Rikicin babban gida Book Complete Document by Real Afreen ce.txt

Author :  Real Afreen Category :  A Books

Chapter   3 / 8

6K to 9K   out of 22.9K words

masoyan mu mungode sosai da qauna Allah ya bar xumunci*😍








🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
~Rikicin~
*{Babban gida}*






Episode *26-30*






"Mexan gani haka iye hydar"!!


Ja dabaya hydar ya farayi yana Sosa qeya kunya ce ta rufesu dikka bama kamar Amra da ce ta tsani ya hydar...


" umma Ku tsaya kiji"
Acewar hydar
Daga masa hannu tayi tare da fadin


"Ya isa hk banason jin dog on bayani...kasan cewa Amra ynxu tanada aure atanta kokunqi ko kunso dole Ku hakura da junanku..Dan hk inna gaisuwa ba banaso inqara ganin haka"


Gabadayansu ajiyar xuciya suka dauke bama kamar amra wacece dik tabi ta tsargu...
Ficewa tayi daga palon bata jira cewar su ba.. Yana fita momy ta fara masa fada akan batason taqara ganin sun kebe da amra saboda inshi akama haka bazeji dadi ba..


Kallan anty Amarya ne suka ratsa jikinsa gabadaya yayi sanyi sai a ynxu ya fara danasanin abinda ya ma amra...


Godiya yama umman tasa kafin yashige daki...




Amra kuwa tana fita da side din anty Amarya part dinsu Arman ta nufa kasancewar yasu taxi daya da safeena watoh qanwar Arman...


Tanazuwa bata iske kowa a Palo ba dan haka ta wuce tanufi dakin su safeena...


Kamwance ta iske safeena akan gado tana karanta novel awayarta mai suna (Tamishi illah) Na Fadeela lamido


Duka Amra takaima safeena..


"Kefa banxace wallahi kiyitafaman aikin karanta novel"


Tsaki safeena tayi tare da miqewa zaune tana fadin
"Ynxu xakizo kidameni"


"Dallah dan ma nazo tayaki hira"
"Au yi hakuri Ashe yanxufa matar yayace"


Tsaki Amra tayi tare da fadin
"Bara bason haka"


Dariya safeena tayi tare da fadin


"Haba Amra yadai kamata ace ki hakura kiso mijinki tinda haka Allah ya qaddara miki..kuma nasan ya Arman baze taba cutar dake ba"


"Hmm kawai amra tace"


Safeena ce hango wayar dake hannun Amra


"Laaa Amra waya kikayi shine bazaki fadamin ba"


"Yi hakuri dan Allah yayanki ne ya bayar abani"


zaro ido safeena tayi tare da fadin
"Ke ba yayanki bane?
Ohhh nagane mijinkine shi".


Duka Amra yakaima safeena nanfa suka fara hira har safeena ta budewa Amra watsapp...
Sunan Mr.man ne ya appear a contact list dinta kawai...
Nanfa safeena tasa mata numbern ta bayar ajasata a groups...
Ba ita ta bar gun safeena ba sai 10...


Part dinsu ta nufa yau bata da niyar kwana a dakin goggo..dakin ta ta shiga direct ...caji ta sa wayarta kafin ta shiga toilet wanka tayi kafin ta nufi kitchen domin diban abinci saboda wata iriyar yinwa da takeji...


Indomie ta dafo ta dawo daki..zama tayi kangado tadauko wayarta ..kunna data dinta tayi...prfle din ya arman ta nufa hoton dake kan dp dinsa ta bude tana kallo...


Ya Arman ne yasha kakinan nasa na sojoji gabindigarsa a hannu murmushi yayi ahoton Wanda ba qaramin kyau yayi ba zuba masa ido tayi nanfa ta tsinci kanta da yin murmushi...


Message taga yashigo Mr.man dasauri ta bar gun prfle din nasa ta nufi gun message tana budewa taga ya rubutoh mata




_😑Kaii baby waya bude miki watsapp baki fadamin ba plxx banso ki kula wani_ I miss u


Murmushi kawai ta dingayi tama rasa mezata rubuta masa






Nanfa suka dinga hira kamar me...




Akwana atashi yau sati biyu da bikinsu... Waya suke Sosai tana zuba masa shagwaba..shiko ya arman ganin ynxu Amra ta sake dashi yasa ya fara tunanin yadawo ya tafi da matarsa kawai...


Kullun sai tayi hoton ta tura masa haka shima sai ya turo mata...




Yau ta kama ranar juma'ah
Zaune Amra da safeena suke suna kwalliya..wayar Amra ce ta fara ruri dasauri Amra ta dauko tare day in murmushi ta kara a kunne...


Sallamar da ta masa ma ita kanta cike da shagwaba tayi ta safeena kuwa kallon Amra kawai takeyi yanda ta zage tana zubawa ya Arman shagwaba...
Abinda yafi bata mamaki ma dataji tace masa my hero...


Nanfa suka dinga soyy a waya abinsu suna hira sai dariya suke...


"My hero wai yaushe xaka dawo ne"


Dadine ya shika Arman dayaji tamasa wanan tam bayar murmushi yayi sosai kafin ya soma fadin


"Dole indawo intafi da matata cox am missing her a lot"


Dariya sosai Amra amtayi tare da jin dadin abin da ya Arman ya fada.. Rufe fuska tayi kamar yana kallon ta itadai safeena na gefe ta zuba mata ido...


Nanfa suka shirya akan xexo daya samu Hutu agun aiki..





3weeks later**


Akwanakinan Amra ciye2 kawai takeyi harda su goro kowa tsiya yake mata...yaukam da masanancin ciwonciki Amra ta tashi..
Kowa gigicewa yayi agidan haka aka sunkuceta sai asibiti nanfa aka mata yan gwaje gwaje aka gane tana dauke da juna biyu...


Kowa mamaki ya farayi amma anty faty ko sanar dasu cewar tayi ai ran da aka daura aure adakin goggo suka kwana shida ita....


Nanfa daga mamaki aka koma murna...
Nanfa anty faty ta kira arman


"Hello Soja Dan gayu...ka taho gida Abban ka na bukatar ganinka emergency"


"Anty faty lafiya?"


"Kaidai kazo kar yayi fushi tam baruwana"


Kashe wayar tayi shiko masa nutsuwa yayi yafara tunanin yadda sedai excuse yasamu ya tafi...


Koda labari ya iske hydar hankalinsa tashi yayi gumi ya dinga hadawa ya kasan nutsuwa...


Safiya kuka tadingayi tare day in alwashin saita zubda ciki nan bazata yarda Amra tahaihu da ya Arman ba Dan Arman nata ne itakadai...


Amra kuwa tinda safeena ta fada mata take kuka ko abinci yaqi ci..hankalin kowa a tashe yake dan ji ake da cikin dake jikinta bama isa yan dakinsu Arman din kamar su goyata itako abinduniya uabi ya isheta...




Inya Arman yazo yazatayi???😭












Kucigaba da kasancewa damu...yazata kasance a episode din gaba?..
Ynxu idan Arman yasan tana ciki yazata kasance????











*Queens online writers*
[7/22, 4:02 PM] Real Afreen ceπŸ’‹: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘ΈπŸ‘ΈπŸ‘Έ
*Queens online writers*








_Daga Alkalamin Queens_



*Asallamu'alaikum naga comments dinku toh ataqaice star din littafin daga farko itace muka maida mata _AMRA_ shikuma kabir ya koma _ARMAN_*


_Masu batun ciki na Arman ne ko ba nashi bane?Toh Ku qara tariyo baya saboda ciki bana Arman bane na hydar ne_




Godiya me tarin yawa ga masoyan mu QueensπŸ˜πŸ‘mun gode Allah yabar zumunci






🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
~Rikicin~
*{Babban gida}*








Episode *31-35*


Washe gari tinda safe kowa ya hallara kowa da sallon girikin da akawa Amra ba Wanda baya farinciki da cikinan inba hydar da safiya da ita kanta ba... Dan cikinan babban tashin hankali ne agaresu bama kamar Amra wacce ba abinda takeyi banda kuka komai taqi yarda taci..


"Hello Arman kanajina"


"Eh anty faty innajinki meyafaru"


"Arman gafa Amra bata da lafiya kuna taqi cin komai fa"


Hankalin Arman ne yaqara tashi sosai Dan hk cikin rawar murya yace abama amra wayar sa mata akayi akunne amma ba abinda yakeyi banda kuka Dan dik atunaninta sunriga sunfada masa cewar tanada ciki...


"My baby kukan me kikeyi karki manta bakida lafiya fa plxxx kici abinci kinji ko"


Shiru amra tayi tana sauraron sa tsananin mamaki ne ya kama amra me ya arman ke nufi ze karbi cikin kenan koda ba bashi bane?


Muryarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da take ciki..


"Kici abinci kinji baby inba hk ba ko nazo bazan tafi dake ba kuka nima rashin lafiya zanyi"


Soma share hawayen ta tafarayi sai aynxu tasamu damar yin mgn..


"Zanci... Yaushe zaka zo?"


"Gobe ko jibi insha Allah"


Addua ta masa kafin sukai sallama akan anjima ze qara kira yaji ko taci abinci...


Nanfa akasamu amra taci amma kusan Rabin abinda taci dik ta amayar dashi...


Daddare Aka sallamosu suka koma gida dakin goggo ta sauka saboda goggo ta takura sai dai ita zata kula da Amra ba ai mata musu ba aka barta...


Dakin nan data fara kwana nan aka sauketa aka ta....


Dik abinda tace tana buqata suna mata amma har yau bata dena kuka nan ba kowa na mamakinta...
Washe gari da safe Amra na kwance ta rufe ido kamar tana barci amma idonta biyu..ji tayi an turo qofa ahankali ta bude fuskarta da mamakinta sai ganin safiya tayi...


da sauri ta miqe zaune tabi safiya da ido...ahankali safiya ta soma tafiya har saida takai inda Amra take..


"Murna nazo tayani da kuna baqincikin abinda ze faru dake kwanan insha Allah"
Gaban Amra ne yafadi da jin zancen safiya tinani ta farayi kardai ace safiya yasan sirrin da take biyewa? Toh taya za ayi yasani inbadai ya hydar ne ya fada mata ba...toh ai kuna mgn kirki bata hadasu da hydar...
Qarar bude qofar dataji ne ya dawo da ita hayyacinta..ganin safiya tayi tana qoqarin fita kaikuma ta juyo tana fadin


"Farinciki shin samun cikin baqin cikin kuna shine nixanxama ajalin cikinan sai ya zube ya Arman nawane"..




Sai alokacin Amra tasamu qarfin yin magana Dan taji ba abinda take zargi bane..


" ya isheki haka..mijina yafi qarfinki idan kinacin qasa ki kiyayi ta shiru..ciki kuwa in kinga dama kixubar dashi ynxu ynxunan...ya arman kuwa ya miki nisa"


"Wallahi zaki sha mamaki ne amra ni kike fadawa wa'anan kalaman ko"


Tsaki Amr@ tayi tayi ta koma ta kwanta safiya kuwa ficewa tayi tare da buga qofa bummm...


Yautake ranar da Arman XE dawo dik inda hankalin Amra yake yayi dubu a tashi yake SBD har ynxu a tsorace take ..


Misalin qarfe 11:45am arman ya iso yana isowa akafara mai sannu da zuwa...
Anty faty ce ta jashi sukai part din goggo a Palo ta tsyar dashi ...
Wani Elgmnt din hoto babba takawo masa wanan nade yake...


Ahankali yana murmushi ya bude Dan ganin meye wanan...
Hoton baby ya gani ajiki..


"anty ai wannan hoton jariri ne..me kukeci na baka na zuba insha Allah kun kusa samun jika"


Murmushi anty faty tayi tana fadin...
"Ai munsamu qaramin Soja Dan Amra nada ciki"


Dariya Arman yafara yi itama anty faty sai wangale baki takeyi Dan dik a tunanin ta. Murnace...


"Kaiii anty faty Abun naki harda zolaya kuma ynxu dai inna amra"


"Tana cikin dakin mana dgsk fa nayi Arman"..
Murmushi ya kum ayi yashige dakin Anty faty tabi bayan sa...




Yana ganin amra sukayiwa junansu murmushi


" baby kinji fa anty faty sosuke mu basu baby"


Shiru amra tayi jikinta yafara rawa alamun bemasan tanada cikin ba..


"Wanne ciki kuna banda Wanda ke jikinta"




Shiru arman yayi ahankali fara'a mr dake fuskarsa ta dauke ya juyo yana kallon anty faty..itako gyada kai tayi tana murmushi


"Eh Arman kakusa kazama abba"


"Yuh mean Amra Nada ciki?"


"Eh Arman ciki ne da ita 1month"


Kallon Amra yayi ya fara nunata da yatsa yafara ja da baya har saida yakai qarshen bango kafin smya silale qasa ya zaune dabas...
Anty faty kallon su ta tsayayi Amra yayi amra kuwa kuka tafara harda shesheqa tasa hanunta ta rufe bakinta..
Kusa dashi tafara matsowa dasauri ya daga mata hannu alamun ta tsaya..


"Wai meye haka meke faruwa ne?"


Acewar anty faty wacce ta tsaya kallonsu da mamakin abinda taga sunayi..kuka amra keyi kamar ranta zefita tana fadin


"Kayafemin kayafemin"!!!










_Tofa anfara rikicin babban gida_








*Queens online writers*
[7/27, 2:20 PM] Real Afreen ceπŸ’‹: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘ΈπŸ‘ΈπŸ‘Έ
*Queens online writers*






_Daga Alkalamin Queens_




Note:


*Plxxx munada yar matsala atafiyarmu a novel dinan..a musulunce hukuncin matar auren da tayi zina shine a gefeta..idan muka cigaba da tafiya ahaka toh qarshe jefeta za ayi kuma bamason kashe star din novel din ynxu saboda munada sauran tafiya agaba...Dan haka muncanja salon akan ana gobe daurin auren ne taje gun hydar*


_plxxx kowacce ta karanta abinda ke samaπŸ‘†kar qarshe nazo Anna kawo mana complain akan ga abinda ya kamata plxx_










🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
~Rikicin~
*{Babban gida}*








Episode *36-40*






Acewar anty faty wacce ta tsaya kallon su da mamakin abinda taga senayi...kuka amra kayi kamar ranta zefita tana fadin


"Kayafemin kayafemin"




Kasa magana yayi wasu guntayen hawayene suka zubo masa a fuska dan hk yamiqe cikin zafin nama yanufi qofar fita anty faty kiransa takeyi amma kamar tana magana da dutse...


Itako amra silalewa tayi qasa tana rusa uban kuka..har yakai qofa ya bude ze fita ya juyo yana kallon amra sekuma ya fice daga dakin...


Karasawa gurin ta anty faty tayi tana fadin


"Meye haka ne? Kunqi fadamin abinda ke faruwa kunsani a duhu"


Qinmagana amra tayi sai kuka takeyi itakuwa ganin kukan nata bana qarewa bane yasa anty faty ta miqe ta fice daga dakin abunta tanazuwa gun ammyn amra ta sanar mata abinda ke faruwa cikin sauri suka nufi inda take harda goggo wacce aynxu suka tarar a dakin...


Cikin sauri ammynta ta qarasa..


"Amra meke faruwa ne?kibar kuka nan haka karfa kimanta da yanayin dakike kifadamana meya hadaku..


Cikin kuka ta rungume ammynta tana fadin


" Ammyna Dan Allah Ku yafemin wallahi bahaka bane"


Qara rikitasu tayi sukayi sukayi ta fada abinda ke faruwa amma taqi yarda tafa...


Yaukam safiya batasan meke faruwa ba agidan tayi shirinta tsaf na tafiya gun yayansu dake aure Mina...


Arman kuwa tinda ya tafi dakinsa ya shige ya kulle qofa banda kuka ba abinda yakeyi ..tinani ya farayi toh cikin waye?yama za ayi ace Amra tayi zina bazema taba yiyuwa ba..


Wani sabon kukan ne ya kufce masa ya rasa yanda zeyi..


Anty faty kuwa hankalinta kasa kwanciya yayi Dan haka kiran Abban Arman tayi ta sanar masa abinda ke faruwa..


Kankace me antarasu a dakin goggo amma arman yaqi zuwa daqyar mumy tasamu yafi toh ya taho..


"Kaii Arman meyaa faru ne?banason shashanci fa"


"Daddy bansan meyafaru ba kuta tmbyt"


"Inna maka mgn kana cemin atmbyt ya kuke Neman maida mutane mahauka tane?"


Mumy ce tayi caraf da fadin
"Haba Dan Allah abisa ahankali mana"


"Banaso kiqara mgn kinajina ko?"
Acewar dady
Tabe baki tayi shiru..


Amra kuwa nadaga gefe ba abinda takeyi banda kuku
Kallon Amra dady yayi yana fadin
"Bazakiyi mgn bane kema"


Kukan nata qaruwa yayi sosai ran Abban ta kuwa harya soma baci..miqewa yayi cikin sauri gadan gadan yayi kanta..ganin haka yasa arman ya tsorata kar a illatata cikin sauri yasoma mgn


"Kayi hakuri Abba zan fada"


Cikin sauri amra ta dago kanta ta kalli arman ta girgiza kai dubawa tayi kaf gurinan hydar bayagun..


Dady ne yana abba hkr akan yadawo yazauna..


Goggo ce ta kalli arman wacce se aynxu ta tanka tana fadin
"Kai muke sauraro"


Cikin 'in'ina yasoma mgn..Dan hk amra ta qara sautin Ku kanta


"Ba baba".
" ba ba meye?" Acewar mumy


Rufe idanunsa yayi tare dauke ajiyar zuwa yana fadin


"Ba cikina bane"


Sallati akahau raftakawa apalon kowa na kallon amra wacce ta dunqule kanta a gwowowinta...


"Arman kana da hankali kuwa"
Acewar mumy


"Lafiya ta lau momy.."


Sai kuma ya fashe da kuka yana fadin
"Bacikina bane bansan dashi ba ta yaudareni.."


"Mumy dik sonda nake ma amra tamin haka"


Magana yake yana kuka wani Abun nasa ma basa gane

3 / 8