Chapter 15 Reading MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt Arewa Novels

MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt

Author :  Hauwa Shehu Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 31

42K to 45K   out of 92.7K words

tuwo,
raheela ta turo baki ta juya tashiga, "kitchen" Amar sai bin ta da kallo yakeyi, tana shiga kitchen batafi 5 minutes ba ta kurma ihu tana kira wayyo aunty hannu na, kafin aunty ta mike tuni Amar yariga ta kai wa "kitchen tana durkushe rike da hannu hawaye na zuba, da sauri Amar ya durkusa gaban ta yariko hannu nata, ciki'n sarkewa halshe yace sannu raheela"
Ta balla masa harara ta kuma murguda baki, a zuciyar'shi yace lalle zafin tuwo bai ratsa ki ba tun da har kina iya murguda baki, baiyane sai yace da zafi koh"?
Kafin ta bashi amsa su ka ji sautin murya aunty amarya tana fadar, ke dai maama yaushe za ki yi hankali, garin ya ya ki ka kone hannu ki"?
Amar ne yakarbe zance ta hanyar cewa ae ba sosai ta kone ba, aunty tace shine don tsabar iskanci ki ke yi mana wannan uban ihu"?
Raheela ta fisge hannuta daga riko da ya yi mata, ta mike tsaye tace don ba yana jikin sa bane shiyasa yafadi haka.
Ke dai tsabar raki ne kawai irin naki, Amar yafada yana dariya, raheela ta tabe baki tafice daga "kitchen din aunty amarya tace ae maama abun kuka baya mata wuya kaka tariga ta sagarta ta.
Amar yayi murmushi'n yafito daga kitchen din yace aunty, umma na ciki kuwa"?
A'a batanan ta, tafi katsina wurin bikin aure,
Amar yace Allah yadawo da ita lafiya"
Ameen aunty tafada hade shiga kitchen" din
Amar yakara cewa aunty sai anjima zan dan shiga gari'
Toh Amar adawo lfy"
Allah yasa Amar yafada hade da ficewa daga falon zuciya'rshi cike da muradi kara gani kyakyawar fuska raheela saidai kash koda yafito tashige "part" din kaka dole ya ja motar'shi yakara gaba.
Raheela na shiga falon kaka tafara yi mata kukan shagwaba, saida kaka tayi mata tofi sannan ta yi shiru.

*****DARE*******
Da misali karfe 9:15 na dare Amar da daddy na zaune a hadade falon daddy mai kama da falon sarakuna, daddy na kishigide yayida Amar yake zaune kusa da shi, sai faman zuba fira su keyi har daddy ya gangaro kan zance karatu raheela yace, Amar tun da gobe za koma abuja sai katafi da raheela kayi mata registration" da duk wani abu da take da bukata kuma banaso ta zauna "hostel" nafiso ta zauna gidan'ka domin za ka fi bata kulawa da kuma karatu ta, duk abunda yashige mata duhu za ka taimaka mata.
Tun lokacin da daddy yafara magana Amar yatsinci'n kan'shi da mashahuri faduwa gaba, gaba daya yarasa natsu jikin'shi ya jike da gumi kamar ba Ac a falon, ya naji kayi shiru Amar ko har yanzu kana 'yar tsama da Mama naa ne"?
Da sauri Amar ya girgiza kai hade da fadar Noo" kawai ina tunani irin farin ciki da na'eema za ta nuna in taji raheela za ta zauna abuja, daddy ya yi murmushi'n su na manya yace na'eema da raheela su ne suka gado mu, domin ni da Abdullah haka mu taso, kuma har yanzu da girma yakama, mu muna da kaunar junan mu ko kaka bata gane kan mu shiyasa nake, gargadi ka Amar da rike zumuncin domin kaine babba da kai 'yan uwa ka su ke koyi don haka ina rokon ka da ka rike raheela amana kabata kulawa irin wanda mu iyayye ta za mu bata, ka kuma yi hankuri da halinta saboda kasan reno kaka ce tasaba da shagwaba daddy yakarasa zance'sa yana dariya.
Amar ya sauke gwaron numfashi kamar zai shede ya hadiye wasu yawu masu masifar daci saboda yafara hango bala'e da zai tun karo shi, da kyar iya fadar "insha Allah daddy zan rike raheela amana, zan kuma bata kulawa ta musanman har izuwa lokacin da Allah zai nuna mana ta kamalla karatun ta, ae raheela Qanwa tace ta jini ko ada chan da nake tsangwama ta, ina yi ne domin ko za ta rage rashin ji da takeyi amma a yanzu "no thing's between us"
Daddy ya daga kai alamar ya gansu da karya da Amar ya shararo masa, daga bisani yace shikenan zan tura maka kudi ta "account" dinka sai ka yi mata amfani da su, da sauri Amar yace haba daddy wane irin kudi kuma ko manta da matsayi na big brother"
Daddy ya yi dariya yace da kyau big brother" Amar shima ya yi dariya rashin mafita a haka su ka cigaba da fira.

******WASHE GARI******

Sai a washe gari daddy yashiga "part" din kaka ya sanar'da ita tafiyar raheela, da kuma hukunci da ya yanke akan raheela za ta zauna gidan Amar, kaka tayi shiru tana juya wannan sabo al'amari a zuciyar'ta, saidai batada zabi illah ta nuna amincewar ta domin bataso ta kawo shakku a zuciyar 'ya'yata, don haka kaitsaye ta amince yayida raheela na jin zance tafara kuka, da kyar daddy ya rarrashe ta yace tashi maza ki hada kayanki yana, jira'nki kuma inda ya yi miki abunda bai gamsar da ke ba ki kirani a waya zan har gidan'shi na wanke masa allo shi, ba yanda raheela ta iya dole ta hada kayanta ciki'n katuwar trolley" daddy yakira bala driver ya kai mata trolley din ciki'n motar Amar kaka ta kira Amar su ka kebe ta ja masa kunne hade da gargadi akan raheela, daga nan raheela tayi sallama da mamee da kuma aunty amarya saboda uwar gaiyya wato umma hajara bata ga gari ballatana taga kalubali da yake tunkaro su ita da 'yarta.
Raheela kuka takeyi kamar ranta zai fita saboda kwata-kwata wannan tafiyar bata kwanta mata a rai ba tana tausayawa kan'ta irin rayuwa da zatayi a gidan Amar da na'eema ta rungume kaka ciki'n shashekar kuka tace kaka banaso tafiyar nan bazan iya jure wulakanci ba, da sauri kaka ta rufe mata baki tace kiyi biyayya ga iyayye ki raheela Ki tafi kawai Allah yana tare da ke zan kuma cigaba da yi miki addu'a neman kariya daga rabbil-izzati, raheela ta juya wurin abba taa tace abba zan tafi abba yace toh mama naa kidage kiyi karatu da kyau nima zan cika alqawali zan siya miki tsadadiyar mota, raheela tadaga kai takara juyawa wurin da aunty amarya da mamee suke tsaye tace aunty da mamee za ku yi kewata koh"?
ae kuwa mamee da aunty suka fashe da kuka domin raheela, tayi masifar basu tausayi saboda wannan ce tafiya ta farko da raheela ta tabayi a rayuwata, gani yanda suke kuka yasa daddy yariko hannu raheela yasakata cikin mota sai kace amarya, duk wannan shagali da akeyi Amar yana zaune cikin mota yana danna waya hankali'nshi kwance, daddy yana juyawa raheela ta balle kofa tafito ta balla da gudu ta qanqame kaka tana kuka ita ma kaka tafashe da kuka sai ga kaka da raheela na kuka rija-rija, ba mai rarrashi wani, ciki'n zafi rai Amar yafito daga cikin mota ya banbare raheela daga jikin kaka yace wai miye haka ne"?
da za ku cikawa mutane kunne da ihun kuka, karatun nan ba dole bane za ta iya zamanta, kaka ta galla masa harara da Jajaye idanuta tace kai ka kiyaye ni,
Amar ya janyo hannu raheela da karfi yajefa ta mota yazagaya yashiga a driver seat ya kuma yi lock'' din kofa yayida, daddy yace kai ka bita a hankali ka ji koh"?
Amar ko saurare shi banyi ba yafisgi mota maigadi ya bude masa gate yafice daga gidan raheela nagani an fito, daga unguwar su takara fashewa da wani sabon kuka.....

ALHAMDULLAHI"!
Anan na kawo karshen littafin MIJIN 'YAR UWA TAA kashi na daya sai ku kasance tare da ni 'yar gidan shehu Aliyu bayan sallah inda Allah yanufe ni da kaiwa za kujini dauke da MIJIN 'YAR UWA TAA kashi na biyu tare da sabon littafi na mai suna NI DA YAYA HABEEB.

Nice taku mai muku fatan alkhairi Allah yabamu ikon gudanarda ibadamu a cikin watan Ramadan mai albarka Ameen.


I LOVE YOU OLL MY FANS😍

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[3:45PM, 10/01/2017] ‪+234 810 336 9936‬: [02/07 8:52 am] Jeeddah aliyu🌹: [28/06 3:28 pm] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

{Part 2}
Goron sallah

💕love story 2016💕


Na Hauwa shehu Aliyu🌹

~5⃣3⃣~

Raheela tacigaba da rusa kuka kamar ranta zai fita ko kallon ta Amar baiyi ba yacigaba da driving" sai faman sharara gudu yakeyi kamar Wanda zai tashi sama, har suka fita garin Kaduna raheela tana kuka gani kukan nata yaki karewa yasa Amar yataka birki da karfi cikin tsanani bacin rai ya balle kofar mota yafito ya zagaya ya bude kofar da raheela take zaune yafisgo ta da karfi ya cilla ta waje yakara bude sit din baya yafito da trolley dinta ya ajiye mata a kasa a harzuke yace ni ba dan iska bane da zan dauke ki a Mota kina mini kuka sai ki zauna anan tare da kuraye jeji kicigaba da kuka, ki dama chan kinfi dacewa da abinci kuraye yana karasa zance sa yajuya cikin zafin nama yashiga mota yafisgeta raheela nagani haka ta kurma ihu tabi bayan motarsa da gudu kafarta ko takalmi babu tadinga kwalla masa kira wayyo yaa Amar karka tafi ka barni wallahi tsoro nakeji dan Allah kadawo nadaina kuka wayyo kaka nashiga uku kuraye za su cinye ni tuni motar Amar ta bacewa ganinta dole tajuyo tanufi wurin trolley dinta wani wawa ihu tasaki hade da zubewa kasa sakamako qaya aduwa da ta, taka da Sauri ta rike kafar ta tana gunji kuka, gani jini na zubawa daga kafarta ga kuma qaya ta lutsi cikin naman kafarta yasa raheela takara shiga cikin tashin hankali da kyar ta iya mikewa tsaye tasoma dingishi ta nufi trolley dinta ta zauna akanta tasoma kallon titi tsawon lokacin ta dauko a zaune ko tsuntsu bataga wulgawa sa ba sakamako yau weekend ne mutane basu cika fitowa ba raheela tacigaba da shashekar kukanta kamar daga sama taji muryarsa yana fadar kee in kin gama kukan naki ki taso mu tafi, ni karki bata min lokacin, da sauri raheela tadago ta kalle shi, yana tsaye jikin mota babu alamar damuwa akan fuskarsa tasaki katuwa ajiyar zuciya ta Mike tsaye Sam ta manta da qaya da ke kafarta ae kuwa ta kurma razanane ihu hade da fadar wayyo yaa Amar kafata, da gudu yakaraso waje ta ya zaunarda ita a kasa ya kuma yariko kafarta yaciro qaya da karfi raheela ta dagargaje iya karfinta ta kurma ihu hade da chakumo rigar Amar rungumo ta yayi akan kirjinsa yasoma bubuga bayanta ita kuma ta lafe tana kuka kasa- kasa tsawon dakika bakwai suka dauka a haka daga bisani yadago ta yafito da handkerchief" yadaure mata kafar chan kasan makoshi yayi magana tashi mu tafi, raheela ta make kafada ya zaro idanu hade da fadar uban me zaki cigaba da yi anan"?
Tayi rau-rau da idanu alamar za tayi kuka cikin murya shagwaba tace wallahi ba zan iya tafiya ba kafa na zogi takeyi kamar za ta cire Amar ya kyakyale da dariya daga bisani ya tsagaita da dariyar da yakeyi ya dungure mata kai hade da cewa raheela kin Shiga uku da raki, 'yar wannan qaya ce zata hanaki tafiya"?
Raheela ta galla masa harara tace don ba yana kafar ka bane shiyasa ka ke ganinta 'ya da kaine ka takata da ihu da za kayi sai yafi nawa.
Amar yayi murmushi har kumatu sa suka lotsa raheela batasan lokacin da tasaka dan yatsa ta cikin dimple" din nashi tace yeee" yaa Amar "dimple" Amar yakara kyakyalewa da dariya yace ke fa shashasha ce raheela sai yau ki ka fara gani "dimple" akan fuska ta"?
Raheela ta turo baki tace kullum fuskar ka a murtuke take ta yaya zan gano kanada "dimple" Amar ya girgirza kai yace to sarkin 'yan sharri, sharri zakiyi min"?
Raheela ta tabe baki hade da cewa ba sharri bane gaskiya ce na fada, yace to naji ki tashi mu tafi ko nakara tafiya na barki wannan in natafi bazan dawo ba.
Raheela ta yatsine fuska tace ko yanzu da kadawo waya baka hankuri"?
Da sauri ya mike tsaye yace "okey ki zauna karki tashi, ya juya yanufi mota raheela nagani haka ta Mike tabi bayan shi, tana fadar yaa Amar wannan abar waya zai dauke ta"?
Mtsss.... Amar yaja tsoki yakoma yadauko mata trolley" dinta, tunda suka dauki hanya raheela keta faman korafi ni dai yaa Amar kadauki alhaki na haka kawai kasa nadinga ihu cikin jeji"?
Amar ya tabe baki yayi banza da ita kamar baiji abunda tafada ba
[02/07 8:42 am] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

5⃣4⃣

Gani yayi banza da ita yasa ta shafawa kanta lafiya, ta lafe jikin kujera ta lumshe idanu ta tasoma tunani irin kala rayuwa da za tayi a gidan yaa Amar, da haka baccin yayi awon gaba da ita.
Amar ya ji shiru nata yayi yawa ya juya Inda take zaune ya tayi bacci ya tsura mata idanu tsanani sonta yafara yawagi akan zuciyarsa, ya mika hannu shi yariko hannuta a haka yadinga driving daya hannu shi yana sarke da na raheela har suka Shiga garin abuja raheela tana sharar bacci, kaitsaye Amar yadoshe gidansa da ke maitama, yadanna horn maigadi ya wangame masa gate yanufi "parking space" yayi parking, ya kashe wutar mota yakara samu wadatace lokacin karewa raheela kallo hannu ta da ke cikin hannu shi yafara murzawa a hankali, saida yashare tsawon dakika uku zuwa hudu a haka daga bisani yafara tashe ta cikin husky voice" dinshi raheela"raheela ki tashi mu eso gida, a hankali tafara bude idanu ta tayi doguwar hamma hade da miqa ta balle kofar mota tafito tasoma karewa "compound" din gidan kallo Amar dai yana tsaye yana kallonta tace "wow! What's beautiful house I like it's"
Amar ya girgiza kai ya kwadawa maigadi kira yanuna masa trolley dinta yadauka yashiga mata da ita ciki, gida yakara juyawa wurin ta yace kee in kingama shirme ki, ki zo mu Shiga cikin gida rass rass sauti da yake fita daga kirjin raheela kenan da ta tuna gidan yaya na'eema ne ta zo ta bata fuska kamar za tayi kuka, yakara cewa mu tafi mana dole raheela ta bi bayan Amar suna kaiwa bakin kofar da ke sadaka da babban falon gidan suka ci karo da na'eema da sauri raheela ta juya ta boye a bayan fila yayida hankali na'eema gaba daya yana wurin mijin ta Sam bata Lura da raheela da ke boye ba ta rungume shi hade da fadar I miss you hubby" shima Amar yakara manne ta a kirjin shi har wani shinshina ta yakeyi yace I miss you too baby" raheela da ke labe tana kallo su taja tsoki tace 'yan iska kawai kalli wani rukurkushe juna da sukayi, ko kunya basaji, ta na kallon su suna manne da juna suka shige falon aka bar ta tsaye ga gajiya ga yunwa Sam Amar ya bata da wata aba raheela saida na'eema tace hubby wannan katuwar trolley da Joseph yashigo da ita menene a ciki"?
Dai lokacin Amar yatuna tare yake da raheela da sauri ya ture na'eema daga jikinsa hade da cewa "oh shirt"
ya Mike tsaye yanufi kofar fita da sauri kamar zai tashi sama na'eema da ke tsaye fuskarta dauke da mamaki me Amar ya tuna da shi da yahadasa masa wannan saurin haka yana fita ya hango ta jikin fila yaja yayi tsaye yasauke ajiyar zuciya ya qura mata ido ita kuma ta murguda masa baki yayi murmushi yakarasa kusa da ita cikin sanyaya murya yace baby me yahana ki shiga ciki"?
Raheela tayi rau- rau da idanu ta langwabe kai tace yaa Amar ina tsoro haduwa da yaya na'eema bansan wane irin kala maraba za tayi min ba, tsanani tausayi ta Yakama Amar yariko hannu ta yace karki damu raheela tunda nayiwa daddy alqawali zan kula da ke bana tunani akwai wani mahaluki da zai takura ki "fill free baby remember it's your hero house okey"
Raheela ta daga kai alamar ta gansu da kalaman sa with full confidence" tashiga cikin gidan na'eema fito daga kitchen hannu ta dauke da hadade tray da lemon kwali akai da kuma glass cup's" idanu ta suka hasko mata fuskar raheela da Amar sun jero hannu Amar na danke da na raheela batasan lokacin da tasaki tray hannuta cup's suka sauka bisa tiles suka tararatsi ita kuma tadafe kai hade da fadar innalillahi wa'inna illahi raji'um nashiga uku ni na'eema, wace irin masifa ce yau tasauka a gida na?
Babu shiri Amar yasaki hannu raheela yakarasa wajen na'eema yariko ta yace calm down sweetheart" da sauri ta ture shi idanu ta sun kada sunyi jajir tsanani tashin hankali ya baiyana akan fuskarta cikin sarkewa halshe tace you ask me to calm down yaa Amar as how just tell me as how"?
Ta karasa zance ta cikin daga murya da kururuwa, Amar yadafe kanshi yasoma tunani mafita cikin zafin nama na'eema ta esa wajen raheela tafisgo ta wanke ta da mari ta kuma rufe ta da duka, tana cewa wallahi raheela ko kece 'yar sarkin matsafa na duk duniya baki esa ki rabani da yaa Amar ba don haka yau sai na kashe ki in yaso nima a kashe ni, me na tare miki da za ki zabi hanyar musgunawa rayuwata ki barni na rayu da yaa Amar domin ni nafi chanchanta na kasance tare da shi ba ke ba raheela yayida raheela sai kakari mutuwa takeyi domin ba karamar shaqa na'eema tayi mata ba da gudu Amar yakaraso wajen su yadauke na'eema da wawan mari Wanda yahadasa mata sakin raheela bata shirya ba raheela ta zube kasa numfashi ta na fita guda-guda jijiyoyi kanta sun fito radau-radau kwayar idon ta sunyi jajir, Amar yadurkusa gabanta yadago kanta yadaura bisa cinyoyi shi yace........

💃Happy sallah💃

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[06/07 10:58 am] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

{Part 2}
Goron sallah

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

5⃣5⃣

Yace am so sorry" raheela zan dauki mumuna mataki akan, wannan cin kashi da na'eema tayi miki domin ke amana ce

15 / 31