Author : Safraz Category : Hausa Book Store
kuma kan pastor Emmanuella kawai ta ke ƙoƙarin nufa. Daidai nan Lami ta shigo falon hannunta ɗauke da cup ɗin da ta yi addu'a a ciki, sai ta riƙa tsoma hannunta tana bismillah tare da watsa wa Dinaayah a fuska.
Wani gigitaccen ƙara Dinaayah ta kuma saki tare da yin tsalle ta shaƙi wuyan pastor Emmanuella ta haɗa jikin dogon fridge ɗin da ke falon tana buga kanta. Su uncle Joshua a gigice suka ƙarisa wajenta domin ceton mahaifiyarsu, sai dai mangari ɗaya take masu suke watsewa a ƙasa.
Wuf Benazir ta miƙe tare da mancewa da raɗaɗin azabar da bayanta ke yi ta fita da gudu ko tsayawa saka takalma bata yi ba, Madina na ganin haka ta rufa mata baya. Gudu Benazir ta ke yi tana kuka sosai, jama'a sai kallonta suke suna tambayar Madina abunda ya faru amma ita ma ko kula su ba tai ba sai ma bin bayanBenazir ɗin da take yi itama da gudu.
Kasancewar babu nisa sosai tsakanin gidan Pastor Emmanuella da gidan su iyayan mummy Sarah cikin ƙanƙanin lokacin Benazir ta isa tare da faɗawa gidan da wani irin rikitacciyar kukan da ya ɗaga duka gidan hankali suka rirriƙeta suna tambayar abunda ya faru amma Bena ta kasa magana sai nuna waje take yi da hannu.
Mummy Sarah kuwa tsabar tashin hankali har zaninta na neman kufcewa sai da aunty Suhana ta yi saurin riƙo mata shi tare da tsayar da ita ta gyara ɗaurin da kyau. Tana isa kusa da Benazir ɗin ta rungumeta tare da faɗin, "Kwantar da hankalinki ki faɗa min mai ya faru. Ina 'yan uwanki, ina Dinaayah da Aleesha?"
Nan ma kasa magana ta yi sai nuni ta ke da hannunta izuwa waje. Iyaye mazan gidan ne suka shigo har da Uncle Lukman (wan mummy Sarah). Mari ɗaya ya ɗaurawa fuskan Madina sannan ya ce, "Mai ya faru? Idan ita ta kasa magana ke ai da bakinki!"
"Mun je gidan Pastor ne shine ta kama hannun Dinaayah ta yi ta mata wasu addu'o'i wai za ta raba da Evil spirit kada abunda wai wata Aina'u ta yi ya shafe ta. Kuma ga Dinaayah ɗin can kamar mai aljanu sai dukan mutane ta ke yi, Aleesha ma na can a sume a gidan!" da kuka Madina ta faɗi hakan.
Mummy Sarah da jikinta ke wani irin rawa tamkar mazari da idanu ta yi ta bin bakin Madina har ta kammala magana. A kaf cikin maganganun inda maganar Aina'u ya shigo ne yafi tada mata da hankali har take neman fita daga hayyacinta. Kamun kowa ya ankara Mummy Sarah ta yi fitan bindiga a gidan tare da nufa gidan Pastor Emmanuella domin ɗauko 'ya'yanta. Tuni mutanan gidan suka rufa mata baya har da su ba Lukman da ransu ya ke a mugun ɓace da abunda pastor Emmanuella ta yi ɗin.
Irin gudun da mummy Saratu ke yi ya matuƙar bawa kowa mamaki duk da dama ba wai ƙiba gare ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ta isa gate ɗin gidan kakar tata pastor Emmanuella tare da tura ƙofar da ƙarfi ta shige ciki ko sauraran gate man da ke mata magana bata yi ba don bai gane ba shi sam. Tana shiga su Lukman da ba Lukman suka iso suma suka shigo. Sunday mai gadi ya shiga ƙoƙarin hana su shiga can ciki, duka ɗaya ya Lukman ya masa ya faɗi ƙasa jini na zuba daga hancinsa.
Isar mummy Sarah falon pastor ya yi daidai da wani mugun riƙo da su uncle Joshua su kai wa Dinaayah bayan sun cire hannunta a wuyar pastor dakyar ta koma gefe tana mai da numfashi don bata taɓa tunanin za ta ƙara kwana a duniya ba saboda shaƙar da ta ji tamkar hannun samudawan farko.
"Dinaayah!" mummy Sarah ta ƙwalla kiran sunanta tare da nufa inda take ta riƙo hannunta amma sam su Uncle Joshua sun ƙi sakinta sai ihun addu'arsu suke mata.
Ba Lukman na shigowa kallo ɗaya ya yiwa Dinaayah ya fahimci ba ita bace iskokai ne a kanta.
"Ku kama mu je gida yanzun nan!" ba Lukman ɗin ya faɗi yana kallon 'ya'yansa maza.
Da ƙyar su uku maza suka iya riƙeta suka fita mummy Sarah biye da su a baya tana kuka ko ta kan Aleesha da ke kafaɗan ya Lukman a sume bata yi ba. Lami ma hijjab ta ɗauko ta saka ta bi bayansu bayan ta gargaɗi mahaifiyarta pasto Emanuella kar ta saki ta ce za ta biyo bayansu.
Kai tsaye ɗakin karatun ba Lukman aka yi da Dinaayah aka shimfiɗar a kan carpet don ta ɗan rage haukan da take yi. Aleesha kuma aka yi ɗakin mahaifiyar aunty Suhana da ita aka shafa mata ruwa a fuska ta farfaɗo sannan aka shiga goge jinin da ya ɓata goshinta don ta ji ciwo a wajen har ya yi ƙulu.
Gaba ɗaya mazan gidan zobe suka yi wa Dinaayah sannan suka shiga karanto ayoyin ruqya, da wannan ya sauke wannan ke ɗauka har da ba Lukman da ke shaƙa mata wani turare a hanci da ke ƙara kiɗimata. Ihu ta shiga yi da buge-buge tamkat za ta mutu, can wata kakkaurar murya ta soma magana,
"Ku bari! Ku daina ƙona ni. Ni masoyinta ne ba maƙiyi ba. Na zo na bata kariya ne. Ku bar ƙonani kar ku raba ni da matata uwar 'ya'yana!"
Jinjina kai ba Lukman ya yi jin abunda aljanin da ke jikinta ya faɗi wanda ke nuni da shi ɗin jinnul ashique ne.
"Ku cigaba da karatu kar ku tsaya!" ba Lukman ya faɗi yana ƙara shaƙa mata wannan turaren da ke hannunsa.
"Miƙo min zare!" ba Lukman ɗin ya faɗi domin ƙulle babbar yatsar Dinaayah. Sai dai kamun Mansur ɗansa na uku ya yi wanu yunƙuri Dinaayah ta saki wasu mahaukatan atishawa a jere har uku wanda ke nuni da ya fice daga jikinta. Zurum Dinaayah ta miƙe zaune tana lalube da hannu tare da ƙwalla kiran sunan mummy da ƙarfi.
"Ya fice kafirin!" ya Lukman ya faɗi ransa a ɓace.
"Yana nan guduwa ya yi amma ba fita ya yi a jikinta ba. Jinnul ashique suna da matuƙar naci fiye da tunaninka, ba ƙaramin tashi tsaye za ayi a kan yarinyar nan ba idan ba haka sai ya hana ta aure." ba Lukman ya faɗi.
Jinjina kai ya Lukman ya yi yana kallon Dinaayah da gaba ɗaya jikinta ya saki sai lalube ta ke yi. Tausayinta ne ya mamaye zuciyarsa ganin irin ƙaddarorin da ke kanta. Na farko tabon da ke bibiyarta, na biyu makanta ga kuma na uku ya ɓullo na jinnul ashique.
"Ku kai ni wajen mummyna. Benazir! Benazir!! Kina ina? Aleeshaa!" ta yi ta ƙwala kiran sunansu tana lalube don ta kasa shaƙo ƙamshin wanda ta sani a wajen.
Burum! Mummy Sarah ta shigo ɗakin. Zabura Dinaayah ta yi tana lalube tare da kiran sunan mummy ɗin sabida shaƙo ƙamshinta da ta yi.
"Gani nan, kama hannuna Alyana noor ɗin daddy. Gani nan ba zan bari wani abu ya same ki ba. Taho mu tafi ɗaki." mummy Sarah ta faɗi.
"Mummy mu tafi gida. Kar mu ƙara kwana a nan garin. Ki kira daddy don Allah!" Dinaayah ta faɗi tana riƙe hannun mummy Sarah da ƙarfi.
"Kwantar da hankalinki Dinaayah, ai dama ɗazu daddyn naku ya kira ni ya ke ce min gobe zai zo ya ɗauke mu mu koma gida."
Gyaɗa kai Dinaayah ta yi ta kuma ƙi bari su haɗa idanu ba Lukman da ya kafe ta da idanu yana zargin kamar har yanzu ba ita bace.
"Mu fita daga ɗakin nan mummy yanzu don Allah!" Dinaayah ta faɗi tana miƙewa tsaye.
Mummy Sarah ma miƙewa ta yi tare da kama hannunta, sai dai ko taku ɗaya basu yi ba ba Lukman ya dakatar da su wanda hakan ya saka Dinaayah cizon leɓen bakinta na ƙasa da ƙarfi sannan ta kuma damƙe hannun mummyn.
"Bar ta anan ki yi tafiyarki, za ta dawo da ƙafafunta!" shine abunda ba Lukman ya faɗi yana nufa inda kaskon da ya ke saka turare ya ke.
"Ki sake ta ki fita nace!" ba Lukman ya faɗi da ƙarfi yana zarowa mummy Sarah idanu wanda hakan ya saka ta saki hannun Dinaayah ta fice ba tare da ta shirya hakan ba.
"Ni za ka kawo wa iskanci? To nan gidan da ka ke gani ba gidan da ake shigowa a yi wargi bane. Ubanka za ka ci don sai tabbatar na ƙone jikinta tass, mara tsoran Allah ja'iri!"
Wani irin juyowa Dinaayah ta yi tare da nuna ba Lukman da hannu jikinta na rawa har laɓɓanta tare da faɗin, "Ka fita sabgata ko kuma na illataka. Kai ka san tsayin lokacin da na yi tare da ita da rana tsaka za ka zo ka fara ƙoƙarin raba mu? Ƙaryan ka ta sha ƙarya malam Lukman! Idan kana ji da ƙananan ƙwari to ka sani wannan babban ƙwaro ne a gabanka."
Murmushin gefen baki ba Lukman ya yi sannan ya furta, "Ni kuma zan gwada maka ayoyin Allah na maganin ƙanana 'yan iska da kuma gaggan su. Mintuna biyu na baka ka tattara inaka-inaka ka bar jikin jikata ni kuma na maka alƙawarin barin ka da ranka, idan kuma ka ƙi, to baka ƙi gani ba!"
"Kai ka isa! Ni da Dinaayah mutuwa ce za ta raba mu, kuma wallahi duk wanda ya yi ƙoƙari shiga tsakanina da halal ɗina ko waye shi sai na ga bayansa!"
"Halal ɗinka?" ba Lukman ya faɗi yana kallon cikin ƙwayan idanun Dinaayah da ke wani irin maiƙo yana fitar da ruwan hawaye.
"Eh! Halal ɗina ce don sai da na biya sadaki tukun na aure ta. Kuma yanzu haka 'ya'yanmu biyu tare. Ko so ka ke ni da 'ya'yana mu zama marayu? mara imani!"
Ba Lukman gajiya ya yi da sa'insa da shi sai kawai ya kunna burner ya zuba turaren da ke matuƙar tayar da hankalin ko wani irin kafirin jinni mara tsoran Allah. Hayaƙin na fara sama Dinaayah ta hau wani irin buge-buge tana ihu tamkar gidan zai tsage. Kaf mutanan gida fitowa su kai tsakar gida su kai cirko-cirko suna sauraran ihunta. Aleesha, Benazir da mummy Sarah kuwa kuka kawai suke yi rungume a jikin mummyn.
Sai da aka kwashi tsayin muntuna talatin kamun komai ya lafa daga ɗakin ba Lukman ɗin. Can sai ga ya Lukman saɓe da Dinaayah ɗin a kafaɗa ya wuce ɗakin matar ba Lukman ɗin ya shimfiɗar da ita tare da kunna ƙira'a sannan ya fito ya jawo ƙofar.
"Kar kowa ya je inda ta ke har sai ta tashi da kanta, kuma kar a kashe ƙira'ar. Sarah ki je ba Lukman na kiran ki." Lukman ne ya yi maganar tare da ficewa daga gidan ya nufi nasa gidan don shima ya yi aure last 2years har da ɗansa ɗaya mai suna Nuhu suna kiransa (Ashraf).
Jiki a sanyaye mummy Sarah ta shiga ɗakin ba Lukman ɗin tare da zama a ƙasa kasancewar shi yana kan kujera ne.
"Tun yaushe ta ke fama da wannan matsalar?" ba Lukman ya faɗa ba tare da kalleta ba, idanunsa na kan wasu magungunan da ya ke haɗawa.
"Gaskiya bata taɓa irin haka ba sai yau. Tun da na haifeta yau ne na fara ganin hakan a gare ta."
Ɗan ɗagowa ya yi ya kalleta tare na kusan second biyar sannan ya mayar da kansa kan magungunar tare da faɗin, "Bata taɓa faɗa miki tana wani mafarkar haka wanda bata gane masu ba, ko kuma mafarkin wani na zuwa mata haka cikin bacci?"
"Gaskiya bata taɓa faɗa min haka ba sai sau ɗaya da ta ce min ta yi mafarkin wani na binta da gudu amma bata san ko wanene ba, sannan gabanta ruwa ne wanda bai da iyaka kuma yana da mahaukacin zurfi, idan ta kawo wajen ruwan sai ta tsaya cak! Shikuma mai bin nata sai ya ce mata ya faɗa mata za ta yi gudu iya iyawarta amma ba zata taɓa tsere masa ba. Ni kuma sai na ce mata ta yi addu'a mafarki ne kawai babu abunda zai faru da ita."
"To yarinyar nan tana fama da matsalar jinnul ashique! Kuma idan ba a tashi tsaye ba yarinyar nan za ta afka cikin babbar matsala fiye da wanda take ciki yanzu. Don ba lallai shi aljanin ya barta tai aure ba, idan ma ya barta to babu zaman lafiya tsakaninta da mijin." ba Lukman ya faɗi.
Mummy Sarah tuni har ta soma kuka tana faɗin, "Baba menene kuma jinnul ashiq?"
"Idan aka ce Jinnul Ashiq a na nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji. Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma kokarin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga kokarin kashe mata shi. Su na kuma kokarin hana mace samun ciki, ko kuma in ta samun cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa, ya zamo tun daga haifarsa za a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau’in Aljani shi muke kira JINNUL ASHIQ. Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne mutum yake yi da su."
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ba Lukman yanzu mecece mafita? Ya za ayi a rabaa da shi?"
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ba Lukman ya yi sannan ya furta, "Ga ayoyin da za a riƙa yi a cikin ruwa ana shafe duk jikinta da shi bayan la'asar ko kuma ta riƙa wanka da shi. Amma a waje mai tsarki ake wankan kamar cikin daki kuma ba da sabulu ba. Sannan sauran ruwan kada a zuba shi a kwata ko najasa, saidai a zubawa shuka ko a zuba a inda kasa za ta tsotse. Sai kuma a sake karanta wadannan jerin ayoyi a ruwa wanda ba azuba komai a ciki ba, sai mai lalurar ya dinga sha kullum, kuma kada ya sha wani ruwa sai wannan. Yanzu bari na yi addu'o'in cikin wancen tsaftataccen ruwan saman."
Gyara zama mummy Sarah ta yi domin sauraransa. Sai da ya matso da bokitin kusa da shi sosai sannan ya zuba man _wardi_ a ciki tare da saka hannunsa na dama ya kuma matso da bakinsa gab da bokitin ya soma karatun.
.
– ﻓﺎﺗﺤﺔ ﺍﻟﻜـﺘﺎﺏ
/ ﺁﻳــﺔ ﺍﻟﻜﺮﺳــﻰ
{ ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍْ ﻣَﺎ ﺗَﺘْﻠُﻮﺍْ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦُ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﻠْﻚِ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ ﻭَﻣَﺎ ﻛَﻔَﺮَ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥُ ﻭَﻟَـﻜِﻦَّ ﺍﻟﺸَّﻴْﺎﻃِﻴﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍْ ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮَ ﻭَﻣَﺎ ﺃُﻧﺰِﻝَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤَﻠَﻜَﻴْﻦِ ﺑِﺒَﺎﺑِﻞَ ﻫَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎ ﻳُﻌَﻠِّﻤَﺎﻥِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﻘُﻮﻻَ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻧَﺤْﻦُ ﻓِﺘْﻨَﺔٌ ﻓَﻼَ ﺗَﻜْﻔُﺮْ ﻓَﻴَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣِﻨْﻬُﻤَﺎ ﻣَﺎ ﻳُﻔَﺮِّﻗُﻮﻥَ ﺑِﻪِ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟْﻤَﺮْﺀِ ﻭَﺯَﻭْﺟِﻪِ ﻭَﻣَﺎ ﻫُﻢ ﺑِﻀَﺂﺭِّﻳﻦَ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺇِﻻَّ ﺑِﺈِﺫْﻥِ ﺍﻟﻠّﻪِ ﻭَﻳَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﻳَﻀُﺮُّﻫُﻢْ ﻭَﻻَ ﻳَﻨﻔَﻌُﻬُﻢْ ﻭَﻟَﻘَﺪْ ﻋَﻠِﻤُﻮﺍْ ﻟَﻤَﻦِ ﺍﺷْﺘَﺮَﺍﻩُ ﻣَﺎ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺍﻵﺧِﺮَﺓِ ﻣِﻦْ ﺧَﻼَﻕٍ ﻭَﻟَﺒِﺌْﺲَ ﻣَﺎ ﺷَﺮَﻭْﺍْ ﺑِﻪِ ﺃَﻧﻔُﺴَﻬُﻢْ ﻟَﻮْ ﻛَﺎﻧُﻮﺍْ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ { ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 102
{ ﻗَﺎﻟُﻮﺍْ ﻳَﺎ ﻣُﻮﺳَﻰ ﺇِﻣَّﺎ ﺃَﻥ ﺗُﻠْﻘِﻲَ ﻭَﺇِﻣَّﺎ ﺃَﻥ ﻧَّﻜُﻮﻥَ ﻧَﺤْﻦُ ﺍﻟْﻤُﻠْﻘِﻴﻦَ ( 115 ) ﻗَﺎﻝَ ﺃَﻟْﻘُﻮْﺍْ ﻓَﻠَﻤَّﺎ ﺃَﻟْﻘَﻮْﺍْ ﺳَﺤَﺮُﻭﺍْ ﺃَﻋْﻴُﻦَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﻭَﺍﺳْﺘَﺮْﻫَﺒُﻮﻩْﻡُ ﻭَﺟَﺎﺀﻭﺍ ﺑِﺴِﺤْﺮٍ ﻋَﻈِﻴﻢٍ ( 116 ) ﻭَﺃَﻭْﺣَﻴْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻰ ﻣُﻮﺳَﻰ ﺃَﻥْ ﺃَﻟْﻖِ ﻋَﺼَﺎﻙَ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻫِﻲَ ﺗَﻠْﻘَﻒُ ﻣَﺎ ﻳَﺄْﻓِﻜُﻮﻥَ ( 117 ) ﻓَﻮَﻗَﻊَ ﺍﻟْﺤَﻖُّ ﻭَﺑَﻄَﻞَ ﻣَﺎ ﻛَﺎﻧُﻮﺍْ ﻳَﻌْﻤَﻠُﻮﻥَ ( 118 ) ﻓَﻐُﻠِﺒُﻮﺍْ ﻫُﻨَﺎﻟِﻚَ ﻭَﺍﻧﻘَﻠَﺒُﻮﺍْ ﺻَﺎﻏِﺮِﻳﻦَ ( 119 ) ﻭَﺃُﻟْﻘِﻲَ ﺍﻟﺴَّﺤَﺮَﺓُ ﺳَﺎﺟِﺪِﻳﻦَ ( 120 ) ﻗَﺎﻟُﻮﺍْ ﺁﻣَﻨَّﺎ ﺑِﺮِﺏِّ ﺍﻟْﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ ( 121 ) ﺭَﺏِّ ﻣُﻮﺳَﻰ ﻭَﻫَﺎﺭُﻭﻥَ { ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ 115 : 122
} ﻓَﻠَﻤَّﺎ ﺃَﻟْﻘَﻮﺍْ ﻗَﺎﻝَ ﻣُﻮﺳَﻰ ﻣَﺎ ﺟِﺌْﺘُﻢ ﺑِﻪِ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﺳَﻴُﺒْﻄِﻠُﻪُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠّﻪَ ﻻَ ﻳُﺼْﻠِﺢُ ﻋَﻤَﻞَ ﺍﻟْﻤُﻔْﺴِﺪِﻳﻦَ ( 81 ) ﻭَﻳُﺤِﻖُّ ﺍﻟﻠّﻪُ ﺍﻟْﺤَﻖَّ ﺑِﻜَﻠِﻤَﺎﺗِﻪِ ﻭَﻟَﻮْ ﻛَﺮِﻩَ ﺍﻟْﻤُﺠْﺮِﻣُﻮﻥَ { ﻳﻮﻧﺲ 81 : 82
} ﻗَﺎﻝَ ﺑَﻞْ ﺃَﻟْﻘُﻮﺍ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﺣِﺒَﺎﻟُﻬُﻢْ ﻭَﻋِﺼِﻴُّﻬُﻢْ ﻳُﺨَﻴَّﻞُ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﻣِﻦ ﺳِﺤْﺮِﻫِﻢْ ﺃَﻧَّﻬَﺎ ﺗَﺴْﻌَﻰ ( 66 ) ﻓَﺄَﻭْﺟَﺲَ ﻓِﻲ ﻧَﻔْﺴِﻪِ ﺧِﻴﻔَﺔً ﻣُّﻮﺳَﻰ ( 67 ) ﻗُﻠْﻨَﺎ ﻟَﺎ ﺗَﺨَﻒْ ﺇِﻧَّﻚَ ﺃَﻧﺖَ ﺍﻟْﺄَﻋْﻠَﻰ ( 68 ) ﻭَﺃَﻟْﻖِ ﻣَﺎ ﻓِﻲ ﻳَﻤِﻴﻨِﻚَ ﺗَﻠْﻘَﻒْ ﻣَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ ﻛَﻴْﺪُ ﺳَﺎﺣِﺮٍ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﻔْﻠِﺢُ ﺍﻟﺴَّﺎﺣِﺮُ ﺣَﻴْﺚُ ﺃَﺗَﻰ { ﻃﻪ :66 69
} ﻭَﻗَﺪِﻣْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻰ ﻣَﺎ ﻋَﻤِﻠُﻮﺍ ﻣِﻦْ ﻋَﻤَﻞٍ ﻓَﺠَﻌَﻠْﻨَﺎﻩُ ﻫَﺒَﺎﺀ ﻣَّﻨﺜُﻮﺭًﺍ { ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ : 23
} ﺇِﻥَّ ﻫَـﺆُﻻﺀ ﻣُﺘَﺒَّﺮٌ ﻣَّﺎ ﻫُﻢْ ﻓِﻴﻪِ ﻭَﺑَﺎﻃِﻞٌ ﻣَّﺎ ﻛَﺎﻧُﻮﺍْ ﻳَﻌْﻤَﻠُﻮﻥَ { ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ : 139
} ﻭَﺇِﺫْ ﻳَﻌِﺪُﻛُﻢُ ﺍﻟﻠّﻪُ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﺍﻟﻄَّﺎﺋِﻔَﺘِﻴْﻦِ ﺃَﻧَّﻬَﺎ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﺗَﻮَﺩُّﻭﻥَ ﺃَﻥَّ ﻏَﻴْﺮَ ﺫَﺍﺕِ ﺍﻟﺸَّﻮْﻛَﺔِ ﺗَﻜُﻮﻥُ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﻳُﺮِﻳﺪُ ﺍﻟﻠّﻪُ ﺃَﻥ ﻳُﺤِﻖَّ ﺍﻟﺤَﻖَّ ﺑِﻜَﻠِﻤَﺎﺗِﻪِ ﻭَﻳَﻘْﻄَﻊَ ﺩَﺍﺑِﺮَ ﺍﻟْﻜَﺎﻓِﺮِﻳﻦَ ( 7 ) ﻟِﻴُﺤِﻖَّ ﺍﻟْﺤَﻖَّ ﻭَﻳُﺒْﻄِﻞَ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞَ ﻭَﻟَﻮْ ﻛَﺮِﻩَ ﺍﻟْﻤُﺠْﺮِﻣُﻮﻥَ { ﺍﻷﻧﻔﺎﻝ : 7 8
} ﻭَﻗُﻞْ ﺟَﺎﺀ ﺍﻟْﺤَﻖُّ ﻭَﺯَﻫَﻖَ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞَ ﻛَﺎﻥَ ﺯَﻫُﻮﻗًﺎ { ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ : 81
} ﺑَﻞْ ﻧَﻘْﺬِﻑُ ﺑِﺎﻟْﺤَﻖِّ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞِ ﻓَﻴَﺪْﻣَﻐُﻪُ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻫُﻮَ ﺯَﺍﻫِﻖٌ ﻭَﻟَﻜُﻢُ ﺍﻟْﻮَﻳْﻞُ ﻣِﻤَّﺎ ﺗَﺼِﻔُﻮﻥَ { ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ : 18
} ﻭَﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀ ﺫَﺍﺕِ ﺍﻟْﺒُﺮُﻭﺝِ ( 1 ) ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﻤَﻮْﻋُﻮﺩِ ( 2 ) ﻭَﺷَﺎﻫِﺪٍ ﻭَﻣَﺸْﻬُﻮﺩٍ
( 3 ) ﻗُﺘِﻞَ ﺃَﺻْﺤَﺎﺏُ ﺍﻟْﺄُﺧْﺪُﻭﺩِ ( 4 ) ﺍﻟﻨَّﺎﺭِ ﺫَﺍﺕِ ﺍﻟْﻮَﻗُﻮﺩِ ( 5 ) ﺇِﺫْ ﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﻗُﻌُﻮﺩٌ ( 6 ) ﻭَﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻳَﻔْﻌَﻠُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ﺷُﻬُﻮﺩٌ ( 7 ) ﻭَﻣَﺎ ﻧَﻘَﻤُﻮﺍ ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻥ ﻳُﺆْﻣِﻨُﻮﺍ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻌَﺰِﻳﺰِ ﺍﻟْﺤَﻤِﻴﺪِ ( 8 ) ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻟَﻪُ ﻣُﻠْﻚُ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻰ ﻛُﻞِّ ﺷَﻲْﺀٍ ﺷَﻬِﻴﺪٌ ( 9 ) ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻓَﺘَﻨُﻮﺍ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨَﺎﺕِ ﺛُﻢَّ ﻟَﻢْ ﻳَﺘُﻮﺑُﻮﺍ ﻓَﻠَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏُ ﺟَﻬَﻨَّﻢَ ﻭَﻟَﻬُﻢْ ﻋَﺬَﺍﺏُ ﺍﻟْﺤَﺮِﻳﻖِ ( 10 ) ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﻭَﻋَﻤِﻠُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﺎﻟِﺤَﺎﺕِ ﻟَﻬُﻢْ ﺟَﻨَّﺎﺕٌ ﺗَﺠْﺮِﻱ ﻣِﻦ ﺗَﺤْﺘِﻬَﺎ ﺍﻟْﺄَﻧْﻬَﺎﺭُ ﺫَﻟِﻚَ ﺍﻟْﻔَﻮْﺯُ ﺍﻟْﻜَﺒِﻴﺮُ ( 11 ) ﺇِﻥَّ ﺑَﻄْﺶَ ﺭَﺑِّﻚَ ﻟَﺸَﺪِﻳﺪٌ ( 12 ) ﺇِﻧَّﻪُ ﻫُﻮَ ﻳُﺒْﺪِﺉُ ﻭَﻳُﻌِﻴﺪُ ( 13 ) ﻭَﻫُﻮَ ﺍﻟْﻐَﻔُﻮﺭُ ﺍﻟْﻮَﺩُﻭﺩُ ( 14 ) ﺫُﻭ ﺍﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺍﻟْﻤَﺠِﻴﺪُ ( 15 ) ﻓَﻌَّﺎﻝٌ ﻟِّﻤَﺎ ﻳُﺮِﻳﺪُ ( 16 ) ﻫَﻞْ ﺃَﺗَﺎﻙَ ﺣَﺪِﻳﺚُ ﺍﻟْﺠُﻨُﻮﺩِ ( 17 ) ﻓِﺮْﻋَﻮْﻥَ ﻭَﺛَﻤُﻮﺩَ
( 18 ) ﺑَﻞِ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻓِﻲ ﺗَﻜْﺬِﻳﺐٍﻓِﺮْﻋَﻮْﻥَ ﻭَﺛَﻤُﻮﺩَ
( 18 ) ﺑَﻞِ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻓِﻲ ﺗَﻜْﺬِﻳﺐٍ ( 19 ) ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣِﻦ ﻭَﺭَﺍﺋِﻬِﻢ ﻣُّﺤِﻴﻂٌ
( 20 ) ﺑَﻞْ ﻫُﻮَ ﻗُﺮْﺁﻥٌ ﻣَّﺠِﻴﺪٌ ( 21 ) ﻓِﻲ ﻟَﻮْﺡٍ ﻣَّﺤْﻔُﻮﻅٍ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺒﺮﻭﺝ
} ﺃَﻟَﻢْ ﻧَﺸْﺮَﺡْ ﻟَﻚَ ﺻَﺪْﺭَﻙَ ( 1 ) ﻭَﻭَﺿَﻌْﻨَﺎ ﻋَﻨﻚَ ﻭِﺯْﺭَﻙَ ( 2 ) ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺃَﻧﻘَﺾَ ﻇَﻬْﺮَﻙَ ( 3 ) ﻭَﺭَﻓَﻌْﻨَﺎ ﻟَﻚَ ﺫِﻛْﺮَﻙَ ( 4 ) ﻓَﺈِﻥَّ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮِ ﻳُﺴْﺮًﺍ ( 5 ) ﺇِﻥَّ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﻌُﺴْﺮِ ﻳُﺴْﺮًﺍ ( 6 ) ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻓَﺮَﻏْﺖَ ﻓَﺎﻧﺼَﺐْ ( 7 ) ﻭَﺇِﻟَﻰ ﺭَﺑِّﻚَ ﻓَﺎﺭْﻏَﺐْ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻹﻧﺸﺮﺍﺡ
} ﺇِﺫَﺍ ﺯُﻟْﺰِﻟَﺖِ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽُ ﺯِﻟْﺰَﺍﻟَﻬَﺎ ( 1 ) ﻭَﺃَﺧْﺮَﺟَﺖِ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽُ ﺃَﺛْﻘَﺎﻟَﻬَﺎ ( 2 ) ﻭَﻗَﺎﻝَ ﺍﻟْﺈِﻧﺴَﺎﻥُ ﻣَﺎ ﻟَﻬَﺎ ( 3 ) ﻳَﻮْﻣَﺌِﺬٍ ﺗُﺤَﺪِّﺙُ ﺃَﺧْﺒَﺎﺭَﻫَﺎ ( 4 ) ﺑِﺄَﻥَّ ﺭَﺑَّﻚَ ﺃَﻭْﺣَﻰ ﻟَﻬَﺎ
( 5 ) ﻳَﻮْﻣَﺌِﺬٍ ﻳَﺼْﺪُﺭُ ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﺃَﺷْﺘَﺎﺗًﺎ ﻟِّﻴُﺮَﻭْﺍ ﺃَﻋْﻤَﺎﻟَﻬُﻢْ ( 6 ) ﻓَﻤَﻦ ﻳَﻌْﻤَﻞْ ﻣِﺜْﻘَﺎﻝَ ﺫَﺭَّﺓٍ ﺧَﻴْﺮًﺍ ﻳَﺮَﻩُ ( 7 ) ﻭَﻣَﻦ ﻳَﻌْﻤَﻞْ ﻣِﺜْﻘَﺎﻝَ ﺫَﺭَّﺓٍ ﺷَﺮًّﺍ ﻳَﺮَﻩُ { ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺰﻟﺰﻟﺔ
} ﻭَﻳْﻞٌ ﻟِّﻜُﻞِّ ﻫُﻤَﺰَﺓٍ ﻟُّﻤَﺰَﺓٍ ( 1 ) ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻤَﻊَ ﻣَﺎﻟًﺎ ﻭَﻋَﺪَّﺩَﻩُ ( 2 ) ﻳَﺤْﺴَﺐُ