Author : Zee Yabour Category : Home Of Novels
zasu yi magana",
Ta kai dubanta ga Bongel da cewa "Bayan tafiyar ki wasu sun zo kan neman auren ki, da kaya hadda kud'i, ina son jin k'arin bayani", Bongel ta bud'e baki da niyyar cewa Nene bata son auren, ba da amincewarta ba, sai kuma tayi shiru da tunanin gara ta fara samun Hamma Siddiku da maganar, "Kinyi shiru", Bongel ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da yatsun hannun ta alamar kunya take ji, Nene tayi murmushi tace "Na manta jinin fulani kike, shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi", Bongel a ranta tace "Kiyi hak'uri Nene da na soma b'oye miki abubuwa masu muhimmanci akan rayuwata, bana son k'ara miki damuwa kan wanda kike ciki",
****************************
Ammi itama bakin rai take wurin ganin auren Haidar da Bongel ya tabbata, haka kawai Allah yasa mata k'aunar Bongel, duk abunda tasan mace na buk'ata a kayan lefe ta had'a akwati goma sha biyar, Haka komai na buk'atar gida ta siya kama daga gadaje, kujeru, kayan kitchen da sauran kayan amfanin gida, yau take son yi ma Hajiya mariya kan su turo a kwashe kayan Hafsa, tun rasuwarta basu kwashe ba, a cewarsu tunda Rauda zata maye gurbin ta, a barsu.
*********************************
"Yanzu rashin ta idon har ta ka ga ki kirani kina cewa azo a kwashe kayan Hafsah" Hajiya Mariya ta fad'a cikin masifa, Ammi cikin sanyin murya tace "Kiyi hak'uri ba haka bane, dangin amaryar ne suke son yin jere, kwanaki na matsowa", "Dangin Amarya ko dangin tsiya, mai aikin Dada ce fa za'a aura masa, me suke dashi da zasu jera mata, ina jin k'warya da ludayi su za'a cika d'akunan dasu dan naji ance fillo ce", Ammi tace "Ni dai ba wannan ba, kuma ban kira ayi tashin hankali ba", "Tashin hankali ai kun neme shi, tunda kuka k'i jinin mu, kaya dai ba zamu kwashe ba, dan bamu da buk'atar su, aba Amarya dangin tsiya, sannan abu na k'arshe ku fara had'a kayan Irfan, zan zo d'aukar sa, ba zamu tab'a amincewa kulawarsa ta koma hannun bagidajiya dangin tsiya ba", Ta kashe wayar, Ammi ta bi wayar da kallo tana maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un", Su Hajiya Mariya na neman su zamar musu masifa,
*******************************
Washegari bayan sun gama karin kumallo wanda Bongel tayi sa ne kawai ba dan tana jin dad'in ci ba, Taje b'angaren Hamma Siddiku,
Tayi mamakin ganin sauyi a tare dashi, wanda wannan karon ya sakar mata fuska sab'anin lokutan baya, wanda sakin fuskar ba har zuci ba ne, dan yaci amfanin ta ne, Ta numfasa tace "Kayi hak'uri Hamma da tafiyar da nayi ban dawo ba", "Ah ba komai ai, na fahimce ki Bongel gashi ana shirin auren ki", "Idan ba damuwa ina son a mayar da auren kan Jabeer, bana ra'ayin wancan", Wani mugun kallo Hamma Siddiku ya watsa mata yace "Yau ga yar jakar uba, ke k'undun uban ki, ni zaki mayar mutumin banza, har na bayar da auren ki kizo da wani zance, ban da kina sakarya ga inda arzik'i yake zaki nemi tsiya, toh idan kinga ba'ayi auren ki da dan' birni ma, mutuwa kika yi, tashi ki bani wuri kafin na shure ki", Jiki na rawa Bongel ta fice.
*******************************
An shirya komai na kayan aure da za'a kawo gidan su Bongel, hadda lefe, katin gayyata, goro da sauran tarkace, Mutum biyar mata kad'ai suka shirya tafiya, Cikin motoci biyu jeep prada, kowannen su yasha sutura mai kyau da tsada, Dada wanda tasan basu da gutsiri tsoma ta zab'a, dan kar aje aga gidansu Bongel a dawo ana gulma.
Bongel dake tsakar gida tare da Nene dasu Ramla, Akwati suka ga an soma shigowa dasu, Bongel gabanta ya fad'i hakan na tabbatar mata daga danginsu Hisham, sai dai abunda ta kasa ganewa auren ta da Hisham ne ko Haidar zai tabbata, Da tunanin haka tayi saurin tashi ta shiga d'aki, Nene ma tabi bayan ta, dan tana gani tasan kayan auren Bongel ne,
Dije da fatsuma suka kasa suka tsare, suna yak'e wanda yafi kuka ciwo, ganin uban kaya ya k'ara shaida musu ba k'aramin attajiri Bongel zata aura, ko shakka babu gidan daula da hutu zata, wanda ko a mafarkin su basu zatar mata haka ba.
Su Aunty Mami basu jima ba, suka tafi, bayan wucewar su Nene ta fito, lokacin har Ramla taje da sanar da Goggo Hajjo sunzo, da sauran yan' uwan Nene na garin, mak'wabta ma sun soma cika gidan, kowa na fad'in albarkacin bakin sa, na had'uwa da yawan kayan, Nene tsoro ne ya shiga zuciyarta, su ba kowa ba, basu da komai, taya yarinyar su zata yi auri cikin irin wannan ahalin, hasalima basu da komai da zasu mata kayan d'aki, Data samu Goggo Hajjo da maganar, ta kwantar mata hankali da cewa, Allah ne yayi wannan had'in, ba iyawar su ko dabara ba, kuma su san irin gidan da suka nemi auri, ba zasu buk'aci wani abu daga garesu, kawai suyi k'ok'arin yi daidai k'arfin su, Da haka Dada taji k'arfin gwiwa,
Bongel kuwa kwana tayi juyi kan gado, da tunanin waye ango ta tsakanin Haidar da Hisham, a halin yanzu duka bata sha'awar auren d'aya daga cikin su, Haidar yana munana zato a kanta, da nuna mata k'iyayya k'arara, Hisham haushin sa take ji sosai na d'aura mata zina dan kawai cikar burin sa, hakan na nufin bai san darajarta ba, idan ya sani gara yayi hak'urin rasa ta, akan rusa mata darajar ta, Ta k'arasa da cusa kanta cikin pillow tana hawayen bak'in ciki.
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ASHIRIN DA HUD'U
Haidar tashin sa daga bacci kenan wanda da k'yar ya samu runtsawa a daren jiya saboda damuwa da tunanin auren Bongel da suka hana zuciyar sa sukuni, gaf da sallar asuba bacci ya d'auke sa K'aramin agogon dake kan bedside drawer ya kalla, 9:30 daidai salati yayi ya sanar da ubangiji, yana mamakin nauyin baccin da ya d'auke sa, Toilet ya shiga yayi brush ya d'auro alwala ya fito, ya kabbara sallah, yana idarwa kiran Abba na shigowa wayar sa, sai da ya kammala azkar, kana yabi kiran Abba, ya d'auka yace yazo yana son ganin sa.
Ba tare da ya tsaya wanka ba, ya nufi sashen Abba dan sam baya wasa da abunda ya danganci iyayen sa, Kamar ko da yaushe a falon sa ya same sa, Yace "Abba barka da hutawa", "Yawwa Barka", Ya zauna kujerar kusa da Abban, K'aramar jaka ya mik'a masa yace "Katin auren ka ne a ciki, gasu nan sai ka rabawa yan'uwa da abokan arzik'i, ina fatan kasan an kai lefe jiya", Haidar zancen Abba ya k'ara masa damuwa a kan wanda yake ciki, hakan na nufin auren sa da ita babu fashi tunda har an buga kati an kai lefe, taya zai fahimtar dasu wacece ita, da yasan haka da tuni ya amincewa auren Rauda, dan gara ita akan auren Karuwa, Abba ya katse masa tunani da cewa "Kayi shiru", "Toh In shaa Allah" ya furta, yana d'aukar jakar ya fita.
Kan gado ya jefar da jakar, ya shiga band'aki ya sakar ma kansa ruwan shower ko hakan zai rage masa damuwa.
*********************************
Bongel cikin bacci ta soma jin muryar Goggo Hajjo na fad'in "Ina Amaryar take?", Idonta ta mutsitssika tana tashi zaune, baccin bai isheta ba, kasancewar bata samu runtsawa ba sai bayan sallar asuba,
"Au Bacci kike yi, to tashi ga ruwa can na had'a na wankan ki", Cewar Gwaggo Hajjo, Ta yamutsa fuska alamar bata so, wanda Hajjo ta d'auki hakan matsayin kunya, Ba dan rai yaso ba, ta mik'e ta shiga wanka da ruwan turare da had'in wasu itatuwa masu gyara jiki, tayi tsarki da wasu ruwa a buta da ta bata, Ta fito tana k'yalli tana k'amshi, ta shafe jikinta da mai, ta saka atamfa d'inkin riga da skirt cikin kayan fitar biki, tayi matuk'ar kyau, yan Allah sanya alkhairi nata faman kai kawo gidan, Su Dije kuwa bak'in ciki da hassadar fal zuciyar su.
Bongel kuwa tunanin ta ya tafi kan son sanin wa zata aura, tana jin kunyar tambayar d'aya daga cikin yan' gidansu, zuwan k'awayen ta wanda sukayi primary tare, yasa ta d'an ware suna hira dasu a kai kai, Hajaru d'aya daga cikinsu tace "Bongel kin more samun miji Allah ya bamu danshin ki", Saura suka ce "Amin", A zuciyarta tace "Da kunsan irin auren da zanyi babu mai marmarin irin sa, in dai har ya kasance Haidar zan aura", Tana rufe baki, Mairo tace "Hafsah amaryar Haidar", A razane ta d'ago ta kalleta da cewa "Ina kika san sunan angon", Dariya tayi tace "Gashi nan rubuce a katin gayyata", Wasu miyau ta had'i na bak'in ciki had'i da fargabar wacce irin rayuwar aure zatayi da mutumin da ya nuna mata k'iyayya fiye da kowa a duniya, A zahiri tayi k'ok'arin b'oye damuwarta but a bad'ini damuwa ce shimfid'e a zuciyar ta.
*****************************
Alhaji Sani maigoro ya kalli Iv d'in ya k'ara kalla, Cikin tsananin b'acin rai yace "Yanzu dan cin fuska ni Alhaji Abbas zai aikowa katin gayyata hadda goro", Hajiya Mariya tace "Ka daina mamakin halayyar su, ni duk abunda zasuyi yanzu ya daina bani mamaki", Ya jinjina kai yace "Wallahi ko ta halin k'ak'a sai na cimma burina, na daina tsoro ko fargabar komai", "Haka nake so naji kace Alhaji, nima yanzu zanje na d'aura musu nawa", Ta karb'i IV a hannun sa, tana fita.
************************
Ammi na zaune tare da k'annen ta, suna shirye-shiryen yinin biki da d'auko amarya jibi idan an d'aura aure, Hajiya Mariya ta shigo kamar an jefo ta babu sallama, Kowa ya kai duban sa gare ta, Ammi tace "Sannu da z.......", Ta katse da d'aga hannu tace "Dakata ba wannan ya kawo ni ba, ina irfan shi nazo tafiya dashi", Ammi tace "Haba Mariya abun duk bai kai haka ba", Hajiya Mariya ta k'ara gyara tsayuwa tace "Ni fah babu sauran mutunci tsakanina daku, jikana nazo a bani", Anty Binta d'aya daga cikin k'annen Ammi tace "Haba Maman Hafsah, bai kamata ana jin kan ku ba, ina ce an zama d'aya", "Wallahi ba'a zama ba, idan an zama ba zasu k'i jinin mu ba, dan haka kawai a bani Irfan",
Abba ne ya shigo rik'e da hannun irfan, yace "Gashi mun yarda kulawar shi ta koma hannun ku", Kowa yabi Abba da kallo mamaki, Ammi ta bud'e baki da zumar yin magana ya mata alama tayi shiru, Ita kanta Hajiya Mariya was shocked ba haka tayi tsammani ba, jiki a sanyaye taja hannun Irfan d'in tana ficewa ba tare da ta nuna musu ba haka taso ba,
Bayan fitar ta Abba ya wuce d'akin Ammi, tabi bayan sa, sanin hakan na nufin yana son magana da ita,
Bakin gado ta same sa a zaune, ta kalle sa rai babu dad'i tace "Meyasa ka zab'i bata Irfan, kasan irin shak'uwar dake tsakanin sa da mahaifinsa, da ahalin gidan nan", Abba ya numfasa yace "Ina mai tabbata miki Irfan ba zai wuce kwana biyu a gidan su ba, zasu dawo dashi", "Meyasa kace haka?" Ta tambaya da mamaki, Yayi murmushi yace "Ki kwantar da hankali, kuma bana so ki sanar da Haidar komai, idan ya tambayi Irfan, kice yaje kwana biyu", Tace "Toh" tana gamsuwa da mijin nata, tasan ba zai tab'a kawo abunda zai rusa farin cikin su ba.
***********************************
Hajiya Mariya cike da bak'in cikin plan d'in ta bai yi ba ta dawo gida, sam ba haka taso ba, Falo ta bar Irfan wurin yan' aiki, ta shige d'akin ta cike da takaici, taso tada rigimar a bata Irfan, ta yadda hakan zai sa Su Ammi suji tsoron rabuwa da Irfan, a fasa auren da Bongel, ace ya auri Ramla dan Irfan ya zama wurin su, sai gashi tashi d'aya Abba ya damk'a mata shi, zirga zirga take a d'aki, ta kasa zama tana tunanin hanyar b'ullowa al'amarin.
***************************
Hisham walwalar sa ta rage sosai, office ma ya daina zuwa, kullum yana gida, he is depressed, abu biyu suka taro suka jagula masa lissafi Bongel na fushi dashi, ta kasa tsayawa ta fahimce shi, ganin yana gaf da rasata, duk iya tunanin sa na yadda zai hana auren yiyuwa ya kasa, Bai tab'a zaton Haidar zai amincewa auren ba jin sun had'a shimfid'a, yasan ko shakka babu saboda shi ya kasa fallasawa su Dada, anya ba zai samu Dada da kansa ya gaya mata sun had'a shimfid'a da Bongel ba, yana jin ta haka kawai zai samu mallakar ta, yayin da wani b'angare na zuciyar sa ke hana sa.
***************
Rauda ta sawa ranta ko ta wacce hanya sai tabi dan ganin ta mallaki Haidar, zuciyarta ba zata tab'a iya hak'ura dashi ba, ko a lokacin da ta soma ganin su taso ita yake so ba yayar ta ba, yanzu kuwa ba zata bari wata mace ta samu gurbi a zuciyar sa idan ba ita ba, ado tasha sai dai wannan karon ta b'oye gashin kanta da yasha attach, ta saka mayafi madaidaici dan ta fuskanci hadda yanayin shigarta ke sa yake shunning d'in ta, tayi simple makeup tayi kyau dan itama kyakkyawa ce, Mukullin motar ta, ta d'auka ta fice gidan ba tare da sanin Hajiya Mariya ba.
****************************
Haidar yau tun zuwan sa office ba abunda ya aikata, bashi da natsuwar yin komai, gashi tun shigowar sa ma'aikatan wurin ke masa Allah ya sanya alkhari wanda bai ga abun fatan alkhairi ga auren Karuwa ba, takardun dake gabansa kallon su kawai yake ba tare da ya aiwatar da komai ba, shigowar Rauda yasa ya d'aga kai ya kalli k'ofa, ta sakar masa murmushi tana shigowa cikin yanga da yauk'i kamar zata fad'i, Haidar ya d'an kawar da kansa gefe, zama tayi saman kujera tace "Yaya ina wuni", "Lafiya lau" ya amsa da sakin fuska, "Ya aiki?", "Alhamdulillah", Ta soma jan sa da hira, ya d'an sake mata, a zuciyar sa yana jin yayi amfani da ita wurin kaucewa auren sa da Bongel, ko auren ya tabbata ya rabu da ita cikin sauk'i.
*************************
Rauda cike da tsantsar farin ciki ta dawo gida, ta tarar da Irfan yana zaune falo yana kallon carton, ta jawo sa da cewa "Yaushe kazo?", "D'azu granny tazo dani", Ta shafa kansa da cewa "Bara ina zuwa", D'akin Hajiya Mariya ta nufa, cikin tsantsar farin ciki take sanar da ita, irin tarbar data samu daga Haidar yau, Sam zancen bata d'auke sa da muhimmanci ba, a ranta tace "Ya samu wacce zai aura ai dole zaki ga far'ar sa, tunda ya gujewa auren ki", A zahiri kuwa ta nunawa Raudah ta cigaba da basa kulawa, ta haka zata samu gurbi a zuciyar ta, bata son Rauda ta cire rai ga samun sa, dan ba zata yi k'asa a gwiwa ba wurin ganin ta zama surukar gidan Maishanu a karo na biyo, Ta gamsu da zancen mahaifiyarta ta fito tana murna taja Irfan zuwa d'akin ta.
***************************
Ana saura kwana biyu d'aurin aure Asiya tazo malumfashi, Bongel tayi farin cikin zuwan ta, zata samu wacce zata rik'a fad'awa damuwar ta, tana rage nauyin k'irjin ta, ana gobe d'aurin aure Asiya da sauran k'awayen Bongel na garin suka shirya fulani day, Bongel taso hana su, suka ce sai sun yi, a farfajiyar gidan suka shirya, k'awayen amarya sukayi ankon kayan fulani, kowacce rik'e da k'warya da nono, Amarya tayi ado cikin kayan fulani tayi kyau sosai, ta fito sak fulani, kid'an k'warya kawai ke tashi a farfajiyar gidan, k'awayen amarya na chashewa sai dare kowa ya watse, Bongel tun kafin su watse ta koma cikin d'aki, fargabar d'aurin auren ta gobe yasa sam bata walwala, Asiya ta fuskanci haka, ta sameta dan k'ok'arin kwantar mata da hankali.
"Bongel" Asiya ta kira sunanta, "Na'am" ta amsa tana tashi daga kishingid'en da tayi, "Nasan damuwar ki akan auren Haidar ne, ina so ki cire damuwar komai a ran ki, In Shaa Allah Haidar zai zama abokin rayuwar ki nagari, da sannu zaku so juna, baki shan jin labarin wanda sukayi auren da babu soyayya daga baya ya koma soyayya ba, baki san labarin auren Fetta da Suraj ba, sunyi aure babu soyayyar junan su, daga k'arshe suka mutu a soyayyar juna", "Kada ki had'a aurena da na wasu, nawa yasha bambam da saura, Taya kike tunanin mutumin da ya nuna mun k'iyayya fiye da kowa a duniya ya zama abokin rayuwata, ya kike tunanin k'iyayyar sa gare ni ta koma soyayya, hakan ba zai tab'a yiyuwa ba, ki rik'a auna zantukan ki a ma'auni kafin ki furta su", Asiya tayi murmushin takaici, tasan Bongel ba zata fahimce ta yanzu ba, amma tana da kyakkyawan zaton gaba zasu so juna ita da Haidar.
********************************
K'ofar gidansu Bongel ya cika da al'ummar Annabi yan' d'aurin aure, wakilan amarya da ango duka sun hallara, wanda Hamma Siddiku ne wakilin ango sai washe baki yake ganin sa cikin manyan mutane an karrama shi matsayin shi na wakilin ango, Haidar na zaune gefe d'aya, kallo d'aya zaka masa kasan ango ne daga shigar sa, kusan ince yafi kowa shiga mai kyau da tsada a wurin, blue shadda ce d'inkin babbar riga, tayi masa matuk'ar kyau, hular sa zanna ta zauna daram a kansa, sai dai sam babu walwala a fuskar sa, kowanne ango yau ranar farin cikin sa ce, sab'anin shi da aka k'ak'aba masa karuwa da sunan zata kula da tarbiyar yaron sa, ya samu natsuwa a tare da ita, ganin gidansu yasa a ransa yace "No wonder take neman maza, ta kasa rik'e talaucin ta, sai ta samu kud'i ta k'azamtacciyar hanya", Yaja siririn tsaki dashi kad'ai yaji abun sa.
*******************************
Hisham yau kwata kwata bai fito daga d'akin sa ba, balle yasa ran zuwa d'aurin aure, ba zai iya halarta ba, kwance yake k'udundune cikin bargo, zazzab'i mai zafi ya rufe sa, k'asan zuciyar sa yana jin ba zai tab'a hak'ura da Bongel ba, ko anyi auren yana da tabbacin sai ta fito ta aure sa, sanin Haidar ba zai tab'a son ta ba, ya d'arsa abu a zuciyarsa mai wuyar gogewa, yasan mu'amalar aure ba zata tab'a shiga tsakanin su ba, ga