Chapter 14 Reading SAFREEYYAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY Yusra Abubakar Musa.txt Arewa Novels

SAFREEYYAH COMPLETE HAUSA NOVELS BY Yusra Abubakar Musa.txt

Author :  Yusrah Musa Abubakar Category :  Hausa Novels 001

Chapter   14 / 15

39K to 42K   out of 43.4K words

ya kalleta yana cewa" Safara'u d'an uwanki Abdullahi yazo mana ziyara ya dade a nan bayan tafiyar ki Adamawa inaga dai ba rabon ku gana ko kuma sai bikin nan naki tunda yan kwanaki suka rage sai a sanar dashi kinga da zai tafi ma har wata salula ya barmin wai muna kiran sa niko bansan inda zan kunno maganarsa muji ta ba tana nan a ajiye Hadiza dauko mata wannan salular ta gani ko zata iya danno mana shi".



To Hadiza tace tana mikewa ta shiga daki Safah kam zuba ido tay cikin mamaki taga meye na Allah yake nufi da salula sai taga hadiza ta kawo mata waya keypad a kwallinta tana cewa" gata duba mana tunda ke kinje binni kila kinga ana amfani da ita mude bata shigo mana nan ba".



Dariya Safah tay tana karba tace" wai dama waya kuke cewa salula na dauka wata camera zan gani katuwa bari muga indai akwai kati na kira shi".


Bude wayar tay tana shiga cikin contect ba number sai guda daya itama ba suna tunani tayi may be ko itace number tashi dan haka kawai ta danna kira tayi sa'a kuwa ta shiga saidai harta katse ba'a daga ba dan tsaki tay tana cewa" to ai gashi na kira ta shiga amma ba'a daga ba kodai kawai ya zura ku a kwalba ne"?.


Dariya na Allah yay yana kallonta yace" eh ba'a kwalba zaki ce ba a bututun mai ko mizirari ya samu sake kunno shi mu gani" murmushi Safah tay wai sake kunno shi kamar gidan radio kara danna kiran tay wannan lokacin kuma sai aka kashe.


Na Allah ta kalla tana fadin" to gashi yanzu ma ta shiga ya katse kiran dama dai kila ya baku ne dan kuyi ta kallonta matsayin photo decoration tunda bata da wani amfan........


Bata karasa ba wayar tahau ringtone dan zubawa number ido tay bata daga ba Hadiza tace" to ya kunno naji tana kara kuma banji maganar saba ko saita gama zamu jishi"?.


Kai Safah ta girgiza dariya na cinta jin abinda Hadiza ke fada batai magana ba ta daga kiran tana sawa a handfree ta mika musu".


Kallon ta na Allah yay" me zamuyi ko haka ne kunnowar"? Ba arziki Safah ta mike da gudu tana yin hanyar kofar gida sannan ta saki dariyar da take rikewa tana cewa"kasa a kunne kayi magana zaka ji shima yayi".



"To na Allah yace yana karawa kamar yadda tace yayi yace" salama alekum Abdullahi kana jina"? daga can bangaren Abduljabbar dake zaune yana duba wani littafi yay murmushi yana cewa" wa alaika salam kakana na kaina ya kake" cikin mamaki na Allah yace" lah ikon Allah Hadiza kinji da gaske ta kunno shi".



Karba hadiza tay tana kallon wayar tace" wai Abdullahi maganar ka nake jine" eh nine meyasa idan nakira wayar saina jita a kashe"? 'Yar dariya Hadiza tay tana cewa" ai bamusan yadda zamuyi mu kunno kaba yanzun ma Safara'u ce data dawo daga Adamawa muka ce ta dannoka".



Dan shiru yay zuwa can yace" wace haka? ko yarinyar da kuke cewa sister nace" zaro ido Hadiza tay" tofa meye sister kuma"? dan rike kai Abdul-jabbar yay" ina nufin kanwa ta da kuke fada lokacin da nazo".


Na Allah yace" eh fa Abdullahi ashe baka manta ba itace".


"Ok bata wayan".



Kallonta Hadiza tay" to gwana idan kin gama dariyar zo ki karba zaku gaisa da yayan naki" dawowa Safah tay tana karbar wayan tare da cewa" hello" dan janye wayar Abdul-jabbar yay yana kallon screen din kamar ita yake kallo dan lumshe ido yay tare da cewa subahanallah mene haka yake shirin faruwa dani"?.


Jin anyi shiru yasa Safah ta kalli wayar ganin ba katse kiran yaiba tace" ina yini"? murya 'kar'kar yace" ya kike"? Dan jinjina kai Safah tay wannan akwai jan aji cikin mazewa tace" kalau yaya dama nace bamu taba haduwa ba gashi muna matsayin yan uwa amma dai zaka zo bikina daga nan sai muga juna ko"?.


Cikin mamakin surutun ta Abdul-jabbar yace" eh zanzo saimu hadu" murmushi Safah tay wanda ya jishi tana cewa" to Allah ya kawoka yayana nagode sosai".


"Ok ba damuwa bari na gama wani abu zan kira saimu karasa maganar" to tace yayin da ya kashe kiran yana rufe littafin tare da dan rufe ido.



Ji yay Amfal na cewa" bros dawa kake waya ne naji muryar mace gashi naga ka shiga yanayi kodai aunty na samu you ban sani ba"? Bude ido Abdul-jabbar yay yana kallonsa yace" eh sai akai ya"? dariya Amfal yay" kai koda naji dama naga kwanakin nan kana yawan tunani ashe hubby ne ya shige ka lallai kace zamu sha bikin babban yaya".



Ko kula shi Abdul-jabbar baiyi ba Amfal yaci gaba" Allah bros har naji dadi kaga nima ya kamata na nemo muyi auren nan tare kuma ba zama honey moon ba kama kafar yaro amma wai a ina ka samu lady ban sani ba kuma da yaushe yar wanne garin ce"?.

Girgiza kai Abduljabbar yay yana kallon Amfal yace" oh kaga matsala ta dakai kenan please ka rabu dani karka dora min headache" dariya Amfal yay" ka huta sosai ango nikam na shiga wanka duk daren dadewa da kake boye min auntyn nawa zan ganta" wanka ya shiga yana cewa" wayyo Allah na dadi kashe hajiya bros zaiyi aure" Abdul-jabbar na jinsa bai tamka ba domin Amfal dan caza kaine ko ba nepa dole sai ana masa uziri.

MRS AL'AMEEN AHMAD💝.

TYPING📲
YUSRAH MUSA ABUBAKAR


💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫
Home of hospitality and harmony



#YUSRAHMS#
NO.45 👉 46
Na Allah dake kallon Safah yace" to yaudai kun gaisa saura haduwa itace mai wuya" mikewa Safah tay tana cewa" bari nadan ari wayar nan nayi kira ina dawowa" cikin tsokana Hadiza tace" a'a fa kodai-kodai" fasa tafiya Safah tay ta juyo tace" kodai-kodai me"? Karfa ku fassara ni na Allah yace" kodai-kodai kin kyasa shine zaki mana dan waken zagaye ki kira shi"?.



Yatsina fuska tay" cafdi wa ya fada muku kunji ku da zargi to bashi zan kira ba nayi ya da murtalan"? na Allah yace" ba wani kedai fadi gaskiya karki yaudare mu muji labari ya canza" dariya Safah tay tana fita tace" yanzu zan dawo muku da salular ku".


Tana fita tafiya tay maidan nisa inda tasan ba mutane kuma bamai jinta takarda ta buda tana saka number ta kira bugu daya kuwa ta shiga kuma tay sa'a aka daga mata.


Dan daidaita murya tay tana cewa" hello hajiya ina yini ya gida ina Alawiyyah"? Daga can bangaren hajiya tace" lafiya dawa nake waya ban gane mai magana ba"? dariya Safah tay tana cewa" hajiya nice fa Safah dama kiran kinai mu gaisa a gurin baba maryam na karbi number".


Murmushi hajiya tay" ayya Safah ashe kece ya gida fatan kun sauka lafiya yasu baffan ki? ki gaida min shi da kyau".

Kai Safah ta daga" to hajiya insha Allahu zaiji".


Shiru sukai na wajen minti biyu ba wanda yay magana sai daga baya hajiya tace" Safah ina fatan dai lafiya babu wata matsala naji kinyi shiru meya faru ne ko akwai wani abu"?.


Zama Safah tay kan wata sararriyar bishiya cikin tunanin yadda zata fadawa hajiya abinda ke ranta tace" am dama wata magana nake son fada miki amma na kasa tun muna nan saboda tsoron yadda zaki fahimce ni amma yanzu ya zama dole na fada miki gaskiyar komai danki dau mataki tun wuri".


"Ok Safah ina jinki fada min ko menene zan fahimce ki kar kiji komai ke tamkar 'yata haka na dauke ki".


Sauke ajiyar zuciya Safah tay cikin rashin jin dadin abinda hajiyan zata ji daga bakin ta tace" dama magana ne akan mk lokacin dana bata tsawon kwana uku ba kowa ne ya sace niba sai shi bayan na fito daga part dinku ya shaka min wani abu a hanci daga nan bansan komai ba sai ganina nayi a gidan sa akan gado kuma da nayi yunkurin gudowa ya tare ni a palon sa yace saina amince masa na bashi kaina zai barni na taho hakan shine burin sa kawai a gare ni".


Yayi iya juyin duniya da lallami naki amince masa a gaba na ya kira wata budurwa tazo gidan wai ta nuna min yadda ake wayewa" dan shiru tay sai kuma ta fashe da kuka tace hajiya kinsan abinda sukai a gaba na ya sadu da ita kuma yace wannan ba bakon abu bane a gurin sa yana da yan mata irin ta baza su kirgu ba da naga basa cikin hayyacin su shine na gudo daga gidan saiya biyo ni hanya ya dauko ni ya dawo dani gidan ku".



Shine washe gari da kika tambaye ni ina naje tsawon kwana uku kunya da nauyin ki yasa na boye gaskiya na kasa fada miki kuma yanzun ma dan Allah hajiya ki fahimce ni kiwa mk fada da nasiha kina masa addu'a Allah ya shirye shi amma kwarai yana da hali mara kyau a boye ki yafe min nasan za kiji babu dadi amma nima ba yadda na iyane ya zama dole na fada miki gaskiya".



Wani irin juyi kan hajiya yake jin abinda Safah ke fada mata wanda batai zato ba dakyar tace" na fahimce ki Safah kuma na gode da kika sanar dani wannan sirrin duk da bansan yawan shekarun da aka kwashe mk yana wannan abun ba ki gaishe min da kowa karki damu kuma kiyi hakuri abinda yay miki sai an jima".



Tun kafin Safah tay magana hajiya ta kashe kiran, numfashi Safah ta fitar cikin razani tare da dafe kai gaban ta yay wani irin yankewa lokaci guda bugun zuciyarta ya karu cikin tashin hankali ta fara maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un sai yanzu take jin dama bata fadawa hajiya ba mema yasa ta aikata hakan wanne hali hajiya zata shiga wanne mataki zata dauka akan mk tana tsoron fitina ta biyo baya.



Tunda suka gama waya hajiya ta kira mk cewa yazo yanzun nan tana neman sa kada ya kuskura ya bata mata lokaci gaba daya nutsuwa kaurace mata tayi zulumi bakin ciki sune tare da abinda mk yake aikatawa wanda bata sani ba su kawai take hangowa duk inda ta kalla mikewa tay ta soma zagaya falon ranta na mata suya akan halayyar mk wanda tana matsayin mahaifiya gareshi bata sani ba saidai taji daga wata majiyar amma tayi asara da bata fahimta tun farko ba ta sani cewa indai aka dauko yar aiki bata cin nisan wuta mk zaisa mata kahon zuka saiya kore ta amma bai taba nuna wani abu akan Safah ba saima yabon girkin ta da yake ta dauka gamon jini ne ashe akwai kullalliyar da yake kullawa a boye.




Shigowar mk kenan ya nufi gurin hajiya dake ta zagaye palon tare da cewa" mum gani lafiya naji kin kira ni a waya muryarki wani iri meya ke faruwa"?.


Juyowa hajiya tay idon jawur dashi tana kallon mk a fusace wanda baiyi zato ba yaji saukar wani 'kwak'kwaran mari a fuskarsa kafin ya dago ta kara wanka masa wani cikin kuka ta soma magana" musaddiq ka wulakanta mu ka tozarta mu kayi watsi da tarbiyyar da muka baka ka nuna kaiba d'a nagari bane yanzu dabi'a ce mai kyau wannan ka dauka kamar kaidai kayi asara ace mazinaci ne mai lalata yaran mutane baka tsoron gaba ya naka yayan zasu taso kila ma sannan ba ranka mk me ka rasa tun yaushe nake binka kai aure ka'ki sai kace min da lokaci ashe kasan irin mummunan aikin da kake aikatawa tun kafin lokaci ya kure maka ka tuba ka koma ga Allah ka daina abinda kake idan kaki akwai ranar mutuwa kuma ita kayi shirinta koda yaushe ba'a sa mata rana ka tuba mk ina gargadin ka".


Jikin mk na rawa cikin tashin hankalin ya akai hajiya tasan yana harkar mata ya dago yana kallon ta yace" mum waye ya fada miki wannan maganar? bansan komai ba".


Hajiya da hawaye ke fita a idonta tace" baka san komai ba kana nufin karya akai maka ba halin ka bane mk duk abinda zakai kasa tsoron Allah a lamarinka maimaikon dana fada maka jikinka yay laushi ka tuba zuwa ga wanda ya halicce ka saika nemi karyatawa kana zamewa harda baka san komai ba"?.


Shiru mk yay cikin damuwa hajiya taci gaba" naji kaddara bakasan komai ba sharri akai maka amma Safah zatay maka karya ne baka aikata ba zata cemin kayi yanzun nan muka gama waya daita ta fada min duk abinda kai mata kaiko kunya baka jiba da kuma ace yarinyar bamai nisan hankali bace ta fadawa maryam me kake tunani kudin mu bashi zai ceto kaba da kuma itadin ta kasance mara kamun kai mai watsi da tarbiyyar iyayen ta kamarka saita biye maka kuyita aikata alfasha bamu sani ba harsai ranar tonon asiri randa cikin ya bayyana gareta kasa mu shiga uku".



Cikin sanyin jiki mk ya durkusa gaban hajiya yana cewa" kiyi hakuri mum na bata miki rai".

Cikin tsawa hajiya tace" ka yarda ka aikata kenan ka yarda halinka ne musaddiq bazan gaji da ce maka ka ji kunya ba kuma kayi asara shashashan yaro kawai kuma kada ka kuskura na ganka a palon nan idan na fito zamu neme ka sai dadyn ka ya dawo fita kaban guri karka sa na kama da wuta da zunubin ka".


Cikin jin kunan kalaman hajiya mk ya mike yana fita a palon zuwa harabar gidan ya shiga motarsa tare da kifa kai a sitiyari ya runtse idonsa saiji yay hawaye masu zafi suna diga masa cikin mamaki ya bude idonsa yana kallon mirron jikin motar ganin tabbas shawayen ne da gaske wani irin dukan glass din motar yay tare da furzar da iska mai tsananin zafi yana jijjiga kansa ko tsoron ya masa ciwo ba yay.



Lokaci guda kuma ya tsaya da komai ya nutsu da wani kalar murmushi wanda bamai gane ma'anarsa sai shi yace" hummm Safah! Safah!! Safah!!! Nine kika tonawa asiri kamar yadda kike fada kika sa ni a tsaka mai wuya na rantse da Allah saina nemo ki duk inda kike zan binciko ki saina dau matakin da zaki dana sani baki da wani amfani yanzu a gareni mutuwar ki na hannuna baza ki sake jin dadin zaman duniya ba musaddiq bamai hada kafada dani ki jira zuwana gareki yau-yau din nan basai gobe ba bana tunanin za kiga wayewar gari domin idona idonki saina kashe ki muje zuwa".



Figar mota yay da mugun gudu ya fita a gidan yana tafiya wani gidan nasa da ban ba inda Abidah take ba waccan gidan sirrinsa ne ko iyayen sa basu san da gidan ba acan ya yada zango kafin ya gama shiri ya tafi neman ta.



Safah na zaune har wannan lokacin akan itacen duk jikin ta a mace ta kasa tashi ga hawaye da yaki tsayawa a idonta jin ana kiran sallar magriba yasa ta mike ta soma tafiya zata koma gidan su Hadiza takai musu waya.



Jitay ance" Safara'u daga ina dama ke nake nema tun safe na aiki Aisha gidan ku baffan ki yace kina gidan su na Allah".


A firgice Safah ta juya ganin murtala yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da kakalo murmushin dole tace" au ashe kaine daga ina haka"?.


Shima murmushin yay suna dan tafiya a hankali yace" na karbo mana ankon mune nida ke gashi naki kije dashi gida wannan ledar kuma cingam ne da zaki rabawa kawayen ki akwai kuma bakin lalle da ja yanzu dana sayo miki ki rangada min kunshi mai kyau sannan akwai kudi a ciki abinda kike bukata zaki iya fadawa Aisha saita sanar min sai anjima na wuce gida".



To nagode Allah ya kara arziki" kai ya daga yana wucewa ita kuma ta shiga gidan su malam na Allah domin tay sallah sai bayan isha ta tafi gida.


Misalin karfe goma na dare mk ya fito cikin shirin kaya bakake harda face mask yana saka wata hula wacce iya idonsa ne a waje zai fita kenan Abidah tace" wannan shigar kuma fa kamar wani shedan ina zaka je karfe goma na dare a haka"?.



Juyowa yay yana kallonta da muryar shi data riga ta canza sakamakon magana da baiyi ba tun la'asar yace" gidan ubanki zanje idan kina da sako shegiyar yarinya na sako dake cikin al'amari nane balle kimin shishshigi". Jada baya Abidah tay da sauri tana cewa" Allah ya baka hakuri" tsaki yaja kamar zai shako ta sai kuma ya fasa yana fita daga palon mota ya shiga kawai yabar gidan tare da zaro wata wuka cikin gidan ta sai sheki take dariya yay yana cewa" kwantar da hankalin ki wuka zaki sha jini nan da yan awanni Safah gani nan gareki".



Har kusan asuba mk na yawo amma babu wani haske akan abinda ya fito nema gashi baisan sunan garin ba balle ya tambaya ganin hasken rana ya fito yasa ya cire wannan bakaken kayan yasa riga da wando irin na mutane yaci gaba da tafiya har yazo wata bishiya ga yunwa na damunsa parking yay da motar yana fitowa ko zaiga wani mutum amma dai babu kowa tafiya ya farayi da kafa har yay nisa da motar jin ya gaji tunda bai saba ba ya tsaya a wata rijiya yana zama kan wani dan dutsi dake kusa da ita kafin ya samu wani yazo.



Yana nan zaune wani almajiri yazo shan ruwa mk na kallon sa saida yasha zaitafi yace" kai danzo na tambaye ka mana".

Cikin tsoro yaron yace" a'a malam ya hana mu yace indai mukaga bako ya kira mu ba dan garin nan ba kar muje" jin ya ambaci malam yasa mk yace" to naji basai kazo ba tsaya anan din nai maka tambayar waye babban malami a garin nan"?.


Kai tsaye almajiri dake sidin robarsa ta bara yace" sunan sa malam na Allah" kai mk ya jinjina" yana da wata 'ya ana ce mata Safara'u ko aurenta ma zaiyi"?.


Kai almajirin ya girgiza" a'a malam na Allah bashi da d'a ko daya saidai malamin mu shine yake da 'ya Safara'u ta dawo daga Adamawa ita da baba maryam gobe ma zaiyi aurenta a masallacin juma'a".


Cikin farin ciki mk jin ya samu almajirin mahaifin ta yace" to gaka ma da har ina kiran ka kana kin zuwa dama gidan sa nake nema ni daga birni nake kuma ni malamin tsafta ne muje ka nuna min gidan

14 / 15