Author : NIMCEY SARAUTA Category : Romantic Hausa Novels
sannan yasa hannu ya jawota zuwa jikinsa,parcing mirrow yayi sannan yasa hannu ya tallafi haɓarta ido ta ɗago tana kallon cikin idonsa ta madubi wanda gaba ɗaya ya sauya zuwa red.
Amma kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki sosai fuskarsa ta nuna hakan kasan cewarsa bai fiya magana da kuma dariya ba.
Idonsa ya mayar ƙasa yana kallon wani wajan,itama wajan take kallo ɗan turo ƙaramin bakinta tayi gaba ganin gaba ɗaya brest ɗinta yake kallo wanda ta manta ta cire rigar"stop looking"taɓe baki yayi sannan yasa hannu yana sosa kansa yace.
"kee ba kijin kunya ne"rolling eyes ɗinta tayi tace"tame"baice komai ba yayi mata nuni da idonsa zuwa manyan brest ɗinta,sajen face ɗinsa ta shafa tace"i think i'm ur wife ko any how na zauna a gidana ls not a problems,am right ta faɗa tana janye jikinta daga nasa.
Ka faɗa ya ɗaga mata alamar bai sani ba,juyawa tayi ta nufi badroom tana waƙar wiskid cikin zazzaƙar muryarta,hankalinta kwance tama manta ta wani maciji a cikinta😝.
Tana shiga yayi saurin ficewa a ɗakin tare da zura hannayensa cikin aljihun wandonsa,a parlour ya tarar da Najwa kwance akan sofa tana rusar kuka ɗan tsaki yaja domin ya tsani kuka,har zai huce sai kuma ya tsaya yana kallonta kafin ya motsa bakinsa kaɗan yace.
"mene?"ya faɗa gana kallon T.V wacce take kunne tana yi ɗaya ji yayi ta riƙeshi ta baya tana kuka,hannu yasa ya zagayo da ita zuwa gabansa tare da kallon cikin idonta"what wrong?"saman faffaɗan ƙirjinsa ta faɗa tace"honey cikina kemin ciwo tun safe"ok what about medicine?ya tambaya yana cilla kwayar idonsa cikin nata,a karo na farko da wata kunyarsa ta kamata,ga wani kwarjini da yayi mata kasa magana tayi sai kasa da tayi da kanta.
Gyara tsaiwa yayi sannan yasa remote ya kashe T.V data dame shi da ƙara dan sam baya san haya niya.
"kije ɗaki zanzo" yana faɗin hakan yasa kai ya fice daga cikin gidan,daret part ɗin Hajiarsa ya nufa a hankali yake tafiya yana ɗan jinjiga kansa sabida yau yana cikin farin ciki mara misaltuwa,a hankali laɓɓansa ke motsawa ya nayin yadda yake juyasu shi zai tabbatar maka da waƙa yake,sautin waƙarsa ce ta fara fituwa ba tare daya sani ba sabida enjoying waƙar da yake,dariya nayi sosai lokacin da naji waƙar da yake.
"ashe da rai nake sonki jaruma bada zuciyata ba,komai ruwa da iska akanki baza na daina kewa ba"
Eyee soyyaya daɗi ba'ai waƙar a wajansu ba sai a nan"juyowa yayi yaga mus'ab wanda da wowarsa kenan,murmushi yayi masa yace"welcome back" ya faɗa yana ɗan hug nasa.
Jerawa sokai har zuwa cikin flat ɗin nasu,a parlour suka tarar da Hajia tana shirin zuwa kan darning domin yin luch.
Sakin hannun Mus'ab yayi sannan yayi saurin ƙara sawa wajan Hajia,shigewa jikin Hajia yayi tare da ɗanyi mata raɗa a kunne,saurin ɗagoshi tayi daga jikinta tana murmushi tayi sannan ta shafi sumar kansa tace"masha Allah naji daɗin hakan Allah ya bata lafiya ita da abinda yake cikinta Congart Dr"
Hannu yasa yaɗan rufe idonsa ba tare daya amsa ba,"uhm nifa bana gane wannan kus² ɗin naku nima aban nasha"cewar mus'ab.
"hh zai zama Daddy very soon,kaga saiya dai nayimin wannan shagwaɓar nasa kaima ya baka waje"
"wow amma nafi kowa farin ciki kace nima zan zama Daddy,wai wace Mummyn Najwa ko beby?"
Najwa kuma?no Bebyn hajia yace"
Ahmad ya bashi amsa lokacin da yake ƙara sawa wajan darning.
"ohh kai ba bebynka bace ko"hajia ta tambayeshi...taɓe baki yayi tare da ɗauke kai yace"tukunna dai" ya faɗa kai tsaye lokacin yana kafa coffee a bakinsa tare da danna wayarsa.
"Allah ya kyauta anaso ana kaiwa kasuwa,Amma dr nayi mamaki a matsayinka na babban likita ka kasa fahimtar beby nada juna biyu,na daɗe da fahimtar hakan nayi maku shirune sabida naga bata wani laulayi amma idan ka lura da yadda take yawan shan Chocolate ice cream fresh milk da holandia,bata iya cin komai fa dan gane da abinci saidai tasha farfesun kifi amma duk ka kasa fahimtar hakan inajin cikin beby ya kusa tafiya wata na 5"
Zaro ido yayi waje yana mamakin hakan dan ya kamata ace ya fahimta amma ya gaza gane komai.
Murmushi Mus'ab yayi sannan yace"wai ya kaga idon beby idan taji tana da ciki".
Tsayawa tayi cak tare da fashewa da kuka domin taji maganar mus'ab da gudu tazu wajan tana kuka.
"na shiga uku Hajia shikenan zan mutu ko nayi yayyun fitsari😅.
Guys more Comments more typing,page ɗin gaba ku shirya masa😍
~SARAUTA👑~
*🤱🏻RAINO ne SILA*
_ADOPTION IS THE REASSON BEHIND_
*NIMCY LUV*
~S@r@ut@👑~
follow on Istagram
Nimcyluv
Follow on wattpad
Nimcyluv
*~DEDICATED~*
~to my luv REAL QUEEN😍🥰🥰💋AMIR ROCKSTAR back soon don't miss it~
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*69-70*
Zaro ido Hajia tayi tana riƙe bakinta sabida dariyar data tasu mata,sosai beby take kuka tana maƙale jikin hajia dan ita mantawa take sirikarta ce.
Hannunta hajia ta kama tana murmushi tare da faɗin"kee rabu da Mus'ab he is joking yana maganar duk sanda kika samu ciki yana maki tunanin rainon yaran.
Kumbura baki tayi tana goge hawayen fuskarta,zaunar da ita hajia tayi akan kujera sannan tace"yau kuma me za'aci?"no bancin komai na kushi"ta faɗa tana kallon warmers ɗin da suke akan darning,ɗan ya mutsa face tayi tace"hajia kamar ƙamshin kifi na keji"murmushi kawai hajia tayi tare da jawo wata warmer a hankali ta buɗe tare da jan wani plat ta fara zubawa beby farfesun kifi na sukunbiya wanda yaji kayan yaji,tunkan hajia ta kama zuba mata tayi saurin janye plat hannu baka hannu kwarya ta faracin farfesun kifin su duka suka zuba mata ido musamman Dr Ahmad Tijjani Asasa,sai yanzu yaga sauyin da tayi ta ƙara ƙiba da kuma haske,hips ɗinta sun ƙara girma musamman brest ɗinta gana ganinta kaga mai juna biyu,wani killer smile yayi yana jin wani daɗi na ratsashi zuwa nan da wata shida zai zama Daddy abinda ya keso ya samu dole yayi sadaka ga almajirar domin a taya beby'n hajia da addu'ar samun lafiya.
Wani hawaye ne ya fara zuba fa gefen idonsa,fakar idonsu yayi yana goge hawayen dole yayi farin ciki domin wannan kyauta ce wanda ba kowa ke samu ba.
Lumshe luntsuma² idonsa yayi a ƙaro na farko da yaji soyyayar beby ta tsarga masa a cikin zuciyarsa,kallon hajia yayi yace.
"Hajia zanje Kano ta jet dubiyar Yarima Sudais"da sauri beby ta ɗago kai tana kallon tare da mai²ta kano,ji take kamar tasan wani acan hannu tasa ta dafe saitin zuciyarta da taji tana buga mata,haka nan taji kamar tayi mantuwa da abu mafi muhimmanci a rayuwarta,a hankali ta tashi zata bar wajan"aa har angama cin kifin duk wannan zumuɗin"cewar mus'ab turo baki tayi tare da kallon A.J tace"Yah..ya"bakinsa yaɗan motsa daga gefe sannan ya juya ya kalli mus'ab wanda yake sheƙa dariya abunsa harara ya watsa masa yace.
"matata ba sa'ar ka bace ka shiga hankalinka"hhh tab muma dai zamuyi aurannan koma samu masu tare mana,jinjina kai kawai A.J yayi baice komai ba.
Beby ce ta miƙe tayiwa hajia sallama sannan ta kama hanyar zuwa flat ɗinsu,shikam A.J kan sofa ya koma yana tunanin tafiyarsa Kano ga kuma zaɓe na gama ya tunkaro da wannan tunanin bacci yayi gaba dashi.
A parlout ta tadda najwa a zaune tana kallon film ɗin THE VOW wanda ake haskawa a zee wrold,"sannu da hutawa"murmushi najwa tayi tace.
"yauwa ƙanwata zo kiji mana"a hankali beby ta tako zuwa kujerar da take parcing najwa ta zauna tace"All ears"wani murmushi tayi tace "kinyi kyau dole honey ya gigice,no bama wannan ba daman wani magani zan baki na gyaran jiki kinsan duk wata matar aure indai tana son farantawa mijinta,hakan tasa nace zan baki sabida zaman tare kingane ko"jinjina kai kawai beby tayi sabida jikinta yayi weak taji tana missing wani abu babba"ok anty ina jira"aa sai gobe za'a kawo zanyi maki magana.
Ok nagode
Da wannan ta tashi tayi shigewarta bedroom ɗinta yau ko ɗakin A.J bata nufa ba.
Washe gari tunda safe A.J ya gama shirinsa na farar shadda wanda akaiwa ɗinki da baƙin zare sai zabga ƙamshi yake anyi masa ɗinkin riga da wando da kuma babbar riga,baƙar hula ya murza tare da baƙin takalmi with black bluetooth,wayarsa ya ɗauka mai ƙirar iphone 11 pro ya shiga TIKTOR ya fara vedio,yana vedio yaji anyi hug ɗinsa ta baya kafin ta zagayu ta gabansa ta fara dariya dimples ɗinta na lumawa,sanye take da abaya pich colour with black stone tayi rolling kanta da vail ɗin abayar,hancinta yaja yana murmushi a haka ya ƙarasar vedio yayi postin nasa.
Kallonta yayi murmushi yace"zan tafi"ɗan kwaɓe fuska tayi yah..ya zani nima pls.
Hannunta yaja sukai parlour a nan suka sami najwa tasha kwalliya cikin duguwar riga ta shadda sai ƙamshi take,dukkansu ya kalla ganin ɗaya fara tas ɗaya kuma chocolate murmushi yayi yace Allah mai iko.
"nizan huce"shine Abinda yace"Allah ubangiji ya kiyaye ya hanya ya kuma dawo dakai cikin amincinsa"jinjina kai yayi yana jin daɗin Addu'ar ta beby ɗan hug ɗinta yayi sannan ya manna mata peak a lips ɗinta,kallon najwa yayi wacce take tsaye tana murmushi hannu ya miƙa mata alamar jikinta na rawa ta isa gareshi tana zuwa ta shige jikinsa.
Beby na ganin haka tayi saurin ficewa wajan compund na gidan tana goge hawayen face ɗinta.
Bayanta ya bubbaga sannan ya shafi kanta,zare jikinta yayi daga nasa sannan yasa kai ya fice daga parlour'n,yana mamakin yadda najwa bata iya ce masa adawo lafiya ba.
"mommy twinst ya akai"juyowa tayi suka haɗa ido tace"mommy kuma?"ta faɗa tana riƙe hannunsa,taɓe baki yayi su kaci gaba da tafiya wajan sabuwar motarsa.
"ina son yara fiye da tunaninki nasan wata rana zaki haifa mani dat why nace maki mommy ok"shuru tayi ba tace komai ba key tasa ta buɗe motar tace"enter"kallonta yayi yace jeki drever zai kaini airport"uhm"kawai ta faɗa tana zama a side ɗin drever shiga yayi ɗaya side yana mamaki a ransa bai gama tunani ba yaji ta yiwa motar key ta fara janta a hankali horn tayi mai gadi ya buɗe mata get ɗin gidan.
Hancin motar da danna waje sannan ta fara dreving cike da nutsuwa,mamaki ne ya cikashi yaushe ta iya mota waya koya mata?amma baice mata komai ba sabida baison dugwan zance.
***
Ya isa kano lafiya kuma yaji daɗin zuwansa,domin yaga farin ciki a fuskar Yarima Sudais duk da kasan cewar baya magana amma minti kaɗai saiya kalli fuskar Ahmad yayi murmushi ko kuma ya kamu hannun Ahmad yana matsawa,ba ƙaramin tausayi Yarima ya bawa A.j ba.
Haka ya zauna a wajan har zuwa yamma sannan ya fara shirin tafiya gida.
Motar masarauta aka bashi zuwa airport inda za'a tura dugari ya ɗaukota zuwa jimawa.
Duk iya ƙoƙarinsa na kaucewa abinda yake hangowa amma abin yaci tura addu'a ya shiga yana yarfar da gomin face ɗinsa motarce tayi kan wani abu da yake tun karo A.J kafin yaji anyi ƙara nan motar ta samu tsayawa.
Da sauri ya kashe motar ya fito yana zuwa ya zaro ido ganin wata mata kwance a ƙasa cikin jini.
***
Bayan tafiyar A.j beby ta koma gida cike da kewa,wajan karfe tara na dare babu Ahmad haka tai ta zuba ido kasan cewar yace mara karfe 7 zai dawo gida.
Ƙofar ɗakinta aka turo cikin sauri ta miƙe tana tunanin A .j ne sai taga najwa hannunta ɗauke da wata farar ruba.
"gashi yanzu aka kawomin nima nawa yana ɗaki,yana da kyau kisha kafin mai gidan ya dawo"
Ok nagode"never mind ta faɗa tana juyawa,kamar karta sha sai kuma tace"bari dai nasha naga gyaran da take magana akai"murfin robar da ɓalle sannan ta kafa a bakinta ta fara sha,tasha babu laifi sannan ta rufe rubar da ajjiye a gefen bed ɗinta.
Wajan 20min tana kwance kafin taji wani mahaukacin ciwo ya tasu mata kuka ta fara tana riƙe cikinta,zabuwa tayi akan bed ɗin sannan ta fara birgima akan carpet ɗin ɗakin,wata ƙara ta saki ganin jini nabin ƙafarta idonta ne ya fara rufewa sabida jinin take zuba daga ƙasanta,kafin idonta ya lumshe numfashinta ya tsaya..
More Comment pls
~SARAUTA👑~
*🤱🏻RAINO ne SILA🤱🏻*
_ADOPTION IS THE REASSON BEHIND_
*NIMCY LUV*
~S@R@UT@👑~
Follow on istagram
Nimcyluv
Follow on wattpad
Nimcyluv
*~DEDICATED~*
To my fans wannan shafin na mosaya nane wasapp,facebook,istagram,snap chart,Tictor,telegram🥰gaba ɗaya masoya na wannan media dana ambata sadaukarwa ne gareku.
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*71-72*
No edit.
Jini ne kawai ke fita ta ƙasanta wanda yake gudu sosai akan carpet ɗin bedroom ɗinta.
Najwa na fita daga ɗakin beby ta daka uban tsalle tare dayin wata shewa ita ɗaya ta fara rawa a tsakiyar babban parlour wanda yake ma rarraba da flat fin kowannensu,hannu tasa ta riƙe waist ɗinta sannan and she stand talking,"wannan shegen cikin da kowa yake ƙaunarsa nasan duk ranar da yazu duniya tuni lokaci na yayi,yanzu nayi maganinta idan wancan uban rawarkan yazu saita gaya masa abinda tasha har cikin ya zube nasan daga nan zai sallameta tunda ta nuna mata sonsa da zuri'a"
Dariya ta ƙarayi tare da juyawa tana faɗin"bani da damuwa ko guda cikin raina..saurin ja baya tayi tare da gwalo ido sabida ganin A.J da tayi ya fito daga ɗakinsa,murmushi ya sakar mata tare da faɗin"sannu da rawa"ɗan murmushi tayi kaɗan sabida gaba ɗaya a tsurace take kallon idonsa tayi wanda ya gama komawa red ga yadda jijiyoyin kansa suka fito sabida azaba.
Wajansa ta ƙarasa tare sunkuyawa tana kallon cikin idonsa tace"hope lafiya kake naga mood naka ya sauya"gaba yayi tare da faɗin"A dey fine,kawai na kaɗe wata mata ne abun tausayi"yana faɗin hakan yayi gaba tare da nufar ɗakin beby gaba ɗaya baiji motsin taba.
tura ƙofar ɗakin yayi a hankali yana shiga ya kalli bed yaga babu kowa,hanyar toilet yabi ko wanka take tsayawa yayi cak sabida karo da yayi da abinda ya gigita shi abu mafi muni cikin abubuwan da suka faro dashi,rana mafi baƙin ciki da kuma takaici a cikin ranakun rayuwarsa.
Idonsa ne ya fara fitar da kwalla mai zafi kana ganin Ahmad kasan yana cikin mawuyacin hali,ko mus'ab zai wahala yace A.J ya taɓa kuka a gabansa amma yau Ahmad da kansa ke zubar da hawaye tabbas wannan abun ba ƙaramin baƙanta masa zuciya yayi ba.
Da sauri ya miƙa hannu ya saɓi beby wacce ke kwamce cikin jini,gudu² sauri² ya fara haɗawa,daret wajan motarsa ya nufa yana zuwa ya buɗe motar sannan ya shimfiɗe beby wacce take kanwar matacciya.
A guje yaja motar zuwa babban asibitiɓ dake garin abuja wanda ya kasance mallakin Dr Ahmad Tijjani Asasa ne.
Akan idon najwa A.J ya fita da beby,wani mugun murmushi ta saki tare da faɗin"yaro baisan wuta ba saiya taka,shegiya ƴar tsintuwa Allah yasa daga nan ki mutu kowa ya huta".
Cikin makirci ta fita a guje zuwa flat ɗin hajia domin ta shaida mata abinda yake faruwa,gaba mata ganin gabanta sabida farin cikin da take ciki yau komai zaizo mata da sauki.
Wayyo rashin yasa najwa ta daki wani ƙarfe nan take ta faɗin ƙasa,yayinda cikinta ya sauka akan wani ƙaton dutse har saida jini ya fita ta hancinta nan take ta suma a wajan babu numfashi.
Wajan 30min tana kwance saman dutsen babu wanda yazu,a hankali hancin motarsa take shigowa cikin gidan,tun daga nesa yake hango mutum a kwance fuskar mus'ab ɗauke da mamakin wanda yazu waje ya kwanta cikin sauri yayi parking motar.
Tattara riga yayi yasa gudu ganin najwa ce kwance saman wani ƙaton dutse wanda yake ta tunanin ɗaukeshi Allah bai bashi iko ba.
Yana zuwa yasa hannun ya janyeta akan dutsen nan idonsa ya sauka akan hancinta wanda yake fitar da jini,da sauri yasa hannu cikin wandonsa ya ɗauka wayar yayi darling number A.J har sau biyu amma bai ɗauka ba,nan ya kira hajia ya shaida mata dukkan abinda ya gani,umarni ta bashi yasa najwa a mota gata nan fituwa.
5min hajia ta fitu cikin sauri tare da salati a bakinta tana zuwa ta fada mota nan mus'ab yaja motar da gudu yayi waje kasan cewar get a buɗe yake.
Jikin sane ya fara rawa lokacin daya gama tabbatar da urbon ɗinsa ya zube,zabewa yayi a ƙasa tare da kifa kansa a tsakin laps ɗinsa ya fashe da kuka,ta cuce shi ta cuci rawarya tayi masa abu mafi muni da kuma baƙin ciki baisan matakin dazai ɗauka akanta ba.
Turo ƙofar ɗakin da akai shine ya sashi saurin goge hawayen face ɗinsa sannan ya ɗago da kansa a hankali nan yayi tuzali Hajia tayi jingine a jikin bangon ɗakin,bayanta kuma Mus'ab ne tsaye idonsa ya sauya yayi red.
A kasalance ya tashi yayi wajan hajia yana zuwa ya faɗa jikinta yana sauke ajiyar zuciya,kansa ya ɗago nan suka haɗa ido da Mus'ab ɗan juya bayan hajia yayi inda ta koma baya suna parcing juna da mus'ab shi kuma ya koma gaba inda ya bawa mus'ab baya,sai lokacin ya samu damar fitar da wasu hawaye masu zafi,saukar hawayen taji a shoulder ɗinta tayi saurin runtsa idonta ta najin wani ciwo a ranta hannu tasa ta ɗan bubbuga bayansa tare da faɗin.
"innallaha ma'ar sabirin"ka ɗauki wannan kasama zuciyarka komai na Allah yana da iyaka daman Allah ya riga daya rubuta hakan wannan cikin bazai taɓa zuwa duniya ba,idan ka yarda da Allah kuma ka yarda ƙaddarar inason kayi hakuri kada ka ɗauki kowanne hukunci akanta itama taji da abinda yake damunta,yara kuma zaka samesu masu