Author : Hauwa Shehu Aliyu Category : Romantic Hausa Novels
[3:31PM, 10/01/2017] +234 810 336 9936: MIJIN
YAYA TAA
love story 2016
Na Hauwa Shehu Aliyu
~~
ASALIN LABARIN*********
Alhaji abdul-razaq matawalle haifafe garin kaduna ne a unguwar tudun wada alhaji abdul-razaq matawalle shaharare dan kasuwa ne, wanda yayi fice a kasar Nigeria" ya mallake "companies da dama daga cikin su akwai company sarafa mangyada da kuma company sarafa shinkafa da sikari ya kuma, mallaki gidaje mai fetur da dama, yana da matar aure guda daya kacal me suna hajiya Raheela amma anfi sanita da suna hajja Rahee "Allah ya albarkace su da haihuwa 'ya'ya biyu maza Muhammad da Abdullah, Muhammad shine babba lokacin da ya kamalla karatun sa na jami'a, alhaji abdul-razaq ya danka masa alhakin kula da duk wani "company da ya mallaka.
Alhaji abdul-razaq matawalle dattijo ne mai halin dantako da kamala gashi da hankuri da tawakali sabani matar'shi hajja Rahee batada hankuri ko miskarazarati gata da dan banza fadan tsiya ga kuma uwa-uba rashin son gaskiya cin mutunci a wurinta ya zame mata, kamar ibada bata tsoron ko ta kwana balle ta tashi 'yar kunar baqin wanke ce ta karshe.
A lokacin da Muhammad yafito da matar da zai aura Saida alhaji abdul-razaq yakai ruwa rana da ita kafin ta amince da auren a cewar'ta ba za ta hada irin da dangin buzaye ba saboda fatima buzuwa ce.
Malam siddiqu dan agadaz shine ainihin suna mahaifin fatima bashida wata sana'a da ta wuce sayar'da shayi a bakin tasha, asalin su buzaye agadaz ne ci rani ya, kawo su Nigeria suka yada zango a kaduna garin gwanna, fateema su biyu iyayye su suka haifa ita da kanwar'ta sadeeya.
Ganin hajja Rahee ta amince da auren yasa ba'a dauki dogon lokacin ba akayi bikin su gudun kada ta chanza ra'ayi saboda ba karamar tsana take yiwa auren ba shekara daya da auren Muhammad da fatima "Allah ya albarkace su da haihuwa 'ya mace ranar suna aka rada mata suna Hafsat a lokacin kuma Abdullah ya kamalla karatu "degree dinsa afanni kasuwanci bayan yadawo daga service" yafara aiki daya daga cikin company mahaifin'sa wata rana abdullah ya zo gaida mahaifan sa kamar yanda yakeyi a kowace safiya alhaji abdul-razaq yayi gyaran murya alamar zai yi magana mai matukar mahimmanci, yace abdullah ina so kabani aron hankali'nka ka saurare abunda zan fada sanin kanka ne banida wani amini duk fadin garin kaduna da yawuce alhaji sambo jiya ya zo mini da wata magana wanda ta haifar mini da dinbi, farin ciki yace yabaka 'yar'sa hajara ka aura domin karin danko zumuncin a firgice hajja Rahee take karewa alhaji abdul-razaq kallon daga bisani ta ya mutsa fuska ta wani girgiza kai tace ina ba zata sabuba bindiga a ruwa wannan ae ta tsuniya ce, alhaji abdul-razaq da Abdullah suka mayarda ganinsu a wurinta tacigaba da zazzaga masifa haba Alhaji wannan wane irin hadi ne"? Kai kanka kasan abdullah bai dace da 'yar gidan alhaji sambo ba, ko ka manta da bakin fenti da gidan shi yake dauke da shi to in ka manta bari na tuna maka Alhaji sambo mijin tace ne bai esa da gidan shi ba 'ya'ya shi daga mazan har mata babu mai, cikkakiyar tarbiya hajiya lami ta mallake shi bashida ra'ayi sai nata, ta shinfida mumuna mulki a gidanshi duk lokacin da yanemi aure sai ta wargaza shi ta hanyar bokaye da 'yan tsinbo daga ita har 'ya'ya ta da gidan mazaje su kazama rayuwa da sukeyi kenan shine yanzu Alhaji ka ke yunkuri hada iri da wannan gurbataciya zuri'a, to ni ban amince Abdullah ya aure 'yar gidan sambo ba saboda nasan cutar'da Shi Abdullah ko magana wuya takeyi mishi salihi yaro za ka hada da annoba bakar kadar ban amince ba yawuna ba har tadasa aya a zanceta alhaji abdulrazaq yana kallon'ta sam babu alamar bacin rai a tare da shi yayi murmushi, yace hajja Rahee kenan kedai bakya rabuwa da rigima shi, aure nufin Allah in yayi hajara ce matar Abdullah baki esa ki hana ba in kuma ki kace ki nuna ikonki a matsayin ki na Uwa ga Abdullah in da rabo cikin aure su sai ki mutu ayi bayan ranki shiyasa, sha'ani na aure ba'a so mumuna furucin ki furta alkhairi ko kiyi shiru kuma da kike zance hajiya lami tana bin bokaye da 'yan tsinbo wannan Duk zargi ne hade da zato tun da, baki taba ganinta da idanuki tana binne laya ba karki mayarda kan'ki tsohuwar banza mana ace duk lokacin da aka tashi zance aure 'ya'yanki sai kin nuna kin amincewar'ki ya juya wurin Abdullah yace Abdullah a matsayina na mahaifi agareka na umurce ka da ka aure hajara tashi katafi "Allah yayi maka albarka abdullah, yace ameen" ya mike tsaye yafice daga falon....
MIJIN YAYA
TAA
love story 2016
Na Hauwa Shehu Aliyu
~~
Duk wata hanya da hajja Rahee za tabi don gani Abdullah bai aure hajara ba tabi saidai hakar'ta bai cima ruwa ba, dole ta hankura ta saboda Matar mutum kabarin'sa aure tsakanin Abdullah da hajara ya tabbata, ana saura kwana biyu a daura aure alhaji abdul-razaq ya kira Muhammad da Abdullah, ya danka musu "key's" na sabon gidan da ya gina musu cikin kwatarda murya yafara yi musu nasiha Muhammad kai ne babba da kai zan fara duk nasan babu rashin jituwa a tsakanika da abdullah amma ina rokon'ka da ka zauna lafiya da dan uwanka, dalilin da yasa kenan na gina muku gida tare don ku zauna a muhalli daya inda daya yayi kuskure daya yadaura shi a hanya "Allah yayi muku albarka gida naku yana malali kuma kowane da part" din sa kai muhammed gobe in "Allah ya kai mana rai za ka tare kai da iyalinka wannan shine, dalilin zaman Muhammad da Abdullah a gida daya bayan sati daya da auren abdullah da hajara Alhaji abdulrazaq yayi "accident yana bisa hanya zuwa sokoto wurin daurin auren dan abokin'sa nan take daga shi har drivern sa Allah yayi musu rasuwa, mutuwar alhaji abdul-razaq matawalle ta girgiza dinbin al'umma Nigeria" hajja Rahee saida ta kwata ciwo da kyar aka samu tadawo haiyyacin ta gani yanda hajja tadawo abin tausayi tuni ta watsar'da masifa da bala'e yasa Muhammad da Abdullah suka yanke shawara gina mata nata "part" cikin gidan'su don tadawo kusa da su wannan shine dalilin zaman hajja Rahee gidan 'ya'yata hajara kuwa sai lokacin tafara fitowa da mugaye halaye'nta duk abunda idanuta suka gano "side din fateema sai abdullah ya siya mata zai sami kwanciyar hankali, hajara kishi da ke yi da fateema in zani taga fateema tadaura sai ita ma tanemo irin shi tadauki zazzafa kiyayya ta azawa fateema Hafsat na da shekara hudu a duniya fateema takara haihuwa wannan karon da namiji ta haifa kyakyawan da shi gashi kuma, fari tass kamar dan larabawa kowa sai yaba kyawo yaro yakeyi sabani hajara da takeji kamar ta shake wuyan jariri ya mutu, sakamako gani yadda Abdullah yake tsananin son yaron, tun ranar da fateema ta haihu hajara takasa gane kan Abdullah ranar suna aka radawa yaro suna abdulrazaq.
abdullah yayi masa laqabi da Amar....
[3:31PM, 10/01/2017] +234 810 336 9936: 🍆🍆🍆🍆🍆MIJIN
YAYA TAA🍆🍆🍆🍆
💕love story 2016💕
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
~7⃣~
Tsananin son da Abdullah yake nunawa Amar yakara saka hajara cikin, kuncin da baqin ciki, don haka tabi ayarin 'yan uwata na kaiwa bokaye da 'yan tsinbo kudin'ta don, taraba Abdullah da 'yan uwan'shi saidai kash aikin bokanta baiyi tasiri akan Abdullah ba gani haka yasa ta koma neman haihuwa idon rufe, taje asibiti likita ya tabbatar mata da cewa lafiyar'ta qalau lokacin ne, na haihuwa'rta baiyi ba amma hajara kasa hankura tayi tasoma amfani da maganin da bokanta yabata wai za ta haihu haka ta dinga daurawa cikin'ta najasa.
Saida Amar Ya shekara hudu a duniya fateema takara haihuwa da namiji aka rada masa suna nazeer.
Hajja rahee nagani hajara tayi shekara bakwai ko 'bata wata bata taba yi ba tayarda masifa da bala'e sai abdullah yakara aure ana cikin wannan rungutsumi, sadeeya kanawar fateema ta kamalla karatun ta na sakadire ta zo gidan fateema hutu tun da Abdullah ya kyala ido yaga sadeeya yace yaga Matar aure tun fateema nadaukar abin da wasa har tagano cewa Abdullah da gaske yakeyi, daki tasaka sadeeya ta ja mata kunne tafita da harka Abdullah saboda baza taba amincewa Abdullah aure ta don tasan kishi da hajara masifa ne ga sadeeya shiru-shiru ce sai ka yini da ita bakaji tayi magana ba, wasu har tsanmani sukeyi ko kurma ce, duk jan kunne da fateema tayiwa sadeeya bai shige ta ba domin kuwa soyayya sukeyi kamar su cinye junan'su, lokacin da Abdullah ya gabatarda sadeeya a wurin hajja Rahee ba karamin farin ciki tayi ba tace ae gara auren 'ya'ya buzaye da zama da juya da yakeyi, batare da sani fateema ba Muhammad yanemawa Abdullah aure fateema, Lokacin da fateema taji labarin har kuka saida tayi saboda tasan hajara sai ta zargi cewa ita ta hada auren abdullah da kanwar'ta sadeeya.
Hajara batasan Abdullah zai kara aure ba sai ranar'da za'a daura aure, wannan duk "plain din hajja Rahee ne a cewa ba za'a sanar'da hajara da wuri saboda kartaje wajen bokaye ta, ta wargaza auren rana da aka daura aure ranar amarya ta tare lokacin da hajara taji abdullah zai kara aure sai tayi 'yar karamar hauka nan take 'yan uwan'ta suka cika gida sai faman zugata sukeyi, wata yayar'ta mai suna asabe ta gyara zaman mullamulai duwawuta bisa kujera tace kaico ki hajara kin janyo muna abin fade a garin Kin barwa zuri'ar sambo da lami tarihi domin kece ta farko ta kuma karshe da aka fara yiwa kishiya, don tsabar iskanci da dakikanci irin naki, sai ki ka mike kafafu batare da kin datse kofar gidan'ki da katon "padlock ba to gashi nan irin wauta da saken da ki kayi ya janyo miki zama inuwa daya da bakar kadara kuma wani abin haushi wai ko sunan amaryar, baki sani ba.
Hajara tasauke katuwar ajiyar zuciya tace wallahi Anty asabe duk wata nake kaiwa lami kudi tana karbo mini taimako wurin malam mai allon karfe, kuma bana wasa da kayan mata" asabe taja tsoki cikin zafin rai tace tun 1986 aikin malam mai allon karfe yadaina ci, duk aljannu shi yanzu na karya ne, ke in zaki falka daga baccin ki falka ki zo aikai ki wurin boka bakamu mai gani har hanji shine, kadai yake da maganin matsalarki, cikin tsananin farin ciki hajara ta amince da hudubar shedan din da 'yan uwata sukayi mata.
tsabar zafin kishi irin na hajara yasa takasa fitowa lokacin da aka kawo, amarya balle taga fuskar kishiyar'ta sai a washe gari da Abdullah yakira su don yayi musu nasiha, su zauna lafiya hajara na shigowa taci karo da fuskar sadeeya zaune kusa da mijin'ta, cikin sarkewa murya tace Abdullah badai sadeeya kanwar fateema facalla ta ita ce amaryar'ka"?
Abdullah yayi murmushi, yace ita ce mana ae nasan za ku zauna lafiya saboda sadeeya ba ruwanta akwai hankali da natsuwa......
🍆🍆🍆MIJIN YAYA🍆🍆
TAA🍆🍆🍆🍆
💕love story 2016💕
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
~8⃣~
Hajara ta zaro idanu ta masu kama da idanu 'yan China" tafisgo dan kwali'n kanta tasha damara tace kan uban nan lallai kuwa Abdullah ka cika cikkake mayaudari Maciyi amana, yanzu duk 'yan mata da ke cikin garin kaduna karasa wanda zaka aura sai sadeeya"?
Babu abinda yau zai hanani naci ubanki siddiqu dan agadaz a gidanan tayi kukan kura ta afkawa sadeeya da duka da kyar Abdullah ya kwance sadeeya hannuta sadeeya sai faman kuka takeyi, saboda batasaba da halin karnuka ba abdullah ya riko hannuta yakaita "side din fateema duk da haka nan saida Hajara tabin su tasaukewa fateema kwadon tijara Hafsat ta sheka da gudu side din hajja Rahee tace kaaka ana fada da mamee da umma Anty sadeeya sai faman kuka takeyi nan take hajja rahee tagano abunda ke wakana, mikewa tayi ta nufi "side din fateema tafada cikin falon dai-dai lokacin da hajara take cewa, kudai yi abun kunya ya da kanwa suna aure gida daya don tsabage kwadayin a mallake abin duniya dama ci rani aka zo matukar ina raye bazan zauna da sadeeya a matsayin kishiya ba.
Ke dakata 'yar gadon mugun abu to aniyar ki ta sharri tabi ki hajja Rahee ce ta daka mata tsawa, hajja tacigaba da cewa da ba'a aure ke da ana auro ki, mafi alkhairi a tare da ke ki zauna lafiya da sadeeya ko kuma kiyi waje road" don ba ki zo da "block's a gara ki ba ballatana ki nuna mana baqin mulki da lami take yiwa sambo kiyi maza ki bace mini da gani 'yar gadon rashin tarbiya da sauri hajara tafice, daga falon saboda duk iskanci'ta tana masifar tsoron hajja.
Hajja ta juya wurin Abdullah tace kai kuma tun da kace za ka iya to kuwa dole ka jajirce ka zama tsayaye namiji in ba haka ba, hajara za ta mayar'da kai shanyaye kamar yadda uwar'ta ta mayar'da ubanta, tana karasa zanceta tafice daga falon fateema da Abdullah suka cigaba da rarrashin sadeeya tun daga ranar da sadeeya tashiga gidan,abdullah a matsayin matar'shi tayi ban kwana da farin ciki da kwanciyar hankali saboda hajara ta tsare gaba ta tsare baya duk don gani ta fitar'da sadeeya daga gidan Abdullah kowa ina taji labarin sabon boka sai ta kai mishi ziyara saidai babu biyan bukata kwatsan ana cikin wannan rungutsumi sadeeya tasami ciki saura kiris hajara ta hadiye zuciya ta mutu abunda take nema shekara da shekaru bata samu ba sai gashi da shigowar sadeeya tasamu tun daga, lokacin tasha al'washi sai ta zubar'da cikin duk wurin boka da taje sai yace mata tabbas sai sadeeya ta haifi cikin nan abinda yakara daga mata hankali kenan bayan wata tara sadeeya ta haihu tasami "twins" duka maza rana da ana mutuwa adawo da sai hajara ta mutu tadawo, don tsabar bakin ciki kasa zuwa tayi taga yaran ranar suna ta zagayo, aka radawa yaran suna abdulhakeem da abdulhaleem haka rayuwa tacigaba gaba da tafiya, wasu na cikin jin dadi wasu na cikin wahala sadeeya, tana daya daga cikin mutane da ke cikin wahala, saboda batada 'yanci tafito tsakiyar gida yanzu hajara na fitowa tafara zagin'ta ta, uwa ta uba ga sadeeya ba iya ramawa takeyi ba "twins" na da shekara uku sadeeya takara haihuwa wannan karo ma "twins ta haifa kuma duk maza aka rada musu suna sadeeq da saleem.
Ranar hajara daki tashiga ta rufe kofa tadinga rusar kukan baqin ciki tana cikin wannan halin kwatsan Anty asabe ta kawo mata, ziyara gani halin da hajara take ciki yasa ta tausaya mata ko zama batayi ba, tace tashi mu tafi daga wannan lokacin kinyi ban kwana da baqin ciki...
🖊excellent writers🖊
Jeeddah Aliyu🌹
[3:32PM, 10/01/2017] +234 810 336 9936: 🍆🍆🍆🍆🍆MIJIN
YAYA TAA🍆🍆🍆
💕love story 2016💕
Na Hauwa Shehu Aliyu🌹
~9⃣~
Hajara ta share hawaye fuskarta ta dauki mayafi da jikka suka fice daga, gidan drivern Anty asabe sai faman sharara gudu yakeyi kamar wanda zai bar duniya tuni sun fita daga cikin garin kaduna yana dauki hanyar Niger state" saida yayi kusan shiga garin minna sai kuma ya yanke wata hanya wanda babu kwata akanta sai jar kasa, haka ratsa daji daga karshe yasami wata 'yar karamar rugga fulani yayi, parking" saboda babu hanyar da mota za tabi zuwa gidan bokan suka fito daga cikin Mota suka soma tafiya da kafa, driven yana gaba suna biye da shi saida sukayi tafiya mai nisa gaske tun nesa suka hangi gidan boka duguzuu zana ce kewaye da gidan sai kayan tsafi da ke daure jikin zanar bukoki ne guda biyu a cikin gidan,Komai girman jikin mutum ba zai iya shiga cikin bukar ta tsaye dole, sai ka duqa saboda kankata kofar babban tashin hankali na farko da za ka fara fuskanta daga jefar kafar ka tsakiyar gidan boka duguzuu, shine wari ,wani masifafe wari na fitar hankali gidan yakeyi hajara ta toshe hanci ta da sauri anty asabe ta buge hannu'ta tace kinga hajara ki rufawa kan'ki asiri ki kuma rufa mini ni da nayi sanadiyar zuwan ki gidanan, karki kuskure ki qara toshe hancin'ki saboda abinda boka duguzuu yatsana kenan in kuma ki ka bari yaganki zai mayar'da ke abar kwatance hajara tafara tsorata da jin furucin Anty asabe.
Drivern anty asabe yace hajiya ni zan tsaya daga nan sai ku karasa cikin,bukar Anty asabe ta wuce gaba hajara ta mara mata baya suna karasawa bakin kofar suka ji wani irin masifafe wari yana musu barka da zuwa Anty asabe tace "ahuuwanku" gafara dai boka duguzuu dan hasarariya wata mushirika dariya suka fara ji tana fitowa daga cikin bukar gaba daya dajin yasoma amsa amon dariyar tasa, tsawon lokacin yadauka yana kwasan dariya daga bisani yace barka ku da zuwa 'ya'ya hasarari barka ku da zuwa abokan zuwa jahanama, barka ku da zuwa fadar boka duguzuu dan asarariya ku shi ku da kafar hagu a lokacin daya fargaba hade da firgicin suka ziyarce hajara jikin'ta yafara rawa Anty asabe nagani haka tariko hannuta suka, fada cikin bukar zaune yake gaban wata katuwar tukunyar tsafi baki wulik da shi fuskar'shi tamkar ta gwaggo biri idanu shi, jajir masu kama da garwashin wuta ga shi da kiba ciki sa kamar na mai cikin wata tara yana daure da walki na fatar damisa cikin sa, sai walkiya yakeyi kamar wanda yashafa mangyada ya zaro kafirai idanusa yadakawa hajara tsawa cikin muryar'sa mai kama da kukan jaki yace ke zauna da