Chapter 2 Reading BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt Arewa Novels

BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt

Author :  Zee Yabour Category :  Home Of Novels

Chapter   2 / 12

3K to 6K   out of 35.6K words

manta da hakan, ta nisa tace "Hakane Asiya, Allah ya shige mana gaba, yasa mu samu cikin sauk'i", "Amin, naji ance Neco itama wani sati za'a saketa, nan da wata biyu za'a fara rabon admission", "Allah yasa muna da rabon shiga jami'a" Bongel ta fad'a a sanyaye", "Amin Amin", Sukayi sallama ta kashe wayar, ta ba matar gidan wayarta, ta mata godiya ta fito.






Ramla ce ta fad'o cikin d'akin kamar an jefota, tana yi tana waiga baya, "Lafiya? Me ya faru?" Nene da Bongel suka tambaya a tare, Jikin Nene ta fad'a ta fashe da kuka, "Dan Allah ki fad'a mana meke faruwa kukan ki na d'aga mana hankali", Bongel ta fad'a tamkar itama zatayi kukan,


Cikin shesshek'ar kuka tace "Wani ne ya biyoni sai ya kasheni", "Subhanallah kisa me kika masa?", Nene ta tambaya a razane, "Zuwa tab'ani yayi wai na yarda dashi, na huta da siyar da awara kan layi, yasan talauci ne yasa haka, zai bani kud'i masu yawa, naja baya ina cewa ya k'yaleni ya k'ara matso ni, shi...nee na mare sa, ya biyoni yana cewa sai ya kasheni", Bongel idonta ta runtse tana ji rad'ad'i a zuciyarta, banda rashi babu abunda zai sa Ramla soyar awara har wani da' namiji yaso jan ra'ayinta da kud'i, ya zama dole ta nemi ilimi, dan kub'utar da k'annenta.


Nene tace "Kinyi kuskure na mare sa, baki san waye shi ba, baki san me zai iya aikatawa", Bongel cikin zafin rai tace "Bai isa ya mata komai ba sai abunda Allah ya k'addara, meyasa ake d'aukar talaka ba bakin komai ba, meyasa rayuwar talaka kullum take cikin gagari", "Duniyar ce haka, shugwabanni ne mune basu da adalchi, ina rok'on ku da Allah kada ku tab'a siyar da mutuncin ku saboda wani abun duniya, k'ima da darajar mace ta kai budurcin ta gidan mijinta, dukiyar da aka tarata ta hanyar zina k'azamtacciya ce kuma bata da Allah, nasan irin tarbiyar da muka baku amma ina rok'on ku da Allah ku k'ara tsare kanku, ku rik'e maraicin ku, kada ku barwa mahaifinku abun fad'e, matuk'ar kuka yi haka baku masa adalchi ba, a kullum tunanin sa da burinsa ya inganta rayuwarku, kuyi k'ok'arin zama abun koyi da alfahari", Nene ta k'arasa tana duban su, "In Shaa Allah" Suka amsa a tare, "Tashi kije kiyi wanka, kiyi alwala kiyi sallah da karatun qur'ani, zaki samu natsuwa", Nene ta fad'a, Ramla tace "Toh" ta tashi.








OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*


Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


*HASKE WRITERS ASSO...*


SHAFI NA UKU


Tun daga ranar Ramla ta daina yin awara, ta koma aiki a wani gida, tana jeka ka dawo, a wata ana bata dubu uku, Bongel sakamakon su na neco ya fito, tayi k'ok'ari sosai, admission ya fara fitowa har list na farko ya fito, list na biyu suke jira, Bongel kullum cikin fargaba da zullumi take, a rana sai ta kira Asiya sau uku dan jin ko akwai wani bayani,


Suna tsakar gida suna wanki ita da Ramla, yaron mak'wabtansu ya shigo, Yace "Wai Bongel tazo inji maman mu", Gabanta taji ya fad'i tasan kiran na Asiya ne, hannunta ta tsame daga ruwan kumfan, ta wanke, taja mayafinta dake kan igiyar dake shanye tsakar gidan tabi bayansa, Fatsuma ta yatsina baki tace "Ayi dai mu gani idan tusa na hura wuta"


Bongel bata bi ta kan maganarta ba ta fice gidan,


"K'awarki ce tayo waya tana son magana dake", Cewar Maman Jabeer tana mik'a mata waya, Tana karb'a kiran Asiya na sake shigowa, Ta d'auka,


"Lafiya dai ko?", Cewar Bongel, Asiya tace "Lafiya ba lafiya ba toh zance, Baba ke sanar dani wannan karon admission yana matuk'ar wahala sai kana da hanya, amma yace mu had'o takardun mu ya rok'i VC ya taimaka", "Amma nagode sosai Asiya, kiyi wa Baba godiya, In Shaa Allahu gobe zan zo da kaina na kawo", "A'ah ba sai kinzo ba, ki aiko ta mota kawai", "Toh shikenan nagode",


Da murna ta koma gida tana sanar da Nene da Ramla, "Kai yarinyar nan da iyayenta mutanen kirki ne, Allah ya saka musu da aljanna" Nene ta fad'a, "Amin Amin".






Sati biyu da tura takardun ta, suna zaune tsakar gida suna hira, suka jiyo sallamar Asiya, Bongel ta mik'e da fad'in "Asiya zuwa ba sanarwa", Asiya tayi murmushi tace "Tare muke da Baba", "Kice zuwan ba naki bane ke kad'ai", Nene tace "Ki masa iso ya shigo" Ta shiga d'aki ta d'auko hijabin ta,




Bayan an gama gaisawa sun sha ruwa, Baba ya numfasa yace "Da farko dai ina fara baku hak'uri, kuyi hak'uri Dan Allah komai kuka gani muk'addari ne daga ubangiji, kamar yadda Asiya ta sanar da Bongel ta tura takardunta, ni na buk'aci haka da niyyar taimaka musu su samu admission tare, amma sai dai hakan bai yiyu ba, d'aya ta samu d'aya bata samu ba" Bongel k'irjinta ne ya duka, jikinta yayi sanyi ta gama sarewa, Baba ya cigaba da cewa "Wallahi ba da son raina haka ta kasance ba, Asiya suka ba admission, itama VC cewa yayi dan tana yar' cikina shine zai taimaka, kuma ko da yara biyu ne nawa d'aya zai d'auka, nayi k'ok'arin aba Bongel admission d'in, Asiya ta hak'ura dan tana gaya mun burin Bongel na son karatu, wallahi sam yak'i yarda da cewa admission ya riga ya fito da sunan Asiya, kiyi hak'uri Bongel wallahi bani da wata hanya, k'asar tamu ce sai dai muce Allah ya sawwak'a"




Tuni hawaye suka wanke fuskar Bongel, ta kasa cewa komai, Nene duk da yadda zuciyarta ke soya tayi k'arfin halin cewa "Haka Allah ya k'addara, mun gode sosai da k'ok'ari baban Asiya Allah ya bar zumunci", "Amin" Ya amsa, Ramla ma jikinta yayi sanyi matuk'a, gaba d'aya hope d'insu akan Bongel yake, yanzu komai ya yanke, Baban Asiya ya jima yana basu baki kafin suka tafi, Asiya ma rai babu dad'i ta tafi.




"Wannan k'asa tamu Allah ya kawo mana sauk'i, na kasa cika burin Bappa na son ganin Bongel tayi ilimi mai zurfi, kayi hak'uri Bappa bani da wata hanya, talaka bashi da galihu a k'asar nan" Ta k'arasa da hawaye, "Ki daina d'aurawa kanki laifi Nene, haka Allah ya k'addaru bazan yi ilimi mai zurfi ba, watak'ila haka zamu k'are rayuwar mu duk da bawa baya yanke rai ga rahamar ubangiji", Abu duk da kasancewarsa yaro ya nuna rashin jin dad'in sa, "Yanzu shikenan nima bazan shiga makaranta ba"
Ya fad'a a sanyaye, Bongel ta jawosa jikinta "Idan da rabo zaka yi ilimin boko Abu", "Allah yasa", Tace "Amin" cike da tausayin sa.






Bongel ta koma sukuku, walwalarta ta rage, rashin samun admission ba k'aramin tab'a ta yayi ba, gashi kullum rayuwa k'ara wuya take musu, babu mai taimaka musu, dangin Nene ba masu k'arfi bane, suma suna fama da kansu, iyayenta ma suna rugar ard'o can wurin funtua.




Asiya wurin printing takardar admission d'inta taji wasu yan' mata na hira, "Wallahi kin taimakeni da kika kaini wurin Hisham, gashi na samu admission cikin sauk'i" Cewar d'aya daga cikin yan' matan, "Ai Hisham sai idan baka je wurin sa ba, admission kamar ka samu amma fah..." Bata k'arasa ba sukayi dariya da shewa, Jin haka Asiya ta k'arasa wurinsu, ta musu sallama suka amsa, "Dan Allah kuyi hak'uri na saurari hirar ku, wata yar'uwata zaku taimakawa itama ta samu admission", Suka kalli juna, D'ayar tace "Ba damuwa bane", "A ina zamu samesa Dan Allah", K'aramin kati ta fito dashi daga jaka ta mik'a mata, Ta karb'a tana mata godiya,


Ta kasa bari ta koma gida, nan take ta soma kiran wayar Maman Jabeer, anci sa'a Bongel ta shigo itama ta kira Asiya kwana biyu basu yi waya ba, "Kinga yar' halak na kira" Cewar Maman Jabeer, Bongel tace "Aikuwa" tana karb'ar waya,


"Albishirin zan miki, na samu wata hanya da zaki samu admission" Cewar Asiya da k'arfi kamar zata fasa mata dodon kunne,"Da gaske?", "Wallahi da gaske nake, idan zaki iya ki shigowa katsina gobe", "Ko a yau kike so zan shigo", "Toh sai kinzo", Ta kashe wayar cike da farin ciki,




Nene farin cikin daya bayyana kan fuskarta ba k'arami bane, haka Ramla da Abu, tun a daren Bongel ta had'a kayanta kala uku da abunda zata buk'ata cikin jaka, Tunda safe ko kari batayi ba, ta shirya tafiya, Nene tabi ta addu'o'i na nasara da kariya, wurin maman jabeer ta ari dubu biyu da zatayi kud'in mota, Fatsuma da Dije nata yada habaici bata ce musu komai ba suna fad'in haka za'a je a dawo.






Tafiyar awa d'aya da rabi ya d'auke su, suka isa garin katsina, suna isa tasha, ta ari waya ta kira Asiya, ta mata kwatancen unguwar su, mai napep ta samu ta fad'a masa unguwar, ya kaita har k'ofar gidansu Asiya, ta sallame sa ya tafi, gida ne k'arami sosai, kana gani kasan suma basu da hali, d'akuna biyu ne sai band'aki a tsakar gida, da k'aramin kicin, Cike da far'a mutanen gidan suka tarbeta, Asiya ta sauketa d'akinsu ita da k'annenta mata uku, haka suke gwamatsawa,




Asiya ta sanar da ita komai, ta fiddo katin ta nuna mata, hakanan Bongel ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, "Amma Asiya kina ganin babu matsala", "Wacce matsala Bongel, zuwa zamuyi mu rok'esa mu fad'a masa buk'atar mu In Shaa Allah zai taimaka ki samu admission", "Toh shikenan yaushe zamu je?", "Yanzu ba zamu tsaya b'ata lokaci ba", Bongel tace "Toh" tana mik'ewa, ta d'auki k'aramar jakarta da takardun ta ke ciki, fuskarta kad'ai ta wanke da ruwa, saboda zufar da tayi, kasancewar lokaci ne na zafi,




"Daga zuwa ba hutawa sai fita" Cewar Mama dake tsakar gida tana yankan alayyahu, Asiya tace "Mama da zafi zafi ake dukan ice", Mama tayi dariya tace "Allah ya bada sa'a", Suka amsa "Amin",








H&H GLOBAL RESOURCES


Shine sunan da suka gani manne a tafkeken ginin dake gabansu, wanda jikinsa duka glass ne yana walk'iya, Bongel ta kalli Asiya tace "Anya bamu kawo kanmu inda yafi k'arfin mu ba", Asiya duk da tasha jinin jikinta ganin girman ginin, ta dake tace "Ki cire tsoro Bongel bakya son shiga jami'a ki cika burin Bappa", Bongel tayi saurin gyad'a kai, Tare suka jera zuwa building d'in, Bongel na ambaton Allah a ranta,




Securities dake tsaye bakin wurin sukayi checking d'insu, suka k'arasa, suna zuwa wurin shiga k'ofa ta bud'e, Karon farko a rayuwarsu da suka ga k'ofa na bud'ewa da kanta, a tare suka zaro ido, Suna shiga sanyin Ac mai rab'a ya soma dukan fatar jikin su, kalle kalle suka tsaya yi, basu san ina zasu yi ba, suna tunanin wacce duniya ce suka kawo kansu, tsabar had'uwar wurin sai suke jin tamkar ba'a k'asar suke ba,


Wata mata ta nufo su da fad'in "May i help you", Cikin daburcewa Asiya tace "Wurin Hisham muka zo", "This way floor 2" Ta nuna musu hanya,




Elevator ne a wurin sukayi tsaye suna faman k'wankwasawa a zaton su nan ne office d'in sa, K'ofar suka ga ta bud'e, budurwa mai ji da kyau da gayu kanta yasha attach ta baza su shi har baya, da fixed nails, zaka rantse ba musulma bace, ta fito banzan kallo ta watsa musu ta wuce, Asiya taja tsaki , Bongel tace "Mu muka kawo kanmu",




Wani babban mutum ne yazo shiga, suka gaishe sa har k'asa ya amsa, a ransa ya yaba da natsuwar su, Yace "Wa kuke nema?", Asiya tace "Hisham", "Muje" Ya fad'a, Suka bi bayansa,


Mamaki ya kama su ganin inda suka shiga, suka ga ya danna abu wurin wasu numbers, sama suka ji ana yi dasu suka had'iye yawun tsoro tare da k'ank'ame juna, dariya suka so su bashi yadda yaga sun tsorata,


Suna ganin k'ofar ta bud'e, suka fito a guje, "Can zaku je nan ne office d'in" Mutumin ya fad'a yana nuna musu wata k'ofa, Mun gode Baba", Asiya ta fad'a,


"Meye muka shiga yanzu mai kamar jirgi" Cewar Bongel, Asiya tace "Nima ban sani ba, ban tab'a ganinsa ko jin labari ba", "Allah yasa mu koma gida lafiya idan ba mun kawo kanmu inda za'a yanka mu ba", Asiya tayi dariya tace "Har kin bani dariya, duniyar ce da fad'i, Allah ne bai tab'a kawo mu ba, wuri ne na masu naira", Bongel bata ce komai ba, har suka kai bak'in k'ofar, Knocking sukayi, Suka ji wata murya tace "Yes", A hankali Asiya ta murd'a k'ofar suka shiga, wata mace suka tarar zaune tana rubuce rubuce a takarda, Ta kallesu tace "Ku k'arasa ciki",




Asiya na gaba Bongel na bin ta a baya, kusan mutuwar tsaye sukayi ganin had'uwar office d'in, hankalinsu bai k'ara tashi ba, sai da suka ga wanda ke zaune kan kujerar dake nuna shine mallakin office d'in, had'uwar sa da kyansa yasa suka k'ara shan jinin jikinsu,


"Ku k'araso mana" Suka tsinci muryar sa, wanda basu tsammaci jin haka ba, A sanyaye suka k'arasa, ya nuna musu kujera su zauna, k'amshin turaren sa mai dad'i ke ziyartar k'ofofin hancin su, idonsa k'yam akan Bongel, duk ta tsargu da irin kallon da yake mata,




Asiya tayi k'arfin halin cewa "Dan Allah taimaka mana muka zo kayi", "Wane irin taimako kenan?", Ta nuna Bongel, "Ita ke neman admission, wallahi munyi iya k'ok'arin mu ta kasa samu shine aka ce muzo wurin ka", Murmushin gefen baki yayi yace "Admission kamar ta samu ta gama but akwai sharad'i", Bongel tayi saurin cewa "Ko wane sharad'i ne zan bi", "Ki dawo gobe ke kad'ai, ga numberta i will let u know inda zamu had'u" Ya k'arasa yana ajiye mata k'aramin katin sa, tasa hannu ta d'auka tana masa godiya, Suka mik'e zasu fita har sun kai k'ofa ya kira Bongel, ta dawo, bandir na 500 ya mik'a mata, Tayi saurin cewa "A'ah mun gode", a tsawon rayuwarta bata tab'a ganin kud'i masu yawan su ba,




"Bana kyauta a mayar mun" Ya fad'a cikin dakewa, Kwarjini taji ya mata ta kasa k'ara musa masa, Hannu biyu tasa ta karb'a da fad'in "Allah ya saka da alkhairi", "Amin" Ya amsa, Ta juya zuwa k'ofar fita, yabi bayanta da kallo, yayi juyi kan kujerar sa yana murmushi.




Har suka isa gida suna jinjina kyautar kud'in da ya musu, suna zuwa suka nunawa Baba, ya musu fad'an karb'a da sukayi, yace kada su k'ara daga yau, suka ce toh, Bongel baccin farin ciki tayi na jin zata samu admission, tana alla-alla safiya tayi sai wani b'angare na zuciyarta na saka mata tunanin meyasa zai ce tazo ita kad'ai.












OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*


Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


*HASKE WRITERS ASSO...*


SHAFI NA BIYAR




Safiyar yau Bongel sukuku ta tashi, duk da tana k'ok'arin b'oye damuwar ta, Asiya taso ta fahimta sai dai bata tambayeta ba, sanin mutum ce mai zurfin ciki, idan ba ita tayi niyyar fad'a maka abunda ke damunta ba, tambayar duniya amsar d'aya ce babu komai,


Ita ta taya Asiya suka gyara gidan suka dama kunu wanda dashi kusan kullum su Asiya ke karin safe, Bongel kad'an ta sha tace ta k'oshi, bata jin sawa cikinta komai,


"Ina tunanin yau zan koma", "Kai haba ba zaki bari ki mana kwana biyu ba", "Ina so na koma na sake shirin dawowa makaranta, naga saura sati d'aya a fara registration, kuma banda abun ki ni da zan dawo garin ku", "Hakane, bama garin mu kad'ai ba gidan mu, dan anan zaki zauna, jiya Baba yace na fad'a miki", Murmushi tayi tana jin dad'in yadda Asiya da iyayenta ke nuna k'auna gareta.




12 na rana ta shirya wucewa, a tsakar gida ta samu Baba da Mama, Bongel har kin shirya wucewa" Baba ya fad'a, Tace "Eh Baba", "Toh ga kud'in da mutumin nan ya baku, kunfi mu buk'atar su, ki kaiwa mahaifiyar ki kwa rage wani abu", Saurin girgiza kai tayi tace "A'ah Baba", "Ki karb'a Bongel, reg na makaranta kina buk'atar kud'i, naira ba zamu tab'a cikin kud'in nan ba wallahi" Ya k'arasa yana mik'awa Asiya "Karb'a ki sa mata a jaka", Asiya ta karb'a ta bud'e jakarta ta jefa, Godiya ta musu sosai, ta tafi da tunanin karamci irin nasu, Asiya da K'anwarta Aina'u suka rakata har tasha, sai da suka tabbatar ta shiga mota, suka taho gida.




***************


Tsaye yake bakin balcony na office d'in sa, hannun sa rik'e da k'aramin mug yana sipping hot tea, ta glass na wurin yake hango motocin dake wucewa ta titi, Kallo d'aya zaka masa kasan akwai abunda ke damun sa, Komawa yayi cikin office d'in, ya zauna kan kujerar sa, ya jawo drawer dake manne da teburin dake gabansa, wani file ya d'auko yana dube dube a ciki,




Hisham cikin sanyin jiki ya tura k'ofar office d'in ya shigo da sallama, Haidar yaji sallamar yayi tamkar bai ji ba, har ya k'araso ya zauna kan kujera tare da fad'in "Yaya Haidar sannu da aiki", takardun ya cigaba da dubawa ba tare da yabi ta kansa ba, Jikin Hisham ya k'ara yin sanyi, bai tab'a masa irin haka ba,




"Yaya Dan Allah kayi hak'uri", Still bai tanka sa ba, "Yaya kada kayi fushi dani", A fusace ya d'ago yace "Tashi ka fita Hisham, is your life ka cigaba da duk abunda kaga dama", "Yay...", Yayi saurin katse sa "I said out", Hisham ya mik'e yana jin duniyar ta masa zafi, So shak'uwa da k'auna ce mai k'arfi tsakanin su, tun tashin sa bashi da abokin shawara kamar Haidar, duk wata matsalar sa shi yake kawowa, basa k'aunar b'acin ran junan su, fushin Haidar a gare sa yasa komai ya jagule masa.




"Ya zama dole na nuna masa fushina wannan karon, ko hakan zai sa ya shiryu, ya gyara halayyar sa" Haidar ya fad'a yana cigaba da

2 / 12