Author : Zee Yabour Category : Home Of Novels
mariya ta marairaice fuska tace "Wallahi ranar da naji, naga alamar ciki tare da ita", Tsaki yayi yace "Burina da nake ganin ya gabato, yanzu ya k'ara nisa", Ta d'aura hannu kan kafad'ar sa tace "Kayi hak'uri Alhaji, Sannu bata hani ga zuwa sai dai a dad'e ba'a je ba, kuma ai wani jinkirin alkhairi ne", Ya jinjina kai yace "Ko nawa ne ni zan bada dan ganin an kawar da cutar sanyin dake jikin ta, ta samu d'aukar ciki", "In Shaa Allah zan yi k'ok'arin ganin haka", "Allah yasa" Ya fad'a yana fusgar da iskan baki mai zafi.
*************************
Rauda ta d'auki shawarar mahaifiyarta sam bata nunawa Haidar alamar babu ciki ba, Yau ma tashi tayi da kakarin amai, ta shiga toilet tana yi kamar zata amayo yan' cikin ta, Haidar yabi ta ya rik'e ta yana mata sannu, Bayan ta dakata, ya jawota suka dawo d'aki, Ta kwanta jikinsa tana jan numfashi da k'yar kamar da gaske,
"Da kuka je asibiti me Dr yace, banji kimun wani bayani ba" Cewar Haidar, "Yace Babyn lafiya lau, ba wata matsala", "Ina result?", "Ai bai bayar da komai ba, sai magani da ya rubuta mun muka siya", Ya bud'e baki zai yi magana, yayi shiru, Ajiyar zuciya ta sauke da yin hamdala a zuciyarta bai d'ago ta ba.
**************************
Bongel bata da exam sai bayan sati d'aya wacce itace jarabawar k'arshe ta semester, Yau tana gida bata fita school ba, sha'awar waina ta tashi dashi, Hakan yasa tun da asuba data tashi sallah ta jik'a shinkafa, Ana kiran azahar ta kammala ta zuba a kuloli, har da Ammi ta d'ibarwa, ta jere a k'aramin basket, ta yafa mayafinta zuwa kai mata, sam Haidar bai mata iyaka da zuwa b'angaren Ammi ba, duk lokacin da taga dama take zuwa ba tare da ta tambayi izinin shi ba, Fitowar ta d'akin akan idonsa, yana zaune falon tare da Rauda, Kyau yaga ta k'ara masa sosai, ya tsinci kansa da kasa d'auke idon sa kanta, yana jin wani yar, K'arasowar cikin falon yasa yayi saurin kawar da kansa, Cikin sanyin murya tace "Ina wuni?", "Lafiya" Ya amsa ba tare da ya kai dubansa ba,
Har ta kai k'ofa, Ta jiyo muryarsa "Ina zaki?", "Wurin Ammi" Ta bashi amsa, Bai sake cewa komai ba, Jin shiru ta bud'e k'ofar ta fita, Rauda kuwa ta cika tayi fam ganin irin kallon da yake wa Bongel, Bai bi ta kan Rauda ba sai ma mik'ewa da yayi, ya nufi dining, Ya hau ci wainar wanda ta masa masifar dad'i.
*******************
Ammi sosai taji dad'in wainar da Bongel ta kawo mata, Tayi ta saka mata albarka, Tana k'ara yaba hankalinta, Ko shakka babu Dada babban gata tayi wa Haidar data had'a sa da ita, Rauda tun zuwanta gidan bata tab'a kawowa Ammi ko ruwa ba, Bongel ta jima a sashen kafin ta koma, Ammi ta bata kyautar humrah mai masifar k'amshi, ta mata godiya sosai.
*********************
Rauda kwata kwata tak'i ba Hisham damar su had'u, a ganinta sai ta gama da matsalar cikin da akace babu, kafin ta dawo kan fitar Bongel gidan, Hisham ba k'aramin haushin hakan yaji ba, amma ya d'auki alwashin shawo kanta, dan yana ganin da taimakon ta zai cika burin sa, Yanzu ma kiranta yake tak'i d'auka bai fasa kiran ba,
Haidar dake zaune gefen Rauda yace "Ba kiran ki ake ba", "Eh wayar bata da amfani", Ta fad'a tana k'ok'arin kashe wayar wanda kiran ya sake shigowa, Haidar ya kai dubansa sunan Hisham rubuce kan screen d'in, Ya kawar da kansa tamkar bai gani ba, yana cigaba da danna wayar sa.
****************************
"Alhamdulillah yau mun kammala jarabawar level one" Cewar Asiya, Bongel ta nisa tace "Lokaci na gudu kamar jiya muka shigo makarantar gashi har mun kammala level one", Asiya tace "Wallahi kuwa, haka watarana makarantar zamu gama baki d'aya", "Allah ya nuna mana lokacin yasa mu gama a sa'a da nasara" Cewar Bongel k'asan zuciyarta tana fatan ganin wannan ranar, ranar da zata cika burin sa, Asiya ta amsa da "Amin Amin, mu tafi gida ko?", Bongel ta dan' yi jim tace "Jibi za'a fara bikin Saude, jiya Nene ta kirani kan batun zuwana sai dai abu biyu ne zasu katange ni ga zuwan", "Me zai hana ki zuwa bayan kullum kina damuna kan cewar kinyi kewar su", Bongel taja numfashi tace "Na farko ban san ta yadda zan tambayi Haidar zuwan ba, na biyun had'uwata da Hamma Siddiku, nasan ba zatayi kyau ba, nayi mamakin tsawon lokacin da aka d'iba ma bai waiwayo ni ba, nayi imani da Allah matuk'ar naje ba tare da kayan d'akin da ya buk'ata ba sai nayi dana sanin zuwa na", Cike da tausayin ta Asiya tace "Tambayar Haidar zuwan ki ba matsala ba ne, matsalar itace Hamma Siddiku, amma ina so ki sani addu'a bata bar komai ba, ita zamu dage da yi", Bongel ta jinjina kai duk da tana jin karaya, amma tayi imani da Allah, yana sane da ita, shi zai kawo mata mafita a rayuwarta da tayi mata d'aurin goro.
****************************
Bongel tana dawowa gida, tayi wanka ta saka doguwar riga mara nauyi bayan ta shafe jikinta da humra da Ammi ta bata, K'amshi mai sanyi da dad'i na fita jikinta, gashinta tayi bakin, jelar sa ta sauka kan gadon bayanta, bata saka d'ankwali ba, Ta zauna k'asan carpet tana had'a handout d'inta na level one wuri d'aya tana sakawa a ghana must go,
Haidar yayi kusan minti biyar tsaye yana k'are mata kallo, a zuciyarsa ya shaida tana da kyau, had'i da komai ake buk'ata a jikin ya' mace, Sai dai kyan nata a wurinsa yake ganinsa kyan dan' maciji, "Fure a cikin juji" Ya furta wanda caraf a kunnen Bongel, Ta d'ago ta dube sa, ta mayar da kanta k'asa ba tare da ta fahimci me yake nufi da kalmar ba, Hannun ta tasa ta jawo dan' kwalinta dake kan gado, ta rufe kanta, Haidar k'arasowa yayi cikin d'akin, K'amshin humra ke dukan hancin sa yana sake jefa sa wani yanayi, Gaf da ita yazo yasa hannu ya d'agota, K'irjinsu tamkar zai manne da juna, ta runtse ido tana saukar da kanta k'asa, Hannu d'aya yasa ya tallabo hab'arta, bakinsa kawai taji cikin nata, yana tsotsar labb'anta na k'asa, Kasa aiwatar da komai tayi sai k'afafunta dake rawa, Haidar kissing d'inta yake kamar zai cire mata lips, Soma fita hayyacin sa yayi, Yayi k'ok'arin controlling kansa, ta hanyar tureta, tayi baya kamar zata fad'i, Idonsa ya runtse ya girgiza kai, Kana ya bud'e su gaba d'aya sun canza launi, Muryarsa na fita da k'yar yace "Ki shirya gobe kije gida", Ya juya ya fita d'akin,
K'irjin Bongel yayi mummunan dokawa, kar dai ya shirya rabuwa da ita, Kanta taji ya mugun sara mata, Ta soma ambaton Allah, a iya saninta babu soyayyar Haidar a zuciyarta, but ta rasa dalilin jin fad'uwar gaban rabuwa dashi, ta danganta hakan da damuwar Nene da k'annen ta bata son ganin fuskokin su d'auke da damuwa, amma tana fatan rabuwar tasu ta zama alkhairi, tana fatan samun sauyi ne a rayuwarta, "Shin Dada da Ammi sun san ya yanke hukuncin kuwa, da amincewar su ko sab'anin haka?", take wa kanta tambayoyin da babu mai bata amsa, Da sak'e sak'e kala kala ta had'a kayanta a akwati guda d'aya, komai na buk'ata ta saka ciki, Daren ranar bata runtsa ba, k'iyamul laili tai tayi, tana sanar da ubangiji damuwarta.
***********************
Tun tashinta komai sukuku take yin sa, tayi wanka ta shirya, ta saka hijab d'inta jalbab, Ya mata kyau sosai, komai ta kasa sakawa cikinta hatta ruwa, Zaune take bakin gado tayi jigum, Irfan ya shigo yace "Aunty ina kwana?", "Lafiya lau my boy" Ta amsa tana murmushin dole, "Kizo inji Daddy", Mik'ewa tayi taja akwatin ta sanin kiran nada alak'a da tafiyarta,
Haidar na tsaye, Rauda na gefensa, Bongel ta fito, Ta gaishe sa cikin ladabi ya amsa, "My dear bara na gyara maka necktie d'in ka" Cewar Rauda cikin salo tana gyara masa tana wani shafo wuyansa wanda da gangan take yi, Bongel kallo d'aya ta musu ta kawar da kanta, Bai hana Rauda ba, sai hannu da ya saka a hannu ya fiddo envelope ya mik'awa Bongel,
Kanta yayi mummunan sarawa sanin ko shakka babu takardar sakin ta ce, tasa hannu ta karb'a, ya jefa cikin k'aramar jakarta, "Direba na jiranki waje zai kai ki", Ya fad'a, Kasa ce masa komai tayi sai akwatin ta da taja tayi gaba, Irfan yabi bayanta da cewa zan bi ki, Haidar ya jawosa yace "Dawo, school zamu je na kai ka", Bongel na fita, Haidar shima ya fito tare da Irfan,
Rauda tsalle tayi ta fad'a kan kujera da cewa "Wayyo Allah na dad'i, shikenan ya rabu da yar' iska, wai mafarki nake ko gaske", Ta mari kanta, "Wallahi da gaske ne, Allah ya hutar dani, ya rabu da ita ba tare da na wahalar da kaina ba, dole na kira Hisham na sanar dashi wannan labari mai dad'i", Ta taka rawa kana ta soma kiran wayar sa, Bugu d'aya ya d'auka da cewa "Haba Rauda, ya zaki mun haka, tun yaushe nake kiran ki", "Maida wuk'ar, yau dai Allah ya hutar damu Haidar ya saki Bongel", "What, bana son wasa" Ya fad'a da k'arfi, "Wallahi tallahi a gaban idona ya bata takardar ta", Hisham ihun murna yayi ya jefar da wayar gefe, ya fad'a kan gado ta baya, farin ciki yake ji na ratsa shi wanda bai tab'a jin irin shi ba.
**********
A mota Bongel shiru tayi ta jingina kanta kan window k'ofa, ta lumshe idonta zuciyarta cunkushe da damuwa had'i da tunanin kala kala, Jin parking d'in mota da hayaniyar yaran unguwarsu da suka dabaibaye motar ganin mota mai tsada da kyau ya tabbatar masa sun iso, Ta bud'e idonta tana jin fad'uwar gaba na da wane baki zata furtawa Nene aurenta ya mutu Haidar ya saketa, tasan zasu sha gori kala kala da habaici wurin yan' gidansu, amma ya bawa ya iya da k'addarar ubangiji, Allah ya riga ya rubuta faruwar hakan, Da tunanin haka ta k'arfafawa kanta gwiwa ta aro jarumta ta sakawa kanta, Ta saki ranta da k'ok'arin b'oye damuwarta, ta fito motar zuwa cikin gida, Tuni yara sun shiga da akwatin ta.
*Hmmm bakina da goro*š¤š·
OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*
Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad
*HASKE WRITERS ASSO...*
ARBA'IN DA BAKWAI
SHIN KINYI REGISTER DA TOP TEN KUWA, IDAN BAKIYI BA TO KI GARZAYA, LITTAFAN HAR GUDA 7 DAGA HAZAK'AN MARUBUTA NA KUNGIYAR HASKE, DA YADDA ZAKI KOYI GIRKI KALA KALA, DA SANIN ABUBUWAN K'ARUWA DA DAMA, DUKA AKAN NAIRA D'ARI BIYAR KACAL
HANZARTA KI BIYA
TA WANNAN BANKIN ZENITH BANK
2083371244 AISHA M SALIS
TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR +447891142004 KO KATIN WAYA TA WANNAN LAMBAR 07043079298
*MAMAN INYASS SHAFIN YAU NAKI NEā¤ļø*
Ramla da Abu da gudu suka zo suka rungumeta, haka sauran yaran gidan, mamaki ya cika Bongel ganin wannan shine karon farko da ta samu tarba daga yaran gidan su, ko da tana makaranta idan ta dawo hutu ko kallon arzikāi bata ishe su ba, Hassan da Hussein kadāai take samun saukāi daga gare su,
Nene na zaune dāakinta tana jera kayan ta da aka kawo daga wurin dāinki cikin akwati, Bongel ta shigo, Cikin ladabi ta gaishe da Nene, ta amsa da farin cikin ganin yarā ta, āGa tuwo can da miyar kubāewa busasshiya na mikiā, Da kallon mamaki tabi Nene dama tasan da zuwanta, Nene ta katse tunaninta da cewa āKo baki ji baā, Tayi saurin cewa āDama nayi kewar miyar kiā, Nene tayi dariya, Ramla ce ta shigo rikāe da kwanukan abincin ta ajiye gaban ta, āSannuā, Cewar Bongel, Ramla tace āKai Adda wai sannu kamar nayi wani aikiā, Bongel tayi murmushi, Bongel taci abincin ne ba dan tana son ci ko jin dadāin sa ba, sai dan kar su Nene su gano akwai wani abu, duk da cewar ya zama dole ta sanar dasu, sai dai ba yanzu ba sai an gama hidimar biki,
āAi baki wani ci tuwon baā, Cewar Nene, āGajiya ce tamun yawa, kwanciya kawai nake bukāataā, Nene tace āKamar wacce tayi tafiya mai nisaā, Tayi murmushi tana kwanciya kan katifar dake shimfidāe a farfajiyar dāakin, baya ta juya musu ta yadda ba zasu gane ba baccin take ba, duniyar tunani ta tafi, yayin da idonta ke hasko mata fuskar Haidar a lokacin da ya mikāo mata takardar, tana jin bāacin rai da damuwa na sake shigarta, tana jin kiran Asiya na shigowa wayarta, takāi dāauka, dan bata san me zata ce mata ba, bata son dāaga mata hankali a halin yanzu.
******************************
Haidar yau yaje makaranta yayi handing over ya tashi daga matsayin lecturer, ko shakka babu ya samu experience sosai, Abba yayi gaskiya da yace ta hanyar lecturing zai kāaru da abubuwa da dama, Daga makarantar company ya wuce, Tun shigar sa office dāinsa ya kasa aikata komai sai tunanin Bongel da yazo masa, Meyasa idan yaga yarinyar ko suka kebāe tare da ita sai yaji ya kasa controlling kansa, jiya daga zuwa sanar da ita zuwanta gida ya bige da kissing dāin ta, āKo shakka babu tana amfani da wani lakāani dake jawo maza zuwa gareta, dashi take mun amfaniā Ya tabbatarwa kansa, Idanunsa ya lumshe ya jingina da kujera yace āI have to get rid of herā, Jin budāewar kāofa yasa ya budāe idon sa yana kallon kāofa, Hisham ne ya shigo fuska dāauke da farāa,
āBarka da hutawa Yayaā, Cewar Hisham, āYawwa barkaā, āYa aiki?ā, Haidar ya amsa āAlhamdulillahā, āPapers na kawo maka kayi signingā, Ya fadāa yana mikāa mata, Haidar ya karbāa yana duba takardun, kana ya saka hannu, ya mayarwa Hisham, Hisham ya sauke ajiyar zuciya da cewa āAshe abunda ya faru kenan, Allah ya kiyaye gaba, banji dadāi ba kwata kwata ba amma haka Allah ya kāaddaraā, Haidar da tsantsar mamaki yake kallon Hisham sam bai fuskanci inda zancen sa ya dosa ba, Ganin irin kallon da Haidar ke masa, yasa bai sake cewa komai ba, dan a zaton sa maganar ce Haidar baya so, Ya mikāe ya fita ba tare da Haidar yace masa komai ba, sai mamaki da ya cika sa.
**************************
āIna Bongel dāin naji ance tazoā Cewar Dije, āEh gata nan bacci takeā, Nene ta fadāa, āIdan ta tashi na dawoā, āAāah zata zo ma da kantaā, Dije tace āTohā tana murmushin da bai kai zuci ba, Bongel kuwa jij shigowar Dije ya kāara dāaga hankalinta tana kyautata zaton ko Hamma Siddiku ya aiko a kiranta, amma a yadda tasan halin shi da kanshi ma zai iya zuwa dāakin, but ba abun mamaki ba ne, dan ya aiko Dije.
Bongel bata tashi ba sai ana kiran sallar azahar, ta fito tsakar gida tayi alwala, ta koma ciki tayi sallah rakaāa biyu, tana idarwa ta jiyo muryar Hamma Siddiku daga waje, hantar cikinta ce ta kadāa, Ta ambaci sunan Allah,
āKizo inji Hamma Siddikuā Ramla ta fadāa, Bongel da kāyar ta iya amsawa da āTohā, Jiki a sanyaye ta fito tsakar gidan, Kanta sunkuye kāasa ta gaisheta, āLafiya lau Bongel ya hanya?ā Ya fadāa da farāa, Jin muryarsa yasa mamaki ya kamata, ya akayi yake amsa mata haka ko ya zata tazo da kayan dāakin ne,
āKin kyauta, kin zama yaā, auren ki yayi man rana, ashe zaki ji maganataā, Cewar Hamma Siddiku, Bongel tayi shiru kanta na sake kāullewa sam bata fahimci ina zantukan sa suka nufa ba, Ya cigaba da cewa āAllah yasa ki dāore haka, idan kina mana irin haka ai babu wanda zai ji mu dakeā, Bongel murmushi kawai tayi ba dan ta fuskanci komai ba, Yaja babbanr rigar sa ya wuce, Ta juyo suka hadāa ido da Nene ta mata murmushi, Dāaki ta koma da tunani birjik, Ramla ce ta shigo, Bongel ta kai dubanta gareta tace āRamla meke faruwa a gida