DINAAYAH SAFRAAZ Free pages Hausa Novels.txt

Author :  Safraz Category :  Hausa Book Store

Chapter   1 / 7

1 to 3K   out of 19.7K words

[9/9, 7:37 AM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_*
(```DiNaayah SafraAz```)
_*BEtweEn two LoveRs*_


*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim*
_Matar Sayyadee_
_Wattpad @MatarSayyadee01_
_Arewabook@Matarsayyadee0_

~FROM THE WRITER OF;~
*ƘANWAR MATATA*
*BA NI DA GATA*
*ƊAN FAARI*
*SAI A LAHIRA*
*NI DA SHI ABU ƊAYA NE*
*ZINA BABBAR BALA'I CE*
*AUREN CIKIN GIDA*
*GARWASHI*
*ANYA UBANA NE*
*MY DESTINY ( ~ƘADDARATA~)*
_AND NOW_
*DINAAYAH SAFRAAZ (ƘANWAR MATATA RETURN)*

_Godiya ta tabbata ga Allah Ubangiji (SWA) da ya ara min rai da lafiyar soma rubuta wannan littafin. Allah kai na ke roƙo ka ba ni ikon rubuta abunda zai zama hujja a gare ni ba hujja a kaina ba!_

😍💖 *To my lovely and amazing fans, ga ni dai na sake dawo wa domin nishaɗantar da ku tare da ilimantarwa kamar yadda aka saba. Ina fatan ba za ku ba ni kunya ba kamar yadda ni ma ba zan ba ku kunya ba. I know, you guys trust me alot, ba zan cika ku da magana ba ku dai kawai ku yi supporting ɗina ta hanyar subscribing, liking da comment. I swear duk wacce ta bari a kai wannan tafiyar ba tare da ita ba she really miss alot. Duk wacce ta karanta ƘANWAR MATATA na san tabbas a ƙage ta ke da na fara ɗaura DINAAYAH SAFRAAZ kuma ba za ta yarda single page ya wuce ta ba.*

_Greetings to you my earthly paradise (Sayyadee) thanks for the support & encouragement_💖💖

*_Special greeting to you my fansa; Queen Zarah, Rahamatou, Halimatu, Mrs Dimples, Maman Musa, Darma (really miss you), Maman Areef, Sa'adatu etc... You're not just my fans but sisters from another mother. I love your support and caring, love you irin lodi-lodi ɗinnan_*

😍💓 ```My comment section people, ina so ku sani idan fa babu ku babu matar Sayyadee. Da bazarku na ke taka rawa domin ku ke bani ƙwarin gwiwa. Ina yin ku irin totally ɗinnan.```

*_The book is dedicated to you my name sake (Sahibata Oum Mufeeda) and all my family members. Allah ya ƙara haɗa kawunanmu waje guda_* 👊🏼💪🏼

Chapter 001

"Mmm! Ƙamshi mai nake ji haka mai daɗi, Who's cooking mom?" Sauban ya faɗi yana shafa ɗamammen cikinsa bayan ya ajiye handout ɗin da ya shigo da shi a kan cuisine. Mummy da ke zaune a kan 1sitter riƙe da lemon juice tana sipping kaɗan-kaɗan ta ce,

"Dinaayah ce ke girki daga dawowanta yanzu-yanzun nan ko hutawa ba ta yi ba. Hijjab kawai ta cire ta shiga kitchen daga na ce mata ina jin yunwa, kuma na yi-na yi da ita ta dawo ta zauna ni zan yi girkin amma ta ƙi."

"Dinaayah ce fa, ke ma kin san ba za ta taɓa yarda ta zauna ba bayan kin furta kina jin yunwa. To wai yaushe ma ta tafi Abujan da har ta dawo? Ba ta ce sai hutu ya ƙare ba?" Sauban ya faɗi yana ɓalle maɓalli shirt ɗin jikinsa.

"Dinaayah da mugun ƙulafucin kuma! Ni da ma na san ba lalle ta iya yin sati biyu ba balle har wata ɗaya da kwana biyar. Yarinyar da kullum tana manne da ni bacci kawai ke raba mu!" Mummy ta faɗi.

"Hmm, ni dama don kar na yi magana ne aunty Zakiyya ta zage ni shiyasa na yi shuru. Don na san Dinaayah ba za ta iya zaman sati guda a Abuja ba balle wata guda har da ƙarin kwanaki biyar. Yarinyar da ɗakin hajiya ma ba ta iya zuwa ta kwana sai wani gari can daban."

"Wai fa yarinyar nan kuka ta saka masu ba bu dare ba bu rana! Ai kuwa aunty Zakiyya ta duddungure ta sannan ta saka driver ya dawo da ita. Tun suna hanya ta kira ni sai balbala faɗa take yi wai kar ta ƙara ganin ƙafar Dinaayar a gidanta tun da ba ta da kirki."

Dariya Sauban ya yi tare da faɗin, "Ai na san aunty Zakiyya ba ƙaramin shaƙa za ta yi ba. Bari na je kitchen ɗin na taimaka mata."

Gyaɗa kai mummy ta yi ta cigaba da sipping lemon juice ɗin da Dinaayar ce ta haɗa mata shi wai ta soma sha kamun ta gama girki.

Da sanɗa Sauban ya nufi ƙatoton kitchen ɗin da ke falon, sai dai yana zuwa baƙin ƙofar kitchen ɗin Dinaayah ta ce, "Welcome ya Sauban! Don Allah buɗe fridge ka kwaso min carrot manya guda biyar ka yanka min."

"Ke! Wai yanzu ɗinma sai da kika gane na zo kitchen ɗin?" ya ƙarisa maganar yana dungurin kanta.

Dariya ta yi kamun ta furta, "Idanuna ne kawai ba sa gani amma hancina yana jin ƙamshi, tun tsayuwarka na gane ka iso saboda ƙamshin jikinka da na ji."

Yana wanke carrot ɗin da ya ɗauko daga fridge ya furta, "Wai kina nufin duk wanda ya zo kusa da ke kina iya gane ƙamshinsa ko bai yi magana ba?"

Gyaɗa kai ta yi sannan ta ce, "Allah ya ba ni wannan baiwar na jin ƙamshin mutun ko da kuwa za ku saka turare iri ɗaya, kai ko da ma babu ƙamshin turaren kwata-kwata. Mutum na tsayawa kusa dani ko gittawa ta inda na ke zan san ko wanene in dai har na san shi saboda ina iya jiyo ƙamshin jikinsa. Ka san fa ba wai sai lallai da turare kaɗai ake iya gane ƙamshin mutun ba. Ko wani mutun akwai irin ƙamshin jiki da Allah ya yi masa."

Jinjina kai Sauban ya yi yana mai faɗin, "Yau na fara jin hakan a wajanki, amma kuma da ki ka faɗa sai na fara hasaso wani abu. Akwai wani course mate ɗina da na haddace ƙamshin jikinsa. Ko ban ganshi ba da na shaƙo ƙamshi zan kira hakan ko wari oho! Zan gane yana wajen da na ke. Ke wallahi ko rigarsa aka kawo min wanda ban taɓa ganinsa da ita ba in har ya taɓa sakawa a jikinsa zan iya cinkar nasa ne rigar. Warin jikinsa har amai ya ke ƙoƙarin saka ni."

Murmushi Dinaayah ta yi tare da kallon inda ya ke duk da kuwa ba gani ta ke yi ba amma sun haɗa idanu sabida fahimtar ainahin inda ya ke tsaye da ta yi sannan ta furta, "Wata ƙila yana ɗauke da wannan cutar ce ta body odour shiyasa ka ke jin haka. Ni kuma ba irin wannan warin na ke magana a kai ba. Ina fahimta da jin ƙamshin duk wanda ya ke kusa dani in har na san shi sosai. Misali, duka 'yan gidan nan na san ƙamshin su kuma ko cikin magagin bacci idan ɗaya daga cikin ku ya gitta ta kusa dani kai tsaye zan ce wane ne?"

Dafa mata kafaɗa ya yi tare da faɗin, "Ban san mai yasa ba Dinaayah, ban taɓa kallon ki a matsayin makauniya mara idanu ba. Wani lokacin ma mance wa na ke yi wai bakya iya gani kamar kowa."

"Oh, wai ne ma? Amma kuma ni ma ban taɓa kallon kaina a matsayin mai naƙasu ba, don na tabbatar Allah shi ya san dalilin da ya sa ya halicce ni a haka. Ni gode masa ma na ke yi domin bai bani damar ganin ƙazantar da ke cikin duniyar nan ba da na ke jin mutane da dama suna faɗi, kuma ranar tashin ƙiyama idanuna ba za su ba da shaida a kaina ba wajen amfani da su domin kallon haramun. Idan zan roƙi Allah akan ganin wani abu a duniyar nan to zan roƙi ya ara min idanun gani tamkar kowa sau ɗaya tak kawai, shi ma domin kallon littafin Allah mai girma tare da ɗaura hannu akan kowacce kalma ina karantawa sannan kuma in kalli fuskan Mom da Dad ɗinmu! Ina jin kewar idanu ne kawai duk lokacin da na shafa Alqur'ani ko kuma fuskokin iyayanmu."

Dungure mata kai ya yi tare da faɗin, "Wato mu ba za ki roƙi ki ga fuskokin mu ba ko?"

Dariya ta yi sosai ta tare da kai hannu saitin da ta san yana wajen ta shafo fuskansa sannan ta furta, "Na san kalar fuskanka mana! Ai kamanninmu ɗaya da kai sosai kai da ya Sam'an."

Harararta ya yi tamar irin tana kallonsa ɗinnan. Ita kuma da ke juya stew ɗin da kan gas sai cewa ta yi, "Hararata ta ke yi ko?"

Waro idanu ya yi tare da faɗin, "Ke! Ya aka yi ki ka san ina harararki?"

Dariyar ta kuma yi kamun ta ce, "Idanuna ba sa iya ganinka, amma sanin halinka da na yi ne ya sa na ji a jikina kana hararata."

Hannu ya kai ya tallabe ƙeyarta tare da faɗin, "Ke ɗin nan ko? Allah ya shirya mana ke! Wani lokacin sai ki riƙa abu kamar aljana wallahi. Kuma da ki ke wani cewa kin san kamanninmu ɗaya da ke ni da Sam'an ai don kin ji kowa yana faɗin haka ne."

"Ba wani nan! Na riga na sani tun kan mutane su faɗa cewar ni da kai da ya Sauban tamkar an tsaga kara haka muke." Dinaayah ta faɗi tana mai kai hannu ta kashe gas sabida fahimtar da ta yi miyar ta soyu.

Juyawa ta yi tare da nufa wajen dishes tamkar mai idanu ta ɗauko plate biyu. Da idanu kawai Sauban ya bi ta cike da matsanaicin ƙaunarta. Da sosai ta ke ba shi tausayi tun suna ƙanana amma daga baya da ya fahimci irin baiwar da Allah ya mata fiye da masu idanu sai ya ji sam bai kallonta a matsayin musaka wacce ta rasa wani ɓangare na ni'imar ubangiji da ya yi wa ɗan Adam. Dinaayah ba bu takun da bata haddace ba a cikin gidan, kama daga ɓangarensu kaf, ɓangare Hajiya har da ɗakin matar babansu aunty Habbooba kasancewar can ɗin ma dandalin firar su ce idan suka haɗu duka da sauran 'yan uwanta. Shara, wanke-wanke, girki da wanki duk babu wanda ba ta yi. Tun daddynsu na faɗa kamar ya ari baki har ya haƙura ya zuba idanu ganin Dinaayar ita ke ƙaunar haka, kuma duk abunda ta ke so yana mugun taya ta sonsa saboda matsanaicin tausayinta da ya ke ji. Ji ya ke da ana kyautar idanu da ya daɗe da cire nasa idanun ya mallaka mata.

"Kawo plates ɗin na taya ki serving" Sauban ya faɗi yare da amsa ya nufi gaban tukunyar da ta sauke white basmati rice with peas and carrot ya zuba a plates ɗin sannan ya juye sauran a cikin kula ya wanke tukunyar tare da mayar da shi inda ya ke saboda Dinaayar, kasancewar ta san ma'ajin komai a kitchen da store, kuma dokar gidan ce da daddy da mummy su ka na na duk wanda ya yi amfani da wani abu a kitchen ya tabbatar ya mayar da shi inda ya ke. Da wuƙa da kayan wuta irin su blander, kettle, electric cooker da sauransu ne kawai ba ta amfani da su sabida dokar da daddy na kar wanda ya bari ta yi amfani da kayan wuta idan ya wuce maƙala cajin waya, shima charger ɗin na jikin socket sai dai kawai ta danna switch ta kunna tare da maƙala cable ɗin a jikin waya. Sai kuma kunna Braille Display ɗinta (Computer ɗin da makafi suke amfani da ita). Shi ma wani lokuta da dama mom, yaya Sauban ko shi kansa daddyn idan yana gida ke kunna mata. Duk da sau da dama ta fi amfani da Laptop sai ta yi using da keyboard ɗinsu na makafi.

Wajen miyar da ke mugun ƙamshi ya nufa sannan ya zuba a ƙaramin bowl guda biyu sannan ya miƙa mata plate ɗaya ya furta, "Ga na mom ki kai mata sai in fito da na mu abinci."

"Amma tare da kai za mu ci ko?" Dinaayah ta faɗi bayan ta amsa plate ɗin da ya kai saitin hannunta.

"Ke ma kin san ai tare za mu ci. Ko da ma mun taɓa raba kwanon abinci ne idan ina gida?"

Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Kawai na faɗa ne don in ji mai za ka ce."

"To ai kin ji, kuma kin ji daɗin saka ni magana."

"Ina miyar mummy?" ta faɗa kasancewar plate ɗin white rice ɗin kawai ya miƙa mata.

"Na zuba mata a kai ai, ki wuce ki kai mata" ya faɗi hakane duk da bai yi hakan don jin abunda Dinaayar za ta ce.

Dariya ta yi tare da faɗin, "Gwada ni wai ka ke yi? Babu miyan akan wannan abincin da ka ba ni, don da akwai zan ji kamshinsa."

"To uwar 'yan jin ƙamshi! Ki je ki kai zan biyo ki da miyar." ya faɗi yana murmushi da yaba basirar da Allah ya mata.

Shi ma bai iya ɗauko duka bawl ɗin miyar da na su plate of rice ɗin ba, bowl ɗin miyan ya fara kaiwa sannan ya dawo kitchen ɗin ya ɗauko na su ya dawo nan tsakiyar falon ya ajiye.

"Sauko mu ci abincin ga na mu a nan, taku huɗu za kiyi." Sauban ya faɗi yana zuba miya a kan white rice ɗin.

Zama Dinaayar ta yi daidai inda ya ke a gefensa, shi kuma sai ya miƙe ya koma yana facing ɗinta saboda abincin ya masu daɗin ci.

Spoon ta ɗauka ta shiga ɗibar miyan tana sakawa a kan shinkafar kamun ta cakuɗa daidai inda ta saka sannan ta kai baki. Duk wanda ya shigo ɗakin ya ga yadda Dinaayah ke cin abinci cikin mutsuwa zai iya rantsewa da ubangijin halittu tana gani da idanunta in har bai santa ba.

Sallama Aleesha ta yi a bakin ƙofa fuskanta ɓutu-ɓutu tamkar an aiko mata da saƙon mutuwa. Amma idanunta na sauka akan tagwainiyarta Dinaayah ta saki wani faɗaɗɗan murmushi tare da nufar Dinaayar da gudu ta rungume sannan ta ce, "I really miss you my twin sis wallahi. Ai har na fara shirin binki Abujan gobe, ashe ma kina tafe." ta ƙarisa maganar tana mai wurgar da labcoat ɗin da ke hannunta sannan ta zauna a gefen Dinaayar tare da amsar cokalin hannunta ta ɗebo shinkafa ta saka a baki.

Ranƙwashi mai zafi Sauban ya sakar mata a tsakiyar ka tare da faɗin, "Dan gidanku ba ki iya gaisuwa da sannunku da gida ba? Kuma da ki ka zauna kina cin abincinmu, who gave you that permission?"

Murguɗa baki Aleesha ta yi tare da faɗin, "Kai don Allah ya Sauban akwai zafi fa." ta faɗi maganar ne tana sosa inda ya kafa mata ranƙwashin.

Mummy duk tana jin su amma ko kallon inda su ke ba ta yi ba don halinsu ne hakan, suna matuƙar-matuƙar ƙaunar junansu amma kuma duk suka haɗu sai sun yi faɗa.

"Kun duba Benazir kuwa? Yau kwata-kwata ban gan gittawarta ba." mummy Sarah ta katse musu rigimar ta su.

A tare Dinaayah da Aleesha suka juyo suka kalli mummy ɗin tare da faɗin, "Yau bata shigo nan part ɗin ba kwata-kwata?"

"Bata shigo ba kam, kuma daddyn ku ya ce kamar a kwance ya ganta lulluɓe da bargo a falo. Ni ma na shiga duba ta ɗazu amma ban samu ganinta ba saboda tana ɗaki a kwance.

Tsam Dinaayah ta miƙe tare da nufa ƙofar fita don kaf gidan idan aka cire ya Sauban da Aleesha, Benazir ɗin ita ce suka fi shaƙuwa sosai kamar ita ce ma twins sis ɗin tata ba Aleesha ba. Don ko Aleesha sai dai ta gwadawa Benazir ɗin mama ɗaya suka sha amma iya shaƙuwa sun shaƙu da juna fiye ma da Aleeshar ta wani ɓangaren.

"Ki tsaya ki gama cin abinci mana! Mummy ke ma da kin bari ta gama cin abincin sai ki faɗa mata, yanzu gaba ɗaya duk ta tashi hankalinta kuma na san wannan abincin sai wani lokacin kuma," Sauban ya faɗa yana ɗan ɓata fuska.

Dinaayah kuwa da sauri ta ƙarisa ficewa daga ɗakin gudun kar mom ɗin ta su ta dakatar da ita tare da tilasta mata cin abincin kamun zuwa dubo Benazir ɗinta.

Gab! Suka ci karo ta yi saurin ja baya don sam ba ta ji tahowa da ƙamshin mutum ba saboda gaba ɗaya hankalinta ya koma wajen Benazir, "Sorry ya Sam'an ban ji tahowarka bane. Benazir ce ba lafiya shine na ke son zuwa dubo ta."

Fuskan nan nasa a ɗaure kamar ko da yaushe wanda kullum mom sai ta yi ƙorafi a kan haka tare da goranta masa tana faɗin kaf danginta da na mahaifinsa babu mai fuskan shanu sai shi. Sam da mugun wuya mutum ya ga dariyar Sam'an, idan abu ya yi abu murmushi kawai ya ke yi wanda wannan dalilinne ma ya sa ake saurin bambamce su tsakaninsa da Sauban duk da kamanninsu da ya yi mugun ɓaci don hatta thumbprint ɗinsu iri ɗaya ne. Komai na su iri ɗaya sak, fara'ar fuska ce kawai ta bambamta su.

"Kai don Allah ya Sam'an! ka riƙa ɗan dariya ko kaɗan ne idan ba haka ba babu budurwar da za ta soka" ta faɗi tamkar irin tana ganin fuskan nan nasa wanda sam ba haka bane, farin sanin da ta yi wa kaf 'yan gidan nasu ne kama daga iyayanta har ƙannenta da kuma yawan faɗin rashin fara'arsa da mutane da 'yan uwa suke yi. Kuma hakan ba wai yana nufin bai shiga cikin su bane, wani lokacin har abinci ana ci tare da shi.

"Ke! Ina wasa da ke?" ya faɗi fuskan nan nasa a ɗaure amma a wajansa wai a hakan da sigar wasa ya faɗi maganar.

Aleesha da ta biyo bayan Dinaayah ce ta ƙariso inda su ke tare da faɗin, "Mr Boss ka dawo?"

Daƙuwa ya musu su duka sannan ya raɓe su ya shige ciki. Dariya suka kwashe da ita su duka sannan suka riƙe hannun juna suka nufi part ɗin amaryar babansu wato maman Benazir.

Knocking su ka yi sannan suka murɗa handle ɗin ƙofar suka shiga, babu kowa a falon sai ƙamshin turaren kasko da ke tashi yana shiga ƙofofin hancinsu. Kai tsaye su ka wuce ɗakin Habbooba da ke upstairs, Aleesha ce ta murɗa handle ɗin za ta tura ta buɗe sai Dinaayah ta yi saurin kaɓe mata hannu tare da faɗin, "Knock first mana malama!"

Turo baki ta yi sannan ta yi knocking ɗin tare da tura ƙofar lokaci guda. Lokaci guda ta zaro idanuwa akan Benazir da ke zaune dirshan a tsakiyar gado tana cin wafer biscuits da ke cikin wani ƙaton dogon kwali. Sai dai turo ƙofar da Aleesha ta yi ya yi daidai da wani irin zabura da Benazir ta yi har tana jifa da biscuits ɗin hannunta ta ja bargo

1 / 7