
Fashewa da kuka Ammj tayi, atake naji wani abu tamkat mashi ya faɗomin akaina silar jin
muryar mahaifiyata, jikina yayi sanyi domin ko ba ita ba banason jin kukan mace tausayi yake
bani gamida kashe jiki.
"yanzu Haidar ka kyauta kenan? kasan kuwa irin wahalar dana sha wajen neman lambarka?
wallahi na rasa me kake so ka zama Haidar? wa yake zugaka ne? kasan kuwa halin da na
shiga? tsawon wata huɗu kenan amma sam na gaza samunka? me hakan yake nufi? Shin kana
fushi dani ne saboda abinda ƙaddara ta riga fata"?.
Shiru nayi, na kasa bata haƙuri ko in ƙwantar mata da hankali saboda banason buɗe bakin ma
ballantana har inyi maganar da zata ɓata ranta, kawai sai na kashe wayar ma baki ɗaya.
Mu'azzam ya ce" yallaɓai ka gafarceni idan na kasance me laifi agareka amma inason inja
hankalinka, kan wani kogin kuskure danaga kanasan faɗawa su iyaye suna da muhimmanci da
girma, musamman ma uwa shiyasa Manzon Allah (S.A.W) ya ce kabi uwa kabi uwa har sau
uku, sannan ya ce kabi uba. saboda muhimmancinta arayuwa Manzon Allah (S.A.W) ya ce da
zaka ɗauki mahaifiyarka zuwa umrah, ka zagaya ka'abah da ita agoye abayanka sau babu
adadi, bai kai ya haihuwarka da tayi ba shiyasa uwa take da wannan falalar, amma Haidar ba'a
fushi da uwa ka kiyaye fushinta akanka, yanzu in baka misali yanzu ba jarabawa kukayi ba ka
faɗi kakeson zana wata? kuma alhali ada kanada ƙoƙari sosai? sanadin hakan yanzu gashi ba
kada wani kataɓus akan hakan kuma wallahi ko kaffara bazanyi ba nasan wannan laifin da kayi
mata shi ne ya hanaka cin wannan jarabawar, tunda ada ka saba kome zakayi sai ka nemi
shawararta, ita kuma ta sanya maka albarka saboda haka ina me jan hankalinka da ka kiyaye
fushin uwa domin ba abune na wasa ba".
Nasiha me ratsa jiki ya dinga yimin, daga ƙarshe na ɗauki nasiharsa na kira Ammi muka
sasanta nayi ta bata haƙuri, da kuma nuna mata nayi kuskure.
sosai nayi sabo da Mu'azzam, saboda na gane zama da aboki nagari yana ƙara maka hasken
makarantar rayuwa.
Ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba, ranar da na nemi Mu'azzam amakaranta na rasa ranar
ban taho da masu tsaro na ba, hankalina ya tashi domin nima ba ko'ina na sani agarin ba balle
in tafi nemansa, sau tari ko ba ranar makaranta ina shigowa don kawai naga Mu'azzam, nasha
bashi shawara akan ya koma gidana amma yaƙi ya ce inyi haƙuri zamansa anan yafi ye masa.
duk wanda nasan zan tambaya na tambaya, amma shiru babu labarinsa wayarsa na kira yafi
sau shurin masaki amma shiru ba a ɗaga ba.
Bansan lokacinda naji wani zazzaɓi ya rufeni ba, jikina ya hau ƙerma. ganin zazzaɓin na neman
kaini ƙasa yasa na bugawa bodyguard ɗina na ce suzo su kaini gida.
suka kiramin likita ya dubani, sannan na samu barci acikin barcin nawa na dinga mafarkin
Mu'azxam wai yana cikin wani hali, yana neman taimakona amma na kasa basa, sai kuka nake
shima yana yi dai dai lokacin na tashi daga barci tamkar wanda aka ƙwarawa ruwa jikina ya jiƙe
sharkaf, ga sanyin AC amma tamkar babu wata alama ko kafar da iska take shigowa ta ɗakin.
Allah ya taimakeni na samu na tashi na shirya, banyi wani cikakkan shiri ba na fito zuwa
makaranta, ina addu'ar Allah yasa Mu'azzam ya dawo.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
abinda bakina yake iya furtawa kenan, saboda nauyin da yayi min daga baya naja bakina nayi
shiru tashin hankali fal jiki da ruhi.
domin na tambayi ƴan hostel ɗinsu sun tabbatarmin Mu'azzam bai dawo ba, suma kuma tun jiya
suke nemansa amma basu gansa ba, kuma gashi wayarsa da glass ɗin idonsa duk suna nan,
da yake yana sanya gilas a idonsa saboda yana da ƴar matsalar ido.
Ganin hakan yasa na bazama nemansa, wajen ƴan sanda na wuce kai tsaye na shigar da
report nan da nan suka fara bincikar case ɗin, ni kuma na dawo gida saboda na gaji sosai gashi
kuma ban saba tuƙi ba duk inda zanje kaini ake, saboda haka naji duk jikina yayi lugub tamkar
wanda aka daka a turmi.
*BAYAN ƘWANA BIYU*
Labarine yazomin da ɗumi ɗuminsa, wai anga Mu'azzam awani gida babu numfashi, wasu
mutanene suka kamasa amma yanzu da suna hannun ƴan sanda ana tuhumarsu.
Bayan an kai shi asibiti aka dubasa aka tabbatar lafiyarsa ƙalau sai gajiya da yayi sun hanasa
ruwa da abinci.
mutum uku ne, kuma duk baƙar fata na dinga kallonsu ina musu Allah wadai domin sun bani
mamaki matuƙa irinsu ne masu lalata mana suna ace duk ƙasar da baƙar fata yaje sai ya zama
wani mugun ƙusan rashin mutunci.
Duk tuhumarsu da ake baku faɗi gaskiya ba, ce wa suke su bazasu faɗi wanda ya aikosu ba da
yake ƙasar turawa ce sai aka ƙara barinsu su huta aka daina matsanta musu, aka biyo musu ta
hanyar dabara da wayo aka barsu ba tare da an ƙara tuhumarsu ba, akayi musu ɗaurin talala
har da abinci me kyau da ruwa ake basu.
Alokacin naji haushi sosai, sai nake ganin kamar basuyi mana adalci ba ya za'ayi masu laifi a
barsu tamkar masu aikin lada? amma dana faɗawa Ammi halin da ake ciki ta tabbatarmin sanya
musu ido suka ƙarayi domin da sun saki jiki shi wanda yasanyasu zai kawo kansa da kansa
tunda yaransa ne. Haka na ɗauki shawarar Ammi, na cigaba da faɗawa Allah akan ya bayyana wanda ya yiwa
Mu'azzam wannan mugun ƙullin, sai gashi kuwa rana tsaka su da kansu yaran sun faɗi waye.
nemansa aka duƙufa dayi amma tuni ya ɗaga zuwa Nigeria, sai dai da passport ɗinsa aka fara
bincikarsa, aka gano ashe ɗan jami'armu ne ma wani ɗan ƙusar gwamnati ne yaron bayajin
magana ko kaɗan, kuma karatun ma da aka turosa bai tsaya yayi ba, sai shashanci da bin
abokan banza da kuma lalata ƴaƴan mutane waɗanda sukazo daga Nigeria da ƴan sauran
ƙasashe.
Ranar har hawaye nayi, saboda tausayin Mu'azzam to me yayi musu? me ya sanyasu yi masa
wannan abin? abinda ya sanyani kuka bai wuce yadda olsa tayi masa mugun kamu ba, gashi
idonsa baya gani sosai saboda ya saba mu'amala da gilashin idonsa, gashi shi ba ɗan kowa ba
balle a ƙwato masa ƴanci, amma ni nayi alƙawarin kama wannan yaron aɗauresa har ƙarshen
rayuwarsa.
Ganin yadda nake hawaye yasa Mu'azzam dafa kafaɗata ya ce" Haidar wai mi yasa kake da
zuciyar mata ne? me yasa kake zubar da hawayenka akaina? banason kana zubar da
hawayenka akan wani, domin idan kana haka zama da mace ma bazaka iya ba idan har tasan
kana da rauni akanta, kuma ina me tabbatar maka na yafewa wanda ya aikatamin wannan
laifin, domin nasa yayi ne sanadin wani abu nashi wanda ni na cucesa ba shi ya cuceni ba,
domin awani hadisi an rawaito ce wa 'WALA TAJASSASU' ma'ana kada mu yawaita bincike. yin
hakan zai iya jefamu cikin babbar matsala".
Da sauri na kallesa wai jin cewar ya yafe masa, naji baki ɗaya idona ya ƙafe hawayen ma sun
tafi wannan wani irin bawa ne me yafiya, me haƙuri"?.
"Haidar nasan kana mamaki dana ce na yafe masa, Annabin tsira yana son mutum me yafiya
domin muma munawa Allah laifi ya yafe mana".
Na buɗe bakina da niyyar yin magana sai ga................
*SHARE*
*$HAIDAR*
*$MU'AZZAM*
ƊAN HALAK GRP LINK
https://chat.whatsapp.com/LcnDvlFNqL0Enq7llnpAVe
*UMMU MAHER*
[7/1, 11:54 AM] UMMU MAHER (MISS GREEN): *_D'AN HALAK_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
*_WELCOME TO UMMU MAHER BUSINESS CENTER_*
_____¥¥¥¥¥¥¥