Author : Yusrah Musa Abubakar Category : Hausa Novels 001
ance kina nema na"?.
Kai Ammy ta daga eh ina neman ki hanne dama mai martaba ne ya kira ni dazu akan wai yana neman shawara ta zai tura Abdul-jabbar aikin soja nace masa eh sbd ina ganin wannan hanyar kadai zanbi na kuntata wa Abdul-jabbar nasa a gana masa azaba ya kasa jin dadin zaman duniya ya gwammace mutuwa da rayuwa".
Kara dukawa hanne tay "haka ne ranki ya dade to amma indai kina son hakan saidai kar Amfal ya bishi domin idan suna tare burin ki bazai taba cika ba GAmfal da Abdul-jabbar akwai kauna da shakuwa mai karfi tsakinin su kuma zai wahala nan gaba ki samu kan Amfal domin Abdul-jabbar yana da shiga rai kamar yadda mahaifiyar sa take".
Mikewa Ammi tay tana cewa"da kyau hanne tunani mai kyau zan koma gurin mai martaba na fada masa cewa Amfal bangaren likitanci zaiyi shine kadai hanyar raba su na gode sosai hanne tashi kije kuma kada ki bari kowa ya sani ni da ke ne idan maganar nan ta fita kinsan sauran".
Jiki na rawa hanne tace"a min afuwa ba wanda zaiji hakan".
"Ok yayi jeki".
Bayan fitar hanne Ammi tay shiri ta koma gun Emir da salon jawo hankali saidai ta makaro baya magana biyu yace shawarar farko data bashi yafi so iya tashin hankali Ammi ta shiga har bacci ta daina yi amma hakan baisa ta juya ra'ayin Emir ba kuma tana ji tana gani suka tafi UK a tare yayi da har ramar bakin ciki tay kullum tana cikin saka da warwara".
Sauke ajiyar zuciya Ammy tay bayan ta dawo daga dogon tunani ta kalli kofar da suka fita rai bace ta soma magana "laifi nane tun farko dana bawa mai martaba gurguwar shawara amma ba komai indai ana tare Abdul-jabbar nayi alkawari baza ka taba jin dadi ba duk hanyar da nasan zaka kuntata zan bita komai had'ari kuwa saina kaika kasa".
Har kamar ni Adama wai dan dana haifa zaice bani da wani amfani a gunsa saboda da kai lallai Abdul-jabbar ka kira mutuwar ka saika gane kuren ka domin kai d'ana bai ganin daraja ta ".
MRS AL'AMEEN AHMAD CE๐.
ANA TARE INSHA ALLAH.
Yaukam na gama typing sai idan Allah yaja kwanan mu zuwa gobe saimu dora inda muka tsaya.๐
Typing๐ฒ
๐๐๐๐๐๐
SAFREEYYAH
๐๐๐๐๐๐
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION๐๐ซ
๐๐ Yusrah Musa Abubakar
BARKAN MU DA KWANA 'YAN GROUP DINMU NA ANNURI AND VIP WOMEN24 TV DA GROUP DIN HAJARA @BLA & NI,'IMATULLAH FANS GROUP GA GAISUWA MAI TARIN YAWA DAGA YUSRAH .๐๐๐.
Start your day beautifully with fajr prayer and quran recitation.
O Allah s w t make us among those who never miss salah๐ AMEEN๐๐.
Yan uwa mu dage never stop learning because life never stop teaching.
Yusrah Musa Abubakar
#YUSRAH#
NO.05๐ 06
Shiru tayi sai kawai wani abu ya sake fado mata lokaci mai tsawo daya wuce ta riga maman Abdul-jabbar auren Emir kuma ta dade bata haihuwa bayan mutuwar uwar gidan sarki ya auri maman Abdul-jabbar ta wata hanyar ban mamaki da ba zata manta ba.
Mai martaba yaje ziyara masarautar adamawa ya kuma yi kwanaki sakamakon dama can shida sarkin adamawa abokanai ne na hakika bayan yayi sati ya nemi komowa gida .
Bayan sunyi ban kwana da sarkin adamawa kuma yayi masa rakiya mai dan nisa suka sake yin ban kwana barowar su adamawa kadan suka riske wani karamin kauye dake bakin titi a hanyar kuma dama suna bukatar ruwa zasu zubawa mota dan hakan sukai parking a bakin titin.
Driver ya fita domin samo ruwa amma abin mmk garin kamar anyi yasa babu kowa a waje gashi ba halin ya shiga gidan mutane yana cikin tsaye wata kyakkyawar yar fulani tazo wucewa da korai da yawa a kanta kamar yadda fulani keyi idan zasuje tallen kindirmo(nono).
Da sauri ya tare ta yana cewa "dan Allah idan kina da ruwa kidan bamu zamu saka a mota dakatawa tay tare da juyowa tana kallonsa tace"daga ina "amsa driver ya bata sarkin kano ne munzo ziyara masarautar ku ta adamawa zamu koma gida".
Kai ta daga tana cewa"to jira ni anan bari na kawo muku "sauke kayan tay tana shiga wani gida sai gata ta fito da guga taje wata rijiya can nesa kadan ta debo masa cikin kwaryar ta daya tana kawo masa godiya yayi tare da karba yaje danya sawa mota tana tsaye tana jiransa duk abinda ke faruwa Emir na ganin su maganar ce dai bayaji.
Mayar mata kokon driver yay zai juya ta ciro katuwar kwarya mai cike da kirdirmon tana bashi tace"wannan kyauta tace zuwa ga sarki ina mika gaisuwa amsa driver yay cikin mmk yace" kuma kwaryar taki fa,"?murmushi tay tana daukar kayan ta tace ba komai jeka da ita".gdy ya mata.
Sannan cikin girmamawa ya koma mota yaiwa Emir bayani umarni ya bashi cewa yabi bayan ta yaga inda zata shiga yazo ya fada masa"kamar yadda yace haka ya rika binta a baya har ta shiga wani gida sa'an nan ya komo ya fadawa Emir daga haka yace su kama hanya".
Abu kamar wani almara kullum Emir da ita yake kwana yake tashi ga yana yawan yin mafarkin ta tun abin baya damun sa har yazo yake hana shi gudanar da mulki yadda ya kamata karshe saida ya dangana gurin mahaifiyar sa hajiya ya mata bayani kuma ta gamsu har yadda baiyi tunani ba ya dauka zata masa fada cewa zai auri talaka yar kauye wacce ba jinin sarauta ba amma sai yaga sabanin haka yayi matukar farin ciki kuma yasa a shirya masa tafiya zuwa garin dan hajiya tace harda ita za'aje.
Alhmdllh sunzo kauyen malam na Allah kamar yadda mutane sukaiwa garin lakabi domin wani babban malami ne da ake cewa baba na Allah ya fara kafa garin kuma shine mahaifin wannan yar fulanin.
Da yake drivern yasan gidan sai basu sha wata wahala ba suka je a kofar gida suka samu malamin yana karatu yayi matukar mamakin ganin su da kalar hamshakan motocin da irin suturar jikin su dake nuni da cewa sudin yan gidan sarauta ne.
Sallama suka masa ya amsa cikin aminci duk zaton sa hanya ce ta bace musu sai yaji labari sabanin haka cewa gurin sa suka zo .
Cikin gida ya shiga yana sanar da matar sa cewa sunyi baki ta shinfida tabarma yadda yace haka tay sannan ya koma waje ya shigo dasu.
Sosai sukai mamaki jin abinda ya kawo su da kuma silar hakan ita kanta fatima dake nesa dasu tana hura wuta saida gaban ta ya fadi jin sarkin kano ne data bashi ruwa yasa a mota kuma cewa wai yana sonta shine abinda yafi daga mata hankali su kansu iyayen ta sunyi mmk kuma basu amince ba dan sarkin ya fi karfin auren yarsu.
Cikin nuna karamci malam na Allah yace"to alhmdllh masha Allah gaskiya naji dadi da nuna kaunar ka akan yata kuma na gode saidai ina mai baka hakuri bazan iya baka auren diya ta ba bawai dan wani abu ba a'a kawai dai kayi hakuri".
A marairaice Emir yace"dan Allah na roki wannan alfarmar ka tausaya min ka bani auren Zarah ina sonta".
Hadiza babar su Fatima dake gefe tace "hakurin dai shine yafi alkairi don yarmu ba sa'ar auren ka bace kafi karfin ta".
Kafar malam Emir ya rike cikin magiya ya ce "dan girman Allah ka taimake ni wallh nayi alkawarin rike ta amana".
Shiru malam yai domin Emir ya tokare dukkan hanzarin da yace dan girman Allah to saidai ya bayar dan Allah din.
Sosai hajiya ke musu magiya domin tasan irin mugun halin da danta zai fada idan basu bashi auren yarta su ba dakyar suka amince a gurin suka yanke mgn da komai wanda hakan ba karamin farantawa Emir yay ba .
Da suka tashi tafiya ya nemi a bashi damar ganin fatima amma saita gudu dole ya hakura suka tafi kamar yadda suka ce a wata uku za a tsaida maganar aure haka akai .
Ganin ta shigo dakin su da gudu yasa Zainab tace"ya haka yar kauye kawai sai kace wanda suka ce zasu gudu da ke ni kinzo zaki balla min kafa ki cuci Abubakar dina ".
Shiru Fatima tay Zainab taci gaba "kuma yanzu idan Saminu yaji me zaki ce masa gashi wani yayi masa shigar sauri".
Kamar zatai kuka ta kalli zainab tana cewa"ni wallh ban sani ba har kunyar fita nake ji tun kafin ya sani ina ma nayi aure kafin mu hadu".
Zainab tace"tab ai kuma duk dadewa ba zakiyi ba saikun hadu din tunda shine mijin idan Allah yayi zamu sha taushe".
Harararta Fatima tay"wai nikam ba nike gaba dake ba yaushe na zama abin tsokana"? Dariya zainab tayi sai kuma ta rufe baki tana cewa"yi hakuri mantawa nayi".
Mikewa Fatima tay tana cewa"eh mezai hana ki manta tunda kafadar ki ta taro tawa bari nabar miki dakin saiki cinye".
Fita tayi tabar zainab na dariya da kuma tunanin abinda ya faru mai kama da tatsuniyar gizo da 'ko'ki.
Nan gari ya dauka cewa malam na Allah ya koma na Allaro zai sayar da yarsa yaga kudi ya gigice idonsa sun rufe ya manta malinta sosai maganar tai maasa kuna amma ya shanye bai taba tankawa ba.
Abun yana mugun damunsa har saida ya samu matar sa suka zauna yace"Hadiza kinji irin maganganun danake gudu ko gashi yanzu gari sai gulmar mu ake wai mun sayar da Fatima kiga fa gashi Zainaba almajiri na Abubakar zan bawa auren ta amma ban fita ba sai naji ana cewa wai dan kar ace na damu da duniya ne a zage ni me yasa mutane basu da adalci komai baza kai musu gwanin ta ba duk abinda kai a matsayin baka tsoron Allah kake".
Hadiza tasan za'ai haka amma dole hakuri zasu dauka kuma su toshe kunnen su dan haka hakuri sosai ta bashi tare da kwantar masa hankali.
Lokaci yayi kuma an daura auren dukkan su yayin da yan garin suka samu kyautuka a gurin sarkin kano wanda sunyi mamaki a ranar Fatima tay bankwana da iyayaen ta amma Emir yace ya dace suje suga mahallin yarsu malam yace a'a inda rai wata rana zasu zo haka kuwa aka wuce da ita tana gani ta koma sabuwar rayuwa.
Yayin da ita ma yar uwar ta take kauyen su da mijin ta Abubakar kuma suna zaune lafiya.
@Taskar Annuri writer's masu hankali da nutsuwa.
MRS AL'AMEENAHMAD CE.
TYPING๐ฒ
๐ซANNURI WRITER'S ASSOCIATION๐ซ
Godiya ga masoya sosai sosai godiya.
๐๐๐
Friday may Allah accept your duas and protect you&your families from all calamities Ameen๐
May Allah open the door of success and happiness for all of you(Muslims)Ameen๐.
JUMA'AT MUBARAK๐
๐๐๐๐๐๐๐๐๐
#YUSRAH#
NO.07๐ 08
Lokaci mai tsaho ya wuce har Fatima nada ciki da Fatima taga gata sosai dan Emir ya auri mata da yawa basu haihu ba yayi zaton a shine sai kuma yanzu daya budi ido yaga Fatima da ciki abinda bai taba zato ba.
Hankalin Adama(Ammi) ya tashi sanda ta bude ido taga Fatima da ciki ba hanyar da bata biba dan zubar dashi amma ta kasa sbd tsaron da Fatima take samu a dai dai wannan lokaci ne itama Ammi ta fahimci tana da cikin wanda hakan ba karamin sanya ta farin ciki yay ba dashi kansa Emir da kuma hajiya sosai ake tarairayar su Ammi ganin tana da ciki kuma nata mai mugun laulayi ne kullum tana cikin jinya saita dauke hankalin ta akan Fatima ta koma jida kanta.
Sanda cikin Fatima ya isa haihuwa ita kuma Ammi yana wata hudu ranar juma'a ta tashi da nakuda sosai wanda ba shiri akai asibiti da ita kuma bata iya haihuwa da kanta ba sai cs akai mata aka fito da kyakkyawan baby boy fari tar kamar uwar sa.
Fadar farin cikin da masarautar ta shiga bazai yuwu ba kawai dai sunyi farin ciki kuma ba'a bata sallama saida jikin ta ya warware kana suka dawo gida ranar da suka dawo kwanan babyn tara dan haka washe gari akai shagalin suna kuma baby yaci suna mahaifin Emir wato"ABDUL-JABBAR"yan uwan fatima sunzo kuma da suka tashi tafiya bayan suna suka nemi tafiya da ita Emir bai hana ba.
Watan ta biyu akaje da tawaga aka dauko ta a dai dai wannan lokacin kuma itama ammi ta haihu namiji shima ranar suna yaci sunan kanin mahaifin Emir wato"AMFAL"hakan ba karamin farin ciki yasa sarki ba ganin Allah ya azurta shi da samari guda biyu lokaci daya.
Wata rana kawai fatima ta tashi da wani irin zazzabi daya firgita Emir dan haka asibiti suka wuce a duba lafiyar ta abu kamar wasa duk iya kokarin likitoci ba suyi nasarar samo ranta ba domin lokacin rayuwar ta ya kare.
Bazan iya fasalta muku irin tashin hankalin da kowa ya shiga ba dan Emir gado aka bashi a asibitin sbd tunda akace masa ta rasu ya fadi a gurin ya suma abin tausayi dole bada shi aka raka ta makwancinta ba daya farfado yayi kuka yayi bakin ciki ya dangana kuma dukkan soyyayyar sa ya tattare ta akan marayan dansa yana matukar tausaya masa da baisan komai ba.
Ya nemi Ammi ta hada su ta shayar amma sai tayi masa wani kallon bazan yi ba tana cewa "gaskiya ranka ya dade bazan iya shayar da har yara biyu ba danni ban zama nanni ba dana ma daga dole nake shayar dashi kawai ka nema wacce zata kula maka da danka nima naji da nawa".
Wannan magana ta bakantawa Emir rai cikin bacin rai yace"Adama ni kike kallon tsabar idona kina fada min mgn son ranki nagode ta inda Fatima ta fiki kenan a gurina har kwanan gobe da soyayyar tanake kwana itace jigon numfashi na da ana munsanye wallh dana zabi Fatima ta dawo gare ni itace matar data dace dani ba keba Adama".
Kuka Ammi ta saki cikin shashsheka ta soma mgn"yanzu ranka ya dade ni kakewa fatan mutuwa sbd wata yar talakawa wallh bazan yarda ba".
Sarki dake kallon ta da wani irin bacin rai dukawa yay yana daukar dan dake cinyar ta yace"hawainiya ma da take tashi taga ba uwa ba uba ba gatan kowa Allah ne ke kula da ita don haka wannan din ma ai dana ne shima basai kin shayar dashi ba zan kaisu gidan rainon tare sai ki zuba ruwa a kasa kisha".
Cikin tashin hankali Ammi ta fara bashi hakuri yay banza da ita yana fita binsa tayi tana kuka har sashin hajiya a gaban hajiya ta zuba gwiwoyin ta tana kuka tace"dan Allah hajiya na roke ki kice ya bani dana wallh na tuba zan shayar da su dan Allah ranka ya dade kayi hakuri bazan sake ba".
A tsawace Emir yace"ta fice daga nan din kafin ya tura ta gidan su jin haka tasan saki yake nufi ita kuma tana mutuwar son shi dan haka da gudu tabar inda suke tana fita ko kwali babu a kanta kamar sabuwar kamu.
Tana ji tana gani aka kai su gurin raino da batasan ko ina bane kullum cikin magiya da bada hakuri take amma amsar daya ce ta gama bawa Amfal nono har abada.
A kwana a tashi ba wuya har suka isa yaye sannan Emir ya karbo su ya dawowa da hajiya su ya hana Ammi Amfal haka suke ta girma agun hajiya har suka isa moro suka kai matsayin makaranta kuma aka saka su tare komai tare suke ba abinda yake rabasu duk zaton su hajiya ce babarsu.
Emir yakan dauki Abdul-jabbar lokaci zuwa lokaci ya kaishi garin su fatima yayi kamar sati sa'an nan yaje ya dauko shi .
Wani abin ban tsoro zainab kanwar Fatima itama ta haihu diya mace ansa mata suna SAFARA'U saidai ita daga kwanciya bacci ma aka tashi babu ita ta rasu lallai malam na Allah ya dau dangana yayin da kowa yake matukar tausaya masa a yanzu haka baida da ko daya dama iya sune kuma sun rasu.
Bayan girman safara'u Abubakar yayi aure saidai baiyi dacen mace ta gari ba domin safah bata samun sassauci ko kadan a gurinta kullum cikin ukuba take amma da malam na Allah ya nemi karbarta sai abubakar yace yayi hakuri in sha Allah zaidau mataki.
Haka gidan Emir ke rayuwa cikin aminci da kaunar yayan sa har suka dago samari sosai kuma a wannan lokacin ne sarki ya nemi shawarar Ammy kan yana so Abdul-jabbar zaije aikin soja tace hakan yayi ita a nata ganin mugunta tayi masa kuma sai hakan yafi masa alkhairi abunda ya faru kenan a baya kafin wannan lokacin.
Tofa ๐ค hakan na nufin da mahaifiyar Abdul-jabbar da mahaifiyar Safara'u uwa daya ubah daya suke?๐ tab muje zuwa.
Zama Ammi tay jagab akan kujera tare da zuba tagumi lallai tana bukatar shawara idan ta sake Amfal zai mata nisan da baza ta iya janyo shi gare ta ba yanzu mene abin yi ta ina zata fara?ta tambayi zuciyar ta shiru tay babu amsa dole ta hakura zuwa wani lokaci kafin hanne ta dawo.
Bayan fitar su kallon Amfal Abdul-jabbar yay yana rike masa kunne yace"sai yaushe zakai hankali ne?kai kowa ma ka mayar dashi kakan ka Ammi fa mahaifiyar kace ya kamata taji dadi ka rungume ta kasan dadin uwa ina fada maka haka a matsayi na na dan uwan ka ba wai ina baka umarni bane ita uwa dadi ne da ita duk da ban sani ba amma ance kowa ya rasa ta yayi kuka shi yasa nake gargadin ka kai da ka samu taka a raye please ka shiga jikin ta ka samu wannan dadin da ake fada wanda a kullum ni ina kwadayin hakan amma na sani bazan samu ba har abada".
Kallon sa Amfal yay jiki a sanyaye yana rungume shi cikin tausayawa muryar sa harya fara rawa yace"dan Allah ka daina cewa haka ka kaddara dukkan mu ni da kai marayu ne bamu da uwa ina tare da kai dan uwana iya rai da mutuwa komai namu daya ne ".
Murmushi Abdul-jabbar yayi yana kallon shi yace"to naji lokacin magriba harya wuce ya kamata muje muyi sallah sai mu koma gurin hajiya kar kasa tayi ta jiran mu kuma bamu koma ba"wucewa sukai suna hira cikin jin dadin kasantuwar su tare a koda yaushe.
Typing๐ฒ
######################
#############=##=####
################=##
####===#==##=####=
#########====###
#############
###========
####===#
#####
##=
#
Kuna ina yan group ku fito na shigo๐๐.
Wannan page din naka ne dan uwa rabin jiki Cpt.SALEEM MUSA ABUBAKAR mai tambarin no going back .
๐Yusrah Musa Abubakar๐ก
๐ซANNURI W ASSOCIATION NAKU NE๐ซ
Prophet Rasoolullahi s a w peace be