Chapter 10 Reading BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt Arewa Novels

BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt

Author :  Zee Yabour Category :  Home Of Novels

Chapter   10 / 12

27K to 30K   out of 35.6K words

Dada sai Nene ta d'ibar musu, Ita da Fatsuma bak'in cikin ganin Bongel ta samu gidan hutu da arzik'i yasa suka shirya makircin, kayan abincin suka sayar, kowacce tasa kud'in adashe.




Nene na bakin murhu tana hura wuta, Ramla na dakan kayan yaji, Hamma Siddiku ya shigo kamar an jefo sa, Cikin ladabi Ramla ta gaishe sa, ya jefa mata tsiyacin kallo kana ya juya kan Nene, "Munafuka mai bak'in hali, wato ni ban muku bak'in cikin silar samun arzik'i ba ni zaku yi ma, komai kun kama kun kanannad'e hatta kayan abinci gidana sai dai muci tuwon dawa, amma gashi ke tuwon shinkafa kike girkawa", Ya nuna tukunyar dake gabanta, Mamaki yasa Nene kasa cewa komai, ko sati ba'ayi ba, ta raba kayan abincin da Dada ta aiko musu rabi, ta basu rabi, toh me yake nufi da zantukan sa banda son ganin laifi da k'iyayya, Ya katse tunanin ta da cewa "Wallahi ku bini a hankali ko kowa ya rasa", Yana fad'ar haka ya bula rigar sa ya wuce, Tunanin kalmar sa ta k'arshe ta d'aurewa Nene kai, me yake nufi da hakan, Sunan Allah ta ambata da neman tsarin da dukkan sharrin su.




****************************


"Wannan ce semester ta k'arshe da zaka kammala lecturing ya kamata ace mun soma tunanin hanyar b'ullowa Alhaji Sani na zance basa share d'insa", Cewar Abba, Haidar ya jinjina kai yace "Hakane nima na soma tunanin, dan wata d'aya ya rage nayi handing over", Abba yace "Gud, sai muyi tunanin hanyar da ta dace", Haidar yayi nodding kai tace "I will try my best wurin ganin hakan bai kawo matsala ko rabuwar kai ba", "Allah ya taimaka" , Yace "Amin", Suka d'auka zancen wani business na gina borehole.




***********************


"Cikin Rauda bai isa asan me zata haifa ba?" Alhaji Sani ke tambayar Hajiya Mariya, Tayi dariya tace "Banda abun ka Alhaji cikin da ko wata biyu bai rufa ba", "Ahtoh na k'osa naji ne kinsan itace bangon jinginar mu yanzu", Hajiya Mariya ta jinjina kai tace "Hakane amma In Shaa Allah namiji ne, kamar yadda Hafsah ta ajiye da' namiji, haka Rauda itama", Alhaji Sani yace "Allahu yasa", "Amin", "Kawo mun abinci", Tace "Toh" ta tashi.










OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*


Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


*HASKE WRITERS ASSO...*


ARBA'IN DA UKU


SHIN KIKA YI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK’AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K’ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D’ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298




Hamma Siddiku ne ya shigo gida rai a jagule, fuskar sa sam babu far’a, Dije ta tarbe sa da cewa “Lafiya dai Baban sa’ade”, Ya sauke ajiyar zuciya yace “Ina fah lafiya, daga gidansu mijin sa’ade ne suka turo, wai gobe zasu kawo kayan saka lalle”, Dije tace “Toh meye abun damuwa, ina ce abun farin ciki ne”, “Ke wataran sam baki hange nesa, sanin kanki ne bamu tanadi komai na bikin nan ba, ko cokali bamu ajiye mata ba”, Dije taja numfashi tace “Hakane yanzu meye abun yi?”, “Zanje na samu Bongel na d’aura mata nauyin kayan d’aki”, Dije baki ta tab’e tace “Baban Sa’ade da abu kake, wanda kayan abinci ya gagara samu, kayan daki zai samu”, Hannu ya d’aga mata yace “Barni dasu kawai, wannan ya zamar mata wajibi, ba zan musu silar arzik’i suci su kad’an ba wallahi, ba zai yiyuwa ba”, Ya fad’a yana girgiza kai, “Toh shikenan”, Dije ta fad’a dan a ganinta abu ne da bai yiyu ba, kayan d’aki ai ba wasa bane, duk da cewar Bongel na aure gidan daula,


Ya katse tunanin ta da cewa “Bani hula ta, yanzu ma zaan tafi”, Dije ba musu ta d’auko ta basa, Ya saka ya fice gidan.






*********************


Bongel yau da wuri ta dawo kasancewar lecture d’aya tayi, Tana dawowa ta shiga kitchen yin girki dama na safe kad’ai tayi, Rauda na kwance kan doguwar kujerar falo ta d’aura k’ada d’aya kan d’aya, wayarta a hannu tana sana’ar wato chatting, Tana labartawa k’awayenta irin kulawar da take samu daga Haidar, da hutun rashin aiki tunda ta samu ciki, suna k’ara zugata da fasa mata kai, tana jin ba wanda ya kai ta.




****************


Hamma Siddiku masu gadin sun barsa ya shigo jin cewar shine mahaifin Bongel, Kai tsaye falon gidan ya shiga ba tare ya jira an masa iso ba, Kallo d’aya Rauda ta masa tasan daga dangin Bongel ne, ta yatsina fuska kamar taga kashi, Ganinta da yanayin kayan dake jikinta yasa ya koma baya, Rauda ta mik’e da cewa “Ya’ tayi auren kud’i, ana sintirin zuwa gidanta dan’d’anar arzik’i”, Kalmar ta sauka kan kunnen Bongel da fitowar kitchen kenan, K’ofa ta kalla sanin ko shakka babu maganar tana da alak’a da ita, Hamma Siddiku ta gani tsaye ya juya baya, Mamakin zuwan sa tayi amma a zahiri kallonta ta maida kan Rauda tace “Ki iya bakin ki, zan iya tolerating a kaina but banda iyayena”, Ganin zallar b’acin rai shimfid’e kan fuskar Bongel, Tsaki kawai Rauda tayi ta shige ciki, dan taga alamar tayi wata magana Bongel d’in zata iya kai mata duka,




“Hamma sannu da zuwa”, Cewar Bongel da fulatanci, Ya amsa yana shigowa, Kan kujera ya zauna da cewa “Wash wannan lumsassun kujera haka, ai mutum ya samu irinta bashi ba ciwon baya”, Bongel tace “Bara na kawo maka ruwa”, “Idan ruwa ne ina ce su na baro gida, lemo da abun motsa baki zaki kawo mun”, Ta amsa da “Toh” jiki sanyaye, ko bai fad’a ba su tayi niyyar kawo masa, tace ruwa ne hausar bahaushe,




Minti biyar ta dawo d’auke da tray mai shak’e da kayan motsa baki, Hamma Siddiku ya tank’washe hannun riga ya soma fisgar cinyar kaza, “Wannan yarinya anyi muguwa, kina cin dad’i haka kin manta da iyayen ki”, Ya d’auki kwalin lemo ya bud’e yana sha, Bongel na gefe zaune tana addu’ar kar Allah ya jefo Rauda ko Haidar su k’ara rainata, sam bata son abunda zai k’ara jawo mata zubewar mutunci wurin Haidar d’in, Hamma Siddiku sai da yaci ya k’oshi, yayi gyatsa, Yace “Waii ina ma mutum zai rik’a samun haka kullum”, Bongel bata ce komai ba, dan duk ji take a takure, a zuciyarta tana addu’ar Allah yasa yace zai tafi,




Gyaran murya yayi yace “Nazo ne na sanar dake batun auren Sa’ade saura wata d’aya kacal”, Bongel farin ciki ya bayyana kan fuskarta, a tunaninta Hamma Siddiku ya fara sonta da har yazo sanar mata da zancen bikin, Tunaninta ya katse da cewa “Kinfi kowa sanin bamu da k’arfi, bamu da kowa mai shi yanzu sai ke, dan haka ya zama dole kiyi kayan d’aki”, A razane ta d’ago ta kalli Hamma Siddiku, Yace “Kallon uwar me kike mun, mai bak’in hali wallahi dole ne kiyi, meye amfanin yi miki silar auren ba dan muma mu samu ba, toh bari kiji ko kiyi kayan d’aki ko billahil lazi ki had’u da mummunan b’acin rai”, Yana fad’ar haka ya mik’e ya fita yana kufar baki,




Bongel kasa tashi tayi a wurin, sai kanta data d’aura kan kujera, tana ambaton sunayen Allah, wane irin tashin hankali ne k tunkaro rayuwarta, “Ya Allahu ka kawo mun sauk’i cikin al’amurana”, Ta fad’a tana jin zuciyarta ta mata nauyi, Banda son zuciya irin na Hamma Siddiku ya zai ce tayi kayan d’aki ko itace mai kud’in ba wanda take aure ba sai kai, basu tab’a damuwa da wane hali take ciki ba, ya zamanta da Haidar d’in yake, ya lafiyarta, amma yazo mata da buk’ata mai girma wacce tafi k’arfinta, ko akwai soyayya da zaman lafiya tsakaninta da Haidar buk’atar tayi girma balle babu, “Ya Hayyu Ya Qayyum” Take maimaitawa,




Rauda dake lab’e tana ji, Kai ta jinjina tace “Hmm lallai mutan k’auye ba hankali”, Tayi tsaki, ta shige d’akin ta,




********************


Hamma Siddiku a k’ofar fita suka ci karo da Haidar zai shigo, Haidar ya gaishe sa cikin ladabi, Ya amsa tamkar zai gurfana gaban sa, Haidar kunyar haka yaji, Ya bud’e briefcase d’insa dake shak’e da kud’i wanda yaso tsayawa banki ya saka baiyi ba, Ya zaro bandir na 500 ya basa, Hamma Siddiku ya shiga godiya, Ya tafi yana washe baki yazo a sa’a, Yana fad’in “Yaro mai alkhairi amma shegiyar yarinyar nan na hana sa yi mana, sai nayi maganin yar’ banza”, Yayi k’wafa,






Haidar har ya shigo falon Bongel bata ji ba, kallonta yayi yana mamakin yanayin ta wanda yake kyautata zaton yana da alak’a da zuwan Hamma Siddiku, Tamkar zaiyi magana, zuciyarsa ta hana sa da cewa “Meye damuwar ka”, D’akinsa ya wuce, ya ajiye jakar, Ya fad’a toilet ya watsa ruwa, A lokacin Rauda ta shigo tana jiran fitowar sa,






Haidar bai jima da shiga ciki ba, Bongel ta tashi ta koma d’akin ta, Tunanin ta wa zata sanarwa ta rage nauyin dake k’irjinta, ba zata iya sanar da Nene ta tada mata hankali ba, Asiya tazo mata a rai, ta d’auki waya ta soma kiran ta, Bugu biyu Asiya ta d’auka, suka gaisa, Ta zayyane mata komai tana k’arashewa da hawaye, Cikin tsantsar damuwa Asiya tace “Nima kaina ya k’ulle Bongel, wannan al’amari nada girma, amma addu’a zamu dage da ita, bata bar komai ba”, Bongel tace “In Shaa Allah” Sukayi sallama ta kashe wayar, Shigowar Irfan ta koya masa assignment ya rage mata damuwa sosai, dan daga assignment d’in ya soma yi mata hirar school, Duk da tana fargabar shigowar Haidar ya gansu tare, bata ce Irfan d’in ya tafi ba.






****************************


Haidar kamar kullum ya gama shirin sa na office, Rauda na zaune bakin gado tana bin sa da kallo, tana yaba tsantsar kyawon sa wanda take jin sabon kishin sa, ya zama dole ta hana kowacce mace rab’ar sa, ta gaggauta fitar da Bongel a rayuwar sa tun kafin soyayyarta ta d’arsu zuciyar sa take ayyanawa a ranta,


Briefcase d’in sa ya d’auka, ga mamakin sa yaji ta rage nauyi, bud’ewa yayi, Idonsa ya zaro ganin babu fin rabin kud’in, Dubansa ya kai kan Rauda yace “Ina kud’in dake jakar nan”, “Haba my dear ina zan sani nikam, ai ni banma san kud’i ka shigo dasu ba”, “Ke bana son wasa” Ya fad’a cikin dakewa”, “Allah ban d’auka ba”, Ta fad’a itama babu alamar wasa, “Toh wa zai shigo d’akin nan ya d’auki kud’i”, Rauda tace “Ai bayan ni akwai mai shigowa”, “Bongel” Ya furta,




Rauda ta girgiza kai tace “Yawwa ka bincike ta”, A hasale ya nufi hanyar fita, Rauda tabi bayansa, Bongel na gyarawa Irfan takalmin sa, Taji tsayuwar Haidar a kanta “Ke ina kud’ina”, Da zallar mamaki ta d’ago ta kallesa, Shima ita yake kallo ya had’e girar sama da k’asa, Murya a natse tace “Kud’i kuma”, “Malama kar ki kawo mun rainin hankali, ina kud’in da kika d’auka”, Dariya abun yaso ya bata, Tayi gajeren murmushi da cewa “K’iyayyar har ta kai ka tuhumeni kan d’aukar kud’in ka”, Kallon tsaf yake bin ta dashi, sai dai bai ga alamar rashin gaskiya a tare da ita ba, Har ya juya zai koma d’aki Rauda tayi saurin cewa “Ai zaki iya d’auka, tunda kina buk’atar kud’i, ina ce jiya babanki yazo kan buk’atar kiyi wa k’anwar ki da za’ayi wa aure kayan d’aki”, Cak Haidar ya tsaya yana juyowa ya zuba idonsa kan Bongel, Mamaki da kunyar zancen Rauda yasa jikin Bongel sanyi, sam bata so su san wannan al’amari ba, Kanta ta sunkuyar k’asa tana jin tamkar k’asa ta rufe ta shige ciki,




Tunanin ganin Hamma Siddiku da yayi, da kuma
yaga kud’in wanda ko shakka babu shi ya sanar da Bongel, Kunya da muzanta da ya gani a tare da Bongel yasa ya k’ara gaskatawa, Ya soma tab’a hannu da cewa “Wow so shine kika yi deciding sace mun kud’i”, Kanta ta d’ago a razane tace “Wallahi ban d’auka ba, ban tab’a kud’in ka ba”, Hannun ta ya jawo da k’arfi zuwa d’akinta,




“Nasan baki isa fita dasu ba tsakanin daren jiya zuwa safiyar yau, so suna nan, fito mun dasu”, Ya fad’a cikin karaji, Bongel cikin b’acin rai tace “Nace ban d’auka ba, idan baka yarda ba, ka duba d’akin mana”, Gaf da ita ya matso, tana jan baya har ta kai bango, Kansa ya buga kan nata, Ya saka idonsa da suka koma kalar ja cikin nata, hancin sa na gogar nata, Numfashin junansu na cud’anya, Yace “For the last time ina kud’in da kika d’auka”, Cikin zafin nama ta ture sa da cewa “Ban d’auka ba”, Baya yayi cikin k’unar zuciya yake dubanta, Kana ya juya zuwa drawer kayanta ya soma fito dasu d’aya bayan d’aya, sai da ya fitar da duka kayan drawer, ya koma akwati, ya fiddo kayan sai ga kud’in a k’ark’ashi, Wani mugun kallo ya juyo ya watsa mata, Bakinta ta bud’e cikin tsabar tsoro, had’i da kid’ima,


Rafa d’aya ya d’auko ya jefa mata a fuska, Yace “Meye wannan nace meye wannan?”, Kanta take girgizawa hawaye na ambaliya saman fuskarta,



“Wacce irin zuciya ce dake da babu imani ko tsoron Allah a ciki, meyasa baki da wadatar zuci sai kin kai hannun ki ga tab’a abun wani, a yau darajar ki ta k’ara zubewa a wurina, tsanarki ta ninku a zuciyata, kin had’a abu biyu da nafi tsana a rayuwata aikata zina da sata, ya zama dole mu raba inuwa dake, had’uwar mu wuri d’aya sam bai dace ba, baki cancanci zama matata ba”, Ya k’arasa yana fisgota da k’arfin bala’i, Hannunta ta fisge cikin zafin nama tace “Ya isa Haidar, baka yi k’arya ba, bamu dace da juna ba, haka bamu cancanci zama inuwa d’aya ba, na gaji da dukkan zargin ka a kaina, idanuwan ka sun riga sun gushe akan gane gaskiya, kana tunanin kud’i suna da muhimmanci da daraja a rayuwata da har zan kai hannuna ga wanda ba mallakina ba, toh kayi kuskure Haidar, ban ce dole ka yarda dani ba, dan nasan ba zaka yarda ba, amma ina so ka daina danganta ni da abubuwa mafi muni zina da sata, idan ba haka ba ka shirya tsayuwa gaban ubangiji dan bada shaidar hakan”,




Haidar da kallo yake bin ta kamar mai son gano wani abu, sai kuma ya juya, Kud’in dake cikin jakar gaba d’aya ya kwashe ya fita, Rauda dake lab’e bakin k’ofa tana jin komai tayi saurin zabura da cewa “Uhmm ka fito”, Kallonta yayi tsaf kana ya wuce, Tabi bayansa tana cewa “Dama nasan ita ta saci kud’in nan, ita kuwa wane irin mutuwar zuciya ne, sata tabb”, Haidar bai tanka ta ba har ya shiga d’aki,




Kud’in ya jera cikin jakar ya fita, Driver ya umarta ya kai Irfan makaranta, dan zai biya banki kar yaja masa makara,




A banki sun tabbatar babu dubu 3 cikin kud’in, abun yaba Haidar mamakin sanin kud’in a cike ya shigo dasu gida, haka bai bar ko naira wurin Bongel ba, Haka ya bayar da dubu ukun, aka cika kud’in aka sa masa account, Ya fito bankin da tunani kala kala a ransa.










FOLLOW, VOTE AND COMMENT






OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*


Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


*HASKE WRITERS ASSO...*


ARBA'IN DA HUD'U


SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298




Bongel kuka take tamkar ranta zai fita, kuka na bak'in ciki da takaici, bata tab'a jin takaicin rayuwar data tsinci kanta irin yau ba, takaicin yau yasha bambam da na duka sauran ranakun, ko a mafarki bata zaci akwai ranar da zata zo, a jefata da k'azafin sata ba, "Shin taya ma kud'in suka zo k'asan akwatin ta?" Shine tambayar da take yiwa kanta yafi a k'irga, sai dai babu mai bata amsar sai ma kanta dake k'ara k'ullewa, Ya zama dole ta fitar da kanta daga rayuwar Haidar, a yau ta k'ara shaida girman k'iyayyar sa gareta, ta hango zallar k'yamatar ta cikin k'wayar idon sa, Da k'yar ta taushi kanta ta sassauta sautin kukan ta, ta koma hawaye wanda ta kasa tsayar dasu, Mik'ewa tayi ta shiga toilet ta d'aura alwala, ta soma nafilfili ta kai goshinta k'asa tana ssnar da ubangiji damuwarta, da rok'on sa ya wanketa daga mummunan zargi, yabi mata hakk'in ta kan wanda ya jefeta da sharrin sata.




*********************


Haidar zaune yake jigum office d'in sa, tunanin abunda ya faru yau ya kasa barin sa, zancen Bongel na k'arshe "Ka shaida tsayuwa gaban ubangiji dan nada shaidar haka", Na masa yawo a kai, yayin da tunanin ina dubu uku suke ke k'ara jefasa tunani, Duk iya hasashen sa ya kasa hasaso komai, sai zuciyarsa dake k'ok'arin canza masa tunanin ba Bongel tayi satar ba, yayin da wani b'angare ke gaskata masa da cewa "Idan ba ita bace ya akayi kud'in suka je akwatin ta", Tsaki yaja tare da buga desk gabanshi yace "Tun shigowarta rayuwata ban huta ba, kullum case, ya zama dole na fitar da ita rayuwata" Yayi assuring kansa, yana cizon labb'an sa na k'asa.




**********************


"Wai yau ba zamu samu girki bane", Cewar Rauda ta fito d'akinta tana hamma alamar daga bacci ta tashi, Bongel na jiyo ta daga d'aki, tana zaune kan sallaya tana karatun Qur'ani wanda shine magani da warakar damuwarta, dashi take samun natsuwa a zuciya da ruhin ta, Rauda jin shiru babu alamar Bongel ta nufi d'akin kai tsaye,




"Sai a fito a d'aura mana girki ko, yanzu pass 5, kinsan yanzu bana jure yunwa", Bongel karatun ta ta cigaba ko kallo Rauda bata isheta ba, "Ko kunyar abunda kika aikata ce ta hana ki fitowa", Bongel sai a lokacin ta juyo ta jefa mata wani kallo tace "Allah yana ji yana gani, baya zalunci shi yasan gaskiya kuma shi zai bayyanata" Ta juya ta cigaba da karatun ta, Rauda baki ta tab'e tace "Hmm salon yaudara", Ta fice d'akin tana nufar kitchen ta had'o cornflakes ta dawo falo ta

10 / 12