RAINO NE SILA COMPLETE HAUSA NOVELS BY NIMCY LUV.txt

Author :  NIMCEY SARAUTA Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 16

39K to 42K   out of 46.3K words

Albarka kada kayi gaggawa.
Ajjiyar zuciya ya sauke tare da zare jikinsa yana ɗan murmushi.
"soo bad bro na Allah ya kawo masu albarka"cewar mus'ab.
Hajia ce ta kalli A.J tace"Ahmad yanzu wannan matar daka kaɗe naga taji sauƙi yaya za'ai da ita?".
Lumshe ido yayi ya najin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri almost 5min sannan ya waro idonsa akan Hajia yace"zata bimu gida,hajia bata da kowa fa"ayya Allah sarki zanso na ganta.
Wai me kukazu yi a hospital haka?numfashi hajia taja kafin tace"munkawo najwa ne,bayan fitarku ta samu tsautsayi,babban tashin hankalin ance mahaifarta ta fashe ba zata taɓa samun haihuwa ba.."sai kuma ta haɗe ɗai tace"Ahamd ashe ni hauka na nake ko,wato rayinyar haryau bata da ƴanci a wajanka,dr ya tabbatarmin da haryau najwa budurwace wannan wanne irin abu ne,babu shakka hakkinta shine ya shafi shibewar jikin beby,ita kuma beby bata da hakkim najwa shiyasa Allah ya saka mata da sakayya mafi muni domin rashin haihuwa babban tashin hankali ne,kuma ni ban aura makasu domin wata rana na raba auran kwara ka gyara domin itama matarka ce"takai ƙarshan maganar rai ɓace.

"am sorry hajia"shine kawai abinda ya iya faɗa,kafaɗa ta ɗaga alamar ita babu ruwanta duk da itama rashin cikin beby yana matuƙar damunta"muje ka kaini wajan waccen baiwar Allah inajin tausayinta"ok kawai ya faɗa sannan ya juya zuwa wajan beby wscce take kwace akan bed ɗin marasa lafiya tayi haske chocolate skin ɗinta ya ƙara fituwa,yana zuwa ya manna mata kiss a lips ɗinta sannan ya shafa kanta cikin sassarfa yabar ɗakin.
Yana fituwa ya shiga wani ɗaki wanda yake parcing na beby,baya suka rufa masa zuwa ɗakin.
Tura ƙofar ɗakin yayi a tsaye ya ganta sosai kunnansa yake ɗauko masa sautin kukanta,gaba ɗaya suka tsaya suna kallonta kasan cewar ta juya masu baya basa iya ganin fuskarta.
A hankali Ahmad ya motsa bakinsa tare faɗin"Assalamu Alaiki" a ɗan razane ta juyo domin ba taji shiguwar mutum ba sai sallama taji.
A razane hajia ta shiga nuna matar da hannu itama kallonta tayi,kafin hajia ta fasa ƙara tare da faɗin.
"Khaleesat"



Pls ba sai kunyi Comments na yafe,domin ba'aimin wanda zai wanken zuciya kamar yadda nake maku kawai zance maku ngd maku sosai bisa abinda kukemin.

Wattpad ina gdy sosai aci gaba da vote and Comments pls



~Sarauta👑~


*🤱🏻RAINO ne SILA🤱🏻*
_ADOPTION IS THE BEHIND_

*NIMCY LUV*
_S@r@ut@👑_

Follow on istagram
Nimcyluv
Follow on wattpad
Nimcyluv




*STOP INTERUPT..🤚🏻*



*73-74*


Cikin ƙaraji da fitar hayyaci khaleeysat tace"Anty lubna"sai kuma ta tafi luu zata faɗi A.J yayi saurin tare ta faɗa jikinsa babu numfashi,kan bed ya ɗura ta tare da gaggawar juna mata drip a jikinta.
Kallon Hajia yayi wacce take share hawayen fuskarta,sosai ta shiga halin kunci da damuwa,zuciyartace ta shiga bugawa da ƙarfi runtsa idonta tayi tana jin kamar yanzu ne komai yake faruwa.
"wai Hajia kinsan tane?"Mus'ab ya faɗa yana riƙe hannun Hajiar,numfashi ta sauke sannan ta fara tafiya zuwa gadon da khaleeysat take hannu tasa ta shafi kyakkyawar fuskarta tace"long story ne wanda ya ruguza rayuwar family namu za kuji komai bari muje gida"ok Allah ya shige mana gaba"cewar Mus'ab.
Jinjina kai kawai A.J yayi ba tare daya ce komai ba,numfashi yaja mai ƙarfi tare da zura hannayensa cikin aljihun wandonsa.
Kai ya shafa bai ƙara kallon kowa ba yasa kai ya fice daga cikin ɗakin asibitin.
Daret room ɗin da zai sa dashi da ɗakin Anusha ya nufa,ɗan tsayawa yayi kamar me tunani sai kuma ya lumshe idonsa,a hankalin yasa hannu ya murɗa handle ɗin jikin ƙofar ya tura nan take ƙofar ya buɗe.
Shiga yayi ya jin gina bayansa a jikin ƙofar yana furzar da numfashi mai zafi tare da lumshe gajiyayyun idonsa,almost 5min ya ɗauka ya sauraran heartbeat ɗinsa dake tafiya da sauri.
Manyan idonsa ya ware a kanta sabida motsin da yaji,a zaune ya ganta ta zuba masa manyan idonsa irin na mage,yayinda gashin kanta ya wargatse ya samu damar sauka akan shoulder ɗinta.
Kallonta yake babu ko ƙiftawa,kaiya ɗan sosa tare da mazawa kamar bashi ya gama kallonta ba.
Murmushi tayi kaɗan hakan ya bawa dinmples ɗinta damar motsawa sam bazai iya sauya halinsa ba akan waskewa da abu,ya nuna kamar bashi yayi ba,tun kallon farko da tayi masa tasan ba haka ta saba ganinsa ba duk da cewa bama abucin dariya bane.
Zama yayi kusa da ita harta kai shoulder su na gogar ta junansu,so yake ya tambayeta ya jiki amma bakinsa yayi masa nauyin lips ɗinsa ya gagara buɗewa.
Dariya tayi tace"yaya jikin naki? Hope evertin is fine?"haka kakeson cewa ko?,jinjina kai yayi yana shafa kwantaccen sajensa mai kyau wanda yake zuba gyalli.
Murmushi tayi ta ƙara cewa"don worry i'm ok kamar banyi ciwo ba haka na keji"hannu yasa ya danna dimple ɗinta na side ɗinsa wanda ya loma sosai yace"thank God beby is ok".
Kansa ya sunkuyar ƙasa yana tunanin yayi mata bayanin cikin nata koya rabu da ita,ɗan sunkuyowa tayi ta leƙashi nan take idonsu ya sarke cikin na juna,ɗan turo baki tayi tare da riƙe haɓarsa tace.
"yah..ya na karanci damuwa a fuskarka dama cikin zuciyarka,pls yah..ya tell me what happen?"ta faɗa idon na nawo kwalla.
Gashin kanta ya shafa yana kallon cikinta yana mai jin zafi a cikin zuciyarsa, "notin happen"yace banda ita da take kusansa babu wanda zai iya cewa yaji abinda yace.
,mood ɗinta ne ya sauya sam ba taji daɗin sauyawar mijin nata ba,,gyara zama tayi tare da faɗin"dukkan abinda ya samu bawa daga Allah ne,babu domin da zai iya sauya ƙaddarasa daga wacce Allah ya shirya masa,tun kafin a haifi mutum Allah ya riga ya tsara dukkan abinda zai sameshi a lauhil mahafus,kenan kaga babu abinda zaka iya sauyawa na daga cikin zanan ƙaddararka,hakuri da shuriya da kuma yadda da ƙaddara shine cikar imanin mutum,Annabi ya ambaci kallamar kada kayi fushi har sau uku,nima yanzu da faɗa kada kayi fushi pls yah..ya"ta kai ƙarshan maganar lokacin da hawaye ya wanke fuskarta.
Wani Ajjiyar ya sauke lokaci ɗaya yaji zuciyarsa tayi sanyi,hannu yasa ya jawota zuwa jikinsa,hannunsa ya tura cikin lafaffan cikinta yana shafawa a hankali,a yau ya tabbatar da abinda ya keji game da ita.
Ƙara mannata yayi a saman faffaɗan ƙirjinsa,lumshe idon tayi tanajin yadda soyyayar mijinta ke ratsa dukkan wata ƙofa na zuciyarta.
Bakinsa ya saman idonta ya shiga tsotse hawayen dake sauka daga cikinsu,gangaro da bakinsa yayi tsakiyar forehead ɗinta ya manna mata kiss.
Saurin shafa sajensa tayi sabida sanyin kiss ɗin daya ratsa jikinta,kallon yadda take lumshe ido yayi sumar kanta ya shafa lokaci ɗaya mood nasa ya sauya daga baƙinci zuwa fellings mai zafi.
Bakinsa yasa cikin kunnanta ya shiga hura mata iska tare da sucking cikin kunanta,ƙanƙameshi tayi tana ƙara shigewa jikinsa zafin dake cikin bakinsa ya fesa mata cikin kunanta,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,bakinsa ya motsa kaɗan yace.
"my unigue a yau zan baki bebies masu albarka,tabbas yau ƙwallo na zaikai ga raga"ya faɗa lokacin daya kwantar da ita akan bed ɗin tare dayin..




🤪yasin na gaji nima so nake na sauke book ɗinnan
Ƴan fadar nimcy Allah ku bani farin ciki kamar yadda na shirya baku,ina sane da masu Comments kuma inajin daɗin hakan ina miƙa saƙon gdy a garesu Allah yayi masu Albarka


Al Quran NG
Surah 1:1

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.


Al Quran NG
Surah 1:2

ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ

Praise be to Allah, the Cherisher and Sustainer of the worlds;


Al Quran NG
Surah 1:3

ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Most Gracious, Most Merciful;


Al Quran NG
Surah 1:4

مَٰلِكِ يَوْمِ ٱلدِّينِ

Master of the Day of Judgment.


Al Quran NG
Surah 1:5

إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ

Thee do we worship, and Thine aid we seek.


Al Quran NG
Surah 1:6

ٱهْدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ

Show us the straight way,


Al Quran NG
Surah 1:7

صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ ٱلْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ

The way of those on whom Thou hast bestowed Thy Grace, those whose (portion) is not wrath, and who go not astray.



~SARAUTA👑~


*🤱🏻RAINO ne SILA🤱🏻*
_ADOPTION IS THE REASSON BEHIND_

*NIMCY LUV*
```S@r@ut@👑```

Follow on istagram
Nimcyluv
Follow on wattpad
Nimcyluv


*~DEDICATED TO~*
```Fadar Nimcyluv ina sonku sosai bana iya fushi daku much luv my guys💋```



*🌈KAINUWA WRITER'S🌈*


*75-76*

waje ya fita ya jawo mata ƙofar ɗakin,yana fita yaga su Hajia da Mus'ab da kuma matar da aka kira da khaleeysat tsayawa kawai yay yana kallon matar tabbas kamar wani ya gani a fuskarta amma ya rasa dawa take masa kama ɗauke kai yay ganin matsu daf dashi.
"Dr ɗauko beby mu zamu tafi gida"kai kawai ya jinjina ba tare da yace komai ba,Najwa ta fitu daga ɗakin da aka saka ta lokaci ɗaya harta faɗa idonta ya fitu sosai,tsaki yaja sannan ya juya zuwa ɗakin beby.
Gaba ɗaya su kabi bayansa da kallo sabida yadda ko wannensu tsaki ya sauka kunnansa,ƙwalla ce ta cika idon Najwa tasan har abada Ahmada bazai taɓa yafe mata abinda ta aikatawa ɗan cikin saba,bayan hannunta tasa ta share hawayen dake shirin zubu mata.
Hannunta Hajia ta kama suka nufi mota side ɗin baya ta shiga ita da wannan matar najwa kuma ta shiga side gaba wajan mus'ab motar yay wa key ya jata da gudun gaske.
Tura ƙofar ɗakin A.J yay a kwance ya sameta ta lumshe ido da alama bacci ya ɗauketa,baison magana kamar yadda baison damunta,sai a lokacin ya tuna gaba ɗaya babu ɗan kwali a kanta,jacket ɗinsa ya cire mai hula ya sanya mata ɗau kanta yay cak yay waje da ita,daret wajen motarsa ya nufa yana zuwa ya buɗe ya sanyata ciki shima ya shiga,jawota yay cikinsa taci gaba da baccinta.
Dreving cikin ƙwarewa gaba ɗaya hankalinsa yay gida burinsa ya kasance da bebyn hajia,hannunsa yasa ya shiga shafa cikinta lumshe shayyayun idonsa yay lokacin da hannunsa ya sauka akan pink nipples ɗinta.
Saurin janye hannunsa yay tare da fitar da wani zazzafar numshi,bakinsa ya kai dai² lips ɗinta ya manna mata kiss.
Ajjiyar zuciya ta sauke sabida sanyin lips ɗinsa daya sauka akan nata lips ɗin ƙara shigewa jikinsa tayi,killer smile ya sauke yana ƙara gudun motar ganin dare yayi.
***
A zaune suke a parlour suna sauraran abinda hajia zata faɗa masu,kowa ita yake sauraro mus'ab A.j khaleysat najwa wai hajia yayinda beby ke ɗakin mijinta tana baccin wahala.
Gyara zama hajia tayi sannan ta fara magana"kamar kuka sani mu uku ne kacal a wajan iyayenmu,ƴan asalin mai duguri nemu aikin mahaifinmu ya dawo damu Abuja,masha Allah mahaifinmu nada arziki sosai wanda yake taimakon takalawa,na samu miji nai aure kasancewar nice babba gidana yana nan abuja,sai wacce take bina Ummahani itama tayi aure a london kasan cewar mijinta ɗan canne,tunda nai aure ban samu haihuwa ba hakan kuma bai daman ba,kwatsam wata rana khaleysat take gawa baffa mijin da zata aura a kano yake,nan yasa akai masa bincike akan guy ɗin.
Sosai ransa ya ɓaci sabida an tabbatar masa ba'asan ko wayeshi ba,hakan tasa tace autar ƴarsa wacce yafi so a duniya ba zata auri wanda bama asan wane shi ba,sosai khaleysat tasa kuka tare da riƙe ƙafar baffa tana gunjin kuka ta fara magana"baffa kayimin kabarni na auresa wlh ina matuƙar sonsa"lumshe ido baffa yay tare da ƙara shigewa cikin tattausar kujerar da yake zaune.
"yanzu hubby duk irin so da ƙaunar da nake maki baki gani ba,na fifitaki dasu luv amma yauda kanki kike bijirewa umarni na wonderfull,ni bazan hanaki auren wanda kikeso ba,amma ki sani muddin kika auri wannan mutumin na cireki sahun ƴarƴar na tunda ba kiga sonda nake maki ba,kije Allah ya taimaka ni bazan maki baki ba iya bijirewa maganata da kikai ya isa"
Yana faɗin hakan ya miƙe yabar kyakkyawan parlour,shuru ne ya biyo baya banda sautin kukanta daya cika parlour'n sai kuma ƙarar A.C.
Mami mahaifiyarsu itace take guge hawayen da yake zubu mata tace"haƙiƙa hubby kinyi kuskure ɓatawa baffa kinfi kowa sanin burin da yake dashi akanki,ni bazance komai ba domin idan baffa ya yanke hukunci babu wanda ya isa ya tunkarosa,sannan nima bazan bijirewa umarnin mijina ba domin aljannata nake nema ina maki fatan alkairi"
Lubna take zaune ta ƙasa cewa komai sabida ƙaton cikin da yake jikinta,a hankali ta miƙe tazu wajan khaleysat tace"hubby kiyi dan darajar ubangiji ki hakura da auren wannan mutumin pls"ta faɗa riƙe waist ɗinta.
Fashewa ta kumayi da kuga tace"luv wlh banyin kaina bane,Allah idan babu khalid ina iya rasa raina Allah ne ya ɗuramin ƙaddarar soyyaya mai zafi"
Babu wanda ya ƙara magana sai Sweety(Ummhani)data miƙe ta nufi hanyar flat ɗin baffan nasu"tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka tace"wlh nasan ba zaka iya jure rashin hubby ba baffa ciwo zai iya kamaka baffa pls try to understand her she is to young ba tasan abinda ya dace ba"
Manyan idonsa ya ɗaga ya kalleta sannan yace"sweety u are mad what kind of rubish tayaya kike tunanin na ɗauki gudan jinina na bawa wanda ba asan asalin saba?yaya kike tuanin rayuwar hubby cinta shanta sintirarta jikokina haba is much abubuwan"maza fice kiban waje kuma ayau kibi mijinki kada ki kwananmin gida.
Jikin sweety na rawa tabar ɗakin,tana fita ya kifa kansa ya fara hawayen rashin gudan jininsa hubby amma dole ya barta duniya ta koya mata hankali.
Haka hubby tabi luv zuwa gidanta.
Kwana uku mijin luv(anty lubna)ya gama komai na auren hubby babu kowa sai kawunsu wanda ya shige gaba aka ɗaura masu aure,sosai hubby tayi farin ciki da hakan tasan wata rana baffa zai yafe mata.
Kuka tayi lokacin da taje gida aka hanata shiga haka luv ta bata hakuri ita sa sweety suka shiga mota zasu rakata abuja.
Khalid ne yace"anty da kinyi hakuri kallin condition ɗin da kike ciki,kema haka anty umma kawai zamu tafi mu biyu haka nan.
Mota suga shiga aka zuba mata kayan ɗakinta a wata babbar motar tare da kuɗi kamar hauka suka bata suna kuka suka rabu.

Jan numfashi hajia tayi lokacin da idonta ya sauya kala,itakam khaleysat sosai take kuka,mus'ab shuru yay baice komai ba.
Tsaki A.J yay lokacin da ransa ya gama ɓaci da kukan da take ganin ba wani shekaru ta basa ba,kuma koda ta basa shekaru hakan ba zaisa yaƙi gaya mata gsky ba.
Idonsa ya ɗaga ya kalleta yace"malama kiyi mana shuru haba"ya faɗa yana zare mata manyan idonsa"saurin shigewa jikin hajia tayi tana kwaɓe baki sabida sosai tsuran A.j ya shigeta.
Shi mamaki yake bashi tana babbar ƴar amma jibi inda take shigewa jikin hajia ko jikin nata ne ohhu?.
Bayan tafiyar hubby dA kwana ɗaya ciwon naguda ya sameni nan da nan aka kaini asibiti na haifi ɗana mus'ab lokacin ahmad yana secondry ss2,nasu na haifi mace sai kuma na haifi namiji.

Abu kamar wasa kullum cikin kiran hubby muke bama samunta,haka muka ɗauki hanyar kano duk da babu wanda muka sani a can ɗin.
Gida muka dawo naje na shaidawa baffa sosai hankalinsa ya tashi domin ya kasa hakura da rashin hubby,nan suka shirya tafiya zuwa kano shida mijina Tijjani.
Wata biyu cif da auren hubby sweety ta haifi ƴar mace fara kyakkyasa aka sa mata Najwa nan take sweety ta rasu sabida zubar jinin da take.
Mijinta yace bazai bada ƴarsa ba zai riƙe wajansa tun daga rana bamu ƙara ganin najwa ba sai a pic.
Satin na zagayuwa baffa suka ɗauki hanyar zuwa garin kano neman hubby.
Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un,ina zaune ni ɗaya a parlour aka kirani a waya aka shaidamin rasuwar baffa da kuma mijina hakan ya faru ne sabida hatsarin da suka samu a hanyarsu ta zuwa kano.
Naga tashin hankali wanda ba'a sa masa rana na shiga halin baƙin ciki da kuma kaɗaici domin ana shaidawa mami itama ta yanke jiki ta faɗi a nan rai yay halinsa su uku aka haɗa aka kaisu gidansu na gsky.
Wajan shekara huɗu da wannan abun na shirya tafiya zuwa kano domin neman izinin wani aiki na haɗin guiwa a wani company,munzu sharaɗa Allah ya haɗamu da wata yarinyar tun kallon farko naga zallar kamar hubby a fuskar yarinyar ban kawo komai na ɗauki yarinyar na tafi da ita zuwa gida na.
A nan take shidamin sunanta Anusha.
Wannan shine labarin a taƙaice.

Wata ƙara khaleysat ta saki tare da faɗin wayyo Allah luv anusha tana wajanki,Allah nayi maka gdy daka nunamin gudan jinina akan na shiga kunci da kuma baƙar rayuwa nan fa fara shaida masu labarin abinda ya faru da ita(kudai masu karatu kunsan labarin khaleysat tun farko no need na ƙara faɗa)

Sosai hubby ke kuka tana ƙanƙame hajia tace"pls luv kaini wajan Anusha dan Allah wlh bana samun bacci kullum akanta.

Murmushi hajia tayi tace "bata nan ai tana flat ɗin waje ai"da sauri ta miƙe tayi hanyar waje,tana gaf da fita taji an riƙe mata hannu saurin juyowa tayi ware idonta tayi sabida ganin A.J a wajanta ya tamƙe fuska kamar bai taɓa dariya ba.
Hannunta ya saki sannan ya juya mata baya yace.

"kada kiyi kuskuran shiga flat ɗina bare ganganci tashin mamata a bacci"dafe ƙirji tayi jin Anusha ce matar Ahmad.
Dariya hajia tayi tace"haba dr wannan fa sirikar kace kuma uwar matarka bana son rashin kunya"

Hannu yasa ya hargitsa sumar kansa wannan habit ɗinsa ne duk lokacin da

14 / 16