Rikicin babban gida Book Complete Document by Real Afreen ce.txt

Author :  Real Afreen Category :  A Books

Chapter   4 / 8

9K to 12K   out of 22.9K words

me yake fada jijiyoyin kansa dik sun tashi..


"Mumy dik abinda nake mata be isheta ba..nabarta agida saboda banason quntata mata har sena soni amma zata min haka"


"Mumy mena ma amra mumy ki tambayayeta laifi na mat*****ta**AAA"


Qarar saukan marin da sukaji ne yasa sukayi saurin juyawa ..Abban amra ne ya mareta..


"Amra irin tarbiyar dana baki kenan?watoh gsky ne shiyasa kika qasa qaryata zancen sa"


Ammynta dake gefe tana hawaye ta soma fadin
"Me muka rageki dashi meyasa zaki mana haka?cikin waye amra"


Kasa jurewa arman yayi ya miqe ya fice..ita kanta goggo hawaye yakeyi tama kasan fadan komai..anty faty kuwa mutuwar zaune tayi..


Kuka kawai amra keyi abba ne yaqara kai mata duka


"Bazaki yi mgn ba"


Dady ne ya soma fadin
"Kubita ahankali wannan hayagagar qara furgita zakuyi"


Abban Amra kuwa kamar an qara ingiza sa wayar wutar dake jikin socket ya zaro... Kiran sunansa akeyi Anna fadin a a.. Amma inna yaqi kan amra ya nufa cikin zafin nama..ganin dgsk yake yasa ta miqe..


"Xan fada abba wallahi ya hydar ne"


Cakkkk Abban nata ya tsaya jikin kowa yayi sanyi..anty Amarya dake gefe tana sharar hawaye saboda tausayin amra tayi saurin miqewa cikin tashin hankali


"Wanne hydar din hydar nawa?"""""😱😱😱😱




Mahaifin hydar dake gefe ya gyda kai yana fadin


" hydar nawane agidan kuma kinsan bazata masa sharri ba"


Jikin Abban amra ne ya mutu besan sadda wayar wutan ta sulale ahanunsa ba.. Samun guri yayi yazauna yana salati..


Cikin zafin nama Abban hydar ya miqe tafita yana qwalawa hydar kira..


Ammyn amra kuwa ba abinda take fadi banda


"Amra kiban kunya ..amra bansanki ba"


Mgn take tana kuka..amra ke gefe har shesheqar kuka takeyi tana fadin


"Dan Allah Ku yafemin"


Afusace abbanta ya dago .
"Zakici ubanki keda yafi yar"


"Wa'iyazubillah habba haba kar hankalinka ya gushe mana saboda bacin rai"


Hydar ke kwance yana shaqar barcin sa bemasan meke faruwa ba baki qofar da yaji anyi ne yasa ya juyo kan ya Ankara yaji saukar wayar wuta ajikinsa da gudu ya dita ya nufi qofar fita kan kace me ya isa tsakar gida muryar Abban sa na rawa yana fadin


"Hydar nixaka kunyata kayiwa matar wanka ciki nixaka kunyata?hydar tsinema zanyi bazan xauna da mazina ci ba"


Su kuwa suna jin hk suka fitoh..
Hakuri aka dinga bama Abban hydar amma ko ajinka..hydar ma kuka yake yana na tuba...


Cikin sauri Abban amra yace dole arman yasaki amra hydar ya aureta shine kwanciyar hankalin mu..


Cikin sauri Amra ta zube gaban ammynta tana fadin


"Kutaimaki rayuwata wallahi banason ya hydar na tsaneshi"


Hakadeta ammynta ta tayi Dan haka ta nufi gurin mumyn arman tana fadin


"Mumy kice kar su rabani da ya Arman wallahi innason mijina "




Kuka takeyi kamar ranta ze fita..












*Queens writers*
[8/7, 2:39 PM] Real Afreen ceπŸ’‹: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘ΈπŸ‘ΈπŸ‘Έ
*Queens Online writers*






_Daga Alkalamin Queens_








_(Home for wisdom & perfect online writersπŸ–Œ)_




*(Q.O.W)πŸ‘‘*










🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
~Rikicin~
*{Babban gida}*








Monday's update 7th August 2017










Episode *41-45*




"Mumy kice karsu rabani da ya Arman Wallahi innason mijina"




Kuka takeyi kamar ranta ze fita....
Ya Arman dake daki yana jiyo zancen su saurinfitowa yayinda kanshi kesara masa sosai idanunsa sunyi jawuri...


Hydar kuwa farinciki yake can cikin ransa ynxu xe kasance da Amra farincikinsa




Isowar ya Arman ne yasa dik hankalinsu ya karkata garesa..


Fuskarsa ba alamun fara'a..
Binsa sukayi da kallo harsaida ya isa gurinda amra take ..kowanensu jikinsa yayi sanyi sutsaya kallon me Arman zema Amra rawar jiki ita kanta tafarayi dan dik ta tsorata...


Ruqo kafadunta yayi ya tsaya kallonta na yan mintina daga bisani ya rungumota jikinsa yayinda hawaye ke xuba afuskarsa..


Wani irin kuka tafashe dashi kamar dama jira takeyi..


Shiru kowa yayi suka tsaya kallon Arman da mamaki..

"Ba Wanda ze rabani da Amra inna son matata"
Acewar arman


Magana yake yana hararar Hydar dake tsaye yana kallonsu ya cika yayi fammm..ita kanta amra yayi mamakin zancen sa sands ta dago ta kallesa..komawa yayi ta lafe kan qirjinsa




"Kaiiii Arman kanada hankali kuwa"


Acewar Abban Arman..


"Abba da hankalina innasan matata ya za ayi arabani da ita kuma Wanda zaku bata bata sanshi"


Kowa agun kasa magana yayi sai Abban Amra ne yake qoqarin amsa shi..


"Arman nima mahaifine gareka bazan yarda kazauna da ita ba..ta bata ma suna ba"


Yana fadan haka be jira amsar da Arman ze bashi ba ya finciki Amra da ga jikin Arman


"Karka kuskura kace komai kuma karka biyoni inhar na isa dakai"


Abban Amra ya fada ..kuka sosai takeyi tana kiran sunan Arman tana bama abba hakuri amma inna janta yakeyi Arman miqa hannu yakeyi yana hawaye..


Kowa agun zubar da hawaye yakeyi..ammynta kuwa kasa daurewa tayi dan haka tabi bayansa tana fadin


"Haba Abban husna kamata ahankali mana karka illatata"


Binsa sukeyi suna basa hakuri amma ita yariga ya zuciya...dakinta ya bude ya jefata har sanda goshinta ya bugi gado ..ihun da tafi ne yasa Arman ya nufi inda suke cikin sauri amma kan ya qarasa abba yasa ma qifar key yana isowa ya sulale bakin qofar yana kuka...
Mumy ce ta tsugunna ta rungume Arman ta baya daqyar tasamu Arman yabar gurin..Abba kuwa tinda yasama dakin key yabar gurin ya nufi dakinsa...

Amra kuwa kukanta tavi me isarta har barci ya dauketa..


Arman kuwa dakinsa mumy ta rakasa saman qafarta ya kwantar da kansa ya sulale qasa itako tana zaune saman gado..


"Mumy dan Allah ki musu magana su dawo min da matata"


"Haba Arman ka hakura da amra ciki ne fa da ita..gsky bazan goyi bayan ka cigaba da zama da ita ba"


Cikin sauri ya dago jajayen idanunsa ya kalli mumy


"Haba mumy!! Itace farinciki na dan Allah karku rabani da ita"


Hawayen fuskarta mumy ta share dan gabadaya tausayin Arman yakamata...


"Kayi hakuri Arman ga safiya itama ai sanka takeyi kuma tafisonka akan Amra"


"Mumy banaso matata nakeso abani"


Shiru mumy tayi na yan mintina...
Taba jikinsa tayi taji harya dau zafi rauu...


Kan gadon tasashi ya koma ta lullubesa ya kwanta yana mata magiya ahk barci ya daukesa










*Washe gari*






"Haba Abban husna ya za ayi kace haka?"


"Nidai nafada dik Wanda ya bata abinci ban yafe ba harsai randa Arman ya hakura da ita dan bazan yarda na basa ita ba kuma itama sai ta yarda zata aure hydar din"


"Haba dan Allah komai fa ahankali ake binsa karka uzura musu dayawa"


"Kifa bar bata bakinki saboda bazan dau wannan shashancin ba"


Shiru ammynta tayi daga bisani ta miqe ta isa Palo da mamakinta Arman ta gani ya kusa qarasa wa qofar dakin amra..
Juyawa tayi ta kalli dakin abba kafin tayi saurin qarsawa


"Arman me kakeyi anan"


"Ammy dan Allah kubari inga matata dan Allah"


Shiru ammy tayi ta rasa mezatace dan tausayin Arman ya ratsata..


Ganin abba na qoqarin bude qofar dakinta yasa ammy tayi saurin boye Arman abayan qofa..Lamarin ba qaramin mamaki ya bama Arman ba..
"Toh meyasa ammy zata boyesa dan Abba ze fitoh"


Yana cikin tunanin yaji ammy na ambaton sunansa..


"Ammy dan Allah kitaimaka kibari naga amra"


"Arman kataimaki kanka ka taimaka amra kataimakeni ka bar nan karka qara dawowa"


"Ammy dan Allah karki min haka laifin me namiki dan Allah kitaimakamin"


Shiru ammy tayi daga bisani tace


"Kajirani inna zuwa"


Juyawa tayi ta nufi dakin abba saman sip ta fara dubawa cikin ikon Allah ta riqo key din dakin..
Jikinta na rawa ta fitoh daga dakin ta nufi dakin amra...


Tsaye taiske arman..tana zuwa suka fara qoqarin bude qofar..
Kwance shame shame suka iske Amra.. Nanfa suka qara rikicewa..taimakon gaggawa suka soma bata dik ta jigata..daqyar suka samu ta farfado idanunta sunyi manya tsabar kuka..
Rungumeta Arman yayi ya roqi ammy data kawo abinci abama Amra...
Batayi wata wata ba yaje ta kawo dan acewar ta bazata iya kashe yarta ba...


Bayan sungama ne ammy ta tattare plates din tana fitowa tayi cikaro da Abba nantake plates din suka zube akasa ...


Gaba dayansu sun tsorata dan fuskar abba atamke take babu alamun fara'a












*Queens Online writers*
*(Q.O.W)*πŸ‘‘
[8/13, 12:31 PM] Real Afreen ceπŸ’‹: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘ΈπŸ‘ΈπŸ‘Έ
*Queens online writers*






_Daga Alkalamin Queens_






*πŸ‘‘Queens online writers*
*(Q.O.W)πŸ‘‘*


_(Home for wisdom & excellent writers)_










🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
~Rikicin~
*{Babban gida}*








Saturday's update 12th August 2017








Episode *46-50*


Gaba dayansu sun tsorata dan fuskarta abba atamke take babu alamun fa'a...wani irin miyau me daci ammynta hadiye...cikin sanyin jiki Arman ya miqe yana fadin


"Abba kayi hakuri laifinane"


Cikin sauri ammy tace

"A'a ba laifinsa bane Nina bude"

Ammy tafada tana girgiza kai..bude baki Arman yayi da niyar mgnda sauri abba ya karbesa da fadin


"Banason dogon surutu danace kar abudeta shine kika budeta ko"


Shiru yayi kafin ya cigaba da fadin


"Kuma kai Arman indai harkanason Amra ta fitoh anan seka hkr da ita ta auri hydar din"


Wani iri Arman yaji baze taba yarda amra ta auri hydar ba..kallon amra abba yayi cike da takaici ya nunata da yatsa


"ke nixaki toxarta ki fita zakka acikin yan uwanki ko?toh in har kinason zaman lafiya tohki auri hydar"


Kuka tafarayi sosai tana fadin


"Dangirman Allah abba kayi hkr kayafemin dan Allah"


"kufita Ku bani wuri ki kulle kofarkimaidamin key din ..dik Wanda ya sake daukowa ransa seya baci..."


Riqe Arman tayi gam tana kuka mecin rai...

Arman kuwa yariga yagama fusata dan haka yasa hanunsa ya cire hanun amra daga ruqon da ta mishi harya kai qofa sai ya juyo ya kalleta kafin yayi wuuff ya fice daga part din...


Side din goggo ya nufa zaune ya sameta shiru ita kadai..
Sallama yayi cikin ruwan sanyi yasamu wuri a qasa kusa da goggo ya zauna..


"Arman ya akayine"


"Goggo dik sun birkitamin tinanina da wanne sukeso inji ne?da abinda amra tamin kokuma da rabani da ita dasukesonyi"


"Arman kati hkr ka sallama mata tabi umarninsu tinda ita ta bata musu..batan tanasonka ba ta bari hydar din yashiga rayuwarta"


"Haba goggo a tunanina ke kadai zankawowa kukana dik fadin gidanan ki fahimceni amma segashi kema kina qoqarin qin taimaka min goggo sun hanata fita sun hanatacin abincin abba so yake ya kasheta"




Shiru goggo tayi kafin ta soma fadin


"Kayi hkr zan aika akiramin Abban nata kaji kayi hkr"

Kasa cewa komai yayi sema qara zamewa da yayi ya sulale qasa ya kwanta...




_Bayan kwana biyu_






*Night*


Cikin sanda Arman yake hawan ladar dayasa jikin bangon dazesadasa da window din dakin da amra take..


Ahankali ya taka harya isa window din..zaune take kan sallaya ta idar da sallah tana sharar hawaye kamar daga sama ta jiyo muryar Arman yana kiran ta..


"Baby!!"


Kalle kalle tafarayi can ta hangosa jikin window ...kofa ta kalla kafin ta qarasa gunsa da sauri ta riqe hanunsa guda daya dake riqe da qarfen window din dayan hanunsa ya miqa mata da leda karba tayi ta bude..
Take away din abinci ne da hollandia dink da fruit.. Kallonsa tayi zatayi mgn yasa hannu akan lebenta yana fadin


"Shhh banason mgn kije kici dik kin rame baby ji bakinki dik ya bushe...ki ajiye leden kar abba ya gani zan karba gobe"


Gyda masa kai tayi kafin ta koma ta zauna gefen gado tafara bude ledar.. Fried rice ce taji salad da nama dan take away din kuma tuwo ne..


Shiko sauka yayi ita kuma ta fara cin tuwon tacinye Tass tasha drink din anan barci ya dauketa...


Tinda sassafe kuwa ta ci shinkafar dik da tayi sanyi sosai amma bayanda ta iya sbd jitayi kamar bataci komai ba daddaren..


Arman kuwa yana jikin window yaga shigar abba part din goggo dan hk yayi saurin fita dan ya roqi ammy ta budemasa yabama amra abin kari..


Dai dai yafitoh kenan sukai cinkaro da hydar wani irin takaicine yacikssa


"Watoh shi hydar yanaan yana sha'aninsa ko ajikinsa..."


Cikin sauri Arman ya qarasa gun hydar..hydar na ganinsa ya fara qoqarin guduwa..


Dasauri Arman yaqara sa..


"Nadade innason haduwarmu..hydar nixakawa hk ko?"
Acewar Arman turo baki hydar yayi ya fara qoqarin yin wani zancen banza dan hk ran arman ya baci..duka ya kaima hydar abaki aikuwa ya fasa masa baki ...sakesa hydar yayi dan hk zaro ido hydar ya farayi yana taba inda jini ke fita...
Rai bace Arman yace

"Kadan ka gani"
Yajuya ya nufi part din su amra hydar kuwa ya sake baki yakasa cewa komai












*Queens online writers*πŸ‘‘
[8/15, 4:16 PM] Real Afreen ceπŸ’‹: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘ΈπŸ‘ΈπŸ‘Έ
*Queens online writers*




_Daga tsakar Queens_






*πŸ‘‘Queens online writers*
*(Q.O.W)πŸ‘‘*


_(Home for wisdom & excellent writers)_







🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
~Rikicin~
*{Babban gida}*






Monday's update 14th August 2017






Episode *51-55*



Part din su ya koma anty Amarya na zaune tanaganin shigowarsa harta kauda ganinta daga garesa sbd ya bata mata rai akan abinda ya aikata sekuma taga jini a bakinsa..

"Meyasa meka?"


Kusa da ita ya qarasa ya zauna
"Ya Arman ne haka kurin fa nazo wucewa ya bugammin baki"

"Kodai wani Abun kace masa hydar"


"A a umma bada abinda kace masa"


Wani irin qululu anty Amarya taji yazo mata..toh meyasa ze dakin mata da,..
Shiru tayi daga bisani ta miqe ranta abace ta nufi toilet ruwa ta debo a bowl da towel tazo tana goge masa gun..


Badai tace komai ba dan daga bisa allamu ranta ya baci..shiko hydar dadi yaji sosai dan dama so yake umman tasa yadawo goyan bayansa harse anbasa Amra...


Shiko Arman part dinsu amra ya nufa zaune ya samu ammy hanan na gefenta suna assignment...


Sallama yayi dik suka amsa masa ya tsugnna har qasa yagaida ta..fuskarta Sam ba fara'a take amsa wa..


"Ammy dan Allah so nake adan budemin amra naga halin da take ciki tinda abba ya fita"


"Kaiiii Arman ka kyale amra ka hakura da ita ta auri Wanda mahaifin ta yakeson bata tinda ita tajawa kanta..ynxu bakasan qin hakura da ita ba kanasata acikin wani hali bane..tinda mutun ya wuni arana so daya ake basa abinci kuma abincin ma can qasa da kwano"


Ammy na kaiwa nan ta fashe da kuka mecin rai..bude baki yayi zeyi mgn ta daga mata hannu da sauri


"Karka cemin komai ka tashi kafita ka tashi nace!!!!"


Ba musu ya miqe ya fice yana waigensu har ynxu ammy na sharar hawaye afuskarta..


Part dinsu ya nufa cikin sauri cikin sa a ya tarar da mumy da safiya a palon


"Son ya naganka haka"


Kusa da ita yazo ya zauna ya daura kansa akan cinyarta..yasan dai zancen nasa baze wuce akan amra ba..


"Mumy dan Allah kije Ku karbomin mata ta karsu kashemin ita"


Magana yake hawaye na zuba daga fuskarsa..gaba daya safeena tausayin yayan nata yakamata sosai


"Kamanya zasu kashe ta?"
Acewar mumy


"Mum abinci fa so 1

4 / 8