Chapter 17 Reading MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt Arewa Novels

MIJIN YAR UWATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY HAUWA SHEHU ALIYU.txt

Author :  Hauwa Shehu Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 31

48K to 51K   out of 92.7K words

waya ne"??
Cikin sanyi murya Amar yace raheela ce kb da raheela nake waya me nayiwa raheela ta tsaneni"??
Cikin dinbi mamaki Dr kabeer yafurta sunanta raheela cabdijam dama har yanzu Amar son raheela yana tare da kai"??
Amar ya yatsine fuska yace kwarai kuwa kb har gobe ina son raheela"
Amma kasan wannan kuskure ne koh"?
I known kb but nima bansan me ke damu na zuciyata tazamo bana iya sarafa ta itace take sarafa ni wasu lokuta zan ji na tsani raheela tsana mai tsanani gaske a wani lokacin kuma sai naji duk duniya ba mace da nakeso irin ta I don't known what's wrong with me" Amar yakarasa zance sa hawaye suka wanke masa fuska abinda yakara jefa Dr kabeer cikin firgici kenan da sauri ya zauna kusa da Amar cikin sigar rarrashi yace kadaina kuka Amar nasan daci da zafi da so yakeda shi, amma na tambaye ka mana"?
Amar yadaga masa kai, Dr kabeer yacigaba da cewa Amar kadaina son na'eema ne sannan kuma kanada labari cewa babu aure tsakani ka da raheela"??
Amar yasaki ajiyar zuciya hade cewa kb ina matukar son na'eema babu abunda ya sauya daga dinbi soyayya da nakeyi mata, ina sane da cewa raheela ta haramta a gareni ae ni ba jahili bane nasan abunda nakeyi"
Harara Dr kabeer ya watsa masa cikin baci rai yace in har kai ba jahili bane to kai kursugumi dan iska ne tayaya zaka bari shedan yayi tasiri a zuciyarka ka hade soyayya'r ya da qanwa wannan ae ganganci ne kayi kokari ka rarrashi zuciyarka ta hakura da soyayya raheela gudun tafka abin kunya.
Har Dr kabeer yadasa aya a sharhi sa Amar yana kallon shi saida ya share tsawon dakika biyar yana kallon Dr kabeer daga bisani yace bazan iya daina son raheela saboda son ta yariga yazame mini jini jiki na kawai zanyi kokari nadanne duk wani " feeling's da nakeji akanta koda hakan yanufi ni zan rasa nawa kwanciyar hankali zan tattara duk wata soyayya da nake yiwa raheela nadawo mata yaa Amar din da tasani a bayan zan dawo mata mugu maras tausayi amma ba wai don na daina sonta ba.
Mtss... Dr kabeer yaja tsoki hade da cewa chan ta matsi maka ita dai bata kallo ka a matsayin masoyi saidai Mijin 'yar uwar taa don haka iska ne kawai yake wahalarda mai kayan kara"
Amar yayi miqa hade da cewa kb kenan bakasan so bane shiyasa amma da kasan dadi da radadi so da ka tausaya min
Kb ya tabe baki yace "please mu ajiye zance raheela a gefe mu yi zance da ke gaban mu.
Ta bangare raheela kuma tana ajiye waya tafashe da kuka tafara zance zuci na Shiga uku ni raheela wannan wace irin masifa ce yaa Amar yake yunkuri jefa ni a ciki"??
Takara fashewa da kuka cikin shashekar kuka tafara magana kamar wata zarara wallahi na tsane ka yaa Amar kuma har abada bazan taba sonka, tsanani na da kai kiyayya ce kuma duk ranarda ka kara furta mini kalma son sai na fadawa daddy" koda hakan yana nufi zai tarwatsa zumuncin iyayye mu haka raheela tacigaba da tsoki burutsu ta ita kadai.
*********************
WASHE GARI****

Da misali karfe 10:30am Amar da na'eema suna zaune bisa "dining table" suna breakfast" cikin rashin walwala Amar yajuya wurin na'eema yace ki shirya za mu fita"
Na'eema tace hubby ka manta yau Sunday"??
Amar ya galla mata harara yace yau Sunday ni chiristan ne da za ki tuna mini yau sunday kinga malama in kinada ra'ayi fita "fine in kuma bakida karki fada mini maganar banza yana karasa magana ya Mike cikin zafin rai har yana ture kujera yanufi falo yabar na'eema cikin mamaki dalilin wannan daukar zafin dole ta mike tashiga bedroom tadauko mayafi da handbag dinta Amar yajuya tabi bayansa yayida raheela da ke dakin ta taji karar tashin mota da sauri ta leqa window" tayi murmushi jin dadi tace umma ta gaida ayshat jarababu kawai kalli fuskoki su a murtuke kamar Wanda aka aikowa sakon mutuwa nima yau zan sake nayi yanda nakeso ba mai takura ni raheela ta kyakyale da dariya mugunta tace za Ku gane kuskure Ku na bari na a gidanku don sai nayi muku barna da zata hadasa yaa Amar ya mayarda ni Kaduna da sauri ta nufi falon tasoma karewa falon kallo tana tunani da me zata fara........

Jeeddah Aliyu🌹🌹
[3:46PM, 10/01/2017] ‪+234 810 336 9936‬: [14/07 8:13 am] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

5⃣8⃣

Kaitsaye tadoshi kitchen ta bude dif freezer" ta zaro idanu tace cabdi aikin wani sai kallo, kalli yanda yaa Amar yacika freezer da naman kaji sai kace bai Sam zafin kudi ba ae kuwa nima yau zan wasa hakora na ta kyakyale da dariyar mugunta taciro kaji har gudu uku ta ajiye su huce tajuya tanufi dining area" ta budi Warmer's din ke ajiye bisa table tabe baki tayi hade da yatsine fuska ta dauki " fork" tasoma cin chip's tana yatsine saida taci Mai esarta ta ajiye fork tadaga warmer tajuye saura chip's din a kasa takara bude wata dayan warmer farfesu ne a ciki da sauri ta kauda fuskarta tasoma bin kowane sako da lungu na dining tana zubarda shi tagangaro har zuwa falo ko ina saida tayayafa masa miyar farfesu tanayi tana kyakyale dariya tana kamallawa tayi jifa da warmer tayi tsalle ta bugi stool ta tsage takara kwashewa da dariya tanufi "fridge" tana budewa ta washe hakora sakamako gani robobi "ice cream birjik ta kwaso manya-manya robobi har guda hudu tace na sha biyu na zubarda biyu ta nemi kujera ta hakince sai kace itace na'eema da kyar tashanye guda daya tabi saura uku din tadinga shafawa "tile's" sai da takarar da shi tass sannan tajefarda "empty roba ta koma kitchen tadaura tafasa kajinta tadawo falo ta kunna kallo tanayi tana addua'ar kada Allah yasa masu gidan su dawo da wuri sai tagama shagalin ta, har raheela ta soye kajin'ta tass Amar da na'eema basu dawo ba mangyada da tayi amfani da shi tajuye shi a kasan tile's din "kitchen" ta kinkime warmer" da ta zuba kajinta takai daki, tun daga kitchen, dining har izuwa falo sai da raheela ta hargitsa su sannan tanufi dakinta ta murza key ta kwaso "lollipop" ta haye gado tayi kwanciyar'ta, tana tsotsan lollipop tana murmushi domin tasan ba karamar ta'asa ta yiwa na'eema sai misali kar'fe 5:30pm Amar da na'eema suka dawo gida suna jefa kafafu a falon suka ja birki sakamako gani yanda falon'su yadawo tamkar na mahaukata, na'eema ta kalli yaa Amar cikin rawar murya tace yaa Amar kana kallo abunda raheela ta aikata koh"?
Amar yayi shiru kamar baiji abunda na'eema tafada, ba gani yadda yayi shiru batare da yace komai ba yasa tacigaba da fada wannan wulaqanci da me yayi kama"?
Ina zamana cikin kwaciyar hankali kaje kadauko mini annoba in kai za ka iya cigaba da jure iya shegen'ta ni ba zan iya ba dole raheela ta tattara kayan'ta tabarmin gidana, tun daga lokacin da raheela ta jefa kafar'ta a gidanan zuciyata take bugawa na nemi natsuwa da kwanciyar hankali'na narasa akan wane dalili zan cigaba da zama da ita lalle kanada bukatar zabi tsanani ni da ita dole ka zabi daya tana karasa zance tajuya, tanufi "bedroom" d'inta karaf idanu ta suka hasko mata kofar "kitchen" a bude kawai sai tafasa shiga dakin tanufi "kitchen" tana jefa kafar'ta tsantsi mangyada da ke zube a kasa ya kwashe ta sai akayi sama da ita aka yarbe ta kanta ya bugi "cabinet" tasaki razananiya qara da sauri Amar yanufi kitchen d'in na'eema nayi masa nuni da hannu wai kada yashigo Sam Amar bai fahimci inda ta dosa ba ae kuwa yana jefa kafar'sa dama gashi sanye da "cover shoe" da karfi tsantsi ya kwashe shi bai fadi a ko ina ba sai bisa ga na'eema kanta yaqara bugu "_tile's" da kyar Amar ya iya mikewa tsaye, ya taimakawa na'eema ta mike kowane su kayan jikin shi yadebi mangyada suna kaiwa falo Amar yasaki hannuta cikin tsanani zafin rai da konar zuciya yanufi bedroom d'in raheela yana murda "handle yaji kofar a rufe cikin yanayi na Wanda zuciyarsa take tafarfasa yafara dukan kofar hade da kiran sunan'ta.....
[14/07 4:08 pm] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

5⃣9⃣

Raheela na jin sa tayi biris da shi sai ma tacigaba da tsotsan "lollipop dinta Amar yakara harzuka yace na rantsi raheela in baki bude kofar nan ba in na kamaki sai nayi miki illah.
Raheela ta tsintsire da dariya ta sauko daga bisa gado tanufi bakin kofa ta rami "key ta leka tace yaa Amar kanaji na kuwa"?
Da sauri Amar yace ki bude kofa nace, raheela ta galla masa bazawara harara kamar tana gani sa tacigaba da cewa in kana yiwa Allah" yaa Amar in ka kamani karka barni da raina ka yanka ni.
Amar yakara hasala sai cika yake yana batsiwa raheela ta kyakyale da dariya daga bisani tace da wannan huci da ka keyi dama zuwa kayi kataya matarka aikin gyara barna da nayi, Amar ya girgiza kai yayi kyaci yajuya ya koma falo tarar'da na'eema tana shara yaja tsoki yanuna ta da yatsa yace duk laifi ki ne na'eema, a fusace na'eema tace da nayi me"?
Sai da ya watsa,mata harara sannan yace da ki ka hana akawo miki 'yar aiki kin dauki baqin kishi kin azawa kan'ki sai kace ke kadai ce mai miji"
Tsanani baci'n rai yarufe na'eema tace tuni na fahimce ka mayarda ni juji duk lokacin da ka debo shara akaina ka ke juyewa, in har raheela tafi karfin'ka bazaka iya daukar mataki akanta, ni zan iya domin duk ranar'da takara kwatata mini wannan dabbaci a gida sai na karya ta.
Amar yayi murmushi domin yasan burga ce kawai irin ta na'eema ko jiya da taki raheela, ta zauna lafiya sa'a ce ta taka, shi kanshi yayi mamaki yadda raheela takasa ramawa, ya tabe baki batare ya tamka mata ba ya haura sama yayida na'eema ta bishi da mugun kallo.

A WASHE GARI******

Amar yakai raheela school saida ya tabbatarda ta zama cikkaka daliba sannan yanufi "hospital" ranar farko da raheela tafara zuwa "school" tayi qawa mai suna Ayshat kabeer, "course" din su daya wannan yasa suka shaqu cikin dan kankani lokacin, duk fadi garin abuja raheela batada qawa in ba Ayshat ba, duk da kasancewar Ayshat ta girmewa raheela kuma gata matar aure amma a hakan suke qawance su.
Raheela tadawo daga "school" ga gajiya ga kuma yunwa da ta kwaso da yake Ayshat ce ta mayarda ita gida
ta balle murfi mota tafito a kasalace tace besty sai gobe in mu hadu, ayshat tayi murmushi tace ke dai kinshiga uku besty Sam bakya da hankuri yunwa, raheela ta ya mutsa fuska tace inada gaskiya ayshat yunwa ba'a bar hankuri bace nantake zata yiwa mutum illah ayshat ta kyakyale da dariya taja motar ta tayi gaba, yayida raheela ta bude kofa tashiga cikin gida Joseph da driver umma hajara na zaune a baki gate" drivern na gani raheela yafara washe hakora wanake gani kamar dan audu"??
Nine raheela mu same Ku lafiya"?
Lafiya qlau dan audu kai da wa ka zo ne"?
Umma hajara ce na kawo, ido raheela ta zaro tace umma hajara fa"?
"Eh dan audu yafada yana kallo fuskar raheela"
Yayi kasa da murya yace inaso nayi wata magana da ke raheela amma dan Allah ta kasance sirri a tsakani mu raheela tayi shiru tana kallon sa daga bisani tace inajinka dan audu'
A haqiqani gaskiya raheela yau na tsorata da abunda kunnuwa
na suka jiyo mini, kamar yadda nasaba kai hajiya hajara wani kauye da ke Niger state wajen bokanta yau ma hakan ce ta kasance baya nayi mata rakiya a bakin kofar gidan bokan har na juya sai na tsince kaina da son jin abunda yakawo ta wajen bokan sai na labe, kamar daga sama naji tace boka duguzuu so nakeyi raheela ta mutu ko ta haukace domin tana daf da ta rusa rayuwar 'yata, tun lokacin da dan audu yafara magana raheela ta shiga firgici hade da rudani ta nemi natsuwarta tarasa sai gumi yake fita daga sasssa jikinta.......

Jeeddah Aliyu🌹
[3:47PM, 10/01/2017] ‪+234 810 336 9936‬: [20/07 3:50 pm] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣1⃣

Cikin rawar murya raheela tace laifi me na yiwa umma da take yunkuri gani bayana"?
Ni ma bansaniba raheela amma duk abunda nafada miki babu ,karya ko kazafi a cikin'sa domin ina da sheda Mai karfin gaske ba ma shi kadai ba har asiri ta karbo Wanda zai yi sanadi da Amar zai manta da ke da iyayye sa tabbas hajiya hajara batada imani domin asiri da boka yabata Wanda za ki haukace ko ki mutu cewa yayi ta nemi Sabon kabari ta binne asiri a ciki za ki mutu in kuma ta binne a tsohon kabari za ki haukace, na rantsi raheela bantaba shiga tashin hankali da firgici irin na jiya, da sauri na bar jikin bukka da na labe na nufi kofar gida, bayan kamar mintuna biyar da fitowa ta, sai ga ta tafito muka nufi Inda nasaba parking d'in mota bayan mu dauki hanyar dawowa garin Kaduna sai take cewa da ni dan audu akwai wani aiki da zan baka zan kuma baka naira dubu hamsi da ina fatar baza'a samu matsala ba domin nasan za ka iya.
Har ta dasa aya a zance ta zuciya ta, tana buguwa da karfi domin na tsorata da lamari ta, nace bakida matsala hajiya amma wane irin aiki ne"?
Kaitsaye tace da ni wannan abun nakeso ka binne mini shi cikin sabon kabari kuma banaso a sami kuskure, karka sake kasaka a tsohon kabari a sabo za ka binne, nace to hajiya angama na mika hannu tabani asirin, har mu ka eso gida ina tunani ta yadda zanyi na kubutarda ke daga wannan halaka saboda na fahimci bataso ki haukace tafiso ki mutu, wallahi raheela daren jiya banyi bacci ba sai kuma gashi yau tace na kawota abuja, wannan ya tabbata min da cewa za ta kawo wa na'eema asiri ne, tasakawa Amar cikin abinci, hannu shi ya zura cikin aljihu rigar shadda da ke jikinsa yaciro wata 'yar batta mai lullube da fatar kura ya mikawa raheela, jikinta na rawa ta amsa yayida dan audu yacigaba da cewa wannan shine baqin asiri da akayi miki yanzu kuma sai kiyi kokari ki ruguza Wanda aka yiwa Amar tasaki ajiyar zuciya daga bisani tace, na gode dan audu insha Allah zan yi iya kokari na nagani hakar' su bata cima ruwa ba, dan audu yace ba komai raheela ae yiwa kaine ki yi maza ki shiga gida kada tsatsayi yasa tafito tagani tare da ke ae kuwa da sauri raheela ta nufi cikin gida har tayi niyar ta bude kofar falo tashiga sai kuma tafasa ta bi kofar baya wance ake shiga falon Amar tasoma sanda kamar barauniya ta leqa falo na'eema saida taga wayam alamar basa cikin falon suna "bedroom" da sauri tanufi " window" dakin na'eema ta leqa na'eema da umma hajara na zaune bisa gado sai faman zuba sukeyi muryar umma ce ke tashi ki tabbata ki zuba masa magani nan domin dan asarariya ya tabbatar mini cewa matukar Amar yaci magani nan hatta da uwar da ta haife sa zai manta da ita, ballatana wata raheela banza, bazara na'eema tasaki murmushin jin dadi tace karki ji komai umma naa yau d'inan zan cika aiki, umma hajara ta Mike hade da daukar "handbag" d'inta tace ni zan wuce banaso Amar ya dawo yatararda ni gidanan, na'eema tace to umma mu je na rakaki, da sauri raheela tashige cikin labule ta boye saida taga fitar su sannan tafada dakin na'eema tasaki katuwar ajiyar zuciya sakamako gani leda baqa bisa "dressing mirror" hannuta na rawa tadauke leda d'in tafice dakin da sauri ta bi kofar da tashigo tafita tana kallo driver yaja mota suka fice daga gidan akan idon'ta na'eema tashiga gida saida ta dauki tsawon dakika biyar sannan tashiga cikin falo tayi sallama mtsss na'eema taja tsoki hade da watsawa raheela kallon banza daga bisani ta kyakyale da dariya cike da nishadi ta haura sama, yayida raheela ta bita da kallo a zuciyata tace "Allah zai kareni daga sharri Ku.
Tun lokacin da raheela tashiga daki take kwance duk yunwa da takeji nemanta tayi ta rasa, sai faman tunani mafita takeyi nan take Ayshat kabeer tafado mata a rai tabbas Ayshat ce zata warware mini wannan matsala.
[20/07 7:22 pm] Jeeddah aliyu🌹: 🍆🍆🍆🍆MIJIN 'YAR UWA TAA🍆🍆

💕love story 2016💕

{Part 2}

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

6⃣2⃣

Domin banida wata abokiyar shawara duk fadin garin abuja da yawuce ta, ya zame mini dole na kwancewa ayshat wannan sarqaqiya ko zan sami mafita.
Tabangare na'eema kuma bata qara tunawa da wani zance magani ba, saida ta kamalla girki ta dare da gudu tafada " bedroom" d'inta saidai kash domin duk Inda take tsanmani zata ganshi ta nema tarasa taja dogon tsaki mai cike da jin haushi a baiyane, tace ba komai don wannan yabata ba komai bane dama raheela ce babbar matsalata kuma dan audu, yace yacika aiki akanta cike da gamsuwa tajuya ta koma "kitchen"
Tun lokacin da raheela tashige d'aki bata qara fitowa ba, har akayi sallah magarib da esha'i tana d'aki zamanta.
Amar da na'eema na zaune a falo Amar kasa hankuri saida yafurta abinda ke ci masa tuwo a kwarya ta hanyar cewa, na'eema yarinya nan lafiya take, nasaba dawowa daga "office na tararda ita zaune a falon nan sabani yau ko motsinta banji ba"?
Na'eema ta yatsine fuska tace, oho ni bansaniba, sai kaje ka duba in tana raye"
Tsantsan mamaki ya baiyana akan fuskar Amar yace "what's nonsense" na'eema me ki ke

17 / 31