Author : Yusrah Musa Abubakar Category : Hausa Novels 001
ta karaso.
Ganin bata san da zuwan saba yasa yay gyaran murya da sauri ta juyo cikin zaro ido zatai magana ya katse ta da fadin"ba wani abu ya kawo niba nazo ne na miki tambaya shin ke 'yar 'kungiyar shan jini ce jiya kika tura a kashe ni ko kuma kina da wani aljani basarake fada min gaskiya domin jiya yaje yayi min warning a kanki nasan saidai in kece kika sashi taya zaisan gida na idan bada hadin bakin kiba"?.
Dafe kirji Safah tay ni kuma sharri zaka min🙄"?.
Kai ya girgiza"ba wani sharri malama kawai ki yarda kin aikata domin ba mafarki nayi ba kuma ba'a rude nake ba a zahiri yazo min yana gargadi na saboda ke".
Cikin haushi Safah tace" bansan akan me kake magana ba kwantar da hankalin ka na kusa bar muku gidan ku sai kaci karen ka da gishiri ba babbaka idan ma kana tunanin na tare maka jin dadi ne basai ka kulla min sharri ba lokaci kadan ya rage min".
Kai ya jinjina bai sake magana ba ya juya yana fita a kitchen din da harara Safah ta raka shi tana jan tsuka" jimin mutum da tsohon sharri a'a ka manta ba 'yar 'kungiyar shan jini baca 'yar 'kungiyar shan bargo ce" cigaba tay da aikinta bata sake bi takan zancen ba dan sai yanzu take tunanin kila ko shawuwa yayi yazo yake karanta mata soko.
Mrs Al'ameen Ahmad ce,😍
Typing📚📝
🍇SAFREEYYAH🍇
💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫
(*()*)👉 🏡home of hospitality👐 and harmony👫(*()*).
📝YUSRAH MUSA ABUBAKAR GIMBA.
INA GAISHE DA DUKKANIN KU 'YAN UWANA NA JINI ALLAH YABAR MU TARE YA 'KARFAFA ZUMUNCIN MU🙏.
Uwani mubi (maman nana,)
Aishat Yakubu (maman Yusuf) Dumus
Yusrah Sallau Musa kano
Batula Adam Naseer kano,
Musa Aliyu Mubi Yola
Samira Ahmad (maman Zainab)
Ummi Ahmad, (maman Nura)
Nura Sani (Abban najasi)
Umar Halifa kano
Balaraba (maman Alhaji) kano
Ibrahim lele Abubakar
Usaina (maman Amatu) kano
Maman Ahmad Dumus
Sallau Sado Bauchi.
💞Mrs Al'ameen Ahmad ce💞
😘 When you are important🌿 to another person that person will always find a way to make time🕛 for you.
👉No excuses😎
👉No lies😉😝
And no broken promises💔.
#YUSRAHMS#
NO.35 👉 36
Ammi ce zaune ta kalli hanne tana cewa" Hanne meye labari kin dade bakya masarautar nan fatan kin dawo min da abin arziki wanda zanyi alfahari dake shin kin samo min wani kwararran malamin ne naga kin dawo fuskar ki fayau da annuri maza fadamin harna matso naji abinda yace miki fatan wannan karon anyi nasara .
Murmushi hanne tay mai ma'ana tana cewa"ai ranki ya dade ki zuba ruwa kawai yau a kasa na farin ciki kisha don na samo miki wani malamin daya san abinda yake saidai yace min zai bincika daga baya na koma amma karna damu ya gano nasara a tattare da aikin kuma yace na miki albishir da cikar burinki a wannan karon zai share miki hawaye ki kwantar da hankalinki duk abinda kike so zaki samu zai miki komai".
Numfashi Ammy ta sauke jin kamar anyi aikin ma tasamu abinda take so lallai kuwa da duk wata baiwa da take part dinta saita samu 'yanci kallon hanne tay tana cewa"da kuwa hanne na jinjina miki lallai za'aje dake kuma idan har nayi nasara zan kaiki zuwa babban matsayi sannan inaso idan kin koma gurin malam kice mas..........
Katse maganar Ammy tay jin an rafka sallama dan zaro ido tay tana kallon jakadiya dake dukushe can bakin kofa cikin bacin rai tace"bansan cewa ke jaka da'ki'kiya bace sai yau muna cikin magana zaki wani fado mana kamar wacce aka turo ki yaushe kika shigo kinji abinda muke tattaunawa kome sokuwar banza".
Jakadiya dake durkushe tana sauraron ta wani irin takaicine ya lullubeta ta sani cewa ta girmi Ammy kodan wannan aita rika bata girma amma saboda itadin ba ahlil sarki bace tana sahun masu hidima yasa Ammy bata ganin darajar ta kuma koba haka ba tarasa metaywa Ammy dama can bata sonta.
Cikin tsawa Ammy tace"ke wacce irin dabba ce jakadiya ba magana nake miki ba kikai banza dani saboda bani da daraja kome"?.
Kai jakadiya ta girgiza tana cewa"kiyi hakuri ranki ya dade banji komai ba sannan mai martaba ne yake nemanki yanzu ki gafarce ni nayi kuskure"ta karasa maganar hawaye na zuba mata domin wannan bakin cikin ya isheta ace don kana karkashin mutum shikenan saiya dau girman kai ya rika wulakanta ka.
Tsaki Ammy tay"naji bacewa ganina magulmaciyar banza harda kuka indai nice kuka ma yanzu kika soma don ni in mutum baiyi min ba bana ra'ayinsa to ya shiga uku bazai tabajin dadi ba ki bini a sannu jakadiya domin saura kiris nasa a tsige ki daga wannan mukamin naki a nada wata domin baki dace da matsayin ba".
Hakuri jakadiya ke bata amma ko sauraronta batai ba tace tayi waje kafin ta nuna mata kalarta mikewa jakadiya tay jiki a sanyaye ta fice yayin da Ammy ta bita da kallon tsana tana yin kwafa tace"zanyi maganin kine bari dai hankalina ya kwanta zaki bayani Hanne ta kalla tana cewa"jeki kawai zan nemeki daga baya sai mu karasa maganar da muke yanzu ba lokaci zanje gurinki ran mai martaba ne".
"To ranki ya dade fatan alkhairi a dawo lafiya"tashi Ammy tay tana wucewa daki donta shirya Hanne data mike itama zata tafi aranta tace"humm Adama gwana gimbiyar sarki zaki bayani sai na gama lalata miki tunanin gabadaya donni ba mahaukaciya ce irin ki ba dazan biye miki ki aikata mugun abu ba wata rana asirinki ya tonu a gane cewa dani kika hada baki zansan matakin dazan dauka a kanki muje zuwa".
Fitowar Ammy kenan bayan ta gama shiryawa ganin har lokacin Hanne tana nan yasa tace"me kuma kike jira baki tafi ba nifa bana son rashin tunani dalla malama bana sallameki ba barnan".
Baki bude Hanne take kallonta aranta tace"tofa ke baki da dama nice dalla malama lallai Adama kin cika amma zan nuna miki baki kaiba kinyi tsararo dani kike zance zan baki mamaki zanyi abinda baki taba tunani ba" a fili kuma sai tace "afuwan ranki ya dade na dauka zanyi miki rakiya ne shiyasa na tsaya".
Cikin sakar mata harara Ammy " haka nace miki uwar yan shishshigi dama ke kike raka ni bansan hanya bane kome dalla ki barnan".
Juyawa Hanne tay cikin jin zafin kalaman ta tafice zama Ammy tay tana huci ba'a jima ba wasu bayi su shidda da kaya iri daya a jikin su suka shigo mikewa Ammy tay tana wucewa gaba su kuma suka take mata baya har bangaren Emir .
Tana shiga ta iske shi yasa waya gaba yana murmushi zama tay tana cewa"ranka ya dade barka da hutawa irin wannan murmushi da fara'a haka koda Amfal kukai waya ne"?.
Murmushin sa bai gushe ba yake duban ta cikin muryar mulki yace" eh ba iya Amfal ba shida dan uwansa ne vidio call mukai dan nayi kewarsu sosai sunce min ma anyi musu karin girma baki ga yadda suka kara kyau da kiba ba kona baki ku gaisa da su dama suna tambayarki".
Cikin jin haushi Ammi tace"ko shine dalilin da yasa ka kira ni na 'bata kafa ta"?.
Kai Emir ya jinjina"eh ba haka bane wannan ma dabam tun dazu nake jiranki na aika a kiraki amma sai yanzu kika zo ko gimbiyar sarki mace daya kike kamar rai".
Murmushi Ammy tay cikin jin dadin gimbiyar sarki daya kike mace guda daya ta rausayar dakai fuskarta bayyane da fara'a tace"wallhi ranka ya dade harna ji ka fasa min kai daka kirani muce guda daya a gareka nice sarauniyar ka kome kace".
"Eh haka ne abinda kika ce gaskiyarki amma yanzu mu aje wannan maganar gefe kiran ki nayi don na sanar dake wani abu mai muhimmanci da zanyi Adama kin sani cewa duk namiji mijin mace hudu ne ko?balle kuma sarki wanda idan yana ra'ayi harda 'kwar'kwara inaso ki bude kunnenki ki saurare nida kyau kuma ki fahimta Adama ina mai baki bushara da cewa inason kara aure zan auri kanwar sarkin Adamawa abokina wacce mijinta ya rasu kwanan baya mene shawararki akan haka ki bani wani bayani dazai taimaka min domin kece makusanciya ta banda hajiya babu wanda yasan wannan zancen saike amma me kika ce"?
Wata irin zabura Ammy tay wanda tasa Emir ya kusa yi mata dariya mikewa tsaye tay cikin tashin hankalin tana kallonsa tace"ranka ya dade da gaske kake mafarki nake kome banji abinda kace sosai ba dan maimaita min.
"Dama nasan ba lallai ki gane kiji ko ki fahimce niba amma idan lokaci yazo kika ga komai azahiri cewa ba mafarki kike yiba daga nan zaki fahimta ki dawo daidai Adama bansan shashanci idan har Allah yasa anyi auren nan ki nutsu ki kama kanki kija girmanki banda hayaniya duk wata hanya da zaki bi kisan baku samu matsala ba matsayin kina babba kuma uwargida toki daure kibi wannan hanyar kar a samu sabani fatan yanzun kin gane"?.
Cikin kuka Ammy tace"wallhi ban gane ba ban fahimta ba bazan yarda kamin kishiya ba mena tare meye bana yi maka ka fada in gyara kurena kishiya bata dace dani ba".
"Haka dai kika ce a naki gajeran tunanin amma ni a wajena kin cancanti kishiya gaba da baya maganar bazaki yarda ba karyane don babu wani abu dazaki iyayi ko zaki wanda zai hana ni abinda naga dama ba aure kuma nan da sati za'a daura saiki kwana cikin shirin taryar sabuwar amaryar ki".
Kasa magana Ammy tay saboda bakin ciki sai kawai ta juya tana barin fadar tasa hankalinta inyai million ya tashi ko ganin gabanta batayi da yake bata cikin nutsuwar da zata iya magana a wannan lokacin kawai kwanciya tayi tare da kara fashewa da sabon kuka gaba daya ta rasa inda zata sa kanta hatta kwakwalwar kanta zafi take saboda daukar caji😢.
(Ayya Ammy sai hakuri fa mukan biki za musha mu gwangwaje💃💃).
Kome kuka ce?😝.
Wash😢 Allah fans typing akwai wuya😑 don haka gobe da jibi baza ku samu typing ba😝 zaku jini shiru zan huta sai ranar asabar in Allah ya bamu aron rai nagode yan whattpad ina yinku sosai ana tare👫💞.
Mrs Al'ameen Ahmad ce,👌.
👍 Taku har a kullum,
😘🙈We will meet again
🤗 Tnk for your support.
ONE☝ LOVE💝
YUSRAH MUSA ABUBAKAR CE..
BARKAN MU DA RANAR ASABAR YAN UWA FATAN KOWA YANA LAFIYA CIKIN FARIN CIKI DA KYAKKYAWAN YANAYI KAMAR YADDA NA MUKU ALKAWARI CEWA TYPING SAI RANAR ASABAR ALLAH YA KAWO MU SAI KU MATSO KUSA MU DORA INDA MUKA TSAYA DAN GANI NAZO KU FITO MU CASHE💃 YAU RANAR TAKU CE FANS WANNAN PAGE DIN NAKU NE MALLAKIN KUNE NA BADA SHI DUKA GARE KU KUN CANCANCI JINJINA👍 DA HANNU DUBU😝.
🌌💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION🌌💫
(🏡home of hospitality🤗 and harmony👌).
📝YUSRAH MUSA ABUBAKAR
DEDICATED TO
MY MOTHER I LOVE YOU MAY ALLAH ACCEPT YOUR DU'AS AMEEN MAMANA💞.
#YUSRAHMS#
NO.37👉 38
Hajiya Binta na zaune mk dake gefenta ta kalla tana cewa "bikin Salmah saura wata daya jiya dadin ku kafin ya tafi ya sameni akan na fada maka kafin lokacin bikin ka samo matar aure sai a hada ayi tare na isar da sakon sa yanzu ya rage naka kasan dai halinsa baisai na sake fada maka ba".
Cikin wani irin yanayi mk yace"haba mum aure kuma nida ban shirya yi a kwana kusa ba taya cikin wata zan nemo matar dazan aura please na roke ki idan ya dawo kice masa ba yanzu zanyi ba yadan karamin lokaci".
Wani kallo hajiya ta masa"Allah ko baba to baka isaba ni kaina na gaji da ganinka haka dandai ba yarda na iyane amma ga waraka tazo mk koba kaso dole ka nemo macen aure a wata dayan nan".
Hade rai yay"nidai dan Allah mum ku kara min lokaci zan samo ba yanzu ba".
"To ai ni kuma na dade da gano maka wacce ya kamata ka aura".
Mk da duk yaji hankalinsa ya tashi yace" wa kenan mum"? .
"Abidah mana mk ga mace a gida meye saika fita waje ka auro nice da kaina nayi tunanin hakan naga kuma ya dace mu hada zumunci mu kara karfafa shi".
A firgice mk yake kallon hajiya Binta muryarsa harta sauya yace"Abidah fa kika ce mum? wai Abidah dai dana sani ta gidan nan ko kuma wata ce dabam a wani wurin"?.
Dan harararsa hajiya tay"ji wani sokon banza Abidah tanan mana nake nufi 'yar gidan kawun ka 'Dayyabu zaka wani fuske kace wata ce dabam".
Kai ya soma girgizawa"haba mum me zanyi da Abidah gaskiya batai min ba bata cikin tsarin kalar matan da nake son aura ki janye maganar nan mum hakan ba mai yiwuwa bane niba sa'anta bane".
"Bazan janye ba mk inji ubanwa kaiba sa'anta bane meka fita fada min naji kaga fa banson shashancin banza".
"Kiyi hakuri mum amma bana sonta dan Allah ki fahimta".
"Bazan fahimta ba ni Abidah nake so ka aura idan kanada ra'ayi ko gaba kaga wacce kake so saika aura ban hana kaba"tana fadin haka ta mike zata bar gurin cikin magiya mk yace"ki saurari hanzari na wacce nake so ita kadai ce bata da sa'a tafi karfin zama da kishiya kuma gidana na ita kadai ce maishi banyi don nasa mata biyu ba saboda gudun hayaniya".
Ba tare da hajiya Binta ta juyo ba tace" 'yar gidan uban waye ita data fi karfin zama da kishiya waye ubanta a ina take"? shiru mk yay ya kasa magana don yadda hajiya ta hauro kila idan tsautsayi yasa ya budi baki yace Safah ce may be ya jawo silar barin ta gidan shi kuma hakan ne baya so.
Tsaki hajiya taja jin yayi shiru tace"maganar banza ma kenan kaika sani saika fara shirye shirye tun yanzu kayo lefe basai lokaci ya kure ba"gaba tai ta barshi a gurin cikin wani kalar bacin rai.
Fitowa Abidah dake labe tayi tana dariya ta soma taka rawa a gaban sa tana cewa"gaskiya naji dadin wannan al'amari ya mk nan da wata na zama matarka kamar yadda nake mafarki kullum ashe dai tabarya zatai rana kai kuma ka zama turmi dama na fada maka bazan barka ka auri wata bani ba kuma dole ka koyi sona ka zauna dani iya raida mutuwa danna zame maka karfen kafa mai wuyar cirewa ni kujera ce dole ka zauna dani"ta karasa maganar tana sakin gud'a wacce ta sake tunzura mk a fusace ya mike ba tare data lura ba ta rike hanci tana faman 'kara kamar wata gyare😂.
Ji tayi ya damki hannunta ya soma tafiya da ita ko damuwa batai ba dan tasan koma me zaiyi mata dole shine mai auren ta har part dinsa sukaje sakar mata hannu yay yana shiga bedroom zuwa jumawa ya fito rike da bel damkar ta yay cikin son huce haushin sa ya soma shimfida mata a jikinta ihu ta kurma tana bashi hakuri yay banza da ita saida ya zaneta tas sannan ya bude kofa yana turo ta waje ya mayar ya rufe.
Cikin kuka ta daga murya tana kallon kofar tace" Allah ya isa azzalumi kuma hakan bazai hana na fadi abinda nay niyya ba dole kaso ni kuma ka aure ni bayan taimakon ka zanyi ganyar tsiya katon tuzuru kawai mai kwana rungume da filo"tana fadin haka da gudu tabar gurin saboda tsoron karya fito ya kama ta tasan saiya kusa kashe ta.
Zaune suke a daki ranar da maryama ta dawo daga yola cikin damuwa Safah ta kalle ta tana cewa" waini baba sai yaushe zan tafi gida ne? ina so naje naga baffana dasu malam da Hadiza Allah zaman nan din ya ishe ni".
Dariya baba maryam tay"kai Safah mene abin gajiya kuma dama nasan dole zaki kewar su wata biyar ba wasa ba amma ki kara hakuri so nake sai anyi bikin Salmah da Mk sai muje na raka ki kasuwa ki sayowa Baffanki d'an abin arziki ki kai masa dasu Hadizan kema kya sayi wasu yan abubuwan na aurenki da kudin aikin ki kamar kuloli da sauran su kinji ki 'kara hakuri saura yan kwanaki".
Kai Safah ta daga cikin jin dadin lissafin da baba maryam ta mata tace"to Allah yakai mu baba nagode" murmushi baba maryam tay"yauwa ko kefa kin kusa ganin Baffa kwantar da hankali".
* * *
«»«»«» »«»«»« «»«»«»
Kamar yadda Emir ya fadawa Ammy cewa zuwa sati amarya zata sauka hakan ne ya faru ankawo ta lafiya kuma part dinta yana kusa da part din Ammy a ranar dai Ammy ko iya runtsawa batayi ba tayi kuka tayi bakin ciki har bazai misaltu ba babban abinda yake daga mata hankali kuma yake bata tsoro taga amaryar ba wata babba bace dan batafi kanwarta ta biyu ba abin firgicin anan shine karfa nan da wani lokaci ta ganta da ciki ace itama zata haihu kila ba haihuwa daya bama yayanta suzo suyi yawa itama ya zama ta samu abin kirki a dukiyar sarki saidai ta dawo gefe ta zuba ido tay kallo wata banza tazo sama takai ta fita morewa ita data zauna dashi tsawon shekaru.
Ammy dake zaune idonta a rufe tana wannan maganar a zuciyarta a firgice ta bude idonta gani take kamar har hakan ta faru muryarta har wani sauti take bayarwa mai amo cikin takaici tace" inaaanh karya ne wallahi ni za'a wulakanta hakan bamai yiwuwa bane bazan taba barinki haihu ba saidai koni koke idan ba neman a tozartani a idanun bayi ba meye da girmana za'ai min kishiya bazan taba yarda da wannan ba".
Shiru tay tana huci daidai shigowar Hanne bayan ta gaishe da ita tun ba tace komai ba Ammy ta dube ta tana cewa"daga ina kike tun dazu ina jiranki"?.
Gyara zama Hanne tay tana cewa"ki hakuri ranki ya dade sako ne ya iske mu daga mai martaba cewa yana bukatar dani da jakadiya da Gambo sannan da bayi masu take baya muje mu raka masa amaryarsa fadarsa amma ki gafarce ni tuba nake".
Wani irin dafe kai Ammy tay jin hajijiya na diban ta da sauri ta nemi kujera ta zauna numfashinta na neman