Author : Safraz Category : Hausa Book Store
ﺃَﻥَّ ﻣَﺎﻟَﻪُ ﺃَﺧْﻠَﺪَﻩُ ( 3 ) ﻛَﻠَّﺎ ﻟَﻴُﻨﺒَﺬَﻥَّ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺤُﻄَﻤَﺔِ ( 4 ) ﻭَﻣَﺎ ﺃَﺩْﺭَﺍﻙَ ﻣَﺎ ﺍﻟْﺤُﻄَﻤَﺔُ
( 5 ) ﻧَﺎﺭُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻤُﻮﻗَﺪَﺓُ ( 6 ) ﺍﻟَّﺘِﻲ ﺗَﻄَّﻠِﻊُ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺄَﻓْﺌِﺪَﺓِ ( 7 ) ﺇِﻧَّﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢ ﻣُّﺆْﺻَﺪَﺓٌ ( 8 ) ﻓِﻲ ﻋَﻤَﺪٍ ﻣُّﻤَﺪَّﺩَﺓٍ {
} ﺃَﻟَﻢْ ﺗَﺮَ ﻛَﻴْﻒَ ﻓَﻌَﻞَ ﺭَﺑُّﻚَ ﺑِﺄَﺻْﺤَﺎﺏِ ﺍﻟْﻔِﻴﻞِ ( 1 ) ﺃَﻟَﻢْ ﻳَﺠْﻌَﻞْ ﻛَﻴْﺪَﻫُﻢْ ﻓِﻲ ﺗَﻀْﻠِﻴﻞٍ ( 2 ) ﻭَﺃَﺭْﺳَﻞَ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢْ ﻃَﻴْﺮًﺍ ﺃَﺑَﺎﺑِﻴﻞَ ( 3 ) ﺗَﺮْﻣِﻴﻬِﻢ ﺑِﺤِﺠَﺎﺭَﺓٍ ﻣِّﻦ ﺳِﺠِّﻴﻞٍ ( 4 ) ﻓَﺠَﻌَﻠَﻬُﻢْ ﻛَﻌَﺼْﻒٍ ﻣَّﺄْﻛُﻮﻝٍ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻔﻴﻞ
} ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺃَﺣَﺪٌ ( 1 ) ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟﺼَّﻤَﺪُ ( 2 ) ﻟَﻢْ ﻳَﻠِﺪْ ﻭَﻟَﻢْ ﻳُﻮﻟَﺪْ ( 3 ) ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦ ﻟَّﻪُ ﻛُﻔُﻮًﺍ ﺃَﺣَﺪٌ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻹﺧﻼﺹ
} ﻗُﻞْ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﺮَﺏِّ ﺍﻟْﻔَﻠَﻖِ ( 1 ) ﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﺧَﻠَﻖَ ( 2 ) ﻭَﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﻏَﺎﺳِﻖٍ ﺇِﺫَﺍ ﻭَﻗَﺐَ ( 3 ) ﻭَﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﺍﻟﻨَّﻔَّﺎﺛَﺎﺕِ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻌُﻘَﺪِ ( 4 ) ﻭَﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﺣَﺎﺳِﺪٍ ﺇِﺫَﺍ ﺣَﺴَﺪَ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻔﻠﻖ
} ﻗُﻞْ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﺮَﺏِّ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ( 1 ) ﻣَﻠِﻚِ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ( 2 ) ﺇِﻟَﻪِ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ( 3 ) ﻣِﻦ ﺷَﺮِّ ﺍﻟْﻮَﺳْﻮَﺍﺱِ ﺍﻟْﺨَﻨَّﺎﺱِ ( 4 ) ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳُﻮَﺳْﻮِﺱُ ﻓِﻲ ﺻُﺪُﻭﺭِ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ( 5 ) ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺠِﻨَّﺔِ ﻭَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻨﺎﺱ
} ﻭَﺍﻟﻠّﻪُ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﺄَﻋْﺪَﺍﺋِﻜُﻢْ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠّﻪِ ﻭَﻟِﻴًّﺎ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠّﻪِ ﻧَﺼِﻴﺮًﺍ{ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 45
} ﺫَﻟِﻚَ ﺍﻟْﻔَﻀْﻞُ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻠّﻪِ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠّﻪِ ﻋَﻠِﻴﻤًﺎ { ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 70
} ﻭَﺗَﻮَﻛَّﻞْ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻛِﻴﻠًﺎ { ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : 3
} ﻭَﺭَﺩَّ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﺑِﻐَﻴْﻈِﻬِﻢْ ﻟَﻢْ ﻳَﻨَﺎﻟُﻮﺍ ﺧَﻴْﺮًﺍ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ﺍﻟْﻘِﺘَﺎﻝَ ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻗَﻮِﻳًّﺎ ﻋَﺰِﻳﺰًﺍ { ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : 25
} ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﺒَﻠِّﻐُﻮﻥَ ﺭِﺳَﺎﻟَﺎﺕِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻳَﺨْﺸَﻮْﻧَﻪُ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺨْﺸَﻮْﻥَ ﺃَﺣَﺪًﺍ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻛَﻔَﻰ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﺣَﺴِﻴﺒًﺎ { ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : 39
} ﺇِﺫْ ﻳُﻮﺣِﻲ ﺭَﺑُّﻚَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﻤَﻶﺋِﻜَﺔِ ﺃَﻧِّﻲ ﻣَﻌَﻜُﻢْ ﻓَﺜَﺒِّﺘُﻮﺍْ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍْ ﺳَﺄُﻟْﻘِﻲ ﻓِﻲ ﻗُﻠُﻮﺏِ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍْ ﺍﻟﺮَّﻋْﺐَ ﻓَﺎﺿْﺮِﺑُﻮﺍْ ﻓَﻮْﻕَ ﺍﻷَﻋْﻨَﺎﻕِ ﻭَﺍﺿْﺮِﺑُﻮﺍْ ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﻛُﻞَّ ﺑَﻨَﺎﻥٍ ( 12 ) ﺫَﻟِﻚَ ﺑِﺄَﻧَّﻬُﻢْ ﺷَﺂﻗُّﻮﺍْ ﺍﻟﻠّﻪَ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟَﻪُ ﻭَﻣَﻦ ﻳُﺸَﺎﻗِﻖِ ﺍﻟﻠّﻪَ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟَﻪُ ﻓَﺈِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﺷَﺪِﻳﺪُ ﺍﻟْﻌِﻘَﺎﺏِ ( 13 ) ﺫَﻟِﻜُﻢْ ﻓَﺬُﻭﻗُﻮﻩُ ﻭَﺃَﻥَّ ﻟِﻠْﻜَﺎﻓِﺮِﻳﻦَ ﻋَﺬَﺍﺏَ ﺍﻟﻨَّﺎﺭِ { ﺍﻷﻧﻔﺎﻝ : 12 14
} ﻳَﻮْﻡَ ﺗُﺒَﺪَّﻝُ ﺍﻷَﺭْﺽُ ﻏَﻴْﺮَ ﺍﻷَﺭْﺽِ ﻭَﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕُ ﻭَﺑَﺮَﺯُﻭﺍْ ﻟﻠّﻪِ ﺍﻟْﻮَﺍﺣِﺪِ ﺍﻟْﻘَﻬَّﺎﺭِ
( 48 ) ﻭَﺗَﺮَﻯ ﺍﻟْﻤُﺠْﺮِﻣِﻴﻦَ ﻳَﻮْﻣَﺌِﺬٍ ﻣُّﻘَﺮَّﻧِﻴﻦَ ﻓِﻲ ﺍﻷَﺻْﻔَﺎﺩِ ( 49 ) ﺳَﺮَﺍﺑِﻴﻠُﻬُﻢ ﻣِّﻦ ﻗَﻄِﺮَﺍﻥٍ ﻭَﺗَﻐْﺸَﻰ ﻭُﺟُﻮﻫَﻬُﻢْ ﺍﻟﻨَّﺎﺭُ ( 50 ) ﻟِﻴَﺠْﺰِﻱ ﺍﻟﻠّﻪُ ﻛُﻞَّ ﻧَﻔْﺲٍ ﻣَّﺎ ﻛَﺴَﺒَﺖْ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﺳَﺮِﻳﻊُ ﺍﻟْﺤِﺴَﺎﺏِ { ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ 48 : 51
} ﻭَﻗُﻞِ ﺍﻟْﺤَﻖُّ ﻣِﻦ ﺭَّﺑِّﻜُﻢْ ﻓَﻤَﻦ ﺷَﺎﺀ ﻓَﻠْﻴُﺆْﻣِﻦ ﻭَﻣَﻦ ﺷَﺎﺀ ﻓَﻠْﻴَﻜْﻔُﺮْ ﺇِﻧَّﺎ ﺃَﻋْﺘَﺪْﻧَﺎ ﻟِﻠﻈَّﺎﻟِﻤِﻴﻦَ ﻧَﺎﺭًﺍ ﺃَﺣَﺎﻁَ ﺑِﻬِﻢْ ﺳُﺮَﺍﺩِﻗُﻬَﺎ ﻭَﺇِﻥ ﻳَﺴْﺘَﻐِﻴﺜُﻮﺍ ﻳُﻐَﺎﺛُﻮﺍ ﺑِﻤَﺎﺀ ﻛَﺎﻟْﻤُﻬْﻞِ ﻳَﺸْﻮِﻱ ﺍﻟْﻮُﺟُﻮﻩَ ﺑِﺌْﺲَ ﺍﻟﺸَّﺮَﺍﺏُ ﻭَﺳَﺎﺀﺕْ ﻣُﺮْﺗَﻔَﻘًﺎ { ﺍﻟﻜﻬﻒ : 29
} ﻫَﺬَﺍﻥِ ﺧَﺼْﻤَﺎﻥِ ﺍﺧْﺘَﺼَﻤُﻮﺍ ﻓِﻲ ﺭَﺑِّﻬِﻢْ ﻓَﺎﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻗُﻄِّﻌَﺖْ ﻟَﻬُﻢْ ﺛِﻴَﺎﺏٌ ﻣِّﻦ ﻧَّﺎﺭٍ ﻳُﺼَﺐُّ ﻣِﻦ ﻓَﻮْﻕِ ﺭُﺅُﻭﺳِﻬِﻢُ ﺍﻟْﺤَﻤِﻴﻢُ ( 19 ) ﻳُﺼْﻬَﺮُ ﺑِﻪِ ﻣَﺎ ﻓِﻲ ﺑُﻄُﻮﻧِﻬِﻢْ ﻭَﺍﻟْﺠُﻠُﻮﺩُ ( 20 ) ﻭَﻟَﻬُﻢ ﻣَّﻘَﺎﻣِﻊُ ﻣِﻦْ ﺣَﺪِﻳﺪٍ ( 21 ) ﻛُﻠَّﻤَﺎ ﺃَﺭَﺍﺩُﻭﺍ ﺃَﻥ ﻳَﺨْﺮُﺟُﻮﺍ ﻣِﻨْﻬَﺎ ﻣِﻦْ ﻏَﻢٍّ ﺃُﻋِﻴﺪُﻭﺍ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻭَﺫُﻭﻗُﻮﺍ ﻋَﺬَﺍﺏَ ﺍﻟْﺤَﺮِﻳﻖِ { ﺍﻟﺤﺞ 19 : 22
} ﻭَﺍﻟﺼَّﺎﻓَّﺎﺕِ ﺻَﻔًّﺎ ( 1 ) ﻓَﺎﻟﺰَّﺍﺟِﺮَﺍﺕِ ﺯَﺟْﺮًﺍ ( 2 ) ﻓَﺎﻟﺘَّﺎﻟِﻴَﺎﺕِ ﺫِﻛْﺮًﺍ ( 3 ) ﺇِﻥَّ ﺇِﻟَﻬَﻜُﻢْ ﻟَﻮَﺍﺣِﺪٌ ( 4 ) ﺭَﺏُّ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻭَﻣَﺎ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻤَﺎ ﻭَﺭَﺏُّ ﺍﻟْﻤَﺸَﺎﺭِﻕِ
( 5 ) ﺇِﻧَّﺎ ﺯَﻳَّﻨَّﺎ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀ ﺍﻟﺪُّﻧْﻴَﺎ ﺑِﺰِﻳﻨَﺔٍ ﺍﻟْﻜَﻮَﺍﻛِﺐِ ( 6 ) ﻭَﺣِﻔْﻈًﺎ ﻣِّﻦ ﻛُﻞِّ ﺷَﻴْﻄَﺎﻥٍ ﻣَّﺎﺭِﺩٍ ( 7 ) ﻟَﺎ ﻳَﺴَّﻤَّﻌُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﻤَﻠَﺈِ ﺍﻟْﺄَﻋْﻠَﻰ ﻭَﻳُﻘْﺬَﻓُﻮﻥَ ﻣِﻦ ﻛُﻞِّ ﺟَﺎﻧِﺐٍ ( 8 ) ﺩُﺣُﻮﺭًﺍ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏٌ ﻭَﺍﺻِﺐٌ ( 9 ) ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﻦْ ﺧَﻄِﻒَ ﺍﻟْﺨَﻄْﻔَﺔَ ﻓَﺄَﺗْﺒَﻌَﻪُ ﺷِﻬَﺎﺏٌ ﺛَﺎﻗِﺐٌ { ﺍﻟﺼﺎﻓﺎﺕ 1 : 10
} ﻭَﺳُﻘُﻮﺍ ﻣَﺎﺀ ﺣَﻤِﻴﻤًﺎ ﻓَﻘَﻄَّﻊَ ﺃَﻣْﻌَﺎﺀﻫُﻢْ { ﻣﺤﻤﺪ : 15
} ﺧُﺬُﻭﻩُ ﻓَﻐُﻠُّﻮﻩُ ( 30 ) ﺛُﻢَّ ﺍﻟْﺠَﺤِﻴﻢَ ﺻَﻠُّﻮﻩُ ( 31 ) ﺛُﻢَّ ﻓِﻲ ﺳِﻠْﺴِﻠَﺔٍ ﺫَﺭْﻋُﻬَﺎ ﺳَﺒْﻌُﻮﻥَ ﺫِﺭَﺍﻋًﺎ ﻓَﺎﺳْﻠُﻜُﻮﻩُ ( 32 ) ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻟَﺎ ﻳُﺆْﻣِﻦُ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢِ ( 33 ) ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺤُﺾُّ ﻋَﻠَﻰ ﻃَﻌَﺎﻡِ ﺍﻟْﻤِﺴْﻜِﻴﻦِ ( 34 ) ﻓَﻠَﻴْﺲَ ﻟَﻪُ ﺍﻟْﻴَﻮْﻡَ ﻫَﺎﻫُﻨَﺎ ﺣَﻤِﻴﻢٌ ( 35 ) ﻭَﻟَﺎ ﻃَﻌَﺎﻡٌ ﺇِﻟَّﺎ ﻣِﻦْ ﻏِﺴْﻠِﻴﻦٍ ( 36 ) ﻟَﺎ ﻳَﺄْﻛُﻠُﻪُ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟْﺨَﺎﻃِﺆُﻭﻥَ { ﺍﻟﺤﺎﻗﺔ 30 : 37
Sai da ya kai har ƙarshe sannan ya cire hannunsa a ruwan ya kulle tare da kallon mummy Sarah ya furta, "A yi kamar kwana uku ko biyar ko bakwai ana yin haka. Sai kuma ita mai lalurar ta kula wajen yawan karanta ( ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻳﺤﻴﻰ ﻭﻳﻤﻴﺖ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ kafa dari bayan sallar magriba da asuba. Ta kuma dinga karanta addu’ar Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺏ ﺍﻟﺴﻤﻮﺍﺕ ﺍﻟﺴﺒﻊ ﻭﻣﺎ ﺃﻇﻠﺖ ، ﻭﺭﺏ ﺍﻷﺭﺿﻴﻦ ﻭﻣﺎ ﺃﻗﻠﺖ ، ﻭﺭﺏ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ﻭﻣﺎ ﺃﺿﻠﺖ ، ﻛﻦ ﻟﻰ ﺟﺎﺭﺍ ﻣﻦ ﺷﺮ ﺧﻠﻘﻚ ﻛﻠﻬﻢ ﺃﻥ ﻳﻔﺮﻁ ﻋﻠﻰّ ﺃﺣﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﺃﻭ ﺃﻥ ﻳﺒﻐﻰ ، ﻋﺰ ﺟﺎﺭﻙ ﻭﺟﻞ ﺛﻨﺎﺅﻙ ﻭﺗﻘﺪﺳﺖ ﺃﺳﻤﺎﺀﻙ ، ﻭﻻ ﺇﻟﻪ ﻏﻴﺮﻙ ).
Kuma ta dinga karanta suratu Yaasiyn, ArRahmaan, Qaaf da Suratul Mulki bayan sallar La’asar. Shi tsawon kamar kwana uku ko biyar ko bakwai za ta yi"
##Matar Sayyadee
#Dinaayah
#THE SECRET
#JINNUL ASHIQ
#Mummy Sarah
#KAISAAR
#Benazir
#Hatred
#EteRnaL Love
#Between two lovers
##DINAAYAH SAFRAAZ
_Free pages fa basu da yawa, guda biyar ne kawai don haka ku hwara payment, sannan don girman Allah idan kin san za ki saya ne domin ki fitar kar ki zo na yafe naki cinikin_
`DINAAYAH SAFRAAZ ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVDENCE OF PAYMENT 08128755583`
```Ina ƙara baki shawara sister, kar ki bari ayi wannan tafiyar babu ke```
[9/16, 10:53 PM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_*
(```DiNaayah SafraAz```)
_*BEtweEn two LoveRs*_
~Story and written~
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim*
_Matar Sayyadee_
_Wattpad @MatarSayyadee01_
_Arewabook@Matarsayyadee0_
```Messenger of Allah (ﷺ) said, "There are three signs of a hypocrite: When he speaks, he lies; when he makes a promise, he breaks it; and when he is trusted, he betrays his trust."```
[ _Al-Bukhari and Muslim_].
*Another narration adds the words: 'Even if he observes fasts, performs Salat and asserts that he is a Muslim".*
عن أبي هريرة ، رضي الله عنه ، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: “آية المنافق ثلاث: إذا حدث كذب، وإذا وعد أخلف، وإذا أؤتمن خان" ((متفق عليه)) .
Chapter 005
`NOT EDITED`
"Ba Lukman in sha Allah ba zan yi wasa da duk abunda ka ce ayi ba. Zan tashi tsaye kuma in rage bacci akan samuwar lafiyar 'yata. Idan wani abu ya samu Dinaayah haukacewa zan yi, Dr kuma zuciyarsa ce za ta buga."
"Babu wani abunda zai same ku dukkan ku. In sha Allah zai rabu da jikinta in har kuka dage a kanta. Shi ma Ibrahim ɗin idan ya iso goben zan ƙara shaida masa komai da duk abunda ya kamata a yi mata. Yanzu idan ta farka wannan ruwan shi zai fara wucewa maƙoshinta. Sannan kuma ta yi wanka da ruwan a cikin baho sai ku kawo min ruwan domin zubar da shi a inda ya kamata." Ba Lukman ya faɗi yana cigaba da rarrabe magungunar da ke gabansa.
"Allah ya ƙara girma ya kuma saka da alkhairi!" Mummy Sarah ta faɗi tana mai miƙewa tsaye ta fice daga ɗakin.
A tsaye ƙofar ɗakin karatun ba Lukman mummy Sarah ta ga Lami mahaifiyarta tsaye tana kaiwa da komowa. Tana ganin Sarah ɗin ta nufo wajenta tare da kama hannunta suka nufi ƙofar gida. Sai da suka je inda babu idanun mutane sannan Lami ta kalli Sarah hankalinta a matuƙar tashe tare da faɗin, "Sarah mai ke faruwa? Mai ya samu Dinaayah?"
Share hawayen da suka zubo mata a idanu mummy sarah ta yi sannan ta furta, "Ba Lukman ya ce aljani ne a jikinta kuma ya aure ta. Sai dai ya bayar da magani da addu'o'in da za a riƙa mata in sha Allah za rabu da ita har abada. Amma mama mai yasa grandma ta aikata wannan shirme? Abunda muka daɗe muna ɓoyewa shine ta yi ƙoƙarin bayyana shi a yau. Da wani irin ido da baki za mu kalli Dinaayah mu faɗa mata cewar ba mune iyayanta na asali ba? Haba mama! Yanzu pastor Emmanuella ta kyauta mana kenan?"
Dafa kafaɗarta Lami ta yi tare da faɗin, "Ki kwantar da hankalinki, mama ba wai ta bayyana komai bane. Akwai yadda za ayi har yanzu a cigaba da ɓoye wannan sirrin. Idan Dinaayah, Aleesha ko Benazir sun tambaye ki akan abunda su ka ji mahaifiyata ta ce, ki faɗa masu depression ke damun pastor sabida rashin jikarta Aina'u da ta yi a wani hatsari shiyasa duk wanda ta gani sai ta riƙa tunanin Aina'un ce."
Doguwar ajiyar zuciya mummy Sarah ta yi tare da jin wani relief don itama shawarar da Lamin ɗin ta bayar ya mata kuma da hakan take ganin za ta kawas da zargi a zukatan 'ya'yan nata.
"Shikenan zan faɗa masu hakan. Ki koma gida mama gobe In sha Allah kamun mu wuce zan zo gidan amma ni kaɗai ko kuma tare da Dr, na san ma tare za mu zo, sai dai ba za mu zo da su Dinaayah ba gudun ƙara faruwar abunda ya faru a yau."
"Babu komai Sarah, ni ma ba zan so ku zo ke da 'ya'yan ba duka. Tsufa sosai ya kama mom ɗina shiyasa ta ke yin wani abu kamar yarinya a yanzu, mu kanmu haƙuri muke yi da ita a yanzu." Lami ta faɗi.
"To shikenan mama, amma babu matsalar komai ko?" mummy Sarah ta faɗi.
"Babu komai Sarah. Allah ya muku albarka tare da zuri'arku gaba ɗaya. Ki koma wajen Dinaayah kar ta farka daga bacci." Lami ta faɗi.
Sai da mummy Sarah ta rungume mahaifiyar tata tukun sannan ta rakata har waje don har yau dai taƙi karɓuwa a cikin gidan iyayan marigayi Nuhu wato mijinta.
Ko da ta dawo ɗakin da Dinaayah ke kwance, su Benazir ta taras riƙe da Alqur'ani suna ta yi wa 'yar uwansu karatun duk da wanda ke tashi cikin MP sai dai volume ɗin a can ƙasa ya ke daidai wajen kunnenta. Gaba ɗayansu babu wacce bata tsiyayar da ruwan hawaye duk da karatun da ke fita daga bakunansu. Mummy Sarah ma sai ta nufi wajen da aka yi sa tamkar cupboard a falon wanda Ƙur'anai ne da mabanbamta littattafai da aka jera a wajan ta ɗauko izifi sittin ta buɗe ta shiga karatun itama.
Sun kwashi fiye da awa guda suka karatun, duk wacce ta shigo ta ga abunda suke yi sai itama ta ɗauko nata Alƙur'anin ta bi sahunsu. Sallar la'asar ya tada su. Fitarsu bai fi da mintuna biyar ba itama Dinaayah ta farka wasai tamkar ba ita ce wacce aka yi fama da ita ɗazu ba. Sai dai ba komai ta iya tunawa ba idan aka cire maganganun da pastor Emmanuella ta faɗi lokacin da suka je gidan. Abunda ta tuna last shine lokacin da paston ta durƙusar da ita ƙasa tana mata ihun Halleluja a kunne.
Wani irin durowa ta yi daga kan gadon tare da soma tafiya ba tare da sanin ainahin inda ta nufa ba. Guum! Ta buge da bango kasancewar ba hanyar falon tayi ba. Baya ya kuma yi ta canza hanya sai da wannan karon ma karo ta ci da keken ɗinkin da ke ɗakin gab da ƙofar da za ta sada mutun da falo. Bata haƙura ba ta cigaba da lalube har ta yi nasarar fitowa daga ɗakin daidai lokacin da mummy Sarah ke shirin tada sallah.
Da sauri mummy Saran ta iso inda Dinaayah ta ke tare da riƙo hannunta ta zaunar da ita a kan kujera sannan ta ce, "Dinaayah mai yasa kika fito ke ɗaya? Ai da kin kwaɗa kiran sunana na zo na fito da ke da kaina."
Murmushi Dinaayah ta yi tare da faɗin, "Mum yanzu kin fara min kallona makauniyar da kika ce baki taɓa ba kenan?"
Da saurin mummy Sarah ta girgiza kai tare da faɗin, "Ba haka bane Naayah. Na san ke ɗin 'yar baiwa ce kuma mai tarin basira, na san za ki iya fitowa da kanki. Amma matsalar ita ce nan ɗin baƙon wajenki ne baki haddace komai na gidan ba. A gida na taɓa yi miki ƙorafi akan kin sauko daga upstairs zuwa downstairs?"
Girgiza kai Dinaayah ta yi tare da furta, "Baki taɓa ba mom. Yanzu ma ko da kika ji na ce haka kawai na faɗa ne don inji mai za ki ce."
"To kar ki sake!" mum Sarah ta faɗa tana mai kamo hannunDinaayah ta riƙe a hannunta tana kallon fuskanta. Babu inda ta baro mahaifinta, fara ce tass mai dogon hanci da matsaƙaitan idanu irin na mahaifinta dr Khalil. Tana da tsayi don duk gidan idan aka cire su Sauban tafi kowa tsayi. Abunda ya sa mutane da yawa basu yarda Dinaayah makauniya ce shine, idanunta farare ne ƙal, ƙwayar idanun kuma kalar blue mai ɗan duhu (tamkar na turawa), sa ɗigon ciki kuma ash haka yake. Idanunta ya fi komai kyawu a fuskanta. Da kallo ba za ka taɓa fahimtar ita ɗin makauniya bace. Saboda idanun tsaye suke waje ɗaya basu karkace ba kuma ƙwayar basa rawa.
"In sha Allah mum ba zan sake ba. Amma mum ina son in tambaye ki, mai ya faru? Don the last thing da zan iya tunawa shine mun je gidan grandma ɗinki tana ta faɗi wasu maganganu da ban gane ba wai zata min addu'a saboda kar na biyo halin mamata Aina'u. Wai ba nononta na sha ba naki na sha don haka ba zan taɓa yin irin halinta ba. Sai kuma ta ja hannuna zuwa ciki ta shiga min karatunsu na 'yan coci to tun daga nan I can't remember anything that happen sai tashi na yi na ganni a kan gado."
"Suma ki ka yi shiyasa baza ki iya tuna komai ba. Wannan maganar da grandma ɗina ta faɗa kuma ba komai bane sai shirme. Tana da wata jika sunanta Aina'u to ta yi hatsari ita da 'yarta suka mutu shine hankalinta ya tashi har ta samu depression a kan haka don ƙwaƙwalwarta ma sai da ta taɓu, shiyasa duk wacce ta gani in har cutar ta motsa sai ta fara wannan zancen banzan da ta miki. Shirme ne kawai irin na marasa hankali da tawakkali."
"Ni ma dai haka nace wannan rashin hankaline. Ta yaya ma za a ce ba kece kika haife ni ba! Ba zan taɓa ganin wannan ranar ba a rayuwata in sha Allah. Ai mum duk yarinyar da ta fito a cikin wata macen ba ke ba I'm sorry for her! Ba zan ce ba tai sa'a ba, amma dai she miss don babu uwa tamkar ya ke a duniyar nan a yanzu. You're mummy like no other!"
Rumgumeta Mummy Sarah ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sai dai wani irin tsoro da tausayine ya mamaye zuciyarta. Sosai ta ke tsoron ranar da tsautsayi zai saka Dinaayah ta gano ba ita ce asalin mahaifiyarta ba. Ba ma wannan ne asalin abunda ke tsoratata da ɗaga mata hankali ba, faɗawa Dinaayah irin abunda mahaifiya tata ta shuka a duniya kamun barinta duniyar shi yafi komai yagalgala natsuwarta tare da ninninka tashin hankalinta don ta tsani duk abunda zai ɗagawa 'yarta Dinaayah hankali.
"Allah kai ne Allah, ubangijin sammai da ƙassai, ubangijin abunda ke ƙarƙashin ƙasa da cikin ruwa, ubangijin dukkan halittun duniya, kai na ke roƙo ka taya mu binne abunda muke ƙoƙarin bunnewa shekaru kusan ashirin da uku." A cikin zuciya mummy Sarah ta yi maganar.
"Ungo wannan kofin ki shanye ruwan tass ki ban cup ɗin!" mummy sarah ta faɗi tana miƙa mata.
Babu musu ta amshi cup ɗin ta shanye tass sannan ta miƙa mata.
"Bari 'yan uwanki su shigo su raka ki kiyi alwala ki zo ki yi sallah. Ni bari na tada nawa." mummy Sarah ta faɗi tana miƙewa tsaye yayin da Dinaayah ta gyaɗa mata kai.
Sai da ta yi raka'a biyu sannan su Benazir suka shigo ɗakin kasancewar ba a nan ɗakin su kai ta su sallar ba. Da sauri Benazir ta zo ta zauna kusa da Dinaayah, Aleesha ta zauna ɗaya ɓangaren.
"Ya jikinki sister?" Benazir ce ta yi maganar tana riƙe hannun Dinaayah ɗin.
"I'm very ok fa! Ku kwantar da hankalinku. Ban jin komai a jikina, yanzu dai ku kai ni in yi alwala in zo inyi sallah." Dinaayah ta faɗi.
Miƙewa su ka yi suka kama hannunta su ka kai ta wajen da ake alwala bayan sun ciko mata ruwa a buta sun aje mata a gabanta. Kaf baƙin da su ke tsakar gidan babu wanda ya san cewa Dinaayah makauniya ce saboda yadda ta ke alwalar cikin natsuwa kamar tanda annabi (SAW) ya koyar. Bayan ta gama ta miƙe suka kama hannunta har ɗakin da suka baro lokacin mummy Sarah ta idar da sallah. Sai Dinaayah ta hau kan dardumar da ta sauka ta tada nata sallar.
Benazir da Aleesha sai suka bi bayan mummy Sarah da ta shiga uwar ɗaka. A bakin gado suka same ta zaune ta buga tagumi, duk sai suka nemi waje suka zauna jiki a sanyaye suna kallon fuskanta da ke bayyanar da matsanaiciyar damuwa.
"Mummy mai ya faru? Mai yasa kike cikin damuwa?" a tare su kai mata tambayar.
"Dole na shiga damuwa, Dinaayah tana cikin wani hali. Baiwar Allah ga rashin idanu yanzu kuma wani bala'in ne ya ke bibiyarta. Ba Lukman ya ce jinnul ashiq ne ya shige ta kuma da alama ya jima a jikinta sai yau asirinsa bayyana." mummy ta faɗi.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Jinnul Ashiq fa? Caɓ! Wallahi mummy jinnul Ashiq ba sa taɓa bari mutum ya yi aure, idan ma ya yi sai sun kashe ko kuma su hana shi haihuwa da zaman lafiya." Aleesha ce ta yi maganar hankalinta na daɗa tashi.
Benazir kuwa tsit ta yi tana kallon fuskan Aleesha da ke magana idanunta ba sa ƙiftawa har sai da ta ji tsoron yanayinta ta girgiza ta. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki tare da faɗin, "Mum to yanzu menene mafita? An samu yadda za a cire shi Ashiq ɗin a jikinta?"
"In sha Allah an samu. Yanzu haka ma ruwan addu'ar yana ɗakin ba Lukman, idan mun tashi tafiya da su za mu tafi da kuma sauran magungunan da naga yana harhaɗawa." mummy Sarah ta faɗi.
"To Alhamdulillah!" Benazir ta faɗa tana kuma sauke ajiyar zuciya.
"Mum ina tunanin na san abunda ya saka aljanin nan ya hauro jikin Dinaayah yau." Aleesha ta faɗa.
Da sauri mummy ta kalle ta tare da faɗin, "Menene shi?"
"Kakarki ce ta za komai. Ita ta riƙa wasu maganganun da hankali ba zai ɗauka ba. Tana ta wasu maganganun da ke nuna kamar ba kece kika haife mu ni da Dinaayah ba. Dole in saka kaina a ciki tunda kowa dai ya san ni da Dinaayah 'yan biyu da muka fito ciki ɗaya kuma aka haife mu a rana ɗaya."
"Wallahi Aleesha ni ma tambayar da nake so na yi wa mum kenan!" Benazir ta