Chapter 9 Reading MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt Arewa Novels

MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt

Author :  Hauwa Shehu Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 31

24K to 27K   out of 92.7K words

gudu raheela takoma daki ta kuma tadawo da gudu tace nadauki 500 amma zan dawo miki da chanji Kafin kaka tabata amsa har takarasa fita daga falon bata ankara ba taji tayi karo da mutum, tana dago idanu'ta taci karo da nazeer tasaki ihu hade da cewa "oh shirt" nazeer yace "oh No" suka hada baki suka ce "oh yes" nazeer ya mika mata hannu suka tafa raheela tace yaya nazee yaukar yaushe yace da yamma amma na Lula ciki'n gari ban diro gidanan ba sai da tsakiyar dare raheela ta zaro ido hade da cewa guduwa kayi kenan"?
Nazee yayi wani yarfe hannu yace kin ji ki da wani wai guduwa abu sai, kace dan "boarding school" raheela ta kyalkyale da dariya tace amma dai batare da izzini abba ko daddy kadawo ba"?
Nazee ya tabe baki yace da izzini su nazo me zai sa nayi shigo gidanmu da tsakiyar dare ke bari na takaita miki labari ko su yaya Abdul basu san nayo kd ba.
Raheela takara zaro idanu tace cab lalle yau da kai da daddy nazee ya yatsine fuska, hade da cewa share kawai tawan nima irin na yaa Amar zanyi bazan iya cigaba da aiki a karkashin "company" raheela tace uhh..kaji da shi ni dai mutafi ka kaini "school" bisa "bike" dinka
nazee ya galla mata harara yace tun da ga "driver" ki yadawo ba to ba inda zan je a shagwabe raheela tace "please nawan wallahi yau test" nakeda kuma gashi nayi latti nazee yace mu tafi na sauke ki sarkin naci....

🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣6⃣~

Amar na esa gidan Aunty suwaiba yayi "parking" a waje "gate" ya kira na'eema yace yana kofar gida ciki'n zumudi, na'eema tadauki mayafi'nta takara feshe jikinta da hadin turare boka, sai wani bahago kallo Ramlat take aika mata duk da na'eema taga yanayi Kallon da Ramlat take watsa mata sai tayi kamar bata ganta ba tanufi kofar fita tana wani, rausaya direct" waje motar'sa tanufa tun lokacin tafito amar yake faman kallon'ta yana kuma mamaki yanda ciki'n Dan kankani lokaci sonta yayi tasiri a Cikin zuciyar'sa tana karasowa ta bude kofar mota tashiga kamshi turare ta yabugi kofufi'n hanci sa, ya lumshe idanu daga bisani yabude Su ya watsa su bisa, fuskar'ta yayida na'eema ta rikice domin idanu amar suna daya daga ciki'n halitta shi, da ke tafiya da imani 'yan mata tace ina kwana yaa amar"?
Hamm..,yasauke ajiyar zuciya hade da cewa kwana kuma na'eema ko dai bacci ki ke ji"?
Ta wani rausayar'da kai cikin sigar kissa da kisisina tace a'a amar yadago mata hannu shi yace ki kalle agogo ki ga karfe nawa, yanzu ta tsurawa agogo nashi kirar "Rolex" idanu a baiyane tace 1:11p.m amar yayi shiru yana nazari abunda zai furta sai dai bashida zabi da yawuce ya furta domin jin yakeyi in har bai furta hakan ba ruhi sa zai iya fita daga gangar jikinsa don haka ya yiwa kan'sa kiyamullaili ta hanyar cewa na'eema gani nazo gare ki yau ba'a matsayin dan uwa ba nazo gare ki ne a matsayin masoyi na'eema ina son'ki kuma in har kin amince ina son mu raya suna ma'aki {s.w.a}.
na'eema tasaki wani mushiriki murmushi na jin dadi tace na amince da kai yaa Amar dama Chan na jima jirgin son'ka yana yawo da ni kai ne ka so ka watsa mini kasa a ido, akan raheela, rass...gaban amar yafadi sakamako sunan raheela da na'eema ta kira sai kawai yatsince kan'shi cikin wani yanayi mai wuyar fassara, da kyar ya iya bude bakin'sa yace ki ajiye zance raheela a gefe "cos yanzu ke ce a gadon mulki zuciya'ta dadi yakara kashe na'eema haka su ka cigaba da fallasa asiri zuciya'rsu tsawo sati daya tayi a abuja babu abunda takeyi sai soyewa da amar.

******************

KARSHEN TIKA TIKA TIK***

Kamar yanda amar yasaba zuwa kaduna duk karshen mako hakan ce tafaru kasancewa yau juma'a karfe 12:03pm yatashi daga "office" direct gidan'shi da ke maitama ya wuce ya watsa ruwa ya chanza kayan zuwa wata tsadadiyar farar shadda galila yasaka bakar hula kubbe takalmin kafar'sa ma black" ne sai yafito tamkar sabon ango ga jikinsa na fitarda kamshi turare "natural vitality" kaitsaye yanufi "wuse 2" bai wani jima da tsayuwa ba na'eema tafito janye da 'yar karamar "trolley" din'ta da sauri amar ya balle murfi Mota yadunfare ta fuskar'sa dauke da murmushi ita ma ta mayar masa da martani hada su fari da ido ya karbi "trolley" din ya jefa a "seat" din baya ya kuma bude mata kofa tashiga ya zagaya yatayarda mota suka dauki hanyar kaduna tafiya ce akayi mai cike da firar so da kauna shiyasa suka dauki dogon lokacin kafin su eso garin kaduna, amar yadanna "horn" maigadi ya bude musu "gate" yanufi "parking" yayi parking" su ka fito daga ciki'n mota'r yayida amar ya kafe na'eema da fitinanu idanu shi, yace "sweety" ga mu a gida "Allah ya kawo mu lafiya da fatar in kinga umma ba za ki manta ni na'eema ta kada kwayar idon'ta tace matukar zan mantawa da kaina to zan iya mantawa da kai, yanzu ma don ya zama dole na shiga ciki don taga shedar nadawo lafiya ina esa mata da sakon aunty Suwaiba zan fito mu cigaba da firar mu mai sanya ni nishadi, ciki'n jin dadi amar yace shiyasa nake kara son'ki "sweety naa" bari nima na shiga na gaida mamee da kuma kaka.
Rass-rass gaban na'eema yafadi saboda tasan matukar yashiga "part" din kaka dole sai yahadu da raheela ita kuma abinda batason faruwa shi kenan saboda tagani kamar amar in yahadu da raheela asiri zai daina aiki akan'shi tafin da amar yayi mata akan fuskar shi yayi sanadiyar dawowa da ita ciki'n natsuwa ta tunani me ki ke yi "sweety naa"? tambaya da amar ya watsa mata kenan ciki'n yanayi na kwarewa da yaudara tace banaso dai-dai da "seconds" daya ka yi min na nisanta da kai yaa amar don haka ka sanar'da daddy zance aure mu kafin ka koma kaduna.
Amar ya dan murmusa yace angama sahiba taa da haka suka rabu ita ta nufi "part" din umma shi kuma yanufi "part din mamee.

********************

Da misali karfe 3:15pm achaba yasauke raheela a kofar gida yayi dai-dai da lokacin da amar yafito da motar'sa zai fita unguwa, karaf idanu shi suka sauka bisa fuskar raheela da ke sanye da "uniform" tana kachaniya fitowa da kudi daga aljihu wando ta tafito da naira dari ta mikawa dan achaba tace bani chanji cikin tsananin mamaki dan achaba yake kallon'ta yace wane irin chanji kuma, malama"?
Raheela ta galla masa harara tace chanji da kasani ko kana nufi bakasan chaji ba"?
Dan achaba yace "eh lallai yarinya kin zo da reni hankali na dauko ki tun daga "salvation" ki bani naira sannan kuma kice nabaki chanji dallah malama ki cika min kudi na raheela ta murtuke fuska tace kai kadaina yi min "shouting" ba fa abun hawa ne ba mu da a gidan'mu kawai nayi ra'ayi hawa achaba don haka kabani chanji na baka kudinka, tun lokacin da amar yaganta tasauka bisa achaba yayi "parking" yana kallon abunda ke faruwa tsakaninta da dan achaba cikin fushi da dacin rai ya balle murfi Mota yanufi waje ta fuskar'sa dauke da tsantsan kiyayya ta.....

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[3:40PM, 10/01/2017] ‪+234 810 336 9936‬: [6:07PM, 5/18/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN
'YAR UWA TAA🍆🍆

💕Love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣7⃣~

Tun kafin amar yakarasa waje su yaji muryar dan achaba yana fadar ke karki nemi ki kure mini maleji, nayi miki rashin mutunci kuma da Ki ke zance abun hawa, to uban wa yahana ki hawa abunda ku ke da, shi sai ki ka buge da hawa achaba dagani yanayi Zubi ki na 'yan aiki ne.
Raheela ta zaro idanu hade da dakawa dan achaba tsawa kai mallam karka saki ka zage ni, kuma kudi'n ba zan ba yarba in kana da karfi ka kwata, kafin dan achaba yabata amsa amar yakaraso batare da ya kalli gefen da raheela ta ke ba yaciro 1000" ya mikawa dan achaba yayida raheela ta kawar'da fuskarta taki kallon sa da sauri dan achaba ya karbe kudi amar yajuya cikin salon tafiyar sa ta kasaita, dan achaba yace yallabai chanji ka, batare da yajuyo ba yace na barmaka raheela tabi amar da kallon mamaki, a zuciya ta tace me wannan mutumi yake nufi ne naga Sai wani shan Qamshi yakeyi"?
ta tabe baki takara da cewa Chan ta matsi maka ta juya wurin dan achaba ta balla masa harara hade da cewa dallah malam ka ja rukubabe mashin dinka ka bar mana kofar gida dan achaba ya kyalkyale da dariya yace yanzu nan 'yan mata kiyi sa'a wannan balarabe yaya naki mai kama da ke saidai yafi ki hankali da natsuwa ya biyani kudi na da na gwada miki rashin mutunci mai "remote" bai jira jin ta baki raheela ba yaja babur dinsa yayi gaba.
Raheela ta turo karamar kofa tashiga ciki'n gida da shigar'ta falon kaka ta jefar'da "school bag" bisa kujera tacire rigar "uniform" ta jefar tayi saura daga ita sai "vest" kaka dai na zaune tana kallon'ta da gudu tashiga "kitchen" sai ga ta da "plate" din abinci tana tafiya tana ci kaka ta girgiza kai tace wai raheela yaushe za kiyi hankali"? ta turo baki tace me nayi"?
Kalli yanda ki ke cin abinci a tsaye kuma nasha yi miki fada kidaina wannan gudun naki na wahalar'da jini jiki amma kin ki dainawa, ta tabe baki tace shegiyar na debo kaka bakiji yanda hanji na yake tsuwa ba kaka tace ko yau kenan ba kiyi "breakfast" ba"?
Raheela ta washe hakora hade da zaunawa kusa da kaka tace kaka bana fada
Miki tara kudi nakeyi ba in lantana za ta tafi kauye na bata tasiyo mini awakai nayi kiyo, kisan tace awakai akwai arha a kauye'n su kudin da na tara za su iya siy......ke dallah dakata kaka ta taka mata birki tace miyasa bakida ta natsu raheela"? Ke kenan kullum da sabon iya shegen da za ki bullo da shi, ina murna kinfara hankali ashe sabuwar hauka nan tafe wance taci uban ta da.
Raheela ta bata fuska ta ajiye "plate" kasa tace na fahimci tun lokacin da nace banaso yaa amar ki ka dauki zafi da ni shin kaka ko kindaina sona ne"? takarasa magana'rta kamar za tayi kuka kaka tayi murmushi tace raheela sarkin rigima yau kuma rigimar akaina tasauka, ki ajiye magana'r amar a gefe saboda tuni na rufe shafi'n ta ina ki kin ga wurin ajiye awakai a gidanan'"?
Ciki zumudi raheela tace a bayan gida mana kuma ba wanda zai ce komai in har ki ka ce ke ce ki ka siya min.
Kaka taja tsoki hade da cewa banaso zance banza raheela, in karki kuskure ki kara yi min zance awakai nan sai na saba miki.
Raheela ta turo baki ta mike tsam ta tsallake "plate" din abinci tafice daga falon ta nufi "part" din'su tana shiga babba falon ta tarar'da umma hajara da na'eema a zaune suna kule-kulen makircin su dadi ya lullube raheela sakamako gani na'eema da sauri ta nufi kujera da na'eema da ke zaune tace lah''! Yaya na'eema yaushe Ki kadawo"?
Ke miye haka wannan ae dabbanci ne da dakikanci miye hadi na da ke da za ki watsa mini wannan tambaya"? na'eema takarasa zanceta hade da ture raheela tafadi kasa bakin'ta ya bugi "stool" yashe sai jini ke zuba tasaka hannuta tadafe bakin nata a tsorace tadago tafara aikawa na'eema kallon mamaki, takara sauke ganinta bisa fuskar umma taga umma na murmushin mugunta, takara dawowa da ganinta wurin na'eema, kafin tayi wani yunkuri na'eema tacigaba da cewa wannan soman tabi ne ki ka fara gani mudi'n baki fita hanyar yaa amar sai na kassara ki domin amar nawa ne ni kadai.
Raheela tasaki murmushin takaici tace haba!'' yaya na'eema yanzu akan da' namiji ki ka zabi ki watsar'da kaunar da mu ke yiwa junan mu"?
Kwarai kuwa domin nafi kaunar shi akanki nafi so na rayu da shi akanki, ke yanzu ba komai bace a wuri'na face makiyiya na'eema na dinga aya a zanceta umma hajara tafara zazzaga nata, ina gargadi Ki da babba murya ki fita hanyar amar da na'eema, in kuma ki ka ki za ki sha dibin mamaki domin rayuwarki za tadawo tamkar ta alade.
Da kyar raheela ta mike tsaye idanu'ta su ka cika da kwalla, ta kalli umma hajara ciki'n rauni murya tace, tabbas umma kinyi nasara datsa kaunar da ke tsakanina da na'eema, saidai kuma har abada ba za ki iya raba jini da ke gudana a jijiyoyi jikin'mu ba tun kafin na mallake hankali kaina nakeji wannan kazamar kalma daga bakin'ki amma kuma umma akwai abunda har izuwa yanzu da ki ka kasa amincewa da shi wanda har yanzu yake wahalar'da ke shine yarda da kaddara, in har baki manta ba kaka tasha fada miki cewa ni kainuwa ce dashen Allah, ba yanda za ki yi da ni dole ki rungume ta annabawa, domin da mugun alkaba'e ki yana tasiri akaina da yanzu bana numfashi a doron kasa.
Ciki'n fushi umma tace karya ki keyi shegiya 'yar gadon talla shayi a wannan karon ni ce mai nasara domin na raba ki da amar rabuwa ta har abada ki kuma saurara zuwa bala'e da ke jira ki.
Umma kenan ni yaa amar baya gabana koda ace ina sonshi zan iya sadaukar da soyayya da nakeyi masa ga na'eema ballantana banaso shi don haka ku je chan ku karata da shi.
Wannan karo na'eema ce tabata amsa ta hanyar cewa, haka za ki qare babu
Mashishini har abba yagaji da ke yasamu mai bakin uwa yabashi sadaka kuma ki bace mana da gani domin uwar'ki da ki ke takama da ita batanan sai ki koma inda ki kafito batare da raheela takara furta uffan ba tafice daga falon.
tana fita daga falon tanufi "part" din kaka tana tafiya tana kuka, amar da ke tsaye a "compound" yana waya da Dr kb yadago da sauri sakamako sautin kuka raheela da yasauka ciki'n kunne sa ya tsura mata idanu har ta kawo kusa da shi yana kallon'ta ta raba gefe'nsa ta wuce tashige "part" din kaka ya bi ta da kallo yana so ya tambaye ta, me take yiwa kuka sai kuma yaji tamkar an dinke masa baki.
Raheela na shiga falon taci karo da kaka zaune inda tabarta, gani yanda raheela take kuka yasa kaka cikin firgici tace ke lafiya kuka me ki keyi"?
Ciki'n shashekar kuka raheela tace zamewa nayi a "bathroom" din aunty amarya baki na yafashe, kaka tayi murmushi tace kai raheela yanzu don kin zame shine ki ke wannan barar baki, ni har nayi tunani ko hajara ce ta taba min ke.
raheela ta girgiza kai domin tasan matukar tafadawa kaka abunda yafaru yau mai rabata da umma hajara sai "Allah don haka sai ta yanke shawara da ta boyewa kaka asalin abunda umma da hajara su kayi mata.
kaka ta rarrashe ta har tadaina kuka saidai kuma lebe bakin'ta na sama ya kumbure.
*************************

WASHE GARI*****

Amar yasami iyayye sa da zance na'eema daddy da Abba sunyi matukar farin ciki'n don haka su ka hada dan karami'n "family meeting" a falon kaka "daddy, abba, mamee, aunty amarya da kuma umma hajara gaba daya su suna zaune bisa kujeri falon kaka, yayida amar, nazeer, Abdulhakeem, Abdulhaleem, da na'eema suna zaune kasa bisan "carpert" raheela ce kadai ke zaune bisa kujera kusa da kaka.
Daddy Yayi gyara murya yace hajja dama wani abin farin ciki ne yasamu yara nan amar da na'eema ne su ka hada kansu shine mu ga yadace a sanar'da ke saboda mu naso a hade su gaba daya har su abdul ayi biki'n kowa yahuta yajuya waje da nazeer yake zaune yace kai kadai yarage ka kawo mana wance ka keso, nazeer yayi murmushi da sauri raheela takara shigewa jikin kaka domin tasan itace zabi nazee kamar daga sama taji murya nazeer yana fadar......
[8:23PM, 5/18/2016] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

~3⃣8⃣~

Nima "daddy nasami wance nakeso sunanta bahijja saidai ba mu gama fahimta juna ba saboda ban fi sati daya da haduwa da ita ba.
Cabdijam tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Cikin yanayi na tashin hankali raheela da kaka su ke kallon mutane falon, tuni jikin raheela yajike sharkaf da gumi'n yayida umma hajara tsantsan farin cikin ya baiyana akan fuskar'ta abba yace ba matsala nazeer sai kabani "address" din gidan su yarinya zan yi bincike akan'ta, ciki'n jin dadi nazeer yace toh abba.
Daddy ne yafara angara da shiru da kaka tayi yafara yawa Cikin girmamawa yace hajja kinyi shiru ba ki ce komai ba"?
Ciki'n tsanani fushi kaka tace ban amince da aure zumuncin ba don haka na soke aure tsakani amar da na'eema shi ya je yanemo matar'sa a waje ita ma taje tafara lalube mijin'ta a waje duk wanda ke Cikin falon ya girgiza da jin furucin kaka musanman amar da na'eema da kuma jahanama ga "passenger" umma hajara, Abba ne yayi yunkuri neman Karin haske daga wuri'n kaka yace hajja ba mu muka hada su ba su ne suka hada kansu kaka ta zaro idanu ta masu cike da masifa tace kai Abdullahi ka kiyaye ni banaso maganar banza duka'nku a karkashin iko na ku ke kuma ba wanda ya esa ya zantarda wani hukunci batare da amincewa ta don haka ku tashi ku bace mini da gani munafuci banza da wofi duk wani munafuki, ina sane da shi a gidanan sai nayi magani shi nace ku tashi ku fice daga falon kaka takara daka masu tsawa, da sauri mamee da aunty amarya su ka fara mikewa suka fice umma hajara ma ba'a bar'ta a baya ba ta Mara musu baya zuciyar'ta cike da haushi takaici kaka yayida "daddy da Abba suka bi ayari su abdul suka fice yazamana saura amar da na'eema da suka fita haiyyaci su sai

9 / 31