Chapter 3 Reading BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt Arewa Novels

BONGEL COMPELET BOOK (1to48) by ZeeYabour.txt

Author :  Zee Yabour Category :  Home Of Novels

Chapter   3 / 12

6K to 9K   out of 35.6K words

duba takardun,


Ya d'auki lokaci yana dube dube kusan kowacce drawer a office d'in sai da ya duba, kansa ya dafe ya furta "Ya Allah" ganin bai samu abunda yake so ba, "Ya zama dole naga Abba", Mik'ewa yayi ya fita office d'in nasa, elevator ya shiga zuwa floor 3,




Wata aljannar duniya kenan ba k'aramin tsaruwa da had'uwa floor d'in yayi ba, Kai tsaye office d'in Abba ya shiga ba tare da ya jira an masa iso ba, Yaci sa'ar samun Abba shi kad'ai yana karatun newspaper,


Ya gaishe sa cikin ladabi, Ya amsa da sakin fuska, Bayan ya zauna, Abba ya ajiye newspaper dake hannun sa yace "Tunda na ganka a irin wannan lokacin nasan akwai dalilin zuwan", Kansa ya gyad'a sama yace "Eh ina da magana Abba", "Ina jin ka" Abba ya fad'a yana tattaro hankalinsa kan Haidar,




"Abba ina tunanin lokaci yayi da ya kamata mu cirewa Maigoro share d'insu ya zama business d'inmu babu share na kowa a ciki", Haidar ya fad'a, a ransa yana addu'ar samun goyon baya daga mahaifinsa, Abba ya gyara zaman sa yace "A ko da yaushe tunanin mu yakan zo d'aya da kai, na dad'e ina wannan tunanin sai dai bansan ta yadda zan b'ullowar al'amarin ba", Yaji dad'in jin haka sai dai zancen Abba na k'arshe ya sa shi fargaba,




Abba ya cigaba da cewa "Before muyi hakan dole sai munyi tunanin wata hanya na bunk'asa kasuwancin mu ta yadda raba business d'inmu dasu ba zai tab'a mana kasuwanci ba, duk da cewa munfi so k'arfi a ciki, mu muka fara kafa business d'in, ya zama dole mu k'ara ilimin yadda zamuyi running business d'in mu individual", Haidar ya numfasa yace "Wane irin ilimi Abba, ina da PHD akan business admin, degree da masters on economics,


Abba yace "You still have to learn more", "How?" Ya tambaya, "You have to be a lecturer in economics department", "Lecturer" Haidar ya fad'a a razane, "Yes" Abba ya fad'a yana d'aga masa kai, "Amma Abba taya zan zama lecturer, ba zan iya lecturing ba", "Haka zaka daure, ta hanyar lecturing zaka k'ara samun ilimi kan kasuwanci, lecturer dole zai rik'a research kullum da zurfafa tunani, ta lecturing zaka k'ara samun experience", Shiru yayi yana nazarin yadda zai zama lecturer, gaba d'aya yana jin hakan ba ajin sa bane, gashi sam baya son hayaniya, "Kayi hak'uri ka bi abunda nace, ta haka zamu cimma burin mu In Shaa Allah, idan kayi hak'uri na dan' lokaci ne zaka yi", Abba ya fad'a yana assuring nasa, "Allah ya shige mana gaba" Ya furta yana jin sarewa a tare dashi, Abba ya amsa da "Amin".




************************


Har k'ofar gidansu driver ya kawota, tare da wata tsohuwa ya kawo su unguwar, tun daga can aka biya ya kawo tsohuwar har gida, ita ya fara ajiyewa kana ya kawo Bongel,


Tana fitowa cikin motar sukayi ido hud'u da Hamma Siddiku mugun kallo ya jefa mata ya wuce cikin gida, jikinta yayi sanyi, tayi wa mutumin godiya yaja motar sa ya tafi, Ta d'auki k'aramar jakarta zuwa cikin gida, tun daga k'ofar gida take jiyo muryar Hamma Siddiku yana zuba ruwan bala'i,




Tsaye yake kan Nene yana sauke mata bala'i, "Iskancin yarinyar taki har ya kai k'ato ya ajiye ta da mota bakin gidan nan, dama nasan ba wata makaranta data tafi nema katsina, yawon karuwanci kawai kika tura ta, toh ba zai yiyu ba, ba'a k'ofar gidan nan ba, taje can tayi yawon karuwancin ta", Nene har cikin ranta take jin zafin kalmar karuwanci da yake jifan yar'ta dashi, hak'uri irin nata yasa ta kasa ce masa uffan, sai d'aki da ta shige abunta, Ramla suka rufa mata baya, "Au shigewa kika yi baki da lokacina ko, toh wallahi bara na shaida miki duk ranar da tayo abun kunya sai kun bar gidan nan ku dukan ku",


Bongel bata san sanda zuciya ta d'ibeta tace "In Shaa Allah ba zanyi abun kun..." Bata k'arasa ba ya kife ta da mari, kafin ta d'ago ya k'ara mata, Da gudu Abu da Ramla suka fito daga d'akin suna kama Yayar su, Hamma Sidddiku ya cigaba da zage zage, Bongel duk da zafin marin da yadda zuciyarta ke k'unar b'acin rai, ta dake bata bar d'igon hawaye ya zuba kan fuskarta ba, bata son ganin damuwa kan fuskar mahaifiyarta da k'annen ta,




Tana shiga d'akin tayi saurin fiddo jamb admission letter d'inta ta mik'awa Nene da fad'in "Na samu admission" Tayi hakane dan kawar musu da b'acin ran da Hamma Siddiku ya saka su, Nene a take murmushi ya sub'uce mata tace "Alhamdulillah Alhamdulillah Allah abun godiya bazan iya misalta farin cikin da nake ciki ba" Abu ya tashi yana ta tsalle, Ramla ma bakinta ya kasa rufowa,




Ta fiddo kud'i cikin jaka ta ajiye kan cinyar Nene, "Ina kika samu wannan kud'i masu yawa?" Nene ta tambaya tana zaro ido, "Wanda ya bani admission ne ya bani yace nayi hidimar shiga makaranta", Karon farko a rayuwarta tayi wa Nene k'arya dan sam bata son abunda zai tada mata hankali, "Toh ai sai ki karb'a ki ajiye wurin ki", "A'ah Nene dubu ashirin kad'ai zan karb'a na lallab'a dasu, sauran ayi cefane da sauran hidimar gida, ki cire ko dubu goma ce ki fara k'aramar sana'a", "Allah ya miki albarka, yasa ki fara karatun a saa", "Amin Amin",




Bongel a ranar data cika kwana biyar gida, ta shirya komawa katsina makaranta, a cikin kwanakin babu irin bak'ar maganar da basu sha ba wurin su Fatsuma, a cewar su Bongel yawon karuwanci taje katsina, ta samu kud'i, gashi har sunyo cefane, idan ba yawon banza ba, ina zata samu kud'i, Daga Nene har Bongel ba wanda yabi ta kansu.



Bongel ta had'a kayanta tsaf na tafiya, Goggo Hajjo ta kawo mata yaji, k'uli k'uli da garin kwaki tace ta k'ara, Ta mata godiya sosai da nuna jin dad'in ta, Haka Nene ma ta yabawa Goggo dan tafi k'annen mahaifinta da ko abunda ba'a so basu bayar ba, kuma dukkansu ta musu sallama, amma ba wanda ta samu amsar kirki daga gare sa,



"Maganar zaman ki gidansu Asiya sai nake ganin rashin dacewar haka, suna fama da kansu kije ki k'ara musu lalura, babu wurin kwana ne a makarantar taku" Cewar Nene, Bongel tace "Akwai Nene", "Toh me zai hana ki zauna a can", "Sai nake ganin kamar idan nayi haka ba zasu ji dad'i ba, dama ina tunanin neman aikatau na d'aukewa kaina wasu lalurori", "Kinyi tunani mai kyau, rayuwa tayi tsada yanzu, kowa yana ji da kansa, baka k'arawa mutum d'awainiya ba", Ta jinjina kai alamar gamsuwa da zancen Nene, "Allah ya tsare ki ya kare ki, Allah ya baki ilimi mai amfani da albarka", "Amin"




Har k'ofar gida suka mata rakiya, ta tafi da burin watarana zata kawo sauyi a rayuwar ahalin ta.




**********************


Bongel ta koma katsina da kwana biyu suka soma registration na makaranta, ranar farko ba k'aramar wahala suka sha ba, kasancewar su sabon shiga, ko'ina sai sun jira layi bana wasa ba, sunyi applying scholarship gwamnati zata rik'a biya musu kud'in makaranta,


"Wai Allah! wallahi na gaji, haka zamu rik'a fama kullum", Asiya ta fad'a tana tsayawa, Bongel tace "Nima na gaji, amma ya muka iya tunda ilimi muke nema", Asiya tace "Hakane amma Dan Allah tsaya mu huta", Bakin wata bishiya suka zauna, sun d'auki kusan minti ashirin kafin suka tashi,


Sai yamma suka dawo gida a gajiye, wanka suka fara yi, suka ci abinci, kowacce ta kwanta tana huce gajiya,




********************


"Ya kamata zuwa yanzu an kai k'arshen komai, amma kullum babu wani bayani, idan ra'ayi ne bakwa yi ku fito ku fad'a" Ammi da wayar ke kunne ta tana sauraran mai maganar tace "Ba haka bane Hajiya Mariya, ina so ku bamu nan da sati d'aya", "Kullum maganar d'aya ce dai, a baku lokaci kaza, idan lokacin yazo kuma babu wani bayani", "In Shaa Allah wannan karon hakan ba zata faru ba", "Allah yasa, Ina Irfan banji motsin sa ba", "Gashi nan", Ta mik'a masa wayar yana mata gwaranci, kafin ta kashe,




Ammi shiru tayi damuwa d'auke a fuskarta, har Haidar ya shigo bata ji shigowar sa ba, "Ammi barka da dare", Sai muryarsa kawai taji, "Barka kadai" Ta fad'a a sanyaye, Yana zama Irfan ya d'are cinyar sa,


"Ammi ina fatan lafiya?" Ya tambaya cike da kulawa, Ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajiya Mariya ce ta kira k..." Saurin katse Ammi yayi ta hanyar yin tsaki yace "Suna nema su zamarwa mutane liability, ana dole ne", Ammi tace "Wallahi bani da damuwa sai su", "Ki daina damuwa Ammi, kada ki sawa kanki wani ciwo, In Shaa Allah ba da jimawa ba zamu kawo k'arshen komai", "Allah ya yarda", "Amin In Shaa Allah",




Hisham ne ya shigo da airpods a kunnen sa yana jin wak'a, sai dai yazo saitin Ammi ya cire ya gaisheta, ya juya kan Haidar yace "Yaya barka da dare", "Yawwa" Ya amsa ganin Ammi, sanin rashin amsarwa zata so jin ba'a si, Hisham sanyi yaji a zuciyarsa na amsarwa Yaya Haidar, tun ranar ya daina masa magana, ko yayi baya amsa masa, yasan ganin Ammi ne, dan haka da gangan ya rik'a jan Haidar d'in da hira, dan dole ya rik'a amsa masa, har ya saki jiki suna hira har Ammi.






OUM MUHRIZ
Zee Yabour: *BONGEL*


Na Zee Yabour
ZeeYabour on wattpad


*HASKE WRITERS ASSO...*


SHAFI NA HUD'U




Ta shirya tsaf cikin atamfar ta d'inkin riga da skirt, sai hijabinta iya gwiwa, "Bazan gaji da cewa kinci sunanki Bongel ba, wallahi ke kyakkyawa ce Hafsah", Cewar Asiya, Bongel tayi murmushi tace "Kema ai kyakkyawa ce", "Ban kama k'afarki ba, kefah kafin a samu mai kyau irinki sai an tona", "Uhmm ni dai muje ki rakani bana son zuwa ni kad'ai" Ta fad'a a marairaice, "A'ah kar mu fara da karya masa sharad'i, dama ce muka samu kada mu bari ta sub'uce", Bongel tace "Hakane kuma, kira sa naji ina zan same shi",




Hisham fitowarsa daga wanka kenan, yana goge gashin kansa da k'aramin towel wanda ya taru kamar na mace sai dai gashin ya k'ara masa kyau, Wayar sa ta soma ruri, ya kai dubansa ganin bak'uwar lamba yasa a ransa yarinyar jiya ce, dan baya expecting kira da sabuwar number yau a wannan lokacin, yayi receiving tare da saka handsfree,




"Assalamu alaikum" Ta fad'a cikin natsuwa, "Wa alaikis salam", "Ina wuni?", "Lafiya lau", "Nice ta j.." Ya katse da fad'in "Na gane, mu had'u a bakin company", Ta amsa da "Toh", Ta mik'awa Asiya wayar, "A'ah kije da ita, ko da buk'atar amfani da ita zata taso", Tace "Toh",




Kusan minti ashirin da tsayuwarta a wurin, dallelliyar mota tayi parking a gabanta, tented ce shi ya hana mata ganin na cikin motar, glass ya sauke ya mata alama da hannu tazo, Ganin Hisham ne ta k'arasa bakin mota, "Shigo" Ya fad'a, Kai ta girgiza tace "A'ah", "Baki shirya karb'ar admission ba kenan", "Na shirya" Ta fad'a da sauri, ganin yana shirin tada mota tayi saurin bud'ewa ta shiga, ba abunda ke tashi cikin motar sai kid'a, sam bata son kid'a, sai yatsina fuska take,




Daidai wani k'aton gida taga yayi horn, security ya taso ya bud'e, tayi mamakin ganin gida suka zo, "Fito" Yace mata, Jiki a sanyaye ta fito, tana bin harabar gidan da kallo, dan ba k'aramin kyau ya mata ba,


"Mu shiga ciki ku gaisa da Matata", Ya fad'a yana murmushi, tabi bayan sa, a ranta tana ayyana matar sa ta dace da miji mai tsantsar kyau, gayu had'i da dukiya,




Falon sam bai nuna akwai d'an adam dake rayuwa cikin sa ba, "Bara na kirata" Ya fad'a yana shiga ciki, Few minutes ya fito, Yace "Ki sameta ciki, tace kanta na ciwo, kinsan masu laulayi", Bongel tayi murmushi a ranta tana mamakin kirki irin nasa, dama akwai masu kud'i masu sauk'in kai,




Tana shiga d'akin ya rufa mata baya, tare da saurin saka key ya kulle ya zare mukullin,


Jin an rufe k'ofa ta juyo a razane, "Dan Allah kar ka cutar dani ka barni na tafi", Murmushin gefe baki yayi yace "Kina tunanin a banza ake samun admission" Yayi dariya ya cigaba "Ki kwantar da hankalin ki, ki bani kanki yau kad'ai, ki samu admission cikin sauk'i da kud'ad'en kashewa", "Dan Allah kaji tausayina ka k'yaleni kada kamun komai, Dan Allah ka rufa mun asiri", Tana fad'a tana ja baya, yana biyota har ta fad'a kan gado kwance, ya hau kanta ya cire hijabinta da k'arfi ya wular, ya soma romancing d'in ta, hawaye ke ambaliyi saman fuskarta, tana nadamar kawo kanta, ko shakka babu tayi babban kuskure na biyo sa,




*********************




Namiji ne da ya amsa sunansa namiji, yana cikin jerin maza ajin farko, mai jini a jika, kyau, had'uwa had'i da gayu duk ba'a bar sa a baya ba, Fari ne sosai wanda ya had'u da na halitta da hutu, fatar sa kad'ai zaka kalla kasan naira da hutu sun ginu a wurin, Tsaye yake bakin dressing mirror na tantsamemen gadonsa royal, yana combing kwantaccen gashin sa na fulani, comb d'in ya ajiye a ma'ajiyar sa, ya fesa turare sun kai kala biyar, ya gyara zaman necktie d'in sa, Ya fito d'akin cikin takunsa na k'asaita,


Da sauri escort d'in sa ya taso da zumar bud'e k'ofar mota, "Zan shiga gidan Ammi", Ya fad'a a takaice, yana bin wata k'aramar k'ofar da zata sada shi da gidan, ba tare da yabi ta gate ba, ganin babu motocin Abba, ya tabbatar masa ya fita aiki kenan,




Dattijuwar mata yar' kimanin shekaru hamsin na zaune falo wanda aka narkawa dukiya, ta sha ado na matan manya, hutu da naira ya b'oye tsufanta zaka rantse ba zata haura shekaru arba'in zuwa da biyu ba, yaro dan' kimanin shekara biyu yana zaune kan cinyarta tana bashi chips, "Ammi ina kwana?" Ya gaisheta yana russunawa, "Lafiya lau",Ta amsa da sakin fuska, Yaron ya sauka jikinta yana nufar sa, yana fad'in "Daddy" cikin gwarancin sa, "Wato kaga babanka ko", Ammi ta fad'a tana dariya,


D'aukar sa yayi ya soma masa wasa yana cilla sa sama, yaron kuwa sai dariya yake, ya jima yana masa wasa, kafin ya mik'awa Ammi shi, Yace "Ammi wai ba zaki samu mai tayaki hidimar yaron nan ba, kema kina buk'atar hutu", Ammi ta nisa tace "Yaran ne na kasa dacewa, kowacce da nata matsala, lokaci yayi ma da ya kamata ace ka k'ara aure, shekarar Hafsah biyu da rasuwa, ya kamata ace ka dangana, ka samar wa yaron ka wacce zata maye masa gurbin uwa da ya rasa", "In Shaa Allah" Shine kad'ai abunda yace yayi saurin fita, sam baya son ana masa maganar aure.




Ganin fitowar sa, Escort d'insa yayi saurin tasowa ya bud'e masa gidan baya, ya shiga, ya mayar ya rufe, Driver yaja motar,


Wayarsa ya jawo ya soma kira, amsa d'aya ake basa a kashe, idan ya kira wayarsa yaji a kashe yasan babu inda zai same sa sai guest house, "Muje guest house" Ya umarci driver, "Ok Yallab'ai" Ya fad'a cike da ladabi, Banda yana buk'atar takardun dan kusan akansu ne zasu zauna meeting da wasu yan china, zasu mishi signing da ba abunda zai kai sa can,


"Ba sai ka shiga ciki ba" Ya fad'a, a bakin gate yayi parking, Escort yayi saurin fitowa ya bud'e masa, ya fita, Kai tsaye ya shiga cikin gida, alamun kamar kuka ya soma jiyowa daga d'akin, Yana sa kansa ciki daidai lokacin Bongel ta d'ago kanta, idonsu ya sark'e cikin na juna, da sauri ya runtse idonsa yana cizon pink lips d'insa na k'asa, ya fice d'akin, bai tab'a mummunan gani irin na yau ba, lokaci d'aya yaji tsanar yarinyar da yaga k'aninsa a kanta, ya tsani zina, yana k'yamatar ta, yasha yi ma Hisham wa'azi kan neman mata baya ji, bai tab'a gani da idon sa ba sai yau, "Meyasa mata basu da hankali, basu san daraja da martabar da Allah ya musu ba, suka zab'i zubar da mutuncinsu akan titi, mata da yawa kyaunsu ke cutar dasu, k'aramar yarinya ta lalata rayuwarta" Ya girgiza kai yana jin haushi da tsanar yarinya na k'aruwa a zuciyar sa, yana jin tamkar ya koma ciki ya mata tsinannan duka sai ya raunana ta,




Hisham yaji shigowar mutum wanda yasan babu wanda zai shigo sai Yayansa Haidar, a daburce ya sauka kanta, ya fito d'akin,




"Yaya kaine, ina fatan lafiya?" Ya fad'a murya na rawa, duk da yasan Yaya Haidar d'in yasan yana neman mata amma bai tab'a kama sa red-handed irin na yau ba, Ko kallo bai ishi Haidar ba yace "Documents na jiya zaka bani", "Ai suna gida d'akina", Tsaki Haidar yayi ya mik'e ya fita, "Me ya hanani duba d'akinsa, da banga wannan k'azantar ba", Yana zancen zuci tare da yin tsaki,


Drivern sa da Escort daga ganin yanayin sa suka san ransa ya b'aci, "Mu koma gida" Shine kad'ai abunda ya fad'a,




Hisham zama yayi falo ya kasa komawa d'aki, kunya ta ishe sa, Yaya Haidar ya kamasa da mace, bai tab'a ganin b'acin rai akan fuskar yayan nasa ba irin yau,


Bongel ta fad'i Alhamdulillah yafi cikin kwando, zuwan wannan bawan Allah ya ceci rayuwarta, Hisham na gab da rabata da budurcinta Allah ya jefo sa, Hawayen idonta sun kasa tsayawa, tsantsar nadamar biyo sa ne shimfid'e a zuciyarta, meya rufe idonta ta kasa tunanin hakan zai iya biyo baya ta amincewa shiga motar sa, ta biyo sa gidan sa, ko shakka babu sunyi ganganci na saurin yarda dashi, "Meyasa maza tunanin su d'aya ne akan yaran talaka, suna ganin da kud'i zasu rud'e su

3 / 12