Author : Safraz Category : Hausa Book Store
ce ba ƙaramin ƙara tunzurata ya yi ba ta kuma fashewa da kuka tana Allah-Allah su dawo gida ta tafi ta faɗawa mummy Sarah abunda Ayraah ɗin ta mata. Shi kansa Bala driver ya yi ban haƙurin shima har ya gaji. Ga Ayraah da Amla ɗin sai jife-jife suke a motar wanda shi kansa sai da aka same sa a ƙeya. Sun yi kaca-kaca da motar.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke bayan ya yi parking. Afreen ce ta soma fitowa ta ɓangaren dama ta kwasa da gudu ta yi part ɗin mummy Sarah tana kuka, ko tsayawa ɗaukar jakarta da lunch box ɗinta bata yi ba saboda ƙosawar da ta yi ta kai ƙarar Ayraah.
Ƙwafa Ayraah ta yi bayan ta zabgawa Amla harara tare da faɗin, "Sai na ɓaɓɓala ki a cikin gidan nan, ni ba tsararki ba ce. Kuma bari daddy ya dawo sai na faɗa masa you disrespect me in the present of my friends don ki jawo min raini!"
Wani wawan harara tamkar idanunta za su zazzago Amla ta watsa mata tare da faɗin, "Kika ce ni ba tsarki bace, to da me kwaɗo ya fi gaya? Mintuna biyar ne kacal ne kawai a tsakaninmu. Kina fitowa ni ma na fito. Shekara ɗaya, rana ɗaya, mintuna biyar ne kawai tsakaninmu! Kuma mummy ta faɗa min gaskiya ai, ni ce na soma yunƙuri fitowa ke kuma da yake dama kin iya mugunta sai kika taɗiye ni ƙafana ya harɗe da umbilical cord ɗina shine ki ka yi sauri ki ka riga ni fitowa."
"Maƙaryaciyar banza! Wallahi mummy bata faɗi haka ba, kuma bari mu shiga ciki sai na faɗawa ya Sam'an abunda ki ka ce da kuma dizgani da ki ka yi a gaban ƙawayena." Ayraah ta faɗi.
"To ki faɗa mana, tsoransa ake ji!" Amla ta faɗi har da wani gyatsine.
Juyawa Ayraah ta yi ta kalli Bala Driver da ke tsaye yana kallon su yana murmushi don idan da sabo ya saba da rigimar 'yan biyun.
"Baba Bala kana dai shaida na ko? In ce dai a kunnanka ta faɗi ba ta tsoran ya Sam'an ko?"
Maganar bebaye Bala driver ya soma yi irin bai gane abunda ta ke cewa ba sannan kuma yana mata nuni da shi bai jin maganar da suke yi kwata-kwata. Turɓune fuska ta yi tare da faɗin, "Mun ɓata da kai baba Bala!" tana gama faɗin haka ta fizgi jakarta ta yi cikin gida ita kuma Amla sai dariya ta ke mata.
Buɗe murya Bala driver ya yi tare da faɗin, "Ayraah ki yi haƙuri kar ki fushi da baba Bala. Ku ba a shiga tsakaninku ne shiyasa ban ce komai ba. Ina iya yin magana in dawo ina jin kunya." da dariya ya yi maganar.
"Baram-baram!" Ayraah ta faɗi bayan ta juyo ta kallesa har da watsa hannu sannan ta juya ta cigaba da tafiya.
"Rabu da ita baba Bala, ai da kanta za ta dawo ba sai ka kira ta ba." Amla ta faɗa tare da ɗaukar jakarta ita ma ta nufi part ɗin mummy Saran.
Cak! Afreen ta tsaya daga bakin ƙofa tana kallon kowa da ke ɗakin jiki a sanyaye kamun ta mayar da kallonta kan mummy Sarah da ke zaune a kan kujera idanunta jazur. Da gudu ta nufe ta tare da faɗawa jikinta ta hau kuka itama duk da bata san mai ke faruwa ba.
"Mummy mai aka miki kike kuka? Why are you crying?"
Shafa kanta mummy Sarah ta shiga yi tare da faɗin, "It alright, na dena kukan ai. Rasuwa aka yi. Babana ne ya rasu yau shiyasa na yi kuka."
Ɗagowa da sauri Afreen ta yi tare da faɗin, "Mom babanki da yake zuwa nan daga Nasarawa? Mai ya same shi?"
Gyaɗa kai mummy Sarah ta yi tare da faɗin, "Eh shi! Lokacinsa ne ya yi."
Rungumeta Afreen ta kuma yi tana fashewa da kuka sosai daidai nan Ayraah ta shigo ɗakin fuska a kumbure, amma ganin mummy na hawaye Afreen kuma na kuka sosai bata san ta yi wurgi da jakarta ba ta ƙarisa inda suke da gudu tana kuka. Itama Amla ta shigowa sai ta bi sahunsu.
Dinaayah ce ta daka masu tsawa tare da faɗin, "Kuna hauka ne? Mummy na cikin damuwa ku kuma za ku zo kuna koke-koke domin ku ƙara mata. Bari na kira ya Sam'an ai yana gidan wanka ya shiga yi."
Gaba ɗaya sai suka yi tsit amma kuma sun ƙi barin jikin mummy Saran har sai da ta kalli Afreen tare da faɗi, "Ki je wajen auntynku ki canzo kaya za mu je Nasarawa yanzu idan daddynku ya dawo."
(tana nufin mahaifiyarta don da Afreen da Benazir mahaifiyarsu ɗaya {Habbooba}. Sauban, Sam'an, Dinaayah da Aleesha kuma duk Mummy Sarah ce ta haife su. Abunda ya sa Benazir da Afreen su ke cewa mahaifiyarsu aunty, saboda sun tashi sun ji Sauban da Sam'an suna faɗa, haka mummy da suke kiran Sarah duk a bakin su Sam'an ɗin suka ɗauka.)
Da sauri Afreen ta tashi ta ɗauki jakarta ta fice daga ɗakin har tana buga ƙafarta, Benazir ɗin ma miƙewa ta yi ta fita domin canza kaya kasancewar wando da riga ne a jikinta.
Hajiya ce ta shigo ɗakin a sanyaye tare da sallama a bakinta. A sanyaye Sarah ta amsa tana mai miƙewa tsaye domin bawa hajiya girma.
"Uwata ashe abunda ya faru kenan, Nura sa'i ya yi! Allah ya jiƙansa da rahama ya baku haƙurin rashi. Yanzu mu kai waya da Ibrahim ta ce min ya kusa ƙarisowa gidan sai mu wuce Nasarawan. Aisha da Marmari daga nesa ma har sun hau hanya." ko gama rufe baki hajiya bata yi ba Dr ya yi sallama ya shigo.
Mummy Sarah na haɗa idanu dashi sai hawaye sha kamar an buɗe fanfo. Kawas da idanu ya yi don kukanta ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ya ke yi ba.
"My condolence, Sarah! Allah ya jiƙan ba Nura da rahama." Khalil ya faɗa yana wucewa sama domin canza kaya zuwa manya kasancewar na jikinsa suit ne.
Ko da ya sauko gaba ɗaya kowa ya shirya shi kaɗai ake jira. Kamar haɗin baki kaya iri ɗaya suka saka saka shi da twince ɗinsa maza. Dub da dama su Sauban gabaa ɗaya kayansu iri ɗaya suke yi.
Gaba ɗaya suka fito suka nufi wajen mota. Dr, hajiya, da sarah da Habbooba suka shiga sabuwar motarsa Rolls-Royce Sweptail. Hajiya, mummy Sarah da Afreen suka zauna a gidan baya Habbooba da dama duk za a fita ita ke yin maza ta shige gidan gaba, Sarah kuma bata taɓa damuwa da hakan ba, yau ma ɗin gaban ta shige ya kame yayin da Dr Khalil ya zauna mazaunin driver.
Sauban da Sam'am Range Rover suka shiga shi da sauran ƙannansa Dinaayah, Benazir, Aleesha, Ayraah da Amla wanda Sam'an ɗin ne zai ja motar. Uncle Abdul-Hakeem shi ma a nasa motar shi da aunty Maryam, aunty Laure da tare suka dawo gidan da daddy daga asibiti, sai kuma Moon da ta kira mijinta ta sanar da shi sannan ya bata izinin tafiya ta'aziyar.
Kasancewar ƙarfe uku da wani abu suka fita daga gida, sai ƙarfe bakwai da hamsin suka isa Nasarawa. Suna sauka bai fi mintuna talatin ba su ya Abdallah da aunty Aysha suka iso suma. Wani sabon babin kuka mummy Sarah suka buɗe ita da 'yan uwanta da suka haɗu a ɗakin ba Lukman. Na'ima yar mummy Sarah an ce suma ya riƙa yi saboda a kan cinyarta ba Nura Allah ya ɗauki rayuwarsa. Ciwo cikin kwana da wuni ya yi Allah ya ɗauki ransa. Kwata-kwata ba shi aka sakawa mutuwa ba saboda shi lafiyarsa ƙalau, ba Lukman da ke fama da ciwon hanta ne ma aka sakawa mutuwar sabida matsanaicin jinya da ya ke yi sai gashi ba Nuran da lafiyarsa ƙalau shine ya mutu sanadin ciwon cikin kwana ɗaya da wuni.
Hajiya ce ta riƙa tausarsu da kalamai da nasiha sannan suka ɗan tsagaita da kukan suka koma yi masa addu'a wanda dama shi ya fi buƙata.
Kyakkyawar masauki aka kai su ya Abdallah, ya Abdul-Hakeem da doctor. Su Sauban kuma a ɗakin 'yan uwansu gwaurayen gidan suka sauka. Sai da su kai isha'i sannan suka fita waje inda 'yan zaman makoki ke zaune suka ƙara yin gaisuwar sannan suka dawo cikin gida zuwa ɗakin marigayyiya Nenne su ka yiwa matan gaisuwa sannan suka koma waje.
Mummy Sarah ta kasa saka komai a bakinta sabida jimamin mutuwar baban nata, sannan hawaye sun kasa tsayuwa a idanunta sai kallon makeken hoton ba Nuhu (mahaiifinta) da ba Nura da ya rasu a yau. Kamar ta kira su amsa haka take ji.
Aunty Suhana yarinyar ba Lukman wacce ƙawa take a wajan mummy Sarah, ita ta tarkata kan su Dinaayah zuwa gidanta domin su fi sakewa. A nan suka haɗu da 'yar aunty Suhanan wanda sa'o'i suke da su Benazir sai dai sun ɗan girme mata. Hira suke ta yi saboda sun sake da Madina sosai. Sau biyu kawai ta Madinar ta taɓa ganinsu a zahiri, lokacin da aunty Hassan (yayar mummy Sarah) ta haihu da kuma mutuwar ƙanin Pastor Emmanuella Debora Daniel (Kakar mummy Sarah ta wajen uwa).
Washa gari gaba ɗaya suka shirya domin dawowa gida ban da mummy Sarah, Benazir, Aleesha da Dinaayah, su sai anyi bakwai daddy zai dawo ya ɗauke su. Su Ayraah sai kuka suke suma za su zauna. Dakyar aunty Laure ta lallashe su sabida school da suke zuwa kuma makarantar bata son fashi kwata-kwata.
Dr Khalil sai da ya ƙara kwantar mata da hankali tare da bata ATM card ɗinsa akan duk abunda ake buƙata kawai ta yi amfani da shi a saya sannan ya mata sallama bayan ya bada sadakan kuɗi masu yawa sannan ya wuce. Hajiya da su ya Abdallah su ma duk sai da suka ajiye kuɗi masu tsoka sannan suka wuce aka bar mummy Sarah da 'ya'ya kawai.
Aunty Habbooba kuwa Allah-Allah ta ke su bar garin don a ƙage take don garin bai mata ba sam!
Ba su tafi ba sai da suka biya gidan Pastor Emanuella Debora domin gaisawa duk da sun haɗu ma a daren don har sha ɗaya suna tare har da mahaifiyar sarah wato Lami. Baba Samueal ma ya zo sai dai shi waje kawai ya tsaya kuma bai jima ba ya tafi don har yau babu jituwa tsakaninsa da surukan nasa, haka ma tsakaninsa da tsohuwar matarsa Pastor Emmanuella Debora (Littafi Ƙanwar matata for more information about the saga. DM 08128755583).
Washa garin ranar da akai ukun ba Nura su Dinaayah suka fara bin gidajen yayyin mummy Sarah domin ziyara. Gidan aunty Hassana suka fara zuwa. Tamkar za ta lashe su tsabar son da ta ke nuna masu su duka har Benazir bata cire ba sai nan-nan da su ta ke. Idan ta kalli Dinaayah sai ta hau sharar hawayen da ita kaɗai ta san dalili. Daga nan su ka tafi gidan Na'ima, ita ma dai kamaar Hassana haka ta yi masu, gidan Marfu'a da Nuratu duk sai da suka je. Duk inda suka je kowacce na wane wannan waje basu kulawa sannan babu wacce bata jawo Dinaayah a jiki ta rungume tare da fashewa da matsanaicin kuka. Su Benazir duk tunanunsu kukan rashin idanun gani da Dinaayah bata da shi suke yi.
Daga nan gida aunty Nuratu suka wuto gidan Pastor Emanuella tare da rakiyar Madina. Su Aleesha ne ke ta kallon gidan ganinsa manne da hotunan Jesus ta ko ina har da ƙaton bana na hoto church ɗin pastor Emannuella ɗin. Dinaayah da ba ta ganin komai kai tsaye kawai ta ke tafiya bisa jagorancin Madina sabida bata san kan inda za su ɗin ba ƙafa kawai ta ke jefawa.
Tun daga harabar gidan akai masu kyakkyawar tarba kasancewar an san da zuwansu. Ɗaya bayan ɗaya Lami ke bin su ta rungume lokacin da ta kai kan Dinaayah wani irin rusa kuka ta yi tare da rungumeta ƙaƙam.
Tsawa Pastor Emmanuella ta buga mata tare faɗin, "Kar ki fara ki yi kuka a kan jikarki, yarinyar nan akwai albarka a jininta, haihuwarta kawai Aina'u ta yi amma nonon Sarah ta sha don haka albarka na yawo a jikinta. Sharrin mahaifiyarta a iya taɓa lafiyarta kawai ya tsaya shiyasa ta fito daga cikin Aina'u a matsayin makauniya. Yanzu zan shiga ciki da ita na yi mata addu'a tare da casting duk wani evil spirit da zai yi ƙoƙari zuwa kusa da ita balle ta yi irin halin Aina'u wacce yanzu haka na san tana wuta!"
Da ƙarfi ta kuma faɗin, "I renounce and ask forgiveness for any negative inner vows made by me or by any of the people for whom I am praying. I ask that Jesus Christ release us from these negative inner vows and from any bondage they have caused us. I take the Sword of the Spirit and cut free myself and those for whom I am praying from all generational sins, weaknesses, character defects, and cellular and genetic disorders, in the name of Jesus Christ."
Pastor Emmanuella ba gama faɗin haka ta kama hannu Dinaayah zuwa ciki yayin da Lamu da su Benazir suka bi bayanta hankalinsu a tashe don sam basu fahimci ko kalma ɗaya daga cikin abunda kakar mummy Saran ta ke faɗi akan Dinaayar ba.
Dafe ƙirji Benazir ta yi tare da zazzaro idanu ganin Pastor Emmanuella ta gurfanar da Dinaayah da ke kuka a ƙasa sannan ta hau magana da mugun ƙarfi tana faɗin, "I bind satan, the spirits, powers and forces of darkness ... l bind any demonic assignments sent against any of the people and areas I am lifting up to the Lord. I bind all interaction, interplay or communication of spirits as it may affect any of the people and areas for which I am praying. I command in the name of Jesus Christ that all these satanic and demonic forces go to the feet of Jesus. I call forth and loose the Holy Spirit of God and the holy angels to come and cleanse every place where satan has had a foothold in the lives and situations of any of these people and areas, and to fill each cleansed area with the life and love of Our Lord Jesus Christ, in the name of Jesus Christ. In the name of Jesus Christ, I rebuke and break any curses, hexes, spells, demonic activity, or any other evil thing that has been sent against me or passed down through the generations to me or to any of the people or areas for whom I am praying."
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku yau ni Benazir mai nake gani haka? Dama Maman mummy Sarah da kakarta arna ne? Kuma wacece Aina'u da suke cewa ita ce maman Dinaayah? Wannan ma ai ƙarya ne da hauka irin ta aljihun baya!"
##Matar Sayyadee
#Dinaayah
#THE SECRET
#BENAZIR
#Mummy Sarah
#KAISAAR
#Between two lovers
##DINAAYAH SAFRAAZ
_Free pages fa basu da yawa, guda biyar ne kawai don haka ku hwara payment, sannan don girman Allah idan kin san za ki saya ne domin ki fitar kar ki zo na yafe naki cinikin_
`DINAAYAH SAFRAAZ ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVDENCE OF PAYMENT 08128755583`
```Ina ƙara baki shawara sister, kar ki bari ayi wannan tafiyar babu ke```
[9/14, 5:56 PM] Matar Sayyadee: *_ƘANWAR MATATA RETURN_*
(```DiNaayah SafraAz```)
_*BEtweEn two LoveRs*_
~Story and written~
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim*
_Matar Sayyadee_
_Wattpad @MatarSayyadee01_
_Arewabook@Matarsayyadee0_
```One notable hadith narrated by Abu Huraira states that one who does not show compassion to children or respect for their elders is not regarded as a Muslim. Another hadith relays the Prophet Muhammad's (PBUH) words that those who do not show compassion to humans will not receive compassion from Allah.```
_Allah says in the Quran, “And We have not sent you (O Muhammad) (PBUH) except as a mercy to the worlds” (21:107). This verse emphasizes the Prophet's role in showing mercy and empathy to all of Allah's creations, including humans, animals, and the environment._
Chapter 004
`NOT EDITED`
"I did my best, it wasn't much
I couldn't feel, so I tried to touch
I've told the truth, I didn't come to fool you
And even though it all went wrong
I'll stand before the Lord of Song
With nothing on my tongue but Hallelujah
Hallelujah, Hallelujah
Hallelujah, Hallelujah
Hallelujah, Hallelujah
Abunda Pastor Emmanuella ta riƙa faɗi kenan da ƙarfi tana bugun kan Dinaayah da ke duƙe jikinta na rawa don gaba kwarmaton da Pastor ke yi ya saka tane neman fita hayyacinta. Idanunta ne suka soma lumshe a hankali kamun ta yi wani irin zabura ta fasa ƙarar da ya gigita gaba ɗaya gida aka taru a kanta har da sauran 'yan uwan pastor da basu san da zuwan su Dinaayah ɗin ba. Ihu take yi da mahaukacin ƙarfi don har jijiyoyin wuyanta sun mimmiƙe.
Pastor Emmanuella kuwa sai ta cigaba da karanto karatunsu na coci itama da bugun ƙarfi wai a cewarta Evil spirit ɗin da ke jikin Dinaayah ɗin ne suka motsa saboda addu'o'in da take yi.
Lami da ke gefe tana kuka tare da ambaton Allah a zuciyarta, ganin tsayuwar ba zai mata ba ga jikarta a cikin mummunan hali wanda a cikin gidan mahaifiyarta komai ya faru, kitchen ta nufa da gudu ta ɗebo ruwa a cup ta shiga tofa addu'ar da duk ya zo mata a baki cikin cup ɗin.
Benazir da Aleesha kuwa tun ihun farko da Dinaayah ta ƙwalla su ka yi kanta su ka rirriƙe ta suna kuka suna kiran sunanta don tunda su ke ba su taɓa ganin haka a tare da ita. Dinaayah da wannan lokacin ihu ta ke kwarara tamkar maƙoshinta zai yage kuma gashi muryanta gaba ɗaya ta canza tamkar na bunsurun akuya wani lokacin kuma kamar na rigalu wanda ke cikin balagar farko.
Wani wawan shaƙa ta kai wa Benazir tare da jifa da ita sai da ta haɗu da kujera bayanta kuma ya bugu sosai, tsabar azabar da ta ji a bayan bata san lokaci da ta furta, "Wayyooo Allah bayana ya ƙarye!"
Ko kamun Aleesha ta yi yunƙurin guduwa ita ma ta yi wurgi da ita sai da ganta ya bugu da gini wanda take ta sume a wajen.
Yunƙurin da Dinaayah ta yi tamkar wata yar dambe ya sa su uncle John, uncle Uche da uncle Joshua riƙe amma wani yunƙuri ɗaya kawai ta yi ta watsar da su