Chapter 19 Reading MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt Arewa Novels

MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt

Author :  Hauwa Shehu Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 31

54K to 57K   out of 92.7K words

raheela zafi ne da shi"?
Dole raheela tabar gidanan domin zamanta a cikin sa babban hatsari ne a rayuwa ta.
Raheela na Shiga d'aki tafada bisa gado tasaki ajiyar zuciya tace, kai gidanan akwai mugaye ita wannan nufi ta, tadaki banza a dole ga jaka sun samu
Mtss... taja tsoki a sannu zan shuka musu rashin mutunci, ta mike ta shiga "bathroom" tayi wanka hade da alwala domin lokacin sallah magarib ya qaraso.
Bayan ta kamalla sallah ta nike sallaya tafito kaitsaye tashiga "kitchen" dama na'eema bata dafa abinci da ita saidai tashiga kitchen tadafawa kanta abunda takeso ci, tadafa "noodles" ta bude "fridge" ta dauki juice mai sanyi tashige d'akinta bayan tacika tumbi ta, ta kira kaka suka sha fira daga bisani ta kira ayshat suna cikin fira ayshat tace raheela kin yi "assignment" d'in Mr Ezekiel"? kinsan gobe ne za'ayi submittted"
Babu shiri raheela ta mike zaune ta zaro idanu hade cewa wallahi na manta besty banyi ba'
"What's bakiyi ba sunan ki margaaya ta bakin indiyawa, kuma ga assignment d'in da dan karen wuya ni ma saida na kira sageer bello ya yi mini, raheela taja tsoki tace sai da safe fira ta qare banaso na fada "track" d'in Mr Ezekiel tana kashe waya ta kwaso takardu tsawon lokacin raheela ta dauka bata tsinana komai ba ta jefarda "Biro tadafe goshi tace "dam it's iya sani na kwakwalwa ta bazata iya wannan assignment ba to yanzu ya sanyi"?
Cikin tsanani jin dadi ta mike tsaye tayi tsalle tace "yes" yaa Amar shi kadai ne zai yi min wannan assignment d'in kutt dazu nan mu ka buga tsiya da shi anya zaiyi min kuwa"?
Nan take ta bata fuska ta kalli agogo taga 9:20pm tasan irin wannan tym yana nan zaune a falon cikin kwarin guiwa ta kwashe takardu ta, tanufi falon ta lebe cikin labule, ta leqa falon ta hango shi bisa "three star" kafafu yadaura kafafu shi bisa stool" ga wani dan karamin basket mai kyali bisa cinyoyi shi ta sauke numfashi tasoma shawara yadda za'ayi tashiga falon gashi shi kadai ne jarababiya matarsa bata nan tsoro nakeji kada nashiga yarufe da duka.....
[21/07 10:01 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣6⃣

Tayi kasa da murya tace yaa Amar, yaa Amar batare da yajuyo ba yace raheela da sauri ta mayarda fuskarta cikin labule tace kai ya akayi yagane ni taqara leqawa taga yana kallon sa cikin kwaciyar hankali tasake cewa yaa Amar" yace raheela banaso tsohon iskanci kinji koh wani Sabon fi'eli ki kafito da shi a dare nan na boyewa cikin labule kina kiran sunana ni da gidana kina nufi za ki tsorata ni"?
Raheela ta turo baki hade da yatsine fuska tace guy" nan shi da matar sa suna taqama da gida sai kace su, suka fi kowa gida kowane su da ya bude baki za ki ji yace gidana ni narasa tsakani shi da ita waye maigidan cikin sanyi jiki tafito daga maboyarta tayi sallama hade da cewa yaa Amar barka da hutawa"
Ya galla mata harara yace saida ki kagama tsohon iskanci ki za ki yi mini sallama"?
Raheela ta rufe bakin ta da hannuta na dama tace kai, yaa Amar wai shi iskanci har tsoho ne da shi"?
Amar yayi mata kallon uku saura kwabo daga bisani yace naki iskanci raheela a wurina kullum tsoho ne raheela tayi murmushi hade da cewa ni kuma nayi maka alqawali wata rana zan zo maka da sabon dal tunda iskanci har burge ka yakeyi'
Amar yace to na gode dama nasan wannan zuwan naki don kiyi min rashin kunya ne yasa ki kafito, da sauri raheela ta zube kasa tayi "kneel down" tace don Allah yaa Amar ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka, karufe mini asiri kamar yadda Allah yarufa maka, banida Wanda zai yi mini wannan taimako in baka kai ba.
Kallon kasan ido yake watsa mata daga bisani ya tabe baki yace wane irin taimako ne"?
Wani "assignment" aka bamu mai matukar wahala narasa yadda zai yi shi "please yaa Amar help me"
Amar yayi murmushi, yasaka hannu cikin dan "basket" d'in da ke bisa cinyar shi yadauki "chocolate" daya yabare yajefa a baki ya lumshe idanu yace "so sweet like honey"
Da sauri raheela tace dagani wannan "chocolate" yafi Zuma dadi'
Amar ya bude idanu shi yace ina ruwanki ko nayi magana, da ke ne"?
gani nayi daga ni sai kai ne a falon nan sai kuma tv saidai in da tv ka ke"?
"Eh da ita nake yakamata ki ja wadanan busashi kafafu naki ki je ki kwanta don ni ba "computer" bane da zanyi miki assignment yanzu nan.
Raheela ta yi rau-rau da idanu kamar za tayi kuka'
Amar ya tabe baki yacigaba da kallon sa yayi banza da ita dagaji da durkuso ta mike ya mika mata hannu, tsabar rudewa irin na raheela a maimako ta mika masa takardun sai ta mika masa hannuta, ya buge mata hannu yace me zanyi da wannan qazami hannu naki"?
Dallah malama bani takardu ta mika masa ta koma gefen sa tayi tsaye cikin natsuwa yake duba "assignment" d'in daga bisani yadago ya ja tsoki yace dak'ik'iya kawai yanzu wannan assignment ne mai matukar wahala"?
Raheela ta rausayar da kai tana tsoro ta bashi amsa yajefa mata takardu ta sai kawai tayi shiru tana kallon yadda yake rubutu.
Na'eema da ke kwance a bedroom d'inta kamar wance aka mintsina ta Mike sauko kasa, tun kafin takarasa shigowa cikin falon tafara zazzaga bala'e da masifa, tace lalle mutane nan kun raina mini hankali dazu kun gama guje-guje Ku na soyayya, shine yanzu kuma Ku ka kafa mini daba a falon to wallahi, bazan dauke wannan mumuna dabi'a a gidanan.
Raheela ta zaro idanu tace yaa Amar amma wannan matar taka batada hankali koh"?
Amar ya yi banza da ita kamar baiji tambaya da tayi masa ba'
Na'eema tace ni ce banida hankali to zan nuna miki hauka don sai nayi miki dukan mutuwa a gidanan'
Cabdijam ki rufawa kan'ki asiri yaya na'eema yaushe ki kayi karfi duka katuwar irina"?
Tausayi nakeji yaya na'eema da wallahi in na ware wannan hannu nawa na sauki shi, akanki ko mijin ki da yake likita bazai gane wane irin hatsari ki ka shiga'
Cikin konar zuciya tace yaa Amar kana kallon rashin kunya da raheela take yi mini koh"?
Rubutu sa kawai yakeyi, kamar baya cikin falon na'eema takara harzuk'a tace ina da yak'ini cewa da sa hannu ka raheela take mini abunda taga dama tajuya wurin raheela idanu na zubarda hawaye tace ke kuma raheela duk abinda za kiyi karki manta yaa Amar MIJIN 'YAR UWA KI ne' raheela ta yatsine fuska tace hauka banza ki keyi yaya na'eema bantaba son mijinki ba kamar yadda shima bai taba sona ba kuma na tabbata har abada ba za mu taba son junan mu cikin muryar kuka na'eema tace in har ke bakya son shi ae shi, yana sonki'
Raheela ta zaro ido tace to ni ina ruwa na chan ta matsi muku, sai ki koma d'aki ki tanadi sabuwar wuka yana shigowa ki barka zuciya sa kifito da ita ki cire sona sai ki saka naki shikenan sai Ku zauna lafiya ni ma na huta da wannan fitana taku'
Na'eema ta watsa mata mugun kallon da jajaye idanu ta, batare da tace uffan ba tajuya inda tafito'
Raheela tasauke ajiyar zuciya tace gaba daya yaya na'eema "brain" d'inta yatoshe tadawo abar tausayi
Amar yadago hade da jefa mata takardu ta yace kidaina gani nayi shiru na zuba miki ido kina mata rashin kunya tara miki nakeyi duk ranarda na dank'e ki sai kin yabawa aya zakinta
Raheela tayi murmushi tattara takardu ta tace na gode yaa Amar Allah yasaka maka da gidan aljannah Firdausi"
Amar yace "Ameen" in da gaske ki keyi
Ta mika hannuta bisa "stool" tadauke basket d'in chocolate tace wannan ni karagewa koh"?
Amar yaja tsoki yace ina ruwa na da ke da zan rage miki chocolate"
Saida takai bakin kofa ta murguda baki tace nima ban hada komai da kai ba daga kai har matarka bakuda hankali mahaukata kawai tana karasa fadar haka tarufe kofa'
Amar yayi murmushi hade da Shafa sumar kan'shi yace my trouble raheela, shiyasa nake sonki bakya bari ko ta kwana ya kashe tv ya haura sama har yayi niyar shiga d'akin na'eema sai kuma yafasa a zuciyar'shi yace da gaskiya raheela fa na'eema batada hankali za ta iya daukar shawarar raheela tashiga da wuka "bedroom" gallawa kofar d'akinta harara ya shige na shi.......

Jeeddah Aliyu🌹
[3:48PM, 10/01/2017] ‪+234 810 336 9936‬: [23/07 3:08 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣7⃣

BAYAN SATI BIYU******

Raheela na kwance a bedroom d'inta wayar ta yayi "ringing" ta yatsine fuska tayi "picking" kasalance tace "hello" jin muryar da batayi zato ba yasa ta mik'e zaune tace yaya hafsat saukar yaushe"? a bangare daya aka amsa da cewa jiya da yamma Amar bai fada miki nadawo ba"?
Tak'ara yatsine fuska hade da cewa wannan uban 'yan miskilaci ne zai fada mini kin dawo ae ba zai fada ba, yaya hafsat tayi dariya tace yaushe za ki zo gida na"?
Cikin zumudi raheela tace gobe daga "school" zan wuce gidanki, da an kwana biyu zan tattaro shirgi na nadawo gidanki da zama ni dama zaman gidanan ya eshe ni gida sai kace "prison"
Yaya hafsat ta kyakyale da dariya daga bisani tace raheela 'yan mata kaka har yanzu baki daina rigima ba koh"?
Nadaina yaya hafsat saidai in an tsokano ni, nakan d'an taba kad'an'
Dariya yaya hafsat tayi sosai daga bisani tace sai kin zo ta kashe waya.
Wani, wawan tsalle raheela tadaka a tsakiyar gado tace karshen zama na gidanan, yazo fuskar ta dauke da farin ciki tanufi "kitchen" tun kafin takarasa shiga kitchen d'in ta tsakayi na'eema ciki, har tayi niyar ta koma falon ta jira har tafito sannan tashiga sai kuma ta tuna da irin matsanaciya yunwa da takeji kawai, sai tafada kitchen d'in.
Jin motsi mutum yasa na'eema ta juyo gani raheela ce sai wani yatsine fuska kamar taga kashi, cikin rashin damuwa da irin kallon da takeyi mata tanufi locker ta bude tafito da kwalin comflask" karaf idanu na'eema suka sauka bisa d'an yatsata da hamzari ta rik'o hannu raheela a firgici raheela take kallon ta a tunani ta ko za ta zanga mata mari ne domin yadda ta danke hannu nata, cikin kad'uwa na'eema tace raheela ina ki ka sami wannan zobe"?
Raheela tasaki ajiyar zuciya saboda batayi tsanmani wannan ne dalilin da yasa na'eema tayi mata wannan mahaukaci rik'o ta fisge hannuta da k'arfi tace dallah malama sakeni, don kinga zobe a hannu na "so what's"
A fusace na'eema tace dole na tambaye ki inda ki ka sami da wannan zobe domin na mijina ne'
Hmm..su miji manya to mijin naki ne yabani
Na'eema tayi shiru zuciyata na tafarfasa jin takeyi kamar tadauki wuk'a ta dabawa raheela a k'aho zuciya, tana tsaye har raheela tagama abunda ta zo yi a "kitchen" tayi tafiyarta, tabarta tsaye tana jinyar dafi da tasake mata tamkar kazar da kwai yafashewa a ciki haka na'eema taja kafafuta tafita daga kitchen d'in tanufi d'akinta.

A WASHE GARI******

Daga "school" raheela ta zarce gidan hafsat ta shantak'e tayi zamanta har 10:00pm ta buga raheela tafito daga bedroom d'in yaya hafsat hannuta dauke da karamar 'yar yaya hafsat mai suna kausar tace yaya hafsat ni gaskiya tafiya zanyi kinga har 10:00pm ta buga ba zai yu na kwana anan saboda ban zo da kaya ba kuma gobe ina da "lecture"
Hafsat ta ja d'an k'arami tsoki tace ko yanzu na kira wayar Abban fahad "still" wayar shi a kashe
Raheela tabata fuska kamar za ta fashe da kuka, tace to yaya hafsat ki bari na hau "taxi"
Hafsat ta zaro ido hade da cewa ba zan sake ki a dare nan ki hau "taxi" bara na kira Amar ya zo yadauke ki'
Raheela tayi murmushin yak'e domin tasan mayuwaci abu ne yaa Amar ya zo yasauke ta
Amar da na'eema na zaune a falon Amar yana duba wasu "file's" na'eema kuma na kallo "ringing" d'in wayar Amar ne yasa yadago daga abunda yakeyi, yadauki wayar gani suna yaya hafsat yana yawo a "screen" yasa yayi saurin "received"
Muryar hafsat ce takarade masa kunne Amar don Allah ka zo ka dauki raheela'
Yatsine fuska yayi daga bisani yace ni driver" ta ne da zan zo na d'auke ta ae ba da izzini na ta wanke kafa ta je gidanki'
Yaya hafsat tayi murmushi tace don ni za ka zo ba don halinta ba "please Amar ka taimaka kayi min wannan "favour"
Amar ya tabe baki yace naji gani nan zuwa batare da yajira jin ta bakin hafsat ba ya kashe waya, duk abunda yake fada bisa kunne na'eema saboda takasa ta tsare sai wani zarar idanu takeyi Amar ajiye "file" d'in ke rik'e da shi ya mik'e tsaye yanufi inda yake ajiye key's d'in mota yadauka na'eema ta mik'e a fusace tace yaa Amar wannan wane irin raini hankali ne"?
Tsanani mamaki ne yarufe Amar kafin yabata, amsa tacigaba da fadar.....
[23/07 4:29 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣8⃣

Wannan ae salon cin amana ne to wallahi" wallahi" matukar ka d'auki kafa ka je d'aukar raheela ni kuma sai na zantarda hukunci mafi muni akanka, domin nagaji da cin amana ta da ka keyi, har zobe ka je aka k'era maka mai Zane "heart" kasaka daya a hannu ka kasaka mata daya to kayi a banza saboda nariga na zana layi mai tsayi a tsakani Ku saidai S0 raheela ya zama ajalin ka amma bazaka taba samu ta a matsayin matar aure ka, ni d'inan da baka so nice abokiyar rayuwar ka ta har abada, shashasha kawai mai kwakwalwa tumakai Wanda baya gudun abin kunya mtss..taja tsoki ta haura "upstairs" da gudu tabar Amar tsaye kamar bishiya kwa-kwa ya sauke gwaro numfashi tsanani tsoron Allah ya kama shi, wai ni na'eema za ta wanke wa allo tabbas na'eema ta shuka mini rashin mutunci na nuna a gidan talabiji na BBC world"
Ya kad'a kai yafice "driving" yakeyi amma ji yake kamar zuciyar'shi za tayi tsalle tafaso kirji shi tafito a haka yak'arasa gidan yaya hafsat, yana yi "parking" akafara yayafi dama garin yadau hadari a kasalance ya kira wayar yaya hafsat yace ki ce da ita tafito ya kashe, yaya hafsat tajuya wajen da raheela take zaune sai taga tadaura kanta a hannu kujera tana bacci, ta d'an bubuge ta, tashi tana bude idanu ta tace yaa Amar ya zo ne"?
Yaya hafsat tadaga mata kai da sauri ta d'auki "handbag" d'inta tace sai da safe yaya hafsat tafita da gudu, tun daga nesa Amar ya hango ta ya girgiza kai ko yaushe raheela za ta girma tadaina gudu oho"
Ta bude kofa tashiga tun kafi ta rufe kofa yafisgi mota da k'arfi gaske, raheela ta murguda baki suna fita unguwar su yaya hafsat aka sake da ruwa da k'arfi don haka Amar yak'ara "speed" dama gashi gwani ne a fagge gudu da mota, cikin 20 minutes" suka eso gida yayi "parking" daf da kofar shiga babban falon suka fito da gudu raheela tanufi kofa tana murda "handle" taji kofa gam Amar yakaraso yadaka mata tsawa yace kofar ma baza ki iya budewa sai na bude miki"?
Har raheela ta bude baki ta bashi amsa yak'ara daka mata tsawa ta hanyar cewa, dallah bani wuri ta matsa masa yana Kama "handle" yana murdawa ya ji kofa a rufe ruff'
Raheela ta kyakyale da dariya, wani mugun kallo ya watsa mata Wanda yayi sanadi da ta hadiye saura dariyar ta, yasoma "knocking" tun yanayi a sannu har yadawo yi da k'arfi daga karshe yadawo kwadawa na'eema kira, a hankali "window" ya bude na'eema ta lek'o kanta ta da sauri Amar yace na'eema wannan wane irin dabbanci ne da za ki rufe mana kofa kenan duk "knocking" d'in da nakeyi kina jina koh"?
Saida tak'are musu wulaqantace kallo sannan tace, na rufe kofa kayi duk abunda za ka yi, gantalalu kawai, maciya amana sai kuma inda Ku ka saba zuwa kuna iskanci Ku, Ku kwana a chan.
Wata irin zufa ce ta k'aryo wa Amar cikin sark'ewa halshe yace me ki ke nufi da na'eema"?
Duk abunda na ke nufi kasani munafuki mai bak'ar fuska'
Raheela kam mutuwar tsaye tayi yayida hawaye suka wanke mata, fuska cikin rawar murya tace haba yaya na'eema me mu kayi miki da ki ka zabi kiyi mana wannan mumuna k'azafi"?
Na'eema tadaka mata tsawa ta kuma nuna ta da yatsa, tace ke k'arama karuwa rufe min baki ba da ke nake magana ba'
Raheela ta kurma ihu tace yaya na'eema ni ki kira da karuwa kin manta ko ni wacece agareki"?
Mtsss... Na'eema taja tsoki cikin zafin rai Amar yanufi window" yace ke na'eema yau na fahimce cewa wani Sabon hauka ki ke ji to zan sauke miki shi ki zo ki bude mini kofa'
Na'eema ta kwabe fuska tace ba zan bude ba yau saidai ko kwana a waje amma ba dai a cikin gidanan ba 'yan iska kawai jarababu karaf ta rufe window" tayi tafiyarta.
Raheela ta durkushe tana rusar
Amar ya shure kofa da kafar shi, yasaki razanane ihu sakamako wani zafi da ya ziyarci kafar sa.
Gani ruwa suna k'ara k'arfi yasa ya kalli raheela yace ke tashi mu tafi
Tadago idanu ta da su ka kad'a sukayi jajir batare da tace komai ba tabi bayan shi ya bude mota yashiga ita ma tashiga a tunani ta fita zai yi sai taga yanufi "parking space" yayi parking yad'aura kanshi bisa "steering" raheela kuma tasaka kanta tsakiyar cinyoyi ta tacigaba da shashek'ar kuk[truncated by WhatsApp]
[3:49PM, 10/01/2017] ‪+234 810 336 9936‬: [23/07 6:46 pm] Jeeddah Aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣9⃣

Tsawon lokacin suka d'auka a haka babu

19 / 31