Chapter 6 Reading BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt Arewa Novels

BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt

Author :  Zee Yabour Category :  Home Of Novels

Chapter   6 / 12

15K to 18K   out of 35.6K words

ita da Haidar, Hisham ma daidai lokacin ya kai duban sa, jin muryar mutane suna fad'in Subhanallah ganin ta fad'i,




Bongel numfashinta ya d'auke na wucin gadi, yayin da zuciyarta ke dokawa da tsananin k'arfi kamar zata fasa k'irjinta ta fito, Haidar sandarewa yayi wurin dan ya kasa gaskata abunda idanun sa ke gane masa, yayin da wata zufa ta tashin hankali ta shiga tsattsafo masa,


Hisham kuwa idon sa ya sake murzawa dan tabbatar da ba gizo suke masa ba, Ganin Bongel ce matsayin amaryar Haidar, kansa ya mugun sarawa tamkar an sara masa takobi, yana jin wani abu ya daki k'irjin sa,




Bongel ganin idon mutane yasa tayi saurin mik'ewa tana gyara mayafinta tare da k'ok'arin tattaro natsuwa, sai dai ganin natsuwar ba zata samu ba, ta rik'e k'afarta alamar kamar taji ciwo tace "Auchh", Sannu aka fara mata, Waleeda ta jata zuwa mota, Jinginar da kanta tayi jikin kujerar mota, kanta na tsananin sara mata, bugun zuciyarta na tsananta, Asiya take buk'atar gani a yanzu,




Asiya na ganin an fito da Bongel, ta biyo bayan su, motar ta bud'e ta shiga, Hamza driver ta umarta ya kaisu gida, ba wanda ya d'aukowa wani maganar ganin bai dace suyi gaban Hamza ba, amma kowa yasan dan' uwan sa na cikin rud'ani.






********************************


Haidar bai k'ara minti biyar a wurin ba ya fita zuwa gida ba tare ya jira sauran abokan sa ba, Yana shiga d'aki ya cire hular sa da babbar riga yayi wulli dasu, Da fad'in "How is that possible, taya ta zama yarinyar da Dada ke son aura mun, wallahi ba zai tab'a yiyu ba, i must ruin everything bazan tab'a bari hakan ta faru ba" Ya fad'a idonsa na kad'awa su koma jajir.




**************************************


"Asiya kaina ya k'ulle, bana gane komai taya Haidar ya zama mijin da zan aura ba Hisham ba, meye alak'ar Dada da Haidar, taya Haidar ya zama mahaifin Irfan", "Nima sune abunda suka d'aure mun kai Bongel, amma ina jin Hisham ya kamata mu nema ko zamu samu wani bayani", "Bana tunanin Hisham nada masaniya a kai", Ta k'ara da cewa "Shiyasa kenan bai tab'a mun zancen auren ba", Ta k'arasa da dafen kanta da take jin tamkar zai rabe biyu, Asiya ta bud'e baki zata yi magana kiran Hisham ya shigo, wanda tun ganin Bongel matsayin matar da Haidar zai aura ya rasa natsuwar sa,


Ta d'auka, Cikin sanyi murya yace "Ina waje", Tace "Toh" tana kashewa ta kai dubanta ga Bongel tace "Hisham ne" Da sauri ta tashi, tana riga Asiya fita waje, Cak ta tsaya dan kallo d'aya ta masa ta hango tsantsar tashin hankali a fuskar sa da tarin tambayoyi, Kafin tayi wata magana yace "Taya haka ta faru Bongel, ki gaya mun taya, dama yaudarata kike kin shirya auren Yayana", Jin kalmar Yayansa ta kalle sa a razane da cewa "Haidar Yayan ka ne", "Kada ki raina mun hankali Bongel, tsawon zaman ki gidan Dada ba zaki ce baki san Haidar yaya na bane", Kuka ta fashe da shi tana cewa "Wallahi ban sani ba Hisham, hasalima kai nake wa kallon mahaifin Irfan, shiyasa ko da Dada tazo da zancen auren mahaifin Irfan na amince, bansan Haidar ba ne" Ta k'arasa tana kuka kamar ranta zai fita, Hisham natsuwa ya d'an ji na jin cewa Bongel bata san da maganar auren ba, Ya numfasa yace "Ki daina kuka Bongel, In Shaa Allah i will try wurin ganin auren ya dawo kaina", "Please try Hisham, ba zan iya auren yayan ka ba", Jin haka ya k'ara sa zuciyarsa tayi sanyi, Sai da ya tabbatar ya lallashe ta, ta daina kuka, sannan suka shiga cikin gida da Asiya, wacce tun fitowar ta bata ce komai ba.




****************************************


Hotonan walima da ake ta sawa a status Rauda ke kallo cikin tsananin b'acin rai da tafasar zuciya, hoton k'arshe da ta kai tayi jifa da wayar k'irar iphone 13, ta fashe, Kuka ta fashe dashi da cewa "Wallahi sai na aure ka Haidar, tun kafin Yaya Hafsah ta rasu nake wa kaina sha'awar miji irin ka, yanzu ga damar samun ka bazan tab'a bari wata ta mallake ka ba", Ta k'arasa da fad'awa kan gado tana kuka tana wulla k'afa kamar k'aramar yarinya.






***********************************


Alhaji Sani ne zaune jigum, ya zurfafa tunani, abincin da Hajiya Mariya ta zuba masa har ya soma sandarewa,


Hajiya Mariya ta shigo tana cewa "Ahh Alhaji baka ci abincin ba", Tana kallon plate dake gabansa, Ya sauke ajiyar zuciya da cewa "Wallahi ba zan iya ci ba Mariya, komai yana neman rushe mun lokaci d'aya, tarin burikana na neman wargajewa", Hajiya Mariya ta dafa kafad'ar sa da cewa "Ka daina fad'ar haka Alhaji, In Shaa Allah sai mun cimma burin mu", "Taya kina ganin an soma bikin Haidar", "Somawa akayi ba'a d'aura ba, ka bari kawai ka gani sai na tabbata auren bai yiyuwa ba", "Taya hakan zai kasance", Shu'umin murmushi tayi tace "Ka bar komai a hannu na",






******************************


Bongel sam bata runtsa ba, raba daren tayi Sallah, tana rok'on Allah zab'in alkhairi a rayuwar ta, Da safe kasa karin kumallo tayi, ruwa kad'ai ta sha, ba yadda Asiya batayi da ita ba, taci abinci tak'i, Yau ya kamata ta tafi malumfashi amma jiran ta bakin Hisham taji ko ya samu nasarar wargaza aurenta da Haidar ya dawo kansa, yasa ta fasa tafiyar.






*********************************


Dada tsaf ta gama sauraren buk'atar da Hisham yazo da ita, nacewa suna son junansu da Bongel, Dan Allah ta maida auren kansu, Ta kalle sa tsaf ta kira sunan sa "Hisham" Ya amsa da "Na'am", "Kayi kuskure tun farko na b'oye soyayyar ka da Bongel, bakin alk'alami ya riga ya bushe, Bongel na riga na zab'ar mata Haidar a matsayin mijin aure dan sunfi dacewa", Zubewa yayi k'asa yana had'a hannayen sa biyu yace "Dan girman Allah Dada ki taimake ni ki aura mun Bongel", Duk da tausayin sa ya kamata, bata jin zata tab'a canza akalar auren zuwa kansa, Tace "Kayi hak'uri Hisham, Allah ya baka wacce tafi Bongel", Kasa tashi yayi da gurfanen sai hawaye da suka soma sauka kan kumatun sa, yana jin kansa na juyawa, a yadda soyayyar Bongel ta kamasa baya jin zai iya jure rasa ta, Dada mik'ewa tayi ta bar falon cike da tausayin sa, dan ba zata iya jure ganin sa a wannan hali ba.






*********************************
Haidar dare d'aya amma duk ya canza kasancewar rashin bacci da bai samu jiya ba, had'i da damuwa da tunani da suka taru suka masa yawa, Kansa ke tsananin ciwo yasha pain relief amma tamkar k'ara masa ciwon kan ake, a daren jiya sai da ya samu hanyar sub'ucewa auren kafin ya d'an samu natsuwa,




Wayarsa ya d'auka ya kira Hisham, Hisham wanda tun fitowar sa gidan Dada, ya samu wani wuri da babu mutane, yayi parking motar sa ya d'aura kansa kan sitiyari cikin tsananin damuwa, Kamar ya share kiran sai kuma ya d'auka, "Kazo guest house kai daa budurwar ka Hafsah", Yana fad'ar haka ya kashe wayar, Hisham ajiyar zuciya ya sauke yana fatan kiran ya zama alkhairi, Motar sa yaja zuwa gidansu Asiya,



Bongel da take jiran zuwan sa, tana jin yana waje, ta saka hijab ta fito, "Ki shigo mota zamu je wani wuri" Shine kad'ai abunda yace mata, Kanta ta girgiza alamar "A'ah", "Zuwa yanzu ya kamata kisan bani da wata manufa a kanki face ta alkhairi, so pls kizo muje", Ta d'an yin jim, kafin ta bud'e murfin motar ta shiga, Yaja su zuwa guest house, Ganin gidan da suka zo gabanta ya fad'i ta kai dubanta gare sa cikin fargaba, "Wallahi tallahi bani da niyyar cutar dake Bongel", Jin haka ta d'an samu natsuwa, Ta fito tana bin bayansa,




Turus tayi k'irjinta na dokawa ganin Haidar hakimce kan kujera, tayi saurin ja baya, Hisham ne ya mata alama da ta tsaya, Cak ta tsaya,




Haidar hannun sa ya soma tab'awa yana tafi, ya mik'e Yace "Wow despite ana shirin auren ki da wani amma kike iya bin saurayi zuwa wurin sharholiyar da kuka saba", Hisham da mamaki ya bud'e baki zai yi magana ya dakatar dashi da hannu "Nasan me kake shirin fad'a, idan bata saba biyo ka nan ba, babu macen data san k'ima da darajarta da zata biyo saurayi gida ko da babu kud'in auren wani a kanta","No Yaya Haidar ba haka ba ne", "Idan baka sani ba Hisham, ina so yau ka sani da idona na ganku", Hisham k'irjin sa ya doka, "Hakan na nufin Yaya Haidar yaga Bongel ranar kenan" Yacewa kansa, Haidar ya juya kan Bongel


"Haidar ba sa'an auren irinki ba ne mai cike da d'auda da dattin zina, Taya kike tunanin zan auri macen data had'a shimfid'a da k'anina, macen data zama tamkar motar haya kowa hawan ta yake, Ni HAIDAR ABBAS MAISHANU bazan tab'a auren karuwa wacce ta had'a shimfid'a da k'anina ba", Cikin zafin rai da hasala da maganganun sa tace "Banyi ba, ban tab'a had'a shimfid'a da kowa ba, ka daina danganta ni da kalaman da ban dace dasu ba" Ta juya kan Hisham tace "Ka fad'a masa gaskiya, ka gaya masa abunda ya faru ranar", Hisham yayi shiru ya kasa magana, Cikin d'aga murya tace "Kayi magana Hisham, ka fitar dani daga mummunan zaton Yayan ka, na gaji na gaji" Ta k'arasa cikin karaji.




FOLLOW, VOTE AND COMMENT






*OUM MUHRIZ*
Zee Yabour: *BONGEL*


Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


*HASKE WRITERS ASSO...*


ASHIRIN DA UKU


Hisham ya bud'e baki zai yi magana wani tunani yazo mishi yace "Yes mun had'a shimfid'a dake Bongel, bana tunanin akwai amfanin b'oyewar haka", Ya fad'i hakane sanin Yayan sa ba zai tab'a amincewa auren ba matuk'ar yaji sun had'a shimfid'a, shi kuma ya samu mallakar Bongel,




Ba Bongel kad'ai ba hatta Haidar zancen ya dake sa, duk da yaga Hisham a kanta, amma ji daga bakin sa, ya k'ara hasasa wutar tsanarta a zuciyar sa, ita komai ta had'a k'arya, iya makirci banda makirci yadda take yi zaka rantse babu abunda ya shiga tsakanin ta da Hisham d'in, taso ayi manipulating d'in sa kenan Hisham ya bayar da shaidar k'arya, Ya fusgar da iska mai zafi daga bakin sa a fili yace "Mak'arciya makira"




Bongel kalmar "mun had'a shimfid'a dake Bongel" ke wa yawo a k'wak'walwa, dishi dishi ta soma gani, jiri na d'ibar ta, tuni ta zube k'asa.




A rud'e Hisham yayi kanta, Haidar har yayo kanta shima sai kuma ya tsaya cak kamar wanda aka rik'e, ya juya ya fice falon.




Hisham a rud'e ya d'auko ruwa a fridge yana watsa mata, ta bud'e idon ta suka sauka kan Hisham, tayi saurin runtse su tana jin tsananin haushin sa, "Am sorry please Bongel, ki.....", Da hannu ta dakatar dashi da cewa "Enough Hisham", Ta mik'e ta nufi hanyar fita, da sauri ya sha gabanta yace "Dan Allah ki saurareni Bongel, wallahi tsananin k'aunar ki yasa nayi haka", Wani banzan kallo ta watsa masa mai cike da takaici, tana jin kamar ta zabga masa mari, k'auna zata sa ya zubar mata da daraja,


"Kiyi hak'uri Dan Allah, i have to do this dan ganin mun mallaki juna" Hisham ya fad'a a marairace, A fusace tace "Bana buk'atar mu mallaki juna in har sai mutuncina ya zube a idon wasu, kasan yadda jifar mutum da kalmar zina take da zafi da rad'ad'i, kasan shaidar zina illar da take wa mutum, meyasa ka zab'i wannan hanya ta zama ta silar auren mu", "Ita kad'ai ce hanya Bongel", "Bani hanya na wuce" Ta fad'a cikin b'acin ran ganin bashi da niyyar gyara mistake d'in sa, Ba dan rai yaso ba ya matsa, Ta fita tana bin hanyar zuwa titi, Bak'in ciki da damuwan suka had'u suka cunkushe zuciyar ta wanda ba zai bayyanu ba, shikenan zargin Haidar a kanta zai k'ara tabbata, watak'ila ma yaje ya sanar dasu Dada dan kub'ucewa auren ta, shikenan mutuncin ta ya zube wurin Dada, Hawaye suka soma ambaliya saman fuskarta, wasu na bin wasu, har ta isa gidansu Asiya, taci sa'a bata tarar da kowa a tsakar gida ba, har ta shige d'aki, Asiya kad'ai ta tarar,




"Lafiya kike kuka, me ya faru?"Asiya ta tambaya cikin damuwa, Kanta ta girgiza tace "Ba komai, kawai auren Haidar ke d'aga mun hankali", "Ki kwantar da hankalin ki, kiyi ta addu'ar zab'in alkhairi" Kanta tayi nodding, Ta jawo kayanta ta soma had'awa, ta yanke shawarar tafiya yau, gaba d'aya hankalinta ya karkata gida, tana son jin d'umin jikin mahaifiyarta, ko zata rage wani rad'ad'i, Haka bata son sake had'a ido da Dada, bata san da wane ido zata kalleta ba, zata koma gida ta amincewa auren Jabeer su Dada a mayar musu kayan su, tafi son auren Jabeer akan Haidar, haka ba zata tab'a iya auren Hisham ba, danginsa na mata kallon mazinaciya wanda tasan abu mai wuya ne su amince ya aure ta, ba wanda zai so dan' sa ya auri mazinaciya.




***************************************


Haidar daga guest house kai tsaye gidan Dada ya nufa, da k'udurin lalata auren sa da Bongel, Sama
Sama ya amsa gaisuwar masu aikin, Dada na kishingid'e kan kujera bacci na son d'aukar ta, Ganin Haidar tace "Ka gama fushin, tunda kaji na nemar maka mata ka d'auke k'afar ka daga gidan nan", "Ina wuni?" Ya fad'a yana kawar da zancen, "Lafiya lau Ango kasha mai", Fuska ba yabo ba fallasa ya zuana saman carpet yace "Dada Dan Allah ina neman alfarma a wurin ki", "Ina jin ka", "Dan Allah ki janye zancen aurena da yarinyar nan, budurwar Hisham ce", Murmushi tayi irin na manya tace "Haidar kenan, idan kasan alkhairin da na hango maka tattare da Bongel da baka ce haka ba, shin ko dan yaron ka ba zaka amincewa auren ba", Da mamaki yake kallon Dada, dama itace Auntyn Irfan, itace Irfan ke yawan magana, taya d'an sa ya shak'u da karuwa, Dada ta katse masa tunani da cewa "Kyau, nasaba, tarbiya, natsuwa da halayya nagari ake nema wurin mace ta gari, Bongel duka ta had'a, ina maka sha'awar auren ta dan tarbiyar yaron ka, da kai kanka ka samu natsuwa da kula a tare da ita", Ya bud'e baki zai sake magana Dada ta dakatar dashi da cewa "Auren ka da Bongel kamar anyi an gama, idan kaga ba'a yi ba to bana numfashi a doron k'asa, kai ko bana raye zan bar wasiyyar tabbatuwar auren ku",


Kansa ya dafe, wacce irin masifa ce ya tsinci kansa a ciki, Taya yaron sa zai samu tarbiya wurin wanda ta kai k'arshe wurin tsantsar rashin tarbiya, taya zai samu natsuwa a tare da Karuwa, ko shakka babu ta zama fuska biyu, macijin sare ka nok'e, Dada kallon kitso take wa rogo, ta b'oye ainihin kalar ta, ta nunawa su Dada ita ta kirki ce, matuk'ar ya aure ta sai ta gwammace gidan yari akan nasa, da k'afafun ta zata bar gidan, Ban da baya son jefa Dada da iyayen nasa a damuwa, da cire k'imar k'anin nasa a idon iyayen su, da ko shakka babu yau zai fasa k'wan dan gujewa auren ta, sai dai girman soyayyar dake tsakanin sa da k'annin sa, da gudun b'acin ran iyayen su, dole ya bar abun a ransa, Ya mik'e ya fita ba tare da ya ma Dada sallama ba, tabi bayan sa da cewa "Watarana da kanka zaka yi mun godiyar gatan da na maka",




******************************


"Kina ganin ya dace ki tafi ba tare da kin sanar da Dada ba" Asiya ta fad'a, Bongel ta numfasa tace "Bana son abunda zai mun shamaki da tafiyata yau", "Ni sai nake ganin ba zata tsayar dake ba", Bongel ta girgiza kai tace "Bar ni kawai na tafi, idan na isa zan kirata", "Shikenan Allah ya tsare ya kai ki lafiya", "Amin", Aina'u ce ta shigo tace "Ga napep din an samu", "Yawwa Aina'u zo ki tayani da wannan" Ta mik'a mata k'aramar jakar ta,


Asiya ta mata rakiya har waje, tana cewa sai mun zo.




****************************


Dada ke had'a kayan fitar bikin Bongel, kala biyar masu kyau da tsada, komai ta saka hadda jewelries, su takalmi da mayafi, alkyabba mai kyau wacce za'a saka mata idan za'a kawota, Anty Mami itama yar' Dada ce tace "Gaskiya Dada kina ji da wannan auren, ban tab'a ganin auren da kika dage a kansa ba irin wannan", Dada tayi murmushi tace "Alkhairin ciki nake hangowa", Anty Mami tace "Allah ya tabbatar da alkhairin sa", "Amin, ki kira Basira kuzo ku tafi, ku biyu kun isa ba sai anyi gayya ba", Anty Mami tace "Toh" tana mik'ewa ta nufi sashen Inna.




*************************


Su Aunty Mami suka dawo suke sanar da Dada, Bongel ta wuce, Dada bata nuna musu bata san wucewar Bongel ba, gudun su ga laifin ta, Tace "Au na manta yau ne tafiyar ta, ku ajiye kayan goben sai a kai mata can garin su, tare da katin gayyata da sauran abubuwan da ya kamata a kai", Aunty Mami tayi dariya tace "Dada tsufa ya soma kama ki", "Kinci gidan ku" Cewar Dada, Suka yi dariya ita da Basira,




Dada mamakin tafiyar Bongel d'in take ba tare da ta sanar da ita ba, bayan sunyi kan idan ta shirya ta kirata, zata aika Hamza direba ya kai ta, duk yadda akayi wani uzurin babban yasa tasan Bongel ba zata tafi haka kawai ba, Ta tabbatarwa kanta da k'ok'arin hana zuciyarta ganin laifin Bongel.




***********************
Bongel sun iso garin malumfashi lafiya, Direba da ya d'auke su ta buk'aci ya kaita gida, ta k'ara masa kud'i, Har ya sauketa ta shiga gidan bata ci karo da kowa d'an gidan su ba, Abu ne yazo da gudu ganin ta ya rungumeta, Ramla ma yau bata je gidan aiki ba ta tashi da ciwon kai, Ta taso ta rungume ta,




Nene dake dakan yaji, ta tsayar da dakan tana duban yar'ta cike da farin cikin ganin ta, "Nene jam bandu", "Jam Bongel", Ramla da Abu suka karb'i kayan hannun ta suna shigar mata dashi ciki, Itama tabi bayan su, Nene ta ajiye dakan ta shiga ciki, ba abunda take buk'ata kamar ji daga bakin Bongel, Nene tace "Su Ramla su fita waje

6 / 12