Chapter 21 Reading MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt Arewa Novels

MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt

Author :  Hauwa Shehu Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   21 / 31

60K to 63K   out of 92.7K words

ni fateema wace irin masifa ce Amar yake kokari kuno kai da ita"?
Daddy yayi gyaran murya, had'e da kad'a kai yace ina shi Amar d'in yake"?
Kaka tace oho!
Daddy yak'ara harzuk'a yace wannan ae wulaqanci ne ya za'ayi ya zo da babbar magana irin wannan kuma yasaka k'afa takalmi yayi tafiyar sa haka daddy yadinga zanga fada kamar zai ari bakin kare, daga bisani yajuya wurin mami yace ke d'auko min waya ta har ni Amar zai kawowa iskanci wallahi yau zai had'u da bacin rai na so ke ya tarwatsa mana zumunci ni da d'an uwana, mami ta mik'a masa waya cikin konar zuciya yadanno number" Amar, ga mamaki sa sai yaji "ringing tone" d'in wayar Amar a cikin falon" daddy yana dagowa ya hango Amar tsaye a bakin kofa, harara daddy ya galla masa yace to isashe ae sai ka shigo da kayiwa mutane tsaye a bakin kofa Amar yak'araso yanemi kujera ya zauna, daddy sake danna number" Abba ta bangare Abba kuwa yana zaune a falon umma hajara na gefen shi, aunty Amarya kuma tashigo falon hannuta d'auke da katon "tray" dai-dai lokacin wayar Abba tayi "ringing" gani suna d'an uwanshi yasa yadaga da sauri daddy naji Abba yadaga kiran yace Abdullah ka tattaro iyalinka duka ka zo da su "part" d'ina akwai magana daddy na k'arasa fadar haka ya kashe waya, cikin hamzari Abba ya mik'e had'e da cewa ku d'auko mayafai ku mu tafi "part" d'in yaya karaf umma hajara tace yau kuma "assembly" safe aka tsiro mana"?
To Allah yasa mu ji alheri, Abba ya girgiza kai yasa kai yafita'
Suna shiga falon kowane su yayi turus musanman umma hajara da ta hango na'eema a tak'ure tana rusar kuka daddy yace bissmillah Ku zauna mana.....

Jeeddah Aliyu
[7/25, 21:02] ‪+234 703 256 6172‬: [25/07 7:41 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣3⃣

Daddy ya kwashe bayani da kaka tayi masa ya fada musu, tun kafin daddy ya dasa aya umma hajara ta zabura cikin hargowa tace, wannan ae wulak'anci ne duk tsawon zaman da yayi da na'eema bai bullo da wannan makirci ba sai zuwa bak'ar annoba nan gidansa in har ka gaji da 'yata ka sake ta mana ke hajara banaso shirme Abba ne ya takawa umma hajara birki in ki ka kuskura na k'ara jin kin furta uffan a zance nan wallahi sai nayi mumuna saba miki'
Dole umma hajara ta kame bakinta sai wani muzurai takeyi, daddy ya juya wurin Amar yace Amar me ka ke nufi da ba'a haiyaci ka ka aure na'eema"?
Iya sanina da amincewa ka mu ka aure ma na'eema duk ciki Ku ba Wanda aka yiwa dole ka, gaugauta sanarda mu manufarka domin nasan irin kala hukunci da zan yanke akanka'
Amar yad'ago jajaye idanu sa yace wallahi daddy bantaba son na'eema ba, ban kuma taba kallon ta a matsayin wance zanyi rayuwa aure da ita saboda zuciyata raheela take so kaka sheda ce akan irin son da nake ma raheela wani abin mamaki sai gashi na waye gari da aure na'eema daddy bana sonta, wallahi bana sonta ku taimake ni ku ceto rayuwa ta daga halaka ku rabani da na'eema domin ba ita bace zabi na cigaba da zama da ita zai iya haddasa mini shiga k'unci da matsala fiye da wanda nake ciki a yanzu.
Har Amar ya dasa aya ba wanda yayi yunk'uri katsi shi, daddy yak'ara juyawa wurin na'eema yace daina kuka na'eema ki fada mana iya gaskiya abinda ki ka sani cikin wannan sark'ak'iya"?
Cikin muryar kuka na'eema ta fayyace irin ta'asa da suka aikata ita da umma hajara, gaba d'aya falon suka d'auki kalma shahada bayan falon yayi tsit kaka gyara zama tace ni kai na naciro laya cikin pillow raheela shiyasa lokacin da Amar ya zo da zance aure na'eema nace ban amince ba domin nasan Amar raheela yake so"
Abba ya mik'e cikin tsanani bacin rai ya shararawa umma hajara tagwaye mari, yace tir da halinki hajara nayi danasani kasance wa miji agare ki, zama da mace mai irin halaye ki masifa ne kin cuce ni kin gurbatawa 'yata rayuwa, kuma wallahi indan wani abu yasami raheela sai nayi shari'a da ke ba zan iya cigaba da zama da ke don haka ki je na sake ki, Saki d'aya, sakamako jin furucin abba na karshe ya haddasawa umma hajara kurma ihu ta zube gaban tana kururuwa had'e da bashi hankuri ka dubi girma Allah" abdullah kayi hankuri kayafe mini wallahi sharri shedan ne, a wannan shekaru ka sakeni ina ka keso na dosa ka rufa mini asiri kadawo da ni d'akina'
Abba galla mata harara yace wane d'aki ae ke yanzu bakida d'aki a gidanan.
Umma hajara tasake rushewa da kuka tarerafa gaban kaka tace na tuba hajja ki sa baki yadawo da ni d'akina, kaka tasauke gwaro numfashi tace tashi ki zauna, ae kuwa da sauri umma hajara ta kai zaune'
Kaka tayi gyaran murya tace kayi hankuri Abdullah tabbas hajara ta aikata mumuna aiki amma tunda tagano kuskure ta sai kayi mata afuwa kadawo da ita ko don albarkaci 'ya da ke tsakani ku da kuma matsayin ubanta a gare ka, kai kuma Amar ba abinda za muyi maka illah mu baka hankuri ka daure ka rarrashi zuciyar ka, ka cigaba da zama da na'eema, saboda raheela ta haramta agareka Allah, ya k'addari na'eema ce matarka.
Amar yayi shiru hawaye na zuba daga idanu sa, daddy yace abinda hajja tafad'a gaskiya ne Amar ka rungume k'addara zama da na'eema, a matsayi na na mahaifika na umarce ka da ka zauna lafiya da matarka ka bata hak'oki ta da suka rataya a wuyanka kuma daga yau na soke zance raheela, ka manta da kataba son wata raheela, kafara shirya sabuwa rayuwa da na'eema da sannu za ka ji kafara sonta.
Abba yace karka tilassa masa zama da ita domin baya sonta, ka barshi yaji da zafi d'aya na rashin raheela "daddy yad'agawa Abba hannu yace karka dawo da hannu agogo baya Abdullah na riga na yanke hukunci kuma bana tunani zan chanza ra'ayi na akan hakan, gaba d'aya falon aka cigaba da rarrashin Amar, shi dai binsu da ido yakeyi saboda ya fahimci basusan zafin son ba daddy yacigaba da cewa na baka awa d'aya ka tattara matarka Ku koma abuja kai, kuma Abdullah kadawo da hajara shikenan na rufe wannan maganar banaso ak'ara tadata.
Abba yace ba'aso raina hajara zan dawo da ke sai don albarkaci magabata na don haka nadawo da ke ina rok'o ki, da ki cigaba da halinki karki fasa Abba yana k'arasa fadar haka ya mik'e yafice daga falon kaka tariko hannu raheela suka marawa Abba baya daga nan kowa Yakama gabansa falon yarage daga daddy sai Amar, daddy yadafe kafad'ar Amar yace kayi hankuri Amar nasan za kayi tunani nayi maka rashin adalci ta hanyar tilassa ka zama da na'eema, ni kuma zumunci mu ne banaso yasami matsala, ka zauna da matarka lafiya Allah yayi maka albarka tashi katafi cikin mutuwar jiki Amar ya mik'e zuciyarsa tamkar garwashi yafice daga falon yanufi "part" d'in kaka......
[25/07 8:50 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣4⃣

Yana shiga falon kaka ya zube a gaban kaka yafashe da kuka kamar k'arami yaro, cikin shasheka kuka yace banaso na'eema kaka bazan iya zama da ita duk lokacin da na kalle ta sai naji na tsane ta kaka ta girgiza kai tausayi Amar yakamata, tace bakada mafita Amar da yawuce cigaba da zama da ita kayi biyayya da umurni mahaifika da sannu za ka ga amfani hakan kaka tacigaba da yi masa nasiha had'e da kalamai masu dadi.
Duk abunda ke wakana tsakani kaka da Amar raheela na cikin "bedroom" tana jin su tace Allah sarki hero ashe da gaske ne kana sona, saidai kash ka taki rashin Sa'a domin ni bana sonka.
Ta bangare umma hajara kuma tana shiga bedroom d'inta na'eema na shigowa, ta rungume umma hajara tace kiyafe mini umma nasan za ki ji ciwo na fallasa asiri ki a baina jama'a banida yadda zanyi ne, umma dole na fad'a domin mu zallunci Amar da raheela, ni kan nayi nadama umma ke ma ina rok'o ki da ki zubarda duk wata kiyayya da ki ke yiwa raheela, cikin zafin zuciya umma hajara ta ture na'eema ta nuna ta da yatsa tace kiyayya yanzu nafara nunawa raheela ita tunda har tayi sanadi da igiya aure na d'aya ta tsinke ni kuma nasha alwashi sai naga bayanta, yadda nakeji kiyayya raheela a raina Sam banaji ta uwata Sadeeya don haka yaki yanzu aka fara tabbas sai naga bayan raheela maza ki tashi ki fita min daga d'aki banaso ganinki duk yadda na'eema taso ta bawa umma hajara hankuri tayi amma daga karshe kora kare tayi mata ta rufe kofarta, na'eema na kuka tanufi "part" d'in kaka tsawon lokacin kaka tad'auka tana musu nasiha na'eema ta mik'e tanufi bedroom wurin raheela tak'ara bata hankuri raheela ta share hawaye ta, tace komai yawuce yaya na'eema ki shiga "bathroom" kiyi wanka bayan na'eema tafito daga wanka, raheela tabata kaya tasaka, muryar daddy suka ji yana cewa ke na'eema kifito ku tafi, na'eema tace lil sis d'auko kayanki mu tafi, raheela tayi murmushi tace bangaji da gani kaka ba sai gobe zan dawo, duk yadda na'eema taso raheela ta bisu amma raheela tak'i na'eema tajuya tafice idanu cike da kwalla Amar yana ganinta yafice daga falon, har wajen mota kaka da daddy suka raka su, raheela ta labe a jikin kofa tana kallon su karaf suka had'a ido da Amar gabanta yayi masifar fad'uwa wani irin sanyi yasoma ratsa k'assa ta da sauri ta d'auke idanu ta, tana kallo har yaja mota yafice daga gidan da kyar raheela ta ja k'afafu ta tashiga bedroom" tayi kwance nan take zazzabi mai zafi yarufe ta.
Tun lokacin da suka d'auki hanya Amar ya kunna "tape" kaset d'in kira'a sheikh husary cikin suratul al-araf yana bi kira'ar a hankali nan take yaji wata natsu tashige shi, saidai yadda yake tsulla gudu abun babu kyau kamar daga sama ya hango garke shanu taf da titi yayi k'okari ya kauce musu inda yadosa baisan akwai wata mota tafe cikin gudun bala'e fiye da gudun da yakeyi nan take motocin sukayi k'azamar haduwa, hatta da engine motar Amar saida ya watsi daga mutane suka kawo musu agaji da kyar aka Ciro Amar da na'eema kowane su kamanu da halitta sa tasauya babu alamu numfashi a tare da su hukumar kare hadari da ababe hawa wato "road safety" su suka d'auki gawarwa ki su Amar zuwa asibiti da yake basu fita daga garin Kaduna ba hadari yafaru.
Daddy da Abba suna zaune a falon kaka aka kira wayar daddy yana dagawa yasake salati had'e da jefarda waya.....

Jeeddah Aliyu
[3:50PM, 10/01/2017] ‪+234 810 336 9936‬: [27/07 5:23 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣5⃣

Abba yarik'o hannu daddy yace me ke faruwa ne yaya"?
Cikin sak'ewar halshe daddy yace Amar da Na'eema sunyi "accident {hatsari} a lokacin d'aya Abba da kaka suka d'auki kalma shahada, Raheela da ke kwance a d'aki tana jin abinda daddy yafad'a taji, mumuna fad'uwar gaba da sauri tadafe k'irjinta, tace "innalillahi wa'inna illahi raji'um" da kyar ta mik'e tanufi falon tana shiga daddy da Abba na ficewa da sauri tafad'a jikin kaka tafashe da kuka, kaka tace ba kuka za kiyi ba maza d'auko hijab d'inki mu tafi asibiti d'in Raheela ta koma d'aki sai gata tafito sanya da hijab suka fice ita da kaka kaitsaye "part" d'in Mami suka shiga mami na zaune a falon da alamu su daddy basu sanarda ita abunda ke faruwa ba, gani Raheela tashigo da kuka yasa mami tace lafiya me ki ke yiwa kuka"?
Kaka ce tayi k'arfin hali sanarda mami nan take jikin mami yafara rawa, ta mik'e tashiga d'aki tasako hijab tace hajja mu tafi kaka tasauke numfashi had'e da cewa Sadeeya da hajara basuda lafiya abinda yake faruwa ba ki shiga ke da Raheela ki sanarda su ni ina wurin mota kuma dan Allah karku bata lokaci, hankali na a tashi yake'
Mami na gaba Raheela na biye da ita a babban falon suka tararda aunty amarya, mami tayi mata bayani a gaugauce daga bisani tashiga d'aki umma hajara tana kwance bisa gado sai sak'e-sak'e yadda za ta ga bayan Raheela takeyi, mami tayi sallama a wulak'ance umma hajara ta amsa tayi wani kwabe fuska kamar kashi shanu, tace me kuma aka zo nema a wurina"? Tsofafi munafukai duk munafuci Ku akanku zai k'are ni naci dubu sai ceto duk uban da yaci tuwo da ni mi.....dallah dakata hajara ni ba wannan ne yakawo ni d'akinki nq zo ne na sanarda ke 'yar da ki ke haukata akanta to sunyi "accident"{hatsari} kuma ba wanda yasan halin da suke ciki suna raye ko suna mace Allah ne masani don haka in kinga dama ki d'auko mayafi ki mu tafi asibiti, umma hajara ta d'ora hannu aka ta rusa ihu had'e da k'unduma asshar mami ta zaro ido tace wa'iyazubillah" hajara kina da hankali kuwa"?
Na rantsi da Allah indan wani abu yasami 'yata wallahi sai na d'auki mumuna famsa akan Amar da Raheela
Hmm...cabdijam lalle hajara bakida imani jahilci ki babba ne ni kan kinga tafiya ta, umma hajara tacigaba da gunji kuka da sambatu marasa kan gado, a "parking space" mami ta tararda kaka, aunty amarya da kuma Raheela da ke ta sharb'a kuka cikin sanyi jiki mami tace mu tafi batare da kowa ya tambaye ta umma hajara ba suka Shiga mota "driver" yaja mota mami ta kira daddy yafad'a musu sunan "hospital"{asibiti} d'in da suke saidai har yanzu babu wani kwa-kwara bayani akan su, mami ta kashe waya had'e da share hawaye da suka zubo mata, umma hajara na fitowa tafara kwad'awa d'a audu kira da gudu yak'araso wurin ta tace mu tafi ka kaini asibiti ka bi bayan munafukai chan, a lokacin d'aya sukayi "parking" a "reception" suka tararda su daddy zaune sai kuma nazee da ya zo daga baya, cikin ihu da kururuwa umma hajara tashigo "reception" d'in tamkar mahaukaciya wayyo na shiga uku na lalace shikenan sun kashe mini ita, me nayi muku mutane da Ku ka zab'i hanyar rabani da 'yata ita kenan gareni'
Ke"hajara wannan wane irin sakarci da rashin yarda da k'addara ne"?
Abba ne yadaka mata tsawa, kin isa ki hana ubangiji yi iko sa ne"?
Nan take umma hajara ta natsu amma duk da haka bata fasa gunji kuka ba tanayi tana fayyace majina da gefen hijabi ta.
Tsawon awa d'aya sukayi a zaune daga bisani suka sami gani likita da ya jagoranci duba Amar da na'eema daddy da Abba na zaune a "office" d'in doctor Abbas A Abbas ya cire farin gilashi sa yak'are wa su Abba kallo yasauke gwaron numfashi, daga bisani yace Alhaji saidai kuyi hank'uri da sauri daddy da Abba suka fara furta kalma "innalillahi wa'inna illahi raji'um" Daddy yace sun mutu koh likita"?
Abba yace mu musulmai ne mu yarda da k'addara dama duk mai rai mamaci ne Allah ya jik'ansu ya gafarta musu'
Dr Abbas yayi murmushi yace Alhaji ba Ku jira na k'arasa zance na kun yanke hukunci, daddy yace Dr ba wani zance da za ka k'arasa a gaban mu aka fita da gawar aboki hatsari su.
Dr Abbas ya Shafa sak'o sa yace Alhaji 'ya'ya Ku suna raye basu mutu ba, saidai suna ciki "critical conditions" mu samu mace tafarfad'o amma Dr Amar zuciyarsa kadai ke aiki kuma yasamu "injury's" da yawa daga ciki harda kariya a k'afarsa ta hagu da hannu sa na dama ita kuma mace tasami kariya a cinya da kuma hannuta, ga kuma "internal injury's" saboda kanta ya bugu duk da haka ita tafarfad'o mu yi mata allura bacci ne za ta farfad'o "around" 6:00pm insha Allah in tafarfad'o za Ku iya ganinta amma Dr Amar sai yadda hali yayi...
[27/07 7:31 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

7⃣6⃣

Daddy da Abba suka share gumi ciki yanayi na mutuwar jiki suka fito "office" d'in Dr Abbas da sauri mami da kaka suka had'a baki wurin tambaya Alhaji ya jikin su"?
Daddy yasauke ajiyar zuciya yace na'eema tafarfad'o sunyi mata allura bacci sai k'arfe 6:00pm zata farfad'o amma Amar ba wani kwakwara bayani akan shi, umma hajara tasaki ajiyar zuciya mai k'arfi gaske duk Wanda ke wurin saida yajuyo ya kalle ta tace Alhamdulilah"! Kaka, mami da kuma aunty amarya suka fashe da kuka, Raheela ta zube kasa da sauri Nazee ya taro ta, Raheela tafashe da kuka gwanin ban tausayi daddy da Abba suka nufi massllaci da ke cikin asibiti domin sallah azhar, Nazee ya kalle kaka yace kaka jikin raheela yayi zafi sosai da alamu zazzabi mai zafi ne yakeso yarufe ta, kafin kaka tabashi amsa umma hajara, tayi karaf tace yoo" ae dole tayi zazzabi tun da abokin shashaci ta rai a hannu Allah"
A harzuk'e kaka ta mik'e ta wankawa umma hajara mari hawaye na zuba daga idanu kaka, tace tir da halinki hajara ke kan kin zama annoba haihuwa ki batayi yiwa iyayye ki rana sun haifo masifa da bala'e rashin imani ki a baiyane yake ae ko ba komai Amar mijin 'yarki ne ki tuna da irin zalunci da Ku kayi masa, duk da haka Amar yayi biyayya da umurni mahaifi sa ya amince zai zauna da 'yarki shine yanzu ki ke binsa da mugaye kalamai to ta Allah ba taki ba insha Allah Amar zai mik'e da k'afafu sa, in yaso sai ki had'iye zuciya ki mutu don bak'i ciki umma hajara ta sunkuyarda kanta kasa tana huci aunty amarya, ta mik'e ta rik'o hannu

21 / 31