DINAAYAH SAFRAAZ Free pages Hausa Novels.txt

Author :  Safraz Category :  Hausa Book Store

Chapter   2 / 7

3K to 6K   out of 19.7K words

har ka saboda a tsammaninta mahaifiyarta ce ta shigo ɗakin.

"Munafuka!" Aleesha ta faɗi tare da nufa inda biscuits ɗin ya faɗi ta ɗauka, ita kuma Benazir ta yi saurin yaye bargon tare da sakin doguwar ajiyar zuciya.

"Ashe yan ukuna ne! Wallahi na ɗauka aunty ce (ita ma auntyn ta ke cewa kamar yadda su Dinaayar da duk yaran gidan suke faɗa) ita na yi wa ƙaryar rashin lafiya ai. Ke kuma ban biscuits ɗina mayya kawai!" Benazir ta ƙarisa maganar tare da kai hannu za ta wafce biscuits ɗin amma sai Aleesha ta yi baya tana kai biscuits ɗin bakinta ta ɓalla.

"Gaskiya kin ɗauki hakkina Benazir! Na ɗauka da gasken-gaske ba ki da lafiya har ina ƙin cin abinci." Dinaayah ce ta faɗi hakan tare da zama a bakin gado ta lalubi hannun Benazir ɗin ta riƙe domin jin temperature ɗinta.

"I'm fine, sister. Aunty ce ke so na bi Sausan (cousin sister ɗinta 'yar wan mamanta) zuwa Maiduguri ni kuma Allah ba zan je ba, weather garin ba dai mahaukacin zafi ba!" Benazir ta faɗi tana yamutsa fuska.

"Kawai saboda ba ki son zuwa Maiduguri sai ki fara ciwon ƙarya! Kuma Allah weather ɗin Maiduguri yana da kyau kuma yana gyara fata. To ki ma kwantar da hankalinki don Hajiya na nan tana shiri ƙarshen shekarar nan gaba ɗayanmu za mu tafi can auren yarinyar aunty Laure." Aleesha ta faɗi tana cin biscuits.

"Ke don girman Allah! Ba dai Surayyar aunty Laure za ai wa aure ba? Yarinyar nan ta kai fifteen kuwa? Na shiga uku!" Benazir ta faɗi har da dafa ƙirji.

"To wallahi ni ma dai na sha mamaki don a bakin da bai ƙarya na ji. Kin san dai Hajiya ba za ta faɗi ƙarya ba." Aleesha ta faɗa.

Sai a lokacin Dinaayah ta saka baki wajen faɗin, "To ba ƙauye bane. Su ai ba su yarda yarinya ta haura sha huɗu ba a ɗakin miji ba tunda ba karatu suke ba. Kin manta labarin da hajiyar ta ba mu lokacin da dangin mahaifin aunty Laure su ka yi amfani da power su ka ɗauke ta a wajan ta su ka mata aure a ƙauye bayan har makaranta ta fara kuma ta yi nisa. Bayan rasuwar mijin ne fa hajiya ta sakawa idanunta kwalli ta kuma taho wa da aunty Lauren a wani ziyara da ta kai Maidugurin sai dai kuma dangin mahaifin yarinyar da ta haifa sun hana tafiya da ita 'yar aunty Lauren wai baza su ba da ba, haka nan hajiya ta haƙura don sun fi ƙarfinta tunda dangin uba ne. Suna dawowa Kaduna kuma hajiya ta jefa aunty Lauren a school, kuma ba gashi yanzu karatun ya taimaka mata ba tana aikinta a asibitin daddy."

"Aikuwa dai! Hajiya na ƙaunar aunty Laure sosai kamar yarinyar da ta haifa a cikinta." Benazir ta faɗi.

"To ai sun shaƙu ne, tun fa tana da eleven years hajiya ta ɗauko ta." Dinaayah ta faɗi.

"Aunty Laure mutuniyar daddynmu!" Aleesha ta faɗi tana dariya tuna irin tsokakar junan da suke yi duk suka haɗu.

"Ku tashi mu je side ɗin mummy mu ci abinci yanzu na gama." Dinaayah ta faɗi.

"Kamar kuwa kin san baƙar yunwa na ke ji, pretending ne ya hana ni fita zuwa kitchen in nemi wani abu na ci." Benazir ta faɗi yayin da ta ke saukowa daga kan gado.

Aleesha da idanu ta bi dogon gashin Benazir ɗin da ya kai kusan har tsakiyar bayanta ga cika da tsayi irin na asalin yaran shuwa arab. "Wai Bena bakya jin kanki na maki nauyin da wannan tulin gashin da kika tara."

Hannu Benazir ta kai ta tattare gashin ta ɗaure da ribbon sannan ta saka hulan tare da faɗin, "Idan zai ƙaru fiye da haka ma ina so. Ni fa ban cikin matan da ke cewa wai basu san gashi saboda suna da shi, son abuna na ke yi sosai." ta ƙarisa maganar tana shafa jan baki a leɓenta.

Taɓe baki Aleesha ta yi tare da faɗin, "Allah Bena idan ba ki rage kwalliya ba wata rana sai aljanun kwalliya sun shige ki. Part din mum fa za mu shine har da wani saka jan baki kamar wacce za ta fita anguwa."

"Hausawa sun ce idan kana da kyau ka ƙara da wanka. Ku taso mu tafi." ta ƙarisa maganar tare da kamo hannun Dinaayah suka fice daga ɗakin Aleesha biye da su a baya.

Tsaye ya ke a tsakiyar falon sanye cikin dark blue suit na company _brooks brothers_ yana gyara zaman tsadaddiyar baƙar cover shoe ɗin da ke sanye a ƙafarsa. Gaba ɗaya ƙamshin _Imperial majesty_ da ya game da _Caron Poivre_ ya bada wani fitinannan ƙamshi mai kwantar da zuciya. Aunty Habbooba a gefensa sanye cikin fari ƙal ɗin lifaya mai zanan ganye da jan kala, sai rigar da ke cikin lifayar kalar baƙi mai dogon hannu, yatsun hannunta ya sha lalle ja sai ɗaukar idanu ya ke, haka ma farar ƙafarta tasha lalle, sannan kyakkyawar fuskanta ya sha kyau. Magana ta ke masa wanda shi kaɗai ya ke jin abunda ta ke faɗi suna murmushi.

"Daddy yana falo tabbas!" Dinaayah ta faɗi saboda shaƙo ƙamshin turaransa da ta yi.

"Aiko dai gashi can shi da aunty tamkar za su gasar kyau." Aleesha ta faɗi tana murmushi don ba ƙaramin kyau dad da auntyn tasu su kai ba. Babu wanda zai kalli dad ɗin ya ce yana da manya 'ya'ya kamar su Sauban da su kai 26years of age ba. Idan suka jero shi da su Sam'an za ka rantse babban yaya ne tare da ƙannansa. Kamar yadda dad bai tsufa haka ma matan nasa mummy Sarah da aunty Habboba don dukkan su babu na banza wannan na wane wannan.

Saukowarsu ta ja hankalin dad da aunty Habbooban suka zubawa stairs ɗin idanu fuska ɗauke da farincikin ganin 'ya'yan nasu.

"The great daddy, Dr. Ibrahim Khalilullah Nurudden!" Benazir ta faɗi tana ƙoƙarin shiga camera a wayarta ƙirar iphone 14pro....



#DINAAYAH SAFRAAZ
##MATAR SAYYADEE
#BETWEEN TWO LOVER'S
#LOVE STORY
#SADAUKARWA
#CIN AMANA
#ZAZZAFAR SOYAYYA
#TAUSAYI
#AFFECTION
##KHALILULLAH NURUDDEEN
#KAISAAR
#SAFRAAAZ THE KILLER

08128755583 no phone calls please, whatsapp only!

Share fisabilillah
[9/10, 2:31 PM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_*
(```DiNaayah SafraAz```)
_*BEtweEn two LoveRs*_


☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️
( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*)💪🏻 ```Takenmu shine ɓunkasa cigaban adabi!```
`We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them`


##Matar Sayyadee
#Kaisaar
#SAFRAAZ THE KILLER
#DINAAYAH
#Benazir
#Aleesha

Chapter 002

Hotuna ta riƙa ɗaukar su shi da aunty Habbooba kamun ta ƙarisa kusa da shi tare da su Dinaayah su kai salfie har da aunty Habbooban.

"The beauty, the precious light and the caring one! 'Yan ukuna Allah ya muku albarka." faɗin Dr Khalilullah yana shafa kawunansu cike da jin daɗi.

Gaba ɗaya 'ya'yansa akwai sunayan da ya saka masu ban da asalin na yanka da kowanne ke da shi. Sam'an shine the _Agelast_ (saboda rashin dariyarsa), Sauban (the Champion), Dinaayah yana kiranta da sunaye uku, (Precious Light, genius ko kuma ya ce Alayna Noor), Benazir (Beauty), Aleesha (The caring one), Ayraah (Lazy Queen), Amla (Silent soul), sai auta Afreen (Little Queen).

Akwai wata irin mahaukaciyar soyayya da shaƙuwa tsakaninsa da 'ya'yansa. Bai haɗa 'ya'yansa da komai ba a duniya. Yana iyakacin bakin ƙoƙarinsa sosai ganin bai fifita ɗayansu akan ɗaya ba, sai dai a bayyane ya ke ga kowa irin ƙaunar da ya ke wa Dinaayah wanda bai rasa nasaba da nakasar da take da shi na rashin idanu. Sosai ya gina soyayya da ƙaunar juna a tsakanin kaf 'ya'yansa, bai yarda iyayan sun raine su akan 'yan ubanci ba. Ya nuna masu dukkansu ɗaya suke domin jini ɗaya ke yawo a jijiyoyin jikinsu, haka Hajiya mahaifiyarsa ita ma tana nata iyakacin bakin ƙoƙarin. Matan nasa ma sun basa haɗin kai sosai don idan kaga kan 'ya'ya sun rabu to tabbas daga iyaye mata ne saboda kishi.

"Daddy, ka yi kyau sosai!" Dinaayah ta faɗi tana shafa suit ɗin da ke jikinsa, ɗaya hannuta kuma yana taɓa fuskansa har zuwa karan hancinsa saboda ɗan duƙowar da ya yi, don duk tsayinta daddyn ya fita tsawo.

"Dagaske Dinaayah? Ki ce idan na fita zan yi kasuwa kenan?" ya faɗi yana satar kallon aunty Habbooba da gefen idanu.

Hannu Dinaayah ta saka a baki ta toshe tare da faɗin, "Ba ruwana kai da aunty ne, kuma ai ka riga ka gama aure. Mum na matsayin mace biyu ne haka ma aunty, ko auntynmu?" ta ƙarisa maganar tana kallon inda ta ke kyautata zaton auntyn na tsaye a wajen saboda ƙamshinta da ta ke ji.

"Faɗa masa dai Dinaayah!" aunty Habbooba ta faɗi tana hararar daddyn da ke murmushi.

Benazir ce ta fashe da dariya kamun ta furta, "Dinaayah, Aleesha! Aunty Habbooba once says.....?"

Dinaayah da Aleesha suka haɗa baki wajen faɗi, "Wallahi ka sha ƙarya daddynsu! Ai ka gama aure ka rufe ƙofa tuntuni. Kai da aure sai dai a aljanna idan ana yi wallahi tallahi."

Gaba ɗaya har daddy dariyar suka saka banda aunty Habbooba da ta yi kicin-kicin tana kallon 'yarta Benazir tare da faɗin, "Sai kin ci gidan ku idan ni tsararki ce, au kwaikwayota ku ke yi? Ki gama laɓe-laɓen ciwon sai ki bi Sausan Maiduguri."

Wani dariyar suka kuma fashewa da shi har da tafawa da daddy. Aunty Habbooba kuwa bin su ta yi ɗaya bayan ɗaya ta tattallabe masu ƙeya tare da kora su waje.

"Kar ki takura mata tunda ba son zuwa take ba. Kin ga biki ma na matsowa na 'yar wajen Laure wanda za a yi ƙarshen shekaran nan, da an gama bikin sai ki ɗauke ta ku tafi zaga dangin," Dr Khalilullah ya faɗi bayan ya mayar da kallonsa izuwa gare ta.

Taɓe baki ta yi tare da faɗin, "To ai shikenan. Dama ai kai ke ɗaure masu ƙafafu suna yin abunda suka ga dama a cikin gidan nan."

Murmushi ya yi tare da faɗin, "Sai na dawo!"

"Allah ya tsare ya kiyaye min kai daga sharrin matan zamani masu yi tamkar su ɗauke mijin wasu su gudu." aunty ta faɗa.

Dariya ya yi mai faɗi kamun ya ce, "Kuma gashi ni sai na cike sauran ƙofofin da suke buɗe ba!" da sigar zolaya na ƙarisa zancen.

"Wallahi ka sha ƙarya daddynsu! Ai ka gama aure ka rufe ƙofa tuntuni. Kai da aure sai dai a aljanna idan ana yi wallahi tallahi." aunty habboba ta faɗi har da tafa hannu.

Dariya Dr ya yi sosai don dama abunda ya ke son ji ta faɗa kenan shiyasa ya zolaye ta. Aunty Habbooba akwai mahaukacin kishi na fitar hankali. Kowa na gidan ya san haka shiyasa 'ya'ya suke tsokalarta wani lokacin. Ko kuma hakanan idan duka suna zaune a falo sai ɗaya ta ɗau wayarsa, ɗaya kuma sai ta kira number ɗinsa, ɗaya kuma sa ta nufe sa da wayar tana faɗin, "Daddy ga wata number da ka yi saving da Sweetheart tana kira." tun kamun dr da ya san tsiya suke wa aunty Habbooba ya amsa wayar caraf aunty Habbooba ke karɓewa idanunta a waje tana kallon screen ɗin wayar, da zarar ta ci karo da sunan ɗaya daga cikin 'ya'yan sai ta yi kansu da gudu za ta make, gaba ɗaya sai su hau yi mata dariya har da dad da mummy Sarah.

"To mai da wuƙar na janye zancena!" ya faɗi yana dariya tare da ficewa daga ɗakin.

Kai tsaye part ɗin hajiya ya nufa. Knocking ya yi a ƙofa, 'yar aikin hajiya mai suna Lawisa ta zo ta buɗe masa ƙofar tare da ɗan rusunawa cike da girmama ta gaida shi, shima cikin sakin fuska ya amsa mata gaisuwar sannan ya wuce ciki yana faɗin, "Ina Hajiya?"

"Tana ciki yanzu ta shiga domin ta kwanta ta huta. A kira ta ne?" Lawisa ta faɗa.

"A a barta ta huta idan na dawo zan shigo." ya faɗi tare da juyawa ya bar ɗakin. Kiciɓis su kai da wansa ya Abdul-Hakeem shi ma za shiga duba hajiyar.

"Dr fita za ka yi?" ya faɗa yana miƙa masa hannu su kai musabaha.

"Eh zan je asibiti ne akwai wani patient da ke ƙarƙashin kulawata shi na ke son dubawa, daga nan kuma zan biya Maiduguri road." faɗin Dr Khalil.

"Ma sha Allah, to Allah ya kiyaye sai ka dawo. Bari na duba hajiya." Abdul-Hakeem ya faɗi.

"Ta kwanta fa, ni ma duba na zo yi sai Lawisa ta ce ta shiga ɗaki domin ta ɗan samu hutu shiyasa ma na juyo."

"Ok to shikenan ni ma bari na wuce idan ta tashi na dawo." faɗin Abdul-Hakeem ɗin tare da jerawa da ƙaninsa Dr Khalil. Sai da suka zo inda za su rabu kowa ya yi hanyarsa, Abdul-Hakeem ya yi hanyar part ɗinsa da ke kusa da na Habbooba, shi kuma Dr Khalil ya yi hanyar part ɗin mummy Sarah.

"Assalamu alaikum!" daddy ya faɗi tare da murɗa handle daidai lokacin da gaba ɗayansu suka amsa masa sallamar suna kallon ƙofar har da Dinaayar da bata gani.

"The _Agelast_ and the _Champion_" ya faɗi yana kallon sashin da Sauban da Sam'an suke zaune waje ɗaya suna kallon abu a cikin laptop ɗin Sam'an ɗin.

Nan da nan fuskan Sauban ya mamaye da fara'a yayin da Sam'an ya furta, "Welcome dad!" fuskan nan babu ko ɗigon fara'a.

"Hmm! Wallahi ka riƙa fara'a ko za ka yi kyawun gani." daddy ya faɗi yana harararsa.

Bai ce komai ba sai ma mayar da dubansa da ya yi kan screen ɗin laptop. Su Benazir sai dariya su ke ƙasa-ƙasa.

"Daddy asibiti za ka tafi?" Benazir ta tambaya tana miƙewa tsaye.

"Eh amma ba jimawa zan yi ba zan biya Maiduguri road. Wannan petient ɗin da ke fama da mouth cancer zan duba. Ina mummyn ku?" ya ƙarisa maganar da tambaya.

"Tana sama, bari na yi sauri na shirya ni ma akwai abunda zan yi submitting sai na hau abun hawa na dawo ko kuma ka taya ni roƙon ya Sauban ya zo ya dawo dani gida." faɗin Benazir.

"Kar ma ki kuskura ki fara, babu inda za ni yau a gidan nan!" ya Sauban ya faɗi yana shurinta da ƙafa kasancewar tana zaune a ƙasan kujeran da ya ke zaune ne.

"Ku yanke shawarar ni bari na duba mom ɗin ku a sama iyayan rigima." Dr ya faɗa yana nufa hanyar stairs ɗin da zai kai shi zuwa ɗakin matarsa sanyin idaniyarsa.

Tura ƙofar ya yi daidai lokacin da mummy Sarah ta juyo da fuskanta izuwa ƙofar, wani irin sanyayyiyar murmushi suka sakarwa junansu kamun nan ya ƙarisa shigowa ya maida ƙofar ya rufe sannan ya jingina da ƙofar ya ware hannayensa tare da faɗin, "Come here!"

Kai tsaye ta nufe sa tare da shigewa jikinsa sannan ta furta, "I miss you soo much! Yau gaba ɗaya sau uku kawai na ganka."

Kumatukanta ya ja tare da soma kallonta daga sama har ƙasa, sanye ta ke cikin atampa maroon colour da ya yi mata matuƙar kyau. Ɗinkin doguwar riga ce A shape ta ji beatwork kuma ba ƙaramin kyau ta yi mata ba, ɗaurin ɗankwalin zamani ta yi da ya ɗan bayyana gashinta ta can wajen ƙeya.

"Ni ma na yi kewarki sosai! Kin yi kyau sosai bari na yi mana hoto" ya ƙarisa maganar tare da fiddo wayarsa ya yi masu hoto kusan kalaa biyar sannan ya soma ɗaukarta ita kaɗai tana masa styles kala-kala.

"Na samu na kallo a office kamun attending petients ɗina." ya faɗi yana mayar da wayar cikin aljihu.

"Ka turo min hotunan ta whatsapp ni ma na samu na kallo kamun ka dawo."

"Sai kin biya tukun!" ya faɗi yana ɗage mata gira ɗaya.

Magana ta raɗa masa a kunne da ya sa shi fashewa da dariya, ita kanta da ta yi maganar sai da ta yi dariyar.

"Aikam kin biya, zan tura miki ina isa asibiti. Amma kuma sai kin cika alƙawarinki idan na dawo."

"Baka da matsala a shirye na ke!" ta faɗi tana ba shi side hug shikuma ya jawota ya rungume gaba ɗaya tare da kissing kumatunta sannan ya furta, "Sai na dawo!"

"Allah ya tsare ya kai ka lafiya kuma ya dawo min da kai lafiya."

"Ba za ki addu'a Allah ya rufe min idanu akan kallon wata wacce za ta dage sai ta yi wuff da ni ba?"

"Ai kai dai ka fi kowa sanin ban tsoron kishiya. Ta zo kowa ta iya allonta ta wanke."

Dariya ya yi tare da faɗin, "I trust you! Amma dai ko yaya ne a riƙa nuna ana jin kishina zan ji daɗin haka."

"Ana kishinka mana. Sosai ma! Kawai dai ban sakawa raina abunda na san zai iya yuwuwa har hakan ya jawo min wata matsala a zuciya da kuma tsakanina da happiness ɗina."

"To ki kwantar da hankalinki ma don na rufe ƙofa, ta biyun ma da na ƙara don an fi ƙarfina ne babu yadda na iya." ya faɗi yana ɗage gira.

Ƙofa ta nuna masa tare da faɗin, "Oya bye-bye Allah ya kiyaye hanya!" ta faɗi hakane sabida sam bata son suna magana yana kawo zancen Habbooba.

"Au korata ki ke yi? Babu komai shikenan, zan tafi amma wallahi sai na dawo anjima kuma a nan zan kwana!"

"Ina maraba da hakan tunda girkina ne!" ta faɗi tana dariya. Shima dariyar ya yi tare da juyawa ya fice daga ɗakin tana biye da shi a baya.

Gaba ɗaya yaran kallon sama su ka yi yayin da iyayan nasu ke saukowa zuwa falon. Tafi suka fara yi raf-raf amma banda Sam'an da kallo ɗaya ya yiwa iyayan nasa ya mayar da kai kan laptop ɗinsa yana yaba kyau da soyayyarsu cikin zuciyarsa don ba ƙaramin burgesa su ke yi ba.

"Wallahi kuma sai na maku hoto, ku tsaya cak kar ku ƙara ko taku ɗaya." Benazir ta faɗi tana ciro wayarta a cikin aljihun wandon da ke jikinta ta shiga ɗaukarsu hotuna.

"Yauwa to yanzu ku sauko sai mu yi dukkan mu. Ya Sam'an don Allah ka tashi ka ɗauke mu" ta ƙarisa maganar tare da aje masa wayar a kan laptop ɗin sannan ta kamo hannun Dinaayah ta miƙar suka ƙarisa inda su mummyn suke tare da Aleesha da Sauban.

Aje laptop ɗin ya yi a gefe sannan ya miƙe ya shiga ɗaukar su hoto fuskan nan babu fara'a tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa. Sai da ya masu kusan kala biyar sannan ya juya camera

2 / 7