Chapter 11 Reading BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt Arewa Novels

BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt

Author :  Zee Yabour Category :  Home Of Novels

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 35.6K words

zauna tana sha.




*************************


Haidar yana dawowa ko hutawa bai yi ba, Rauda ta soma masa complain Bongel bata yi girki ba, Kallonta yayi yace "Me ya hana ke bakiyi ba", Ta marairaice fuska tace "Kasan ni fah ba lafiya ce dani ba", Harara ya watsa mata yace "Ki cire lalaci da ragwanci ki rik'e gidanki", Rauda ta b'ata rai a zuciyarta tana kunkunin ba zata yi ba, Haidar bai sake bi ta kanta ba, ya cigaba da sabgogin gabansa.






Bongel damuwar dake cikinta ta korar mata yunwa, sam bata buk'aci komai ba sai ruwa, wunin ranar su tayi ta d'irkawa cikin ta, daren ranar haka ta raba sa wurin k'iyamul laili da rok'on Allah.




*******************


Rauda ganin Haidar bai sake mata ba yasa ta tafi d'akinta ta kwana,


Washegari Haidar har ya shirya ya fito Rauda na can na bacci, D'akin ya shiga ya kunna fitila haske ya gauraya d'akin, Rauda ba ma'abociyar son haske bace kullum wutar d'akinta a kashe, Haidar dubansa ya kai kanta, yaja siririn tsaki ganin irin kwanciyar da tayi, k'afafunta biyu sun ware da juna, Ya tako zuwa cikin d'aki, Abu yaji ya taka da k'afar sa, kamar takarda ko leda, Ya d'auke k'afar yana kai duban sa, dubu d'aya ce a k'asan carpet d'in, Ya duk'a zai kai hannun sa ya d'auka ba tare da tunanin komai, yaga wasu guda biyu a k'asan, K'irjinsa ya doka da k'arfi yasa hannu ya d'auki kud'in yana bin su da kallo, "Sune kud'in da suka yi missing a nawa kenan" Ya fad'a zuciyarsa na harbawa da k'arfi, Wani wawan duka ya kaiwa cinyar Rauda, ta tashi a zabure,




"Me kud'in nan ke yi a d'akin ki", Jin haka tayi saurin bud'e ido ba shiri, ta kai dubanta ga kud'in dake hannun sa, "Ina tambayar ki kinyi shiru" Ya fad'a a tsawace, Murya na rawa tace "Uhm.. uhmm nima ban sani ba", Kallonta yayi tsaf yana hango zallar rashin gaskiya a tare da ita, Babu alamar wasa yace "Ki fad'a kud'in nan ta yadda suka zo d'akin ki kafin raina ya b'aci", "Nima ban sani ba", K'afar sa ya d'aura kan gadon, yasa hannu d'aya ya jawota gaf da shi, Yace "Ko ki gaya mun gaskiya ko nasa k'afata na tattaka ki", "Kar ka manta ina d'auke da cikin ka fah", "To hell" Ya fad'a cikin b'acin rai, Jin haka jikinta ya sake yin sanyi tana jin tashin hankali na dabaibayeta,




"Kema satar kika mun kenan", Dan sam bai kawowa ransa ita ta kai d'akin Bongel d'in ba, Rauda tayi saurin girgiza kai da cewa "Allah ban sata ba", "Me kika yi toh" Ya fad'a cikin karaji, Murya na rawa tace "Uhmm... ina jin aljanu ne suka kawo d'akina suka kai d'akinta dan su had'a fitina", Kallo mai cike da mamaki yake bin Rauda dashi yace "A yanzu ne kika san aljanu kenan da yazo kan ki", "Kayi hak'uri My dear, amma ina kyautata zaton sune, bayan wucewar ka na samu Bongel na mata magana ta rantse mun bata d'auka ba, na yarda batayi satar ba wallahi, aljanu ne suka kai mata", Shiru yayi yana nazarin Bongel d'in, zai iya yarda ba ita tayi ba, duba da tun zuwanta gidan naira biyar d'in sa bata tab'a b'acewa ba, da halinta ne sata zatayi ko sau d'aya, Haka Rauda baya tunanin zata yi, kuma me zai kawo dubu uku d'akin nata sai dai aikin aljanun,




Karon farko yayi feeling guilty akan abunda ya mata, yana jin bai kyauta ba, wani b'angaren na zuciyarsa na nuna masa ba haka ba, "Ganin kud'in cikin akwatin ta ko waye haka zai yi" Ya fad'a yana son nunawa kansa baiyi wani abu ba, Ya fito d'akin zuwa falon, Daidai lokacin Bongel ta fito da shirin zuwa school, Kallo d'aya ya mata yaga idonta a kumbure alamar tasha kuka, Sai yaji zuciyarsa ta raunana, Ya bud'e baki zai yi magana sai kuma yayi shiru, Ta wuce abunta ba tare da nuna tasan dashi ba,




*********************


A makaranta Asiya tayi ta tambayar me ya faru, tak'i sanar da ita, tace mata kawai yaji ya shigar mata ido, Asiya bata yarda ba, dan kowa ya ganta yasan kuka tayi, Ta rasa zurfin ciki irin na Bongel, suna matsayin aminai wanda sun zama kamar yan' uwa amma abubuwa da yawa dangane da ita, bata sanar da ita, Bongel sukuku tayi a ajin, duk yadda take son b'oye damuwarta abun yaci tura, Lecture Haidar ce dasu ranar, a ajin sam tak'i bari su had'a ido, wanda shima duk yake jin sa unusual karon farko, yana jin sa tamkar mara gaskiya.






*******************


"Bongel da Haidar basu da niyyar rabuwa da juna, ni zan rabasu ta kowacce hanya, na gaji da zaman jira, i want Bongel back in my life, na gaji da amsa sunanta matar Haidar, ina son nan bada jimawa ba ta soma amsa sunan matar Hisham", Hisham ya fad'a yana zagaye d'akin sa, zuciyarsa babu komai ciki sai zallar son kai da son cikar burin sa ta kowacce hanya, Wayarsa ya d'auka ya soma kiran number Rauda da yayi ma saving da Sexy lady, Bugu d'aya ta d'auka da cewa "Hisham manyan gari", Yace "Sexy lady", "Gaskiya suna nan ya fita a bakin ka, yanzu matar yaya", Yayi dariya yace "Toh matar yaya", "Yawwa ko kai fah", Ya numfasa yace "I want us to meet and discuss something very important", Gabanta ne ya fad'i tace "Please Hisham kar ka mayar da hannun agogo baya", Dariya yayi yace "Haba Matar Yaya kina tunanin zan maido abunda ya wuce ne, ko d'aya wani abu ne daban da ya shafi rayuwarmu da cigaban mu", Ta jinjina kai tamkar tana gabansa tace "Toh yanzu ina zamu had'u?", "Idan Haidar da Bongel basa nan, ki sanar dani nazo", Tace "Ok ba damuwa", Sukayi sallama ta kashe wayar da tunanin Me Hisham yake so su tattauna, tana fatan ba wani abu bane da zai kawo mata matsala a rayuwar auren ta.






****************************
Haidar tunanin ba Bongel tayi sata ba, ya hana masa sukuni, yana jin babu dad'i na tuhumar da yayi mata, hakan yasa ya yanke shawarar tura mata text message, wayarsa ya d'auka ya duba numberta wacce yayi saving da Bongel, tun lokacin da ya siyan mata waya, yayi saving ne ba dan yasa wa ransa akwai ranar da zata zo ya kirata ko ya mata text, Yayi ne kawai saboda gudun abunda zai taso,




Bongel tunda ta dawo school ta shige d'akinta ta kwanta, k'arar shigowar text wayarta, yasa ta tashi ta jawo wayar ta duba, "Na fahimci bake kika yi satar ba" Ta karanta ta duba number wacce babu suna, amma tana da tabbacin mai ita Haidar ne, Kaso sittin na damuwarta taji ya rage, jin cewar ya gane ba ita bace, sai dai taso jin waye ya mata sharrin, amma tunda an fahimci ba ita bace, a haka ma ta godewa Allah, Alhamdulillah, Karon farko ta kub'uta daga zargin Haidar, duk da cewa akwai wasu tarin zargin da yake mata, but ta godewa Allah ta kub'uta na sata,






Haidar wayar ya kalla yaga time, yana kyautata zaton zuwa yanzu ta karanta, ya sauke ajiyar zuciya yana jin ya sauke nauyin, Rauda ce ta kwanta kan k'irjin sa, Cikin sanyin murya tace "Please my dear a samu yar' aiki da zata rik'a tayani, wallahi yau ma da k'yar na dafa mana indomie", Janye jikinsa yayi da cewa "Yar' aiki ta gama zama gidan nan, ki tashi kije ki dafa mun jollof na macaroni", "Nace na dafa indomie fah", Hararar da ya watsa mata yasa tayi saurin mik'ewa, tana kunkuni ta fita.


MU HADU GOBE🙂


FOLLOW, VOTE AND COMMENT








OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*


Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


*HASKE WRITERS ASSO...*


ARBA'IN DA BIYAR


SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298




"Wallahi dole ma na kori Bongel a gidan nan, ko dan na samu kan Haidar, na tabbata zamanta yasa baya so a d'auko yar' aiki, ta kub'uta na sata amma wallahi ba zata k'ubuta sauran dake tunkaro ta ba" Cewar Rauda tana shiga kitchen cikin b'acin rai.




*********************
Bongel sosai ta samu bacci daren yau, zuciyarta ta rage nauyin da ta mata, haka kaso talatin na damuwarta ya tafi, tunanin ta d'aya yanzu yadda zata k'are da Hamma Siddiku zancen kayan d'aki.






Washegari tunda safe ta fice school, makarantar kusan kowa ka gani da littafi ko handout a hannun sa kasancewar exam ta gabato, Bongel da Asiya ma k'ebantaccen wuri suka samu suna karatu, Bongel ta maida dukkan hankalinta kan karatun, duk tunanin da yazo mata tana saurin datse shi, fatan ta wannan semester kada ta samu carry over ko d'aya, tana addu'ar Allah ya d'aura ta kan Haidar kada ya kayar da ita course d'in sa.




***************************


Haidar na fita office, Rauda ta d'auki waya ta kira Hisham, Yana kwance a d'akinsa bai fita office ba, yana jiran kiran Rauda, Yana ganin kiranta babu b'ata lokaci ya d'auka, "Kazo yanzu duka sun fita", Cewar Rauda, Ya amsa da "Okay" Ya kashe wayar, Ya mik'e da yin shu'umin murmushi, Yayi shirin sa dan daga can zai wuce office.






Da sallama ya shigo falon, Rauda dake zaune kan kujera, bakinta chewing gum ne tana tauna, ta amsa da sakin fuska, Yace "Matar Yaya" yana zama kan kujera, Ta amsa "Na'am Hisham manyan gari", Yayi dariya kana ya numfasa yace "Nasan ki Rauda, nasan kina cikin jerin mata masu tsananin kishi, dan haka nake da k'arin tabbacin bakya son zaman Bongel a gidan nan", Rauda ta sauke ajiyar zuciya da cewa "K'warai, bana k'aunar na bud'e ido na ganta, burina na zama ni kad'ai a wurin mijina", Hisham yayi murmushin gefen baki yace "Yau zan sanar dake wani abu da baki sani ba, Ina matuk'ar son Bongel, so mai tsanani, babban burina shine na mallaketa matsayin matata", Rauda shiru tayi a zuciyarta tace "Ruwa baya tsami k'asa banza, ko shakka babu taga alamar haka daga kallon da yake ma Bongel d'in", Ya katse zancen zucin ta da cewa "So ina so mu had'a k'arfi wurin ganin mun raba su, Haidar ya zama mallakin ki ke kad'ai, Bongel ta zama tawa", Rauda kanta ta jinjina cike da gamsuwa tace "Toh ta ina zamu fara", Yace "Gud, zan sanar dake plan d'in farko zuwa gobe, yau nazo ne dan jin ta bakin ki, ko zan samu goyon baya", Rauda tace "Kai ma kasan dole na baka goyon baya yadda na tsani kishiya, ai duk abunda zai fitar da ita gidan nan, ina maraba dashi", Suka fashe da dariya,


Dariyar ta tsaya cak ganin Haidar tsaye yana kallon su, Mamaki, tsoro had'i da firgici ya dabaibaye su lokaci d'aya, Kafin d'ayansu yayi magana Haidar ya shige ciki ba tare yace musu uffan ba, D'akin ya shiga ya kwanta, ciwon kai sosai ya dawo dashi gida, wanda tunani da stress ya haddasa masa,




Hisham ya sauke ajiyar zuciya da cewa "Wai! Na d'auka yaji zancen mu", Rauda tace "Wallahi nima har hantar cikina ta kad'a", Hisham yayi dariya da cewa "Sarkin tsoro, bara na tafi sai na kira ki", Tace "Ok sai anjima", Ta tashi ta nufi d'akin,




Ganin Haidar kwance tasan ba lafiya ba, bakin gadon ta zauna tace "My dear ina fatan lafiya", "Headache" ya bata amsa a dak'ile, "Ayyah sorry kasha magani", Ya mata nodding kai, Ta kwanta gefen sa tare da saka hannayen ta ta rungume sa, ba dad'in hakan yaji ba but bai hana ta ba, sai idonsa da ya runtse yana jiran zuwan bacci.




******************************


Bongel sun soma exams, kullum bata da lokaci tana makaranta sai yamma lik'is take dawowa, ko jarabawar safe suka yi sai ta tsaya cikin school tayi karatu, Idan ta dawo haka zata yi aikin gidan, dan Rauda da kanta tayi wa Haidar magana ya raba musu girki, ta gaji da yi ita kad'ai, Haidar ba musu yace kowaccen su ta rik'a yi kwana biyu biyu dan shi kansa yana buk'atar girkin Bongel na Rauda cin dole yake masa, Bongel babu musu ta karb'a, duk da k'asan zuciyarta taji babu dad'i wane irin raba girki ne wanann, babu miji ba dan tana son kusancin su da Haidar ba, sai dai a saninta ranar girki kai ke da miji, amma ita hatta ranar girkin nata Haidar yana wurin Rauda, wane irin rayuwar aure ne ta tsinci kanta, ta kan yiwa kanta tambayar lokuta da dama,






Yau ma ta dawo gida a gajiye, ta shiga kitchen tayi girki, kana ta koma d'aki, Bak'uwar number taga na kiranta, Ta d'auka, "Assalamu alaikum Adda" Taji muryar Ramla, "Wslm Ramla ya gida?", "Lafiya lau Adda", "Ina kika samu waya", Tana dariya tace "Yaya Hisham ne ya siyan mun wai mu rik'a kiran ki kullum", "Hisham" Bongel ta maimaita a ranta tana mamaki, Ramla ta katse tunanin ta da cewa "Ga nene", Nene ta karb'i wayar da yin sallama, Bongel ta amsa tace "Nene ina wuni?", "Lafiya lau, ya mutan gida da karatu?", "Alhamdulillah", "K'anin mijinki yana k'ok'ari sosai, ki mishi godiya kullum baya gajiya da mana hidima", Bongel tace "In Shaa Allah" K'asan zuciyarta mamakin Hisham d'in take, hakan na nufin soyayyarta har yau na cikin zuciyar sa shiyasa yake kyautatawa ahalin ta, ko kuwa yana yi ne kawai dan kyautatawa shine ta kasa ganewa, Ta katsewa kanta tunanin da cewa "Nene ya shirin Bikin saude", "Alhamdulillah yanzu ma ai saura sati biyu, zaki zo dai ko", Tace "In Shaa Allah" tana jin natsuwa a ranta dama ta tambayi Nene ne dan son jin ko Hamma Siddiku ya sameta kan zancen kayan d'aki, sanin k'aramin halin sa ne ya tadawa Nene hankali, abunda bata k'auna, Sukayi sallama ta kashe wayar.




***************************


"Ya kamata muje asibiti dan sanin lafiyar cikin ki", Cewar Hajiya Mariya, Rauda dake kange da waya a kunne tace "Toh Mummy", "So ki shirya gobe zan zo na d'auke ki mu tafi", Tace "Toh", "Yawwa sai anjima", "Bye Mummy", Ta kashe wayar tare da shafa cikinta tace "Babyna nasan ma kana lafiya" Tayi murmushi dan ba k'aramin son cikin take yanzu ba.




*****************
"Wai ke ba zaki hak'ura da Hisham ba, mutumin nan fah ba son ki yake yanzu ba, kullum cikin wulak'anta ki yake" Cewar Fido, Ihsan tace "Hmm Fido kenan kina tunanin zan bar sa yaci bulus, wallahi idan kin ga na hak'ura da Hisham to mutuwa nayi", Ta jinjina kai tace "Shikenan Allah ya taimaka", Ihsan ta amsa da "Amin", Tana taunar chewing gum kamar tsohuwar karuwa.




***********************


Yau ranar girkin Rauda ce, hakan yasa dan dole ta tashi da wuri ta shirya Irfan, ta shiga kicin had'a breakfast, ruwan shayi tayi da irish, dan sune mafi sauk'i, Haidar kad'ai yaci a cewarta zuciyarta ke tashi, Bayan ya kammala ci ya mik'e zai fita, Tace "My dear anjima Mummy zata zo muje asibiti duba lafiyar babyn ka", Kansa yayi nodding yace "Ok" ya saka hannu a aljihu ya zaro kud'i masu yawa ya bata sanin asibiti dole a buk'aci kud'i, Tasa hannu ta karb'a tace "Thanks",




***********************


Likita bayan ya gama gwaje gwajen sa ya buk'aci ganin sa office d'in sa, Suka shiga, Ya gyara zaman madubin dake idonsa ya kai dubansa gare su da cewa "A bisa bincike da mukayi gaskiya bata da ciki", "What" Suka fad'a a zabure, Dr ya jinjina kai yace "K'warai bata d'auke da juna ba, face infection wato cutar sanyi wacce ta mata mugun kamu, shine dalilin da yasa period d'inta ya d'auke na tsawon lokaci", Rauda tuni hawaye suka soma zirya kan kumatun ta tace "Na shiga uku wayyo ni Allah na", "Subhanallah ba wani babban matsala bane ai, za'a d'aura ki kan medication wanda In Shaa Allah zaki samu sauk'i, sai dai ki kiyaye inserting abubuwa a gabanki, ba komai za'a baku mata ku cusa a gaba ba, mafi yawa shi ke jawo muku matsala", Hajiya Mariya kad'ai tayi k'arfin halin amsa sa, Rauda kuwa kuka tamkar wacce akayi wa mutuwa,


Dr ya rubuta musu magunguna da allurai da zata rik'a karb'a, Suka fito, Rauda na kuka, a mota Hajiya Mariya ke lallashin ta tace "Ki daina kukan, ai ba cewa akayi ba zaki haihu ba, yanzu ki fara treating infection nasan kina gamawa ciki zai shiga", "Mummy me zan cewa Yaya Haidar yanzu bayan na gama fad'a masa ina da ciki, ga shegiyar can sai tamun dariya", Hajiya Mariya taja ajiyar zuciya da cewa "Kiyi shiru kar ki fad'awa kowa yanzu har sai mun gama maganin infection d'in, ki barsa a cewar kina da ciki", Ta jinjina kai da cewa "Toh", K'asan zuciyarta zallar bak'in ciki ne, har suka isa gida tana kuka, Ta sauka aka wuce da Hajiya Mariya gida.






Tana ganin kiran Hisham tak'i d'auka, b'acin rai da damuwar da take ciki bata jin magana da kowa, yanzu ita bama ta fitar Bongel gidan take ba, jin cewar bata da ciki ga infection yafi komai d'aga mata hankali.




Hisham yayi tsaki yana cillar da wayar gefe, "Ko gidan uwar wa ta ajiye wayar oho" Ya fad'a cikin takaici, yaso samunta yanzu dan aiwatar da plan d'in sa, a yadda yake ji tamkar yaje ya fitar da Bongel daga gidan Haidar ta dawo gidan sa.






FOLLOW, VOTE AND COMMENT




OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*


Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


*HASKE WRITERS ASSO...*


ARBA'IN DA SHIDA


SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298




Alhaji Sani maigoro ya yarce zufar data keto masa a goshi jin zancen Hajiya Mariya, Fuska d'auke da zallar damuwa da bak'in ciki yace "Ban tab'a jin labari mara dad'i irin wannan ba, wai ma taya za'a ce babu ciki, shin dama ba asibiti ya tabbatar ba hasashen ku kawai ba tare da wani gwaji ba", Hajiya

11 / 12