Author : Safraz Category : Hausa Book Store
ya yi masu salfie har da shi sau ɗaya kawai shi ma don ya san dole mummy ta yi ƙorafi shiyasa.
"Nonsense! Kana tunanin ka burge ni ne? Dama baka shigo ka ɓata mata hotonmu ba da wannan fuskan shanun naka. Ni dai kaf zuri'a ta babu mai irin wannan fuskan, haka ma gefen Dr na wajen uba don uwa duk mune."
A kunnanta Dr ya raɗa mata, "Ina ki ka bar uncle Ameeru? Ai wallahi shi ma bai dariya."
A hankali ta furta itama, "Wallahi yana ɗan sakin murmushin gefen baki wani lokacin, amma ɗanka ko ni ban ce na taɓa ganin murmushinsa ba tun da ya kai 14years, kai ni tun suna yara ma ta inda na ke bambamce su kenan, Sauban na dariya sosai shi kuma fuskan ɓutu-ɓutu ga uban kumatun da suke ƙara masa muni!" ta ƙarisa maganar tana zabgawa Sam'an ɗin harara.
Wani zaro idanu ta yi don a bazata Sam'an ɗin ya sakar mata murmushin da shi kansa bai san lokacin da ya yi ba, kuma hakan ya faru ne cikin sakanni wanda ita kaɗai taga hakan don yana yi kuma ya mayar da fuska ya ɗinke.
"Da ka san yadda ka yi mugun kyau da kayi murmushin nan da baza ka ƙara ɗaure fuska ba har abada. Don sai ka fito sak Dr wallahi." mummy ta faɗi.
"Dagaske mummy ya yi murmushi!" gaba ɗaya suka haɗa baki har da Dinaayah. Shi kuma Sam'an tsam ya miƙe tare da laptop ɗinsa ya nufi hanyar ɗakinsu da ke nan ƙasa.
"Wallahi murmushi ya yi!" mummy ta faɗi. Sauban sai ya yi karaf ya ce, "Ni ban yi wani mamaki ba don ya kan yi once in a while haka ko kuma idan yana hira da budurwarsa."
"Budurwa! Dama akwai wacce za ta iya soyayya da ya Sam'an da wannan fuskan shanun nasa?" Aleesha ce ta faɗi hakan ya yin da Benazir ta ce, "Caɓ!"
Dad da mummy kuma dariya kawai suka yi. "In jira ki ɗin ne kun gama yanke hukuncin?" daddy ya faɗa yana kallon Benazir kasancewar ita ce kaɗai cikin 'yayansa ta zaɓi irin aikinsa, sai dai ita Nurse cr (Pediatric nursing) ta karanta wato fannin cututtukan ƙananun yara. Housemanship ta ke yi a asibitin mahaifinta yanzu haka.
"Na fasa zuwa sai gobe kawai, dama ba wani abu can zan yi ba. Amma daddy idan ka shiga ka cewa nurse Balaraba ta rubuta min attendance." ta ƙarisa maganar tana susa kai.
Daƙuwa ya yi mata tare da faɗin, "Kina wasa da aikinki ko? Na san ai jiya ma baki je ba. Zan ɓata miki rai idan ban ganki a asibiti gobe ba!"
"Ye sir!" Benazir ta faɗi har da sara masa da ya sa su Aleesha da mom dariya.
"Sai na dawo." ya faɗi yana kallon Dinaayah da ke jira ya fita ta yi masa magana. Murmushi ya yi sannan ya juya ya fita Dinaayar ta bisa a baya, mom da ke son yi masa rakiya sai ta koma ta zauna saboda ba ta damar yin magana da mahaifin nata ganin kamar sirri ta ke son yi da shi. Don akwai mugun shaƙuwa sosai tsakaninsu. Ba ta ɓoye masa komai na ta.
Sai da suka isa har wajen motarsa sannan ya jingina da mota tare da faɗin, "Ya aka yi Alayna Noor?"
Sai da ta ɗan turo baki alamar shagwaɓa sannan ta ce, "Daddy wai KAISAAR ne ya ke ta damuwa zai zo nan gidan."
Wani murmushi ne ya suɓucewa daddyn na farinciki kamun ya furta, "To ki bashi izini mana."
Ɗagowa ta yi ta kalle sa tamkar tana gani kamun ta ce, "To ai baka ce komai ba tun wancen lokacin."
"Shekaran jiya na gama bincike a kansa, kuma dama yau ɗin na ke shirin faɗa miki sakamakon. Yaron kirki ne ki ce masa na bashi izini ya zo ya fara neman soyayyarki kamun mu iyaye mu shiga ciki. Idan halayyansa da ɗabi'unsa sun miki sai ki faɗa min. Ko kina son sanin kamanninsa in faɗa miki?"
Girgiza kai ta yi tare da faɗin, "Daddy in dai ya maka to ni ma ya min. Ba na wani son sanin kamanninsa."
"To ko baki tambaya ba zan faɗa miki, yaro ne dogo fari kyakkyawa kuma mai ilimi both the two ga kunya da tarbiyya. Sannan iyayansa mutanan kirki ne kuma aiki ya ke yi a First bank matsayin manager."
Rufe fuska da tafin hannu Dinaayah ta yi saboda kunyar da ta ji. Sai kuma ta ce, "To dad familynsa za su yarda ya aure ni duk da ban iya gani kamar kowa?"
"Alayna, ke da kan ki kin sha faɗa baki taɓa kallon kanki a matsayin wacce ke da nakasa ba kuma ba wai don ina matsayin mahaifinki ba, duk namijin da ya same ki matsayin mata ya gama morewa."
"Dagaske Daddy?" ta faɗi farinciki mamaye da fuskanta.
"Ƙwarai kuwa! Ke dai ki je ki yi ta addu'a akan Allah ya zaɓa miki abunda ya fi alkhairi a rayuwarki, ni ma zan taya ki."
"In sha Allah daddy. Sai ka dawo Allah ya tsare ka ya kiyaye hanya."
"Ameen Alayna noor!" ya faɗi tare da buɗe motar ya shiga ya tada, ita kuma ta ja baya tare da yi masa bye-bye sannann ta juya. Yadda ta ke tafiya da confidence za ka rantse da Allah tana gani domin babu dibi-dibi ko lalubar hanya kasancewar ta haddace komai na gidan tsaf.
Cak ta tsaya tana faɗaɗa murmushinta tare da faɗin, "Aunty Moon sannu da zuwa! Sunaya taho nan."
Da mugun mamaki ƙawar Maimuna ɗiyar wan Dr Khalil ke kallon wacce Dinaayah ta kira da aunty moon tana mata magana da hannu da kuma idanu akan anya dagaske Dinaayah makauniya ce kuwa kamar yadda ta faɗa mata. Kamun ta dawo daga shan ruwan mamakin da ta yi sai ji ta yi Dinaayah ta ce, "Ina wuni?" kuma daidai inda ta ke tsaye ta ke kallo alamar dai ita ta ke gaisarwa.
Wannan karan a bayyane ƙawar aunty Moon ɗin ta yi magana, "Mummyn Sunayaah gaskiya zolayata ki ke yi wannan ƙanwar ta ki ba makauniya bace." ta ƙarisa maganar ne tana waving a fuskan Dinaayar amma sai taga ko sau ɗaya bata kyafta idanu ba.
Murmushi kawai Dinaayah ta yi tare da amsar Sunaayah da ke hannun aunty Moon don idan da sabo ta saba da irin su ƙawar aunty moon ɗin da ba sa yarda ita makauniya ce.
"Ya akai ta san kina nan kuma ba ke ɗaya bace akwai Sunayaah da kuma ni?" a cikin gigitar mamaki ta yi maganar.
"Ai Dinaayah da ƙamshi ta ke fahimtar mutun na kusa da ita, da ta san ki ma sunanki za ta kira. Ta ji ƙamshina da na Sanaayah ne shiyasa ta kira sunan mu, ke kuma ƙamshinki ta ji sai dai bata taɓa jin irinsa ba shiyasa ba ta iya kiran sunanki ba. Yanzu da za ki yi kwana huɗu zuwa bakwai a inda ta ke tsab za ta haddace ƙamshinka ta yadda ko a cikin mutane da yawa ki ke za ta kira sunanki." Maman Sanaayah ta faɗi tana murmushi.
"Caɓ! Lallai Dinaayah ki godewa ubangiji da ya baki wannan baiwar. Ya hana ki idanun gani amma sai ya baki hancin jin ƙamshin gani." ƙawar aunty Moon ta faɗi.
"Alhamdulillah!" Dinaayah ta faɗi tana murmushi.
"Daga wajen aunty Sarah na ke sai na taras bakya ɗakin shine Bena (Benazir su ke cewa Bena in short) ta faɗa min kin bi Uncle Ibrahim waje za ku yi sirri." ta ƙarisa maganar cikin sigar zaulaya.
Dariya kawai Dinayaah ta yi tare da faɗin "Bari na je ɗaki, ki bar min Sunaayah idan za ku wuce sai ki zo ki amshe ta."
"Na bar maki, ai 'yarki ce!" faɗin aunty Moon tare da juyawa domin komawa ɗakin mahaifiyarta aunty Maryam matar wan Dr Khalil.
Tsabar yanda Amina ƙawar aunty Moon ke kallon yadda Dinaayah ke tafiya ɗauke da Sunaayah a hannunta tamkar mai idanu har tuntuɓe sai da taci. Ba ta bar kallon su ba har sai da ta ga sun shige sannan ta juyo tana sauke ajiyar zuciya.
"In dai Dinaayah ce baki fara ganin komai ba daga cikin baiwar da Allah ya mata. Don yarinyar nan da ki ke gani babu abunda ba ta yi kamaa daga girki, shara, wanke-wanke, mopping ke har kitso tana yiwa mahaifiyarta." aunty Moon ɗin ta faɗa.
"Lallai yarinyar 'yar baiwa ce. Ina ma ina da ɗan uwa namiji wallahi da na ce masa ya zo ya samu matar aure. Ga kyau ga natsuwa, uwa uba ga baiwar da Allah ya mata." Amina ta faɗi.
"Na faɗa miki babu abunda ki ka gani in dai Dinaayah ce."
Dinaayah na shiga ɗaki Benazir ta furta, "Ahaf! Ba na faɗa maku ba. Ai babu abunda zai hana Dinayaah amso Sunaayah. Su Naayah sarkin 'yan son yara."
"Allah ya kawo miji nagari ke ma dai ki mallaki na ki 'ya'yan." Aleesha ta faɗi tana dariya.
"Har yanzu ba ku daidaita da KAISAAR ɗin bane?" Mummy Sarah ce ta yi maganar ba tare da ta ɗago ta kalli Dinaayar ba.
Ita ko Dinaayah sauke Sunaayah ta yi a ƙasa tare da nufa wajen mummy Sarah ta rufe fuskanta a kan cinyarta tare da faɗin, "Kai mum don Allah, wa ya faɗa miki wannan maganaar?"
Dariya mummy Sarah ta yi tare da faɗin, "Idan daddynki abokin sirri da shawararki ne, ni kuma ni ce abokiyar sirri da shawararsa!"
"Wani KAISAAR ɗin wai?" Benazir ta faɗa da maɗaukakin mamakin yayin da Aleesha ta watsa hannu alamar bata sani ba........
#KAISAR
#DINAAYAH
#Mummy Sarah
#Dr Khalil Ibrahim
#Nassarawa (Wamba)
#Between two lovers
_Free pages fa basu da yawa, guda biyar ne kawai don haka ku hwara payment, sannan don girman Allah idan kin san za ki saya ne domin ki fitar kar ki zo na yafe naki cinikin_
`DINAAYAH SAFRAAZ ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVDENCE OF PAYMENT 08128755583`
```Ina ƙara baki shawara sister, kar ki bari ayi wannan tafiyar babu ke```
[9/12, 2:44 PM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_*
(```DiNaayah SafraAz```)
_*BEtweEn two LoveRs*_
~Story and written~
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim*
_Matar Sayyadee_
_Wattpad @MatarSayyadee01_
_Arewabook@Matarsayyadee0_
```In Islam, forgiveness is a vital aspect of our faith, and it's a reminder that we're not alone and that we're all connected in our humanity.```
_… verse of Holy Quran, Allah Almighty says: “The reward of the evil is the evil thereof, but whosoever forgives and makes amends, his reward is upon God!_
Chapter 003
Tsam Benazir ta tashi ta dawo side kusa da Dinaayah tare da faɗin, "Naayah (wani lokacin haka suke kiran sunan juna a gajarce) wanene KAISAAR don Allah? Ko KAISAAR ɗin dai da na sani?"
Gyaɗa mata kai Dinaayah ta yi alamar eh tana ƙara cusa kanta tsakankanin cinyoyin mummy Sarah saboda kunyar da ya gama mamaye ta. Murmushi yaƙe Benazir ta yi tana zuciyarta na wani irin zillon tashin hankali don har ta soma ganin duhu-duhu a cikin idanunta. Sai kawai ta hau kan kujeran da mummy Sarah ke kai ta matsar da kan Dinaayah da ke kan cinyar mummy Sarah tare da ɗaura nata kan ta lumshe idanu tana jin tamkar ta fashe da kuka.
Babu wanda ya lura da yanayinta a ɗakin sai ma ɓallewa da Aleesha da Sauban suka yi wajen tsokalar Dinaayah wanda ya saka Dinaayah tashi ta nufi sama domin gujewa tsokalar tasu.
Da idanu mummy Sarah ta bita tana jin wani tsantsan ƙauna da tausayinta na huda gaba ɗaya tsokoki da jijiyoyin jikinta. Ƙwalla ne su ka taru a idanunsa, da sauri ta shanye su gudun kar su Sauban su gani. Sai kawai ta lumshe idanu tarr da kwantar da kai a jikin kujera tana jin wani relief kaɗan tuno da cewar babu wani mahaluƙi da ya isa ya gano ɓoyayyen sirri da suka daɗe da binnewa kusan shekaru ashirin da uku wanda ya yi daidai da haihuwar Aleesha da Dinaayah ɗin.
Idanunta da su kai jazur ta buɗe sakamakon ringing da wayarta ta yi, hannu ta kai ta ɗauki wayar tare da kallon screen ɗin. Ganin sunan da ya bayyana a jiki bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba ta ɗauki wayar tare da karawa a kunne ta furta, "Ya Lukman sai yau ka tuna da ni?" yanayin da ta ji muryansa ne ya saka lokaci guda gabanta ya buga da ƙarfi tare da furta, "Lafiya, mai ke faruwa ya Lukman?"
Daga can ɓangaren ya Lukman ya furta, "Sai haƙuri Saratu, Allah ya yiwa ba Nura rasuwa yanzun nan (wato wan mahaifinta)".
"Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un!" mummy Sarah ta faɗi sau uku tare da fashewa da matsanaicin kuka da ya sa gaba Aleesha, Benazir da Sauban miƙewa tsaye, hatta Sam'an da ya shige ɗaki fitowa ya yi da saurin jin dogon salatin da mummynsa ke jerawa tare da kuka.
"Mummy wa ye ya rasu?" Sauban da Sam'an suka haɗa baki suka faɗa. Aleesha da Benazir kuma jikinsu ne kawai ke rawa.
"Allah ya yiwa ba Nura rasuwa yanzun nan, wan mahaifina da kullum na kallesa mahaifina na ke gani tsaye shima yau ya amsa kiran ubangiji. Kakanku ya rasu Sam'an." ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka sosai.
Kama ta Sam'an ya yi tare da zaunar da ita ya shiga faɗin, "Hakika abin da Allah ya ɗauka nasa ne, kuma abin da ya bayar da shi ma nasa ne, kuma kowane abu a wurinsa yana da ajali. Allah ya girmama ladanki, ya kyautata haƙurinki a kan abin da kika rasa, ya gafarta wa mamacinki. Kar ki kururuwa mum, ki masa addu'a shi kaɗai ya ke buƙata a wajanki a halin yanzu. Allah ya jiƙansa da rahama ya bashi ikon amsa tambayoyi a cikin ƙabari kuma ya sa aljanna Firdaus ita ce makomarsa!"
"Ameen!" Mummy ta faɗi da muryan kuka kamun ta kai hannu ta share hawayen da ke zubo mata sannan ta lalubo number ɗin Dr ta danna masa kira ringing biyu ya ɗaga kiran.
"Har kin fara missing ɗin nawa kenan? Yanzun nan shigowa ta office kenan ko zama ban yi ba."
"Dr......." kuka ya hana ta faɗin abunda take son faɗa masa. Shi kuma jin yanayinta duk sai ya ruɗe ya shiga faɗin,
"Lafiya Sarah? Mai ke faruwa, mai ya sa kike kuka? Wani abu ne ya faru a gidan? Gani nan dawowa yanzun nan!"
Kamun ya yanke wayar ta yi saurin faɗin, "Allah ya yiwa ba Nura rasuwa! Yanzu ya Lukman ya kira ya ke faɗa min." daƙyar ta iya controlling kanta bata fashe da matsanaicin kuka ba, amma hawaye ya jiƙa fuskanta shataf.
"Inna lillah wa inna ilaihir raju'un! Allahu Akbar, Allah ya jiƙansa da rahama, My sincere condolence. Don Allah ki yi haƙuri ki saka dangana a zuciyarki. Bana son BP ɗinki ya hau, ba Nura addu'a kawai ya ke buƙata a wajanku. Gani nan zuwa yanzun nan, ku soma shiri da na zo sai mu wuce Nasarawan."
Gyaɗa kai ta yi kamar yana kallonta sannan ta kashe wayar tare da miƙewa still tana hawaye ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin hajiya domin ta faɗa mata rasuwar. Ko da ta je ɗakin sai ta taras hajiya ta yi nisa a baccin da take yi sai kawai ta juya ta koma part ɗin aunty Habbooba ta sanar da ita, tare suka fito da Habbooba suka nufi part ɗin aunty Maryam tana ƙara kwantar mata da hankali.
Ganin su kawai da aunty Maryam ta yi da yanayin fuskar mummy Sarah hankalinta ya yi mugun tashi don ta san tabbas babu lafiya. Uncle Abdul-Hakeem ma miƙewa ya yi tsaye daga kan kujera tare da faɗin, "Maman twince lafiya?"
Danne kukan da ke yunƙuro mata ta yi tare da furta, "Allah ya yiwa ba Nura rasuwa, yanzu ya Lukman ya kira ni ya faɗa min."
"Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un!" aunty Maryam da uncle Abdul-Hakeem suka haɗa baki su kai ta maimaitawa.
"Allah ya jiƙansa da rahama ya kuma sa can ɗin da ya tafi ya fiye masa nan ɗin, kuma Allah ya baku haƙurin rashi. Kin faɗawa Doctor?" uncle Abdul-Hakeem ya faɗi.
"Eh na kira shi, ya ce mu shirya gashi nan zuwa mu tafi Nasarawan."
"To shikenan nima bari na shirya. Hajiya ta sani?" ya kuma faɗa.
"Yanzun daga can nake sai naga har yanzun bata farka daga bacci ba shiyasa ba ƙyale ta ban tashe ta ba." Mummy Sarah ta furta tana share hawaye.
"To kuje ku shirya, ni zan je na faɗa hajiyan yanzu." uncle Abdul-Hakeem ya faɗi ita da Habbooba suka juya suka fice daga ɗakin.
"Daddyn Moon zan bi ku, in shirya?" aunty Maryam ta faɗi daidai lokacin da aunty Moon ta fito waya a kunnenta tana magana da mijinta. Ganin iyayanta cirko-cirko sai ta yi sallama da Amina ƙawarta da su ka gidan tare, bata jima da wucewa ba shine ta kira ta ta faɗa mata ta yi mantuwa a cikin jakarta.
"Mom, dad lafiya?" ta yi maganar ne bayan ta iso inda su ke.
"Wan mahaifin maman twince ne ta ya rasu yanzu a Nasarawa!" aunty Maryam ce ta bata amsa.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ba dai tagwainin babanta wanda suke mugun kama ɗinnan ba?"
"Shi fa! Wanda za ki ga ba a haɗa cikakken watanni biyu bai zo ya duba su ba." aunty Maryam ta faɗi.
"Allah sarki! Allah ya jiƙansa da rahama. Lallai kam anyi wa mummy Sarah rasuwa. Ta ce min duk ta kalle sa asalin mahaifinta ta ke gani a fuskansa, shi ke ɗebe mata kewar mahaifinta yau kuma gashi Allah ya amshi abunsa. Lokaci ya yi!" Moon ta faɗi.
"Wallahi fa lokaci ya yi. Allah ya jiƙansa da rahama."
Driver ne ya shigo da mota bayan gateman ya wangale masa ƙofa. Hankalinsa rabuwa biyu ya yi tun sanda ya ɗauko yaran a makaranta saboda faɗan da Ayraah da Amla su ke yi, Afreen kuma sai risgar kuka ta ke yi sabida watsa mata miyan stew da Ayraah ta yi a jikin gogaggen farar baby hijjab ɗinta wanda mahaɗine na sport wear ɗin da ke jikinta. Ayraah ɗin ta je watsawa Amla ne sai akai rashin sa a ta samu Afreen, ita kuma Afreen duk duniya ta tsani a saka mata datti, juice ko kuma miya a kaya. Wannan dalilin ya saka ta riƙa rusa kuka don duk ta kalli gaban hijab ɗin sai ta kuma fashewa da kuma. Ayraah ta bata haƙuri har ta gaji, sai ta dungure mata kai tare da faɗin ta yi ta kukan har a yi tashin ƙiyama. Hakan da Ayraah ta