Chapter 7 Reading SAFREEYYAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY Yusra Abubakar Musa.txt Arewa Novels

SAFREEYYAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY Yusra Abubakar Musa.txt

Author :  Yusrah Musa Abubakar Category :  Hausa Novels 001

Chapter   7 / 15

18K to 21K   out of 43.4K words

a gwiwa ba zan tashi tsaye na kokarta da dukkan karfi na kimin rai".
Tsaki Ammy taja mai karfi tana sakar mata harara tace"ke kika sani kuma ke ya dama 'bace min da gani bana bukatar sake ganin ki kada ki kuskara ki sake nufo ni idan ba harda daddad'an labarin da kika san zai sani farin ciki ba 'bace min da gani zaman ki anan din babu abinda yake haddasa min banda bacin rai".


Mikewa hanne tayi jiki a sanyaye tana cewa"tuba nake ranki ya dade kiyi min hakur.............bata karasa ba da saurinta ta fice har tana yin tuntube bata saurari zafin da kafar ke mata ba da gudu ta karasa fitowa daga sashin Ammyn tana komawa can yakin su na bayi sannan tsaya a saitin wata yar karamar shukekkiyar bishiya tana duba yatsan harya fashe jini ya fara fita tsaki tayi .


Tana cewa"azzalumar mata kawai zata sa na cire yatsa na a banza kece dai shashashar mace wacce batasan abinda take ba amma badai niba dan wallh sau dubu na fiki hankali nasan kuma abinda nakeyi da wanda zanyi ya amfane ni domin idan nice a matsayin ki bazan takura kaina da wannan sokoncin kudirin naki ba kodan na samu soyayyar sarki aina rike masa wannan tilon dan nasa Abdul-jabbar amma da yake ke sha ka tafi ce bugun shaho kuma awon igiya gariya kika biyewa jakar zuciyar ki wacce bata saka miki komai sai gidadanci ina tausaya miki Adama kiyayyar da kikewa Abdul-jabbar ba gata ki kaiwa kanki ba kuma tunda kika zage ni kika cimin mutunci kika kaskanta ni dan kina gadara ke matar sarki ce ba matsala ta bace ba ruwa na da hakan zaki gane shayi ruwa ne bazan sake wahala akan cikar burin kiba kasuwanci zan farayi da tunani ki wacce ta rako mata asararriya kawai".


Ta karasa maganar tana kallon gefe da gefe ko wani na jinta ganin babu alamar kowa yasa ta sauke ajiyar zuciya tana rufe idon ta taje tunanin lokacin data kama Ammy na maganar.




Shekaru masu dan dama da suka wuce Hanne ce tafe rike da babban tray wanda ya kasance cike yake da kayan marmari ta shiga part din Ammy jin ana maganganu yasa taja ta tsaya tare da kashe kunne ji tayi yaro mai karamar murya na cewa"Ammy ki bani inibi da dabino yau Abbana baya nan kuma yanzu naje be dawo ba".




Cikin tsawa Ammy tace"fita anan jimin munafikin yaro harda wani na baka inibi da dabino da yake Fatima ce taban ajiya kanta sheka lahira shiyasa zaka zo ka tambaye ni da kasan yadda na tsani ganin ka da baka iya doso niba kuma nice ajalin ka saina bakantawa rayuwar ka na kuntata ma baza ka taba jin dadi ba har ranar mutuwar ka".


Tana kaiwa nan ta juya zata fara tafiya da gudu ya bita ba zato taji ya rike ta a fusace ta juyo tana fisge hannunta tare da tsika masa mari wanda saida ya kifa a gigice cikin azaba da dauriya ya mike wani irin dundu ta sakar masa tana cewa"hannu na yayi kama dana uwarka ne da zaka zo ka rike ni wallh yaron nan saina kashe k...............


Kasa karasa maganar tay ganin hanne tsaye kuma da alama ta dade da zuwa zaro ido tayi tana kallon hanne tace"ke kuma uban me ya kawo ki nan din a wannan daren lallai zakisan kin ganni ina azabtar da wannan yaron kuma duk wanda kika kuskura kika fadawa hukuncin ki kisa ne a wajena dan duk wanda yasan sirri na bai kamata ya rayu ba mutuwa ce tafi dacewa dashi ko waye".


Hankali a tashe hanne ta zuba gwiwoyinta a kasa jikin ta yana tsananta karkarwar tsoro dan sarai tasan Ammy zata aikata fiye da haka ta soma bata hakuri kallon ta ammi tay naji wannan kafirar magiyar taki ta ishe ni jira ni nan ina zuwa"tana fadin haka ta bude wata kofa ta shiga tare da rufowa da karfi wanda saida hanne ta toshe kunnen ta saboda kara.



Shiru shiru ganin taki fitowa gashi dare yaja sai hanne tay tunanin ko ta manta ne wata zuciyar tace mata ko kuma tayi bacci ba ki tafi kawai gobe kya dawo"mikewa tay tana karasowa ta aje kayan marmarin har zata juya ta tuna yaron da ammi ta mara kallon gurin da yake tayi yana kife har lokaci tun sanda ta mare shi a firgice tayi gurinsa da sauri tana dago shi cikin tashin hankali ko duk zaton ta ya mutu ne amma sai taga akasin haka yadai hada gumi shakaf ya jike waige waige ta fara can ta hango wani karamin towel cikin hanzari ta dauko ta goge masa gumin sannan ta rike hannunsa cikin sanda ta bude kofa suka fita.


Ko ina da haske saidai ba mutane duk an kwanta bacci sun danyi tafiya mai tsayi kafin su karasa sashin hajiya ta tsaya dashi a wani sako tana kallon shi murya kasa kasa tace"Abdul-jabbar me ya kaika gurin Adama tsautsayi ko? kaima kasan ba sonka take ba ka daina zuwa inda take kana zama gurin hajiya ko Abbanka baya nan kuma idan gari ya waye karka fadawa hajiya cewa ammi ta mare ka zaka jawo fitina da tashin hankali a masarautar nan wanda ba'ai zato ba akan haka sarki na iya sakin Adama dan haka kai shiru da bakinka Allah zai saka maka kaji"kai ya daga mata bayyi magana ba.


"Yauwa dan albarka insha Allahu wata rana sai Adama taci arzikin ka kuma ta zauna a karkashin inuwar ka kuma nayi alkawari daga yau zan zama mai kula da dukkan wani motsin ka ta asirtacciyar hanya ba tare da kowa ya sani ba domin mahaifiyar ka Fatima ni tayi min komai a rayuwa itace ta kaini matsayin da nake yanzu kuma har abada bazan manta wannan alkhairin nata ba muje na raka ka" Hanne tace tana jansa suka karasa part din hajiya .


Masu tsaron kofar tane suka tare hanne suna cewa"daga ina meya hada ki dashi kina matsayin baiwa kinsan idan sarki yaji labari sai an kaiki gurin horo an tambaye dan haka fadi gaskiyar inda kika ganshi"?.


Hanne da duk ta rikice jin abinda suka fada kuma tasan ba karamin aikin su bane suce sun ganta dashi su jawo mata masifa dan haka saita yanke shawarar kawai ta musu karya donta kubuta daga zargi,kallon su tayi tana cewa"na fito ne zan rufe kofar sashin bayi kawai na ganshi a tsaye yana waige waige shine na tambaye shi ina zaije sai yace gurin hajiya shine fa na taho na kawo ba wani abu bane ku yarda dani gaskiya nake fada muku".


Wanda ya karbi Abdul-jabbar ne yace"shikenan to yayi jeki"yana fadin haka ya budewa Abdul-jabbar din kofa ya shiga ita kuma hanne ta juya tana komawa yankin su na bayi cikin tausayawa yaron da ko mahaifiyar sa bai sani ba.


Washe gari hanne na gurin aiki sako ya isketa daga uwar gidan sarki cewa tana son ganin yanzu kuma kada ta haura mintu guda bata jeba jikin hanne na rawa da gudunta ta isa part din Adama kishingide ta same ta cikin alkebba sai shan kamshi take tana juya kai cikin nuna mulki gefe guda kuma ga wata baiwa durkushe tana mata tausa a kafafunta gaban ta kuma mutum biyu daya na mata firfita da mafici dayar tana yanka tuffa da karamar wuka tana mika mata a baki sannan ga wani tsaye da wata irin murdaddiyar bulala sai zare ido yake yana muzuraiπŸ™Š.



Zubewa Hanne tay duk jikin ta na shaking saboda tsoro murya na rawa tace"ki gafarce ni ranki ya dade gani nazo bisa sawun wanda kika aika kira na tuba nake idan har nazo a makare ayi min afuwa".


Tashi zaune Adama tay tanaiwa bayin alamar ya isa suje bata bukatar ganinsu mikewa sukai da sauri har suna hada hanya suka fita suna mamakin rashin kirkin wannan mace mai tunkaho da jida sarauta ga girman kai fal ciki,.

Bayan fitar su Adama ta maida kallon ta kan wannan mutumin tana masa alama da ido kaiya jinjina sa'an nan ya karasa inda Hanne take babu zato taji saukar wannan zazzafar bulalar ta sauka a jikin ihu ta kurma cikin neman agaji wanda cikin tsawa Ammy tace ta rufewa mutane baki idan ta sake ko tari ne zata sa ayi mata hukuncin daya fi wannan sau dari.


Hanne naji tana gani katon nan ya rika sharara mata bulala cikin mugunta da iya karfin sa saida ya sauke mata guda ashirin duk bayan ta ya kumbura wani gun ma ya fashe sannan Ammy ta kalle shi cikin murmushi tana tace"dakyau yayi kyau haka nake so babu sassauci ko wasa jeka ka gama aikin ka"dukawa yay cikin girmamawa ya kwashi godiya ya mike yana fita.


Ammy dake tsaye ta zauna kan kujera tana kada kafa kuma tana kallon yadda Hanne ke juya kai saboda azaba murmushin jin dadin hakan tayi ta sani ko ba komai yanzu hankalin ta zai kwanta duk rintsi hanne bazata tona mata asiri ba dan duk fadin masarautar itace mutum ta farko data taba kamata tana azabtar da Abdul-jabbar kuma wannan ba shine karo na farko ba.


Mikewa tayi ta tako har inda Hanne take ta fara zagaya ta tana tafa hunnu tace"yadai bulalan akwai dadi ko? humm kada ki damu wannan somin tabi kika gani indai har zan baki umarni ki karya min dokata ina matsayin shugabar ki to kuwa kina tare da wahala kuma zaki kasance cikin ukuba ta babu wanda ya isa jayayya dani ko waye shi dan haka ina mai gargadin ki da ki kiyaye gaba".


Shin jiya raini ne yasa da na baki umarnin cewa ki jira ni ina zuwa kikai tafiyar ki saboda bankai matsayin ki bini ba kuma uban waye ya fidda Abdul-jabbar daga nan yakai shi sashin hajiya ko duk zakice min bake bace na sani dare ne bazai taba iya komawa da kansa ba fada min me yasa kika aikata haka!? A tsawace ta karasa maganar wanda Hanne saida tayi zaman dabas a kasa saboda firgici.



Muryar ta na rawa ta soma magana"dan girma Allah ranki ya dade kiyi hakuri nayi zaton da naga baki fito ba ko kinyi bacci ne shiyasa na tafi da niyyar yau da safe na dawo ba ina nufin karya umarnin kiba ki gafarce ni uwar gidan mai martaba Abdul-jabbar kuma ba nice na kaishi gurin hajiya ba harna fice yana palon nan bansan komai akan haka ba ranki ya dade gaskiya nake fada miki".


Huci Ammy ta fitar tana kallon hanne tace"naji zonan inason zamuyi magana dake ta sirri mene sunan ki"?da sauri hanne ta matso inda Ammin tace mata tana cewa "suna na HANNE" .
Gyara zama tayi tana yin kasa da murya tace"yauwa hanne wata magana zan fada miki kinga duk fadin masarautar nan a yanzu babu wanda yasan sirrina da kudiri na da kuma shirina akan abinda nake kullawa akan Abdul-jabbar saike dan haka zan 'yanta ki na kuma baki babban mukami zaki zama amintacciya ta zan hada hannu dake domin na cimma buri na akan shafe Abdul-jabbar kuma bana bukatar kowa yasan haka, kin jini kin haddace abinda na fada miki"?.


Hanne da har lokacin jikinta bai daina rawa ba tace"eh ranki ya dade zan iya kowanne irin aiki idan kika sani kuma baza a samu kuskure ba bazan taba saba lamba ba".



Kai ammi ta rausaya hakan yayi tashi kije saina neme ki kuma koda wasa kada ki kuskura ki fadawa wani wata magana wannan tsakanin mune daga ni saike bana bukatar kowa".

Godiya hanne tay tana mikewa ta fita tana komawa bangaren su na bayi ruwa mai zafi ta samu ta dumama jikinta tana tunanin maganar da sukai da ammi lallai tana tsoron ranar da asiri zai tonu ace harda ita a masu aikata muyagun laifuna amma dole tabi ammi ba yadda ta iya kodan tsira da rayuwar ta.


Lokacin da hanne ta dawo daga tunanin ta kwafa tay cikin takaici tana cewa"wallh Adama duk abinda kikai min bashi kika ci akwai ranar biya tana nan zata zo bakisan nima ba kanwar lasa bace kowa yaci tuwo dani miya yasha miyar ma ban rage ba kwanon ya side muje zuwa ga fili kuma gamai doki saura sukuwa".





Mrs Al'ameen Ahmad ceπŸ‘

ONE LOVE WE WILL MEET TOMORROW😜 YAN UWA.


TYPINGπŸ“²


πŸ‡
πŸ‡ SAFREEYYAHπŸ‡
πŸ‡


πŸ’«πŸ’« ANNURI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«


STORY & WRITTEN
BY YUSRAH MUSA ABUBAKAR
»«Mrs Al'ameen Ahmad ce»«



Dedicated to
My mum i love u with all my life may Allah accept your du'ah and help you u anywhere u are mamana πŸ‘.



Abubuwan nasiha guda biyar masu tasiri ga rayuwar mai hankali.
Duniyar da za'a barta😧
πŸ‘‰ meya kawo hadama?
Rayuwar da zata kare😟
πŸ‘‰ina wani farin ciki?
Ana sauraron mutuwa😭
πŸ‘‰ina wata walwala?
Jikin da zai zama gawa😒
πŸ‘‰Me zaisa alfahar?
Karshen da makomar sa kabari😭
πŸ‘‰me ya jawo girman kai?
Duk wanda ya manta da wannan😠
πŸ‘‰to ina yabar hankalin sa?πŸ€”.




πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•‹ πŸ•‹
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•‹ πŸ•‹ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•‹
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•‹
πŸ•Œ πŸ•‹ πŸ•‹ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•‹
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•Œ
==================================
πŸ‘ May Allah open the door of success and happiness for all of you(Muslims) may Allah accept your du'as and protect you and your families from all calamities amin, start you day beautifully with fajr prayer and quran recitation, o Allah s w t make us among those who never miss salah Ameen ya AllahπŸ™.
*JUMA'AT MUBARAK*
πŸπŸ‡πŸ“πŸπŸ’πŸπŸ‰πŸŽπŸŠ.




πŸ€— Ina kuke 'knawayen asali ku fito ku taka rawa, 🎢🎹🎻🎷🎀 ga page dinku ya bayyana ku kadai naba dukkan sa as you wish kuyi yadda kuke so dashi mallakin kune har next page na baku just for remember"πŸŒΉπŸ˜œπŸ’.


Hauwa'u Mu'awiyya Umar Kano (maman Al'ameenπŸ’•)
Hafsat Haris (maman Aliyu)
Fatima Idris (maman Usman)
Suwaiba Yusuf (maman Auwal)
Salmah Hayat (maman Afnan)
Latifah Nura (maman boy)
Asma'u Abdullah (maman mhmmd)
Saudat Yusuf Dutse
Khadijah A Yusuf
Zainab Sunusi Dutse
Khadijah Adams Dutse.

😘Mrs A Ahmad ce
=""==""==""==""==""=



#YUSRAHMS#
NO.25πŸ‘‰ 26
Da dare Safah da baba maryam na zaune a daki suna hira sukaji sallamar mk cikin mamaki baba tace"musaddiq kaine shigo mana ince dai lafiya ko hajiya ce ke nema na".
Shigowa mk yay wanda gaba daya hankalin nakan Safah wacce ke kwance kan katifa da wata rigar bacci a jikinta mai kyau kanta ba kwali kuma a tsefe yake tayi donut dashi baki sitik mai santsi sai sheki yake wani irin abu yaji yana tsirga masa wanda ba shakka yau da ace babu baba maryam a dakin nan bayajin akwai wani abu dazai sa ya dagawa Safah kafa dole saiya kasance da ita.


Baba maryam ce data lura dashi tace"musaddiq nace dai lafiya ko"?da sauri ya dauke kansa daga kallonta ya dawo kan baba maryam duk da hankalinsa da nutsuwar shi na wajen Safan dama saboda ita yazo bazai iya bacci ba har idan bai sakata a idonsa ba kallon baba maryam yay yana cewa"amm babu komai dama nazo na sake duba tane yaya kafan nata"?.


Cikin fara'a baba maryam tace"ayya musaddiq da sauki gaskiya ka kyauta wallh yaro mai hankali nagode sosai da kulawa"kai ya daga tare da. kallon Safah cikin daga mata gira yace"ya jikin naki"? Dakyar Safah tace"da sauki tana sakar masa harara, murmushi yayi yana mikewa yace"ga tsaraba nan a bawa mai jinya saida safe"godiya baba maryam ta masa tana cewa"kuma harda abin arziki mun Allah ya kara budi" amin yace yana fita.


Duba kayan baba maryam ta leda biyu daya babba daya karama babbar ta fara budawa dogayen riguna ne guda biyu masu tsada daidai tsayin Safah da takalmi abinda ya bawa safah haushi harda breziyaπŸ˜‚ a ranta tace"jifa dan iska me zanyi da kayan ka".
Dayar ledar kayan baba maryama ta bude sai gashi ta fito da katuwar kaza mai kamshi ga kuma robar ice-cream guda biyu baba maryam tace"kwarai wallh Safah kiga dan albarka ya kawo miki abin arziki gobe kiwa hajiya godiya kuma shima ki masa gaskiya mutanen gidan nan nada karamci".


"Tashi kici" hade rai Safah tay "ni bazan ci kayan sa ba kawai daga ya kawo abu saina kama ci bansan meye a ciki ba duniya daba tabbas" kallo.n ta baba maryam "haba Safah amma kinsan bazaisa maganin mutuwa a ciki ba ko"?cikin shagwaba Safah tace"Allah baba nidai........katse ta baba maryam tay "Allah keme?karki rantse bansan shirmen banza tashi kici inda yana nan ai bazai ji

7 / 15