Author : Real Afreen Category : A Books
Amra ma kwashe kwanukan tayi ta nufi kitchen din tana kuka..
Mum nazaune tana kallonsa badai tace dashi komai ba se dannar wayarsa yakeyi daga bisani yasoma kiran amra
"Amra Amra!!!
Cikin dashashiyar murya ta amsa ta fitoh tana sharar hawaye...
" kee me aka miki kike kuka..bacewa nayi kije kimaidamin dakina yadda kika sameshi ba..zaki wuce ko sena tashi"
Jiki sanyaye ta shige dakin..Bayan yan mintina Safeena ta fitoh da plate din indomie karba yayi ya soma cin abincin..
Hanyar dakin safeena ta nufa domin taya amra aikuwa ya daka mata tsawa tare da fadin
"Keee inna za kije?"
"Amra zantaya gyaran"
"Dallah wuce kibar min nan"
Sai ynxu mum ta tanka musu
"Safeena shige ki tayata"
Shigewa tayi shikuma ya sunkuyar da kansa qasa
"Kazo nan Arman wulakancin naka ya isheni haka kazo nace ko "
Acewar mum
Miqewa yayi ya nufi inda mum take ya zauna..
"Son meke faruwa ne ya daga dawowarka zaka muxgunawa yar mutane?"
"Mum bata sona dik yaudarata takeyi bayan fadan innasonta shiyasa zatamin dik abinda taga dama menayi da zan fuskanci hakan"
Shiru mum tayi daga bisani tace ya mata bayanin abinda ya faru Qin fadama ta yayi dan acewar sa be so mum taji haushinta..
Sedai mum tati mitarta ta qyalesa..
*Night*
Kwance amra take kan gadon safeena ta rasa meke mata dadi shigowa mum tayi tana fadin
"Ke amra mrkikeyi anan..maza miqe kitafi gurin mijinki kije Ku warware matsala dake tsakaninku tashi maza"
Miqewa amra tayi ta fice batare datama mum musu ba gabanta na faduwa ta tura koda dakin cikin sa'a taga baya dakin..bakin gadon sa ta zauna..
Wayarsa tagani kusa da ita dan hk tadauka gallarey dina yashiga tana kallon hotuma aiko taga hotonan ita da hydar.. Wani iri taji dan tasan da alama abinda yasa arman fushi kenan toh eama ya turo hoton?
Wayar ce ta soma ringing sunan safiya ne darodaro a jikin screen din dauka tayi tare da karawa akunne
"Ya Arman dina Ashe kadaeo shine baka fadamin ba"
.
"Bazaki fita daga harkar mijina ba ko yagi qarfin ki wallahi"
Dariya safiya tayi tana fadin
"Ai kuma na gaba yayi gaba ynxu arman nawane"
"Walllaaahhh***"
Bata qarasa zancen ta ba taji an fizge wayar tana dagowa taga arman..
Kashe wayar yayi ya jefata kan gado ..ya ruqo hanun Amra ya kaita bakin kofa..
"Waya baki ikon shigowa dakina"
Kuka tafarayi tana fadin
"Dan Allah ya Arman ka tsaya na ma bayani"
"Ba abinda zaki cemin SBD nasan ynxu kinriga kinga abinda ykmt ki gani..bakyasona meyasa kk yaudarata..bari kiji zanje in auri wacce take sona..now get out"
"Ya arman plxx ka saurareni dan Allah"
Bude kofar yayi ya turata waje ya rufe qofar abinsa yana hawaye itama kanta kuka takeyi..
Agun ta zauna tana kuka har barci ya dauketa..kinga shiru yasa yaje ya bude qofar yaga ko tafiya tayi ga mamakinsa yana budewa yaga ta taho luuuu zata fadi kasancewar jikin qofar take..
Cikin sauri ya dauketa ya sun kuce ta ya shiga dakin da ita ya kwantar da ita..
Kwanciya yayi shima har yasa hannu ze rungumota jikinsa ya tuno da hotunan haushi yaji ya qara kamasa ya juya gefe ya kwanta..
Asbah nayi ya miqe yaje yayi sallah yana dawowa ya isketa kwance..
Tashinta yayi ta bude ido da mamaki ta ganta a dakinsa
"Zaki tashi ki ficemin a dakin ko ya akayi?"
Miqewa tayi tana fadin
"Ya Arman plxx kasaurareni dan Allah"
"Amra tin muna shiri da juna ki fita adakinan"
Juyawa tayi tafice daga dakin tana kuka tashiga dakin safeena..
"Matar yaya ya akayi ne ainazata kun gyarota"
"Safeena na shiga uku wani yadaukeni hoto da hydar ya turamasa kuma ynxu yace aure zeyi kuma nasan safiya XE aura.wayyoh Allah na""'
Kuka takeyi sosai safeena ta shiga rarrashinta...
_kuyi hkr banda caji anjima Inna samu caji zan qara posting wani tnx fans_
*Real Afreen ceπ*?
π‘π‘π‘π‘
π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Na
_Faty Afreen_
Nasadaukar da wannan shafin zuwa gareku
*Didi lurff*
*Slim small*
*Fadeela lamido*
*Cwt jiddah*
*Hamagee muh'd*
ππNagode da qaunarku gareni
Vote me on watpadd as
*fatyafreen1*
End of book *01*
Episode *96-100*
"Safeena na shiga uku wani yadaukeni hoto da hydar ya turamasa kum ynxu yace aure zeyi kuma nasan safiya ze aura.wayyoh Allah na"
Kuka takeyi sosai safeena ta shiga rarrashinta...
"Kiyi hakuri amra amma waye zeyi hakan?"
Cikin shesheqar kuka amra ta dago tana share fuska tana fadin
"Nasan ba Wanda zeyi haka inba ya hydar ba dan shiga biyoni dakin..wallahi zanje insamesa ya tukurawa rayuwata ya yakeso inyi ne?"
"Amra kar kije ya qara zama wata matsala ki qyaleshi kawai ynxu ki maida hankali ki sa ya Arman ya fahimci balaifinki bane kisa yardarsa ta dawo gareki..saboda idan ya auri safiya akwai matsala"
"Safeena dole senasami ya hydar baze yiyu ace yadinga min dik abinda yaga dama ba"
Shigewa toilet kawai Amra tayi tana share hawaye batare da tajira taji abinda safeena zatace ba
Zaune ya Arman yake a dinning yana danna laptop dinsa..
Amra ce ta fitoh daga daki ta nufo inda yake gaidasa yayi amma hankalinsa na kan laptop dinsa ya amsa ko kallonta beyi ba...
"Ya Arman dan Allah ka tsaya ka saurareni plxx"
"Amra ki qyaleni bana bukatar ki arayuwata kitafi ki bani wuri"
"Ya Arman wallahi ba laifina bane ya hydar ne ya!!!!!
" ya isa!!!"βπΌ
Ya daka mata tsawa tare da miqewa tsaye ya fice daga part dinma..
Kuka kawai takeyi shiko part din goggo ya nufa...
Cikin shesheqar kuka ta nufi dakin safiya wayar safiya ta dauka ta shiga kiran ya hydar
"Hello safiya ya akayi?"
"Ba ita bace"
"Ohhh amra...hhhh dama nasan wataran dole ki nemeni"
"Hmmm anjima wajan karfe 8 mu hadu abayan corridor din part dinku"
"Auuu baby yaukuma son ganina kikeyi"
"Kadaiji me nace"
Tana fadan hk ta kashe wayar tare da fadawa kan gado tana kuka...
Arman ko yana shiga dakin goggo ya iske tana barci dan hk yayi ficewarsa daga gidan ma...
*Night*
Hijab amra tasa ta nufi qofar fita daga dakin safeena ce ta tsaidata da fadin
"Amra inna zaki kuma?"
"Ynxu xanje indawo"
"Indai gun ya hydar zaki gwara ki hakura"
"Ke bacan zani ba ynxu xandawo"
Tabe baki kawai Safeena tayi ta cigaba da danna wayarta dake hanunta...
Fita amra tayi ya arman ta gani zaune saman kujera fuduwa gabanta yayi..ta danne xuciyar ta ta nufi inda yake
"Ya Arman dan Allah xanje gurin ammy indawo"
Beko kalleta ba ya amsa mata da
"Riqe miki qara nayi? Dallah matsamin annan"
Miqe wa tayi ta nufi hanyar qofa wata iriyar ajiyar zuciya yayi ta fita tafe take kamar wata tsohuwar munafuka tana tana tafe tana waige waige...
Safiya dake jikin corridor dinsu tana waya
"Ai qawata gobe zanzo dik yanda za ayi ayi so nake na mallakesa se abinda nace zeyi"
Hango amra yayi tana ta waige waige tsayawa tayi kallonta ga mamakinta sai taga Amra ta nufi bayan dakin anty Amarya.. Cikin sauri ta cewa qawar tata zata qara kiranta tana zuwa...
Katse wayar tayi tabi bayan Amra ga mamakinta se ganin hydar tayi agun
"Uhhh baby tindazu nake jiranki annan"
"Ba abinda ya kawoni nan ba kenan"
Murmushin mugunta safiy tayi taja gefe ta soma kiranta Arman kira biyu ta masa be dauka ba ana ukun ne ya dauka yana fadin
"Safiya ya akayi ne?"
"Ya Arman inna matarka take?"
"Ya akayi?tatafi gurin ammy?"
Wata iriyar guntuwar dariya safiya tayi dan hanka tace
"Toh bawani gurin ammy kazo wajan dakin su hydar ta baya gatanan ita dashi"
Wat!!! Kawai ya fada ya mike cikin hanzari ya fitoh .
Ita kuma can sun at a drama da hydar
"Ya hydar me na maka kkso ka hanani sukuni arayuwata?kafiso kayita hadani da mijina"
"Amra kenan kefa tawa ce kuma kullun inna fadamiki to wai mema na miki? "
Daidai lokacin ya Arman ya qara so gurin safiya ta nuna masa su
Ba abinda jikinsa yakeyi se rawa wani irin zafin kishi ne kecinsa idanunsa sunyi jaaa..
Safiya daga gefe murmushin mugunta da jindadi kawai takeyi...
Amra ce take fadin
"Meyasa zaka sa adauki hotonmu ka nunawa ya Arman?"
Dik abinda suke fada Arman da safiya basa jinsu
Cikin rashin fahimta Hydar yace
"Kamar ya bangane ba"
"Dama bazaka gane ba meyasa zaka tura masa hoton?"
Ruqota hydar yayi GAM yana fadin
"Wai wa anne hotuna kike nufi?"
Arman na ganin haka ya juya yabar gurin afusace..
Tafiyaraa keda wuya amra ta tattaro dikqarfinta ta kwance tare da Marin ya hydar tana fadin
"Karka qara kulani kuma kome kamin bazan yafema ba"
Safiya ganin amra na shirin barcin gurin tayi saurin boyewa aranta tana fadin
"Naji dadi da Arman bega marindata ma hydar ba"
Amra ko part dinsu ta nufa ta shige dakinta dake part din ta kwanta tanata sharba kuka
*Real Afreen ce*