Author : Yusrah Musa Abubakar Category : Hausa Novels 001
upon him said:Be mindful of Allah and Allah will protect you ,be mindful of Allah and you will find him in front of you,if you ask then ask Allah(alone)β,and if you seek help then seek help from Allah(alone) .
#YUSRAH#
NO.09π 10
Tsaye Safah take bayan sallar isha kadan a kofar gidan su tare da Adamu suna zance murtala ya karaso gurin yaso ya kauda kai amma ya kasa sbd son da yake yiwa Safan ba dan karami bane yana matukar kishin ta.
Dakatawa yay tare dayin sallama yana kallon ta a hasken farin watan daya haske ko ina yace"Safara'u ina son zamuyi mgn dan Allah ko minti biyar ne".
Adamu dake hura hanci tunda yasan tafi sonshi ya tare maganar da zatayi da cewa "yaukan na riga ka malam sai a tari gobe "ya karasa maganar yana busawa murtala iskar bakin sa.
Cikin bacin rai murtala ya danko wuyan sa nan fada ya kaure a tsakanin su wanda Baffa dake cikin gida harya jiyo ya fito salati Asabe keyi cikin son muzanta murtala tace"gaskiya yaron nan baka da tarbiya wato da bamu fito ba kashe shi kaso yi ko aiko kaima da an kashe ka jifa yadda ka shake masa wuya kamar wanda ka samu kayan goro".
Murtala bai saurare taba ya fadawa Baffa komai sannan ya tafi shima Adamun tafiya yayi yana zage zage harda da ace su Baffa basu fito ba saiya bazar da murtala a kasa.
Bayan sun shiga gida Baffa dake kallon Safah data zauna a gaban sa yace"Safara'u na sani kin girma tunda kinkai shekarun da za'a iya kiran su ashirin kinsan abinda yake fari da wanda ya kasance baki kafin nace wani abu ina son zan miki tambaya ki bani amsa"shin kina son aure ne waye kike so tsakanin murtala da Amadu"?.
Shiru Safah tayi har saida Baffa ya sake mgn sannan muryar ta na rawa tace"Adamu nake so".
Sosai Baffa yayi mamakin kuru irin nata duk zaton sa zataiwa murtala kara duba da cewa tun tana yarinya yake mata wahala kuma mahaifiyar sace ta raine ta bayan rasuwar zainab.
Sauke ajiyar xuciya baffa yayi yana sake duban ta yace"Safara'u bazan miki dole ba tunda Adamu kike so Allah ya sanya albarka a cikin neman shi kuma murtala Allah ya bashi hakuri da dangana ya kuma bashi mace ta gari".
Cikin jin dadi Asabe dake gefe tana jin kamar ta taka rawa dan murna tace "amin malam ashe mun kusa musha biki gaskiya a bari sai kaka sannan amfanin gona sunzo gida yadda zamu zubar da nera tunda ita kadai ce yarka dole kayi bajinta ta ban mamaki idan ba haka ba ayi yamudidi dakai a gari ace ka fiya son kudi ".
Banza baffa yay mata yana mikewa cikin rashin jin dadin wanda Safah ta zaba baiko saurari Asabe ba yay waje dariya Asabe tay bayan fitar sa ta kalli safah dake shirin shiga daki tace"humm kinyi sa'a wallh da tsautsayi yasa kince murtala kike so da yau saina kusa kashe ki a gidan nan".
Safara'u bata tanka mata ba ta shige daki yayin da Asabe keta jifan ta da maganganu marasa dadi tun tana jiyo ta har bacci ya dauke ta.
Kamar yadda kullum ta saba ta share gidan tas ta hada kwanuka ta wanke sannan ta debo ruwa saida ta gama komai kafin tazo dorawa Asabe abincin sayarwarta ta fice dan ta kaiwa kakanun ta ziyara a hanya suka hadu da Aisha amma sai Aisha tay kamar bata ganta ba .
Shan gaban ta safa tayi cikin mmk tana cewa"lfy Aisha me kuma nayi miki irin wannan shariya haka"?cikin bacin rai Aisha tace"aw bakisan me kika min ba haka ma zaki ce nagode " zata wuce Safah ta rike ta jikin ta duk yayi sanyi tace"dan Allah Aisha menene ki fada min wallh bansan abunda nai miki ba".
Kallon uku saura sisi Aisha ta mata"dama taya zakasan abinda kika min wai dan Allah Safah meye abin ki a jiki yayan mu murtala da bakya sonshi"dan yatsina fuska safah tay"oh dama abinda yasa kike fushi dani kenan?to yanzun dai kiyi hakuri bani da amsar tambayar ki kila zan samu gaba".
Fisge hannunta aisha tay tana wucewa Safah ta bita da kallo daga baya kuma ta kama dariya tana cewa"lallai Aisha ashe zaki dade kina fushi dani mai zanyi da murtala bayan ma na fishi tsayi idan zanyi masa mgn saina kalli kasa tab bazan iya ba ".
Ita kadai take tafe tana surutu harta shiga gidan zaune akan tabarma ta same su da sallama ta karasa tana zama bayan sun gaisa malam na Allah ya dauko mata naman dake rufe a gefe yana mika mata.
Karba tayi ganin abinda yake ciki yasa ta ce"gaskiya tsofin nan kuna jin dadi shi yasa bakwa tsufa ashe kullum tukunyar ku na sama nima yau nazo ayi dani.
Dariya Hadiza tayi "dadin abin ma ba hana ki zuwa mukai ba balle kice mu marowata ne muna gari daya saiki shafe wata bamu ganki ba kin kyauta Safara'u kodan gara ke shi Abdul-jabbar na manta yaushe rabona dashi inaga ko muhammadun ya manta da mune nidai ba nace ba".
Da mmk Safah tace"waye kuma Abdul-jabbar naji kina cewa kin dade baku hadu ba? dadina dake kalan dangi".
Kafin hadiza tay mgn na Allah ya amshe da cewa"dan uwan kine sai rashin sanin juna tunda baku taba haduwa ba sai randa yazo sai kuga juna".
Kallon sa safah keyi tace taya ya zama dan uwa na"?.
Ta dalilin Fatima yayar mahaifiyar ki itace mahaifiyar sa saidai shi yana kano can ne gidan mahaifin sa mu kanmu mun dade bamu ganshi ba amma duk ranar daya zo zaku gabatar da juna saboda kulluwar zumunci ko bayan ranmu".
Kallon sa sosai safah keyi tare da juya maganar a ranta lallai tana son ganin sa tana so su hadu dashi shine kadai jinin ta".
Sauke ajiyan zuciya tay tana cewa "Allah ya kawo shi lfy tabbas ina so mu hadu naga dan uwa na".
Zaku hadu in Allah ya yarda ki kwantar da hankalin ki kinji"kai ta daga alamar to kafin suka aje wanna zancen suka dauko wani dan debe mata kewa ganin tadan shiga damuwa.
Typingπ²
(*(*()*)*) {{}} (*(*()*)*)
π SAFREEYYAHπ
@YUSRAHMS ABUBAKAR
AISHAT MUSA ABUBAKAR
ABBAKAR MUSA ABUBAKAR
I KNOW U LUV ME ALWAYS MAY ALLAH PROTECT YOU EVERYTHING ABOUT YOU IS SO GOOD BUT ONE THING IS WRONG THAT YOU ARE NOT MIND.
MANZON ALLAH S A W
Shafi'ul wara da kai aka bude kullalle rahmar ka ta isarwa wahalalle da makalalle ka sada bayi da Allah zuwan ka shalele badon da kai ba ba'a san azumi da zakka ba.
#YUSRAHMS#
NO.11π 12
Fitowar Amfal daga wanka kenan ya kalli Abdul-jabbar dake tsaye jikin window yana karewa gidan gonar kallo yace"bros na fito shiga kada mu makara".
Juyowa Abdul-jabbar yai yana kallon shi a hankali ya karaso yana dan dukan kafadar sji yace"wani lokacin idan kai wani abu kamar karamin yaro jifa a yadda ka fito babu towel ko bathrobe ne".
Amfal dake kallon kanshi a mirror yace"akwai mana a haka dai na fito dan Allah shiga wankan nan kar mu makara yanzu karfe biyar fa kuma shida ya kamata muje".
Abdul-jabbar bai sake mgn ba ya shige toilet yana jin Amfal na cewa "kila daga can na samo matar aure kaga idan na riga ka yin aure shikenan nan ka zama yaya na kofar gida".
Duk abinda yake cewa Abdul-jabbar na jinshi bai tanka ba harya fito zama yay a gaban mirror kamar yadda suka saba Amfal ne ya taya shi shiri harya kammala sukai wankan kaya iri daya kamar yadda angon ya bukata domin abokin sune .
Sun bata lokaci sosai wajen shiri amma da yake Abdul-jabbar ne matukin nan danan sai gasu tamkar ba gurin events ba babu wata hayaniya domin ba mutane da yawa aka gayyata ba biki ne na manya daga wane sai wani domin kusan duk 'ya'yan masu mukami ne a gun da yayan senatoci sai gwamna da honourable.
Tarba sosai suka samu domin kowa a gurin yasan sudin su waye shi kanshi ango da ya kasance dan gidan minister yana jin ya raina kanshi balle fa saura jawabin akai na musamman akan zuwan su da nuna farin cikin ango da amaryar sa akan zuwan nasu.
Humm yan mata kam anga samari masu aji sai kowacce ta fara dauko mudubi suna duba fuskar su masu gyara daurin kwali nayi ko zasu dace amma gabadaya hankalin ogannin ba a wurin yan matan yake ba yana ga abinda ya shafi rayuwar sune.
Wata budurwa ce data kasa hakuri ta karaso gare su tare da cewa "zan iya zama"? No Amfal yace batare daya kalle taba da mmk ta bude ido a kansa kafin daga baya ta zauna akan daya daga cikin kujerun dake gunnn tana kallon Abdul-jabbar data kasa dauke idon ta a kanshi tace"barka dai suna na Bilkisa kuma ni yar gwanan jihar nan ce dan Allah idan bazaka damu ba kadan bani number wayan ka".
Ko dagowa Abdul-jabbar bayyi ba balle yasa cewa dashi take hankalinta ta mayar kan Amfal tana cewa"please ban phone number shi gaskiya ba mgnr boye boye yayi min kar wata tamin shigar sauri da zafi zafi ake dukan karfe a bari ya wuce yana kawo fitar rabo.
Amfal dake son yayi dariya ya dake yana cewa "ni bani da number shi kuma kin makara domin yana da mace harda yara uku yanzu aure na biyu ya sake ko wata ba'ayi ba ".
Dafe kai bilkisa tay tana kallon Amfal tace to naga kaida shi duk daya ne Allah yasa ba'a riga niba"?zaro ido Amfal yay yana kallon ta yace"ni kuma ki rufa min asiri ban tashi yin aure ba ni yaro ne".
Kai Bilkisa ta girgiza "gaskiya kaiba yaro bane dan haka nayi kamu"cikin jin haushi Amfal yace "da yake farauta kika fito ba ni kuma nayi miki kama da zomoπ ko gafiya saiki kama kikai gidan ku"π.
Murmushi tay "abin baikai haka ba kawai nidai ka amince min ina sonka"banza Amfal ya mata zata sake mgn aka neme ta cewa ta fito filin taro ta fadi wacce amarya da rayuwar ta mikewa tay tana cewa"minti biyu bari na dawo".
Sauke ajiyan zuciya Amfal yay yana kallo Abdul-jabbar da shima shi yake kallo zayyi mgn ya mike yana cewa"malam na mamajo kana iya tasowa mu tafi kafin mayyar taka ta dawo "mikewa yai sunai wa ango alamar fatan akairi suka fita a wajen dan Abdul-jabbar ne dayaga abin Bilkisa bana, hankali ba yaiwa ango text cewa zasu tafi yayi kiran ta fili kafin ta farga su fece har dare yayi dan haka suna zuwa sallah sukai suka bi lafiyar gado.
Sosai abinda Safara'u tayi ya taba xuciyar murtala bai taba kawowa a ransa xata 'kishi tadau Adamu ba saida yaga hakan ya faru.
Saidai abin mmk da lallami ta hanya mafi sauki baba ya sauya akalar safah da addu'a sai son da takewa adamu ya koma kan murtala harma ana batun zuwa rokon arziki hankalin asabe ya tashi bata san safah ta samu inda zata huta tafi so koda yaushe ta kasance cikin wuya dan haka ta samu malam da shawara.
Malam abinda kai baka kyauta ba yarinyar nan Adamu take so amma shine ka mata asiri ta koma son murtala idan kai haka ka ha'ince ta kuma sai Allah ya tambaye ka me yasa ka aikata haka".
Malam dake sauraron ta yace"Asabe bansan shasanci barnan kafin ki tabo min bacin raina".
Mikewa Asabe tay Allah ya bada hakuri malam dan kawai na fada maka gaskiya da kasan yadda ake zagin ka a gari ance kayiwa Adamu kyautar zobe da ka hana murtala Safara'u ka bashi".
Sake cewa yai"nace kibar nan ko baki jini ba "kada kai, asabe tay cikin takaici tana cewa "ba laifin ka bane karatu ne ka dauka a gurin malamin ka malam Na Allah shine ya fara yi Saminun gidan kuka na san Fatima amma sbd kudi ya rude shi ya bawa sarki ita ya hana wanda yaiwa alkawari kaima hakan zakai kenan"?.
Ai na sani murtala nada manyan shanu da awakai ga gonaki kuma ga shago kaima shiyasa idon ka ya rufe sbd za'a rika kawo maka madara ohni Indo amma fa anji kunya".
Malam bai sake sauraron taba ya mike yana barin wurin Asabe data bishi da kallo tace"wallh malam indai ina raye safara'u bazata auri murtala ba idan kuwa ka taurare akan haka zansa kayi kukan bakin ciki da idon ka".
Yau ya kama juma'a dan haka tun wuri Asabe ta dafa abincin sayarwar ta saidai ta rasa inda Safah ta shiga karshe gudun kar ayi mata kwashe ta dau hijabin ta tana bi duk inda tasan tana zuwa amma kowa yace bai ganta ba.
Dole Asabe ta hakura tana dawowa gida tadau hayar wata yarinya a makotansu ta bata tallan abincin ta kuma dau kujera ta dake tana jiran komowar Safan.
Safah na gidan su Na Allah acan ta wuni sai bayan anyi sallah a masallaci tayi musu saida safe tayo hanyar gida tana shiga Asabe ta mike tana cewa"ke yar iska daga gidan ubanwa kike dan raini shine kikai tafiyar ki yawo baki zo kinmin tallar abinci ba ko yau saina ci ubanki".
Kanta tayo zata fara dukan ta cikin tsawa taji ance"idan kika kuskura hannun ki ya sauka a jikin ta na datse igiyar auren ki duk ukun"da sauri ta janye hannunta tare da juyowa ganin malam tay tsaye rike da tasbaha yana ja.
Cikin bacin rai tace"yanzu malam a dakeni a hana ni kuka kawai gashi nan ta jawo min asara nayi kwashen abinci kudin mutane zai hau kaina wallh malam baka da adalci dan ba nice na haife ta ba shikenana ban isa da ita ba "ta karasa mgnr tana fashewa da kuka.
Karasowa malam yay yana cewa"wallh Asabe lokacin da ake rabon hankali bacci kike to bari kiji daga yau doka tace Safara'u ba zata sake tallar abinci ba kinji na fada miki".
Daki asabe ta wuce tana kuka yayin da malam ya kalli Safah dake tsaye yace"jeki kwanta"to tace tana shigewa daki shi kuma ya fita a gidan".
Ina godiya da nuna yabawar ki ga littafin nan my sister Zarah Musa dan Adam hakika bani da kamar ki a kullum roko na ki kasance cikin farin ciki mai dorewa.
Sauran yan uwa na nesa da kusa ina mika gaisuwa ta a gare ku tare da muku fatan alkhairin Allah a koda yaushe yakai muku inda kuke.
Maman Khaleel Zaria
Hajara Abla's Kano
Indo ce Kano
Rabi'at Bichi
Hajara birnin kudu
Zainab birnin kudu
Aishat birnin kudu
Ummi Salis kaduna
Ambaby kwalli kano
Walida kwalli kano
Batila Abdllh Dutse
Ruwaina Abdllh Dutse
Asiya Haladu Dutse
Badariyya Hassan Dutse
Aishat Abubakar Kebbi
Ameerah Hassan Dutse.
Dama wadanda ban fada ba kuma badan na manta ba duk ina gaida ku na gode kuma da yabon ku gare ni.
Bazan taba mantawa dake ba BASIRAH MUHAMMAD DUTSE INA MIKO TA'AZIYYAH TA GARE KI NA RASUWAR YARKI AISHATU BABYπ’ KWANAN BAYA ALLAH YA MATA RAHMA YAKAI HASKE KABARIN TA MU KUMA IDAN TAMU TAZO UBANGIJI YA AMINTAR DAMU YA NUFE MU DA CIKAWA DA IMANIππ. AMEEEEN.
YUSRAH MUSA ABUBAKAR SEE YOU NEXT TOMORROW BE WITH ME AT ALWAYS MY LOVERSπ€π.
Daga Alkalamin hamshakin group din nan mai cike da baiwa wanda kuka fi sani da takenπππ ANNURI WRITER'S ASSOCIATION π€HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI YAYAN TAFIYAR MU BABU RAGO A CIKIN TA BABU YAUDARA KO HA'INCI TSANTSAN GASKIYA MUKE NUNAWAβππ.
ππ«πMrs Al'ameen Ahmad ce.
ππLOVE FOR EVERππ
Typingπ²
3:54pm monday February 2023
πππππππ
SAFREEYYAH
πππππππ
π‘π«ANNURI WRITER'S ASSOCIATIONπ«ππ
ππππππππππ
ππππππππ
ππππππ
ππππ
ππ
π
ππ Yusrah M Abubakar
DEDICATED TO
MY MOTHER I LUV U AND I WILL BE WITH YOU ALWAYS YOU ARE THE BLOOD THAT IS SCULATED IN MY HEART.
WANNAN PAGE DIN NA MALLAKA MAKA SHI KAI DAYA MY BROS ABDALLAH MUSA ABUBAKAR .
On the authority of Anaass (RA)who say:
I heard the messenger of Allah(peace be upon him)said:
"Allah almighty has said:O son of Adam,as long you invoke me and ask of me,I shall forgive you for what you have done,and I shall not mind".
It was related by Attirmidhi,who said that it was a hasan hadith.
'YAN UWA WANNAN PAGE DIN NA SADAUKAR DASHI GA DUK WANDA YA KARANTA LITTAFIN NAN DOMIN PAGE DIN YA TARA DUNBIN ABIM MAMAKIπ.
#YUSRAHMS#
NO.13π 14
Cikin dare safah data kasance a dakin ta a kwance tana bacci kawai taji hayaniya a kanta ta dauka mafarki take saida taji abin bana 'kare bane ta bude idon ta Asabe ta gani tsaye a kanta gaa wasu samari biyu da bata san su waye su ba.
Zaune ta tashi cikin mamaki tana kallon Asabe kafin tayi wani yunkuri taji Asaben na cewa"gata nan kuyi yadda kuke so da ita kuma bance ku tausaya mata ba zan kuma biya ku kudi mai dubun yawa idan kuka keta mata mutuncin ta kuka wulakanta ta".
Jin abinda Asabe take cewa a matukar gigice Safah ta mike tsaye tare da nufar kofar fita tare ta garadan sukai suna finciko ta zuwa cikin dakin daya yace"ke dalla zonan gidan uban wa zaki fita"?ya fada yana fisge hijab din dake jikin ta kara ta saki tana fashewa da kuka ta soma kwalla kiran BAFFA BAFFA ka taimake ni zasu kashe ni.
Dariya Asabe tayi tana cewa"ai yarinya ki daina bata bakin ki domin kin makaro baffan ki yasha maganin bacci bazai san me yake faruwa ba kuma zan baki gargadi idan har gari ya waye kika ce nice nasa a miki haka wallh kashe ki zanyi idan kunne yaji to jiki zai tsira".
Saboda tsabar Safah bata cikin hankalin ta batasan me Asabe take cewa ba damuwar ta rikon da wannan katon ya mata burinta ta samu ta shammace su ta gudu juyawa Asabe tay tana fita a dakin".
Yayin da dukka su biyun suka rufu a kanta kowa da inda ya nufa kuka Safah keyi mai taba zuciyar mai sauraron ta ganin fa idan ta sake da gaske zasu keta mata mutuncin da Asabe tace gashi danne tan da sukai ko motsin arziki ta kasa.
Idon tane ya sauka akan kwalbar data dora maganin sauro akai baima daina ci ba hannunta ta mika da kyar ta samu ta dauko ta daidai dayan ya mike tsaye zai cire wandon sa wanda yake riken da ita ta saici goshin sa wajan saman kansa ta kuwa yi sa'a yayi aski malu ta sakar