Author : Safraz Category : Hausa Book Store
faɗi.
Murmushi mom ta yi tare da faɗin, "Idan ban da rashin hankali da tunani wa zai kawo wannan zancen banza da hofin? Ai ko makaho ya shafa ya san ku ɗin 'ya'yan cikina ne. Ke da Dinaayah ba Identical twins bane, Dinaayah daddynku ta ke kama dashi sak ita da su Sauban, ke kuma da ni kike kama. Amma duk da haka duk inda kuka shiga har Benazir ana kallon ku za a san uba ɗaya ya haife ku saboda jini ɗaya da ke yawo a jikinku."
"Tabbas!" Benazir da Dinaayah suka haɗa baki suka faɗa.
"Gobe dai za mu koma gida in sha Allah. Daddyn ku shi zai zo da kansa ya ɗauke mu." mum ta faɗa.
"Ni bari ma na ɗauko wayata na kira shi, tun da muka zo nan sau biyu kawai muka yi waya da shi" Benazir ta faɗi.
"Shiyasa ya ke ji da Dinaayah, tun da muka zo kullum sai sun yi waya kamun ta kwanta bacci." mum ta faɗa.
Benazir da Aleesha kallon juna su ka yi tare da faɗin, "Kai! Lallai ma Dinaayah shine ko ta faɗa mana.
Miƙewa mummy ta yi tare da harararsu sannan ta ce, "Menene amfanin na ku wayar? Ta fi ku dumuwa da shi ne kawai." tana gama faɗin haka ta fice.
Kiciɓis suka yi da Dinaayah za ta shigo ɗakin itama, "Mum ina wuni? Na idar da sallar." haka Dinaayah ta ke duk ta idar da kowacce sallah sai ta yi gaisuwa.
"Lafiya ƙalau Dinaayah. Ki shiga ciki 'yan uwanki na ciki ku yi hira." tana gama faɗin haka ta gittata ta fice domin zuwa gidan babbar yayarsu Na'ima su yi shawara akan abunda ke cin zuciyarta game da halin da Dinaayah ta ke ciki.
Kai tsaye Dinaayah ta nufe su saboda ƙamshinsu da ta ji wanda shine ya taimaka mata wajen isa inda suke ɗin. Su kuma matsa mata suka yi ta zauna a tsakiyarsu. Tana zama wayarta da ke hannun Benazir ya hau ringing.
_KAISAAR IS CALLING NOW!_
Shine abunda computer ɗin wayar ta ce kamun ta soma ba da sautin waƙar _Ya dab-dab_ wanda shine ringing tone ɗin wayar.
Ajiyar zuciya Benazir ta yi tare miƙa mata wayar sannan ta kwanta flat a kan gadon ta rumtse idanunta da ƙarfi tana jin wani abu mai ɗaci yana tokare maƙonshinta.
"Amin wa'alaikassalam, ina wuni?" Dinaayah ta faɗi a sanyaye bayan ta kara wayar a kunnanta. Murmushi ta saki mai faɗi tare da kuma faɗin, "To ka yi haƙuri don Allah. Tafiyar gaggawa ce ta kama mu, baban mummynmu ne ya rasu shine muka tafi Nassarawa ta'aziya."
Shuru ta yi tana sauraran abunda ya ke faɗi daga can wanda ya sakaa ta yin dariya har sauti ya fito sannan ta furta, "To shikena ai goben zamu dawo In sha Allah. I'm missing you too!"
Ɗaga idanu Benazir ta yi ta kalli Dinaayah sannan ta mayar da kanta. Bata kuma ɗagowa ba har ta kammala wayar sannan ta kalleta tare da faɗin, "Naayah wai yaushe har ku ka yi sabo haka KAISAAR?"
"It's a long story Bena, amma idan mun koma gida zan faɗa miki. Abunda kawai zan iya faɗa miki for now shine cousin sis ɗinsa Aliyaah ce sanadin haɗuwarmu."
"Aliyaah?" Benazir ta faɗi da mamaki sosai a fuskanta.
"Hmm! Sai ka ce baki san Dinaayah ba, ai daddy kawai ke sanin sirrinta. Tun ranar farko da KAISAAR ya faɗawa Naayah yana sonta sai da ta taɗa masa ya bata shawarar abunda za ta yi." Aleesha ta faɗi tana danna wayarta.
"Hmm, lallai!" shine kawai abunda Benazir ɗin ta faɗi tare da lumshe idanu.
Washa gari da wuri daddy ya iso Nassarawa hankali a tashe saboda mummy Sarah ta ɗan soma ƙwanƙwasawa masa abunda ya faru a jiyan. Daƙyar ya samu bacci, ana idar da asubahi ya tada mota ya ɗau hanya.
Tsigar jikinsa mimmiƙewa suka riƙa yi lokacin da ba Lukman ke masa cikakkiyar bayani a kan jinnul ashiq ɗin da ke jikin Dinaayah. Har ƙwalla sai da daddy ya yi tare ɗaukar alƙawarin sai inda ƙarfinsa ya ƙare a kan nema mata magani ko da,kuwa hakan na nufin rasa tasa rayuwar.
"Ku tashi tsaye sosai Ibrahim akan yarinyar nan. Don Jinnul Ashiq wani irin aljani ne azzalumi kuma mai matuƙar naci, don haka kuma sai ku yi naci sosai wajen yin magana da duk abubuwan da na umarce ku da ku yi. Allah ya bata lafiya."
"To amma ba Lukman ya za a yi mutum ya iya gane wani na ɗauke da aljani a jikinsa?"
Jinjina kai ba Lukman ya yi tare da soma magana.
"YADDA ZA A GANE ALJANI YA SHAFI MUTUM:"
a) Alamomin ɓoye (wanda shi mara lafiyar ne kawai ya sansu)
b) Alamomin Sirri (wadanda yan uwan mara lafiyar ne suka san su)
c) Alamomin Zahiri (waɗanda kana ganin mai shafar Aljanu za ka gane)
_Ta ɓangaren namiji:-_
1-rashin sha‘awar aure ko jima’i sam-sam.
2-‘kin miƙewar gaba lokacin da a kai nufin yin jima‘i, alhali kuma haka kawai ma yana tashi.
3-‘kin fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana
iya zama a cikin marainan mutum.
4-saurin gajiya yayin jima‘i da rashin iya komawa
5-jin motsi kamar tafiyar wani abu a gaɓoɓin haihuwa yayin jima‘i.
6-rashin cimma buƙatar jima,i.
7- In ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya dauke ka.
8- Da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo
tun kafin ka fara.
9- komawar gaba da maraina su shige ciki.
10- yawan ciwon kai, Ɓacin rai mara dalili, faduwar
gaba, da dai sauran su.
11- haka kawai sai ka ji ka tsani matarka.
12- Yawan mafarki kana saduwa da wata matar.
13- Yawan samun matsaloli aduk inda ka je neman aure, sai maganar ta lalace.
14- Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai.
15- Matsananciyar sha’awa da tsoron mata da dai sauransu.
YADDA MACE ZATA GANE ALJANI YA AURETA
1- yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi a cikin.
2- a duk lokacin da su kai nufin saduwa kawai sa ta
ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al’adarta bane.
3- jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida.
4- suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba
ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar ta
ba.
5- matsanancin ciwon baya ko kwankwaso.
6-ƙin yarda da jima‘i.
7- Za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban.
8- yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da
taron suna.
9- ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannunsa
a cikinki tare da fizgo wani abu, musamman idan kina da ciki.
10- yawan yin ɓarin ciki ba tare da wani sanannen dalili ba.
11- yawan mafarkin ana binki a guje ko ana kokawa da ke.
12- jin motsi a cikinki, wani lokaci ma har yana
daɗa girma, amma in likitoci suka auna za su ce ba su ga komai ba.
13- rashin son yin magana da kowa da jin haushin mutane haka kawai.
14- tsanar mai gida haka kawai, alhali za ki ji kina sha’awar wasu mazan.
15- Jin wari mara dadi yana fito miki ko ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen
gaba.
16- Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba.
17- Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi.
18- In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suyi mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fadar cewa wance kwarjini take musu.
19- Za ta dinga yawan zama a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane.
20- Idan yarinya tana zuwa makaranta za a ga kokarinta yana raguwa kuma tana ramewa.
21- Yawan ciwon kai da yin jiri.
22- Faduwar gaba, musamman idan magriba ta kusa.
25- da zaran mace ta fara barci sai ta ji an zungureta ta farka.
Da dai alamomi da yawa."
Wani hucin ajiyar zuciya daddy ya saki mai ƙarfi kamun ya kuma jefawa ba Lukman ɗin wani tambayar, "Shin baba aljani kala ɗaya ne kawai ko kuwa suna da yawa?"
Girgiza kai ba Lukman ya yi tare da faɗin, "Aljanu sun kasu kashi-kashi, daga cikinsu akwai; Jinnut Ɗayyar ﺟﻦ ﺍﻟﻄﻴﺎﺭ
Wato Aljani masu fika-fuki da suke tashi sama.
b)Jinnul Ghauwas ﺟﻦ ﺍﻟﻐﻮﺍﺹ
Wato Aljanin ruwa, me zama a cikin ruwa
C)Jinnul Tabaddul ﺟﻦ ﺍﻟﺘﺒﺪﻝ
Aljanu masu dawowa Yara bayan sun tsufa.
d) Jinnul Atfal ﺟﻦ ﺍﻷﻃﻔﺎﻝ
Aljanu masu shiga jikin kanan yara.
e)Jinnul Bakam ko Jinnus Saqam ﺟﻦ ﺍﻟﺒﻜﻢ ﺃﻭ ﺟﻦ ﺍﻟﺴﻘﻢ
Aljanu masu sa rashin lafiyar gaɓɓai.
f)Jinnul jalab wattahdheer ﺟﻦ ﺍﻟﺠﻠﺐ ﻭﺍﻟﺘﺤﻀﻴﺮ
Aljanu masu shiga jikin masu Rukiyyah da masu karance-karance akan Aljanu
g)Jinnul Ghubar ﺟﻦ ﺍﻟﻐﺒﺎﺭ
Aljanu masu yawo a cikin qura.
h)Jinnul Hayyat Wal Aqarib ﺟﻦ ﺍﻟﺤﻴﺎﺕ ﻭﺍﻷﻗﺎﺭﺏ
Aljanu masu siffar Macizai da kunami.
i) Jinnul Sihr ko KhadimulMAGUNLUR السحر
Aljanin da ke shiga jikin mutum ta hanyar tsafi ko sihiri
j) Sakinul Maqabir ﺳﺎﻛﻦ ﺍﻟﻤﻘﺎﺑﺮ
Aljanun Maƙabarta.
k) Khadimul Hammam ﺧﺎﺩﻡ ﺍﻟﺤﻤﺎﻡ
Wato Aljanun Bandaki ko Sarkin Ƙazamai.
l)Amirul Baiti ﻋﺎﻣﺮ ﺍﻟﺒﻴﺖ
Aljanin gida. Aljanun da suke zaune a gidajen mutane.
m)Jinnul ƙariyn ﺟﻦ ﺍﻟﻘﺮﻳﻦ
Nau’in Aljanin da kowa yana da shi.
n)Ifriytun minal Jinni ﻋﻔﺮﻳﺖ ﻣﻦ ﺍﻟﺠﻦ
Nau’in Aljanu masu Azababben ƙarfi.
o) Shaiɗanun mariyd ﺷﻴﻄﺎﻥ ﻣﺮﻳﺪ ﺃﻭ ﻣﺎﺭﺩ
Nau’in Aljanu masu bala’in taurin kai.
p)Jinnul Katfah ﺟﻦ ﺍﻟﻜﺘﻔﺔ
q)Sariqul Jinni ﺳﺎﺭﻕ ﺍﻟﺠﻦ
Aljanu masu satar kayan mutane.
r) Sariqus Sam’i ﺳﺎﺭﻕ ﺍﻟﺴﻤﻊ
Aljanu masu sato maganar Mala’iku.
s)Jinnul Shu’uwn ﺟﻦ ﺍﻟﺸﺆﻭﻥ
Aljanu ‘yan rainin wayo, masu fitinar tsiya.
t)Tabriyqul Jinni ﺗﺒﺮﻳﻖ ﺍﻟﺠﻦ
u)Jinnul Was’was ﺟﻦ ﺍﻟﻮﺳﻮﺍﺱ
Aljanu masu sa Wasu-wasi
v) Jinnul Falsafiyy ﺟﻦ ﺍﻟﻔﻠﺴﻔﻲ
Aljanu masu nazarin rayuwar mutane.
w) Jinnul Ashiq ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ
Wato Aljani mai aurar mace yana hana ta aure ko haihuwa.
Dadai sauransu.
x)Jinnuz Zulam ﺟﻦ ﺍﻟﻈﻼﻡ
Aljanu masu zama a cikin duhu. Waɗannan da na lissafo sune rabe-raben aljanu."
##MATAR SAYYADEE
#SAFRAAAZ THE KILLER
#Aizaad
#DINAAAYAH
#Benazir
#Aleesha
#ALIYAAH
#Ƙanwar Matata Return
##BETWEEN TWO LOVERS
#DInaAYaH SaFrAAz
```This is just the short trailer of the story! Mutanena ban fa ɗauko kashi ɗaya daga cikin kaso ɗari na labarin ba fa. Dama kuma na faɗa free pages biyar kawai zan yi kuma Alhamdulillah na kammala. Mai son jin yadda labarin zai kaya sai yi payment in tsundumasa cikin paidgroup wanda in sha Allah a can cikakken labarin zai cigaba```
*_Free pages sun ƙare ki biya ɗarinki biyar idan kin karanta ƙanwar matata, idan kuma baki karanta ba 1k kacal za ki turo domin complete document na shi ƙanwar matatan sannan kuma in tsunduma ki cikin paidgroup na DINAAYAH SAFRAAZ wato KƘANWAR MATATA RETURN. Don girman Allah idan kin san za ki saya ne domin ki fitar kar ki zo na yafe naki cinikin!_*
`DINAAYAH SAFRAAZ ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVDENCE OF PAYMENT 08128755583`
_Ina ƙara baki shawara sister, kar ki bari ayi wannan tafiyar babu ke_