Author : Zee MD Category : Top Hausa Novels 2025
Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 23
Aysha ta dubi Khalid tace " kasan da wa mukayi waya ? Khalid ya girgiza kai
yana fad'in " taya zan san da wa kikayi nasan dai mace ce , Murmushi Aysha tayi sannan tace "
Mutuniyar ka wai zatazo yau in ina gida , Khalid ya tab'e baki sannan yace " nasan indai tazo to
sai tayi zan cena , kinsan Allah Baby ni nafison inyi rayuwa da wa yayyiyar mace irin ki ,
inason inga budurwa ta tana bani kulawa kamar yadda kike bani , Ruma babu abinda ta iya
sai k'auyan ci itafa ko romance bata bari muyi , kullum sai ta runga cewa in k'ara hak'uri in
mukayi aure tazama tawa komai sai yadda nayi dashi , ...
Aysha tuni taji wani ciwo a zuciyar ta yataso , tabbas ko wacce mace me mutunci babban
burin ta shine ta tsare mutuncin kanta , amman ita ta k'arfi da yaji aka b'ata mata mutuncin ta ,
ta sanadin haka yanzu gashi ta lalace ,hawaye ne suka cika mata idanun ta tayi saurin maidasu
, dan bata so ko da wasa Khalid yasan damuwar ta , Khalid yaci gaba da magana " kin san
wani Abu Baby ? Aysha ta girgiza kai alamun a'a , yace ko sau d'aya bantab'a son Ruma ba ,
saboda bata d'aya daga cikin Matan da nake da burin aura , kawai ina kulata ne dan kud'in
Baban ta , kuma sannan ina son dukiyar kaf tazama tawa nan gaba bayan babu shi , Aysha ji
tayi wata tsanar Khalid ta nunku a cikin ranta , tabbas Khalid azzalumine kuma sai takawo
k'arshen zaluncin sa nan ba da jimawa ba , Murmushi tayi nasu na asalin 'Yan duniya ta dubesa
tace " to meyasa ka yadda zaka aure ta bayan kuma bata d'aya daga cikin matan da kakeso ka
aura ? Murmushi Khalid yayi sannan yace " Baby ai kinsan a k'ark'ashin Mahaifinta nake kinga
da kunya 'yar sa ta nuna tana sona nak'i amincewa , da zarar komai yadawo hannu na zan iya
rabuwa da Ruma ko kuma na auri wacce rai na keso , Aysha tace " gaskiya kai d'in ka iya buga
game amman karkaje fa ayi maka Babban bugun da ya wuce naka , Dariya yasa yana fad'in "
waye zai bugani alhalin ba wanda yasan meye a zuciya ta indai bake ba dana fad'a miki , kuma
ni nasan ina da tabbacin bazaki fad'awa Ruma komai ba , Aysha tayi murmushi tace " haba
Dear taya zan tona maka asiri , ai in nayi haka tamkar na tonawa kaina asiri ne nima , kadaina
ma fad'in haka dan kasan ni taka ce kai nawa ba ta yadda za'ayi inga wani abu da zai zo ya
kawo maka matsala batare da na kaudashi ba , haka Aysha ta karkace tashiga yiwa Khalid
dad'in baki sosai , nan yayi mata alk'wari komai takeso tafad'a zai siya mata , ...
Aysha tanajin haka ta kashe masa ido tace " account d'inka da zurgi kenan My Dear ?
Khalid cike da shauk'in so yace "2 milloine acikin account d'ina yanzu , sai kinsan dayake ban
dad'e dafara zuwa kasuwar ba , kuma ahakan ma ina had'awa da cuwa cuwa batare da me
wajen ya lura ba , nan Aysha taji sirrin Kud'in da Khalid yake dashi , Murmushi tayi cikin ranta
tace " yanzu zaka fara rabuwa da 1 Million kafin nan da kwana biyu ka rabu da sauran ma ,
cike da kissa Aysha tace " ni yanzu abinda nakeso kawai shine muje kasiyamin zobunan gold
da sark'a dan ina son du sosai , Khalid ganin irin yadda Aysha ta kwanto jikin ta ajikin sa ga Na
shanun ta rabin su duk sun fito yasa shi rud'ewa tare da cewa " muje Baby angama ,......
Jabir tunda suka rabu da Aysha yake ta dakon kiran ta amman shuru , gashi ya gwada
layin ta amman baya tafiya kwata kwata , damuwa ya shiga sosai tare da fad'in " wato wayo
Aysha tayimin batare da nagane ba , meyasa na yadda nabar ta ta tafi batate da nabi bayan ta
ba ? tabbas indai yakuma ido biyu da Aysha bazai barta takuma raina masa hankali ba , kuma
ai yagane number motar ta dakuma kalar motar tabbas zai ci gaba da neman ta tamkar yadda
yayi kwanaki , .......
Yau saura kwana biyu Hameed yabar k'asar Nageria , hankalinsa sosai yatashi ganin har
yakusa tafiya bai samu Aysha ba , yaje sau biyu unguwar su Aysha yana ganin ko Allah zai sa
yayi sa'a sundawo , sai dai ko kad'an basu dawo ba kullum gidan arufe yake , yauma yana
zaune a k'ofar gate d'in gidan su yana chat da wani abokin sa a can k'asar London , kwana
biyu zaman cikin gidan baya masa dad'i saboda Hajiyar sa ta damesa da Maganar Abida ,
shikuma har ga Allah bason maganar yake ba , shifa indai ba Aysha ba haryanzu baiga macen
data yi masa ba , dan acan ma London akwai mata wad'an da suke son sa sosai amman duk
yak'i basu fuska........
Koda su Aysha sukaje wajen saida sark'ok'i , sai da Khalid ya siya mata na Million d'aya
da dubu Hamsin , dan zab'a tayi sai dataji masu kud'i dayawa tace su takeso , Khalid sosai yaji
fitar kud'in amman gudun kar ta gane ya dake tamkar wani Alhajin Birni , da suka taho hanya
tasa shi ya biya da ita wani Shopping Mall tayi siyayyar dubu d'ari nan ma ya biya , Khalid
suna fitowa ya nuna shima yanaso tabashi jikin ta dan haka su biya Hotel yakama musu waje ,
ko kad'an Aysha bata damuba dan dama jiran wannan ranar take , dan tasan daga wannan
ranar bazai k'ara ganin Nonon ta bama bare jikin ta , haka sukaje Hotel Khalid ya kwashi gara
sosai ,kusan sumewa yayi saboda sambatu dan iya jin dad'i yajishi a tare da Aysha , sai yake
ganin ko nawa ya kashe mata bai fad'i ba ganin yadda ta rud'ashi shima , sosai yayi mamakin
yadda Aysha ta k'ware wajen iya wasanni ,ko dayake bazai mamaki ba ganin ta wayayyiyar
Yariya wacce tagaji da had'uwa, haka suka gama d'ebewar su sannan sukayi wanka suka nufo
gida......
Aysha tun a farkon layin su tasa Khalid ya sauke ta , koda zata fita daga motar sai da
Khalid yace " Babyna yaushe zamu kuma had'uwa ne ? dan gaskiya kinjiyar dani wani dad'in
da ban tab'a ji ba sai sau d'aya , Murmushi tayi sannan tace " sau d'aya Dear ashe katab'a yin
sex ? Khalid yace " natab'a kwanciya da wata yarinya duk ba'ason ranta ba mukayi kuma shine
farkon yina nima bana cikin nutsuwa amman haryanzu abin na raina , Aysha wani abune
yataho mata ya tokare k'ahon zuciyar ta , kallon sa tayi cike da tsana tace " Saboda me ya
tsaya maka arai kuma alhalin kace ba'ason ranta kayi ba ? jin yadda tayi maganar yasa ya dube
ta , sai sannan Aysha tayi saurin ankarewa ta sassauta muryar ta tace " sorry Dear tausayin
yarinyar naji ,amman meyasa kayi mata haka Alhalin bataso ? Murmushi yayi sannan yace "
gaskiya sha'awarta tadameni kullum in muna tare to sai kinga abata a mik'e saboda yadda nake
shaawar ta , ban daina jin hakan ba har sai randa na kusan ce ta , tana kuka tana magiya
amman haka idona ya rufe na keta mata mutuncin ta , Aysha jitayi kamar a lokacin Khalid yake
keta mata mutunci , hawaye ne ya cika idon ta wanda ta kasa iya maidasu , tabbas Khalid ya
zalince ta dan shine sanadin komawar ta wannan rayuwar , yanzu waye zai aure ta a irin
wannan rayuwar tata ? Meza tacewa Yaranta dazata haifa nan gaba ? taso ace Mijinta wanda
zai aure ta shine zaifara sanin ta a duniya , amman Khalid ya rusa mata duk wani shirin ta ya
lalata mata rayuwar ta , yasa taci gaba da sab'on mahaliccin ta , duk da tashiryu bayan zubar
da cikin da tayi wanda yayi mata , Farouq shine ya maida ta ruwa shima yasa ta koma *'Yar
Hannu* , tabbas Khalid azzalumine ya cuceta a rayuwar ta , jin tayi shuru yasa Khalid yin
magana yace " meye naji kinyi shuru My Baby ? wani guntun Murmushi tayi sannan tace "
wallahi danaji abunda kayiwa Yarinyar nan sai na tuno da wani Malamina a makaranta nima da
yayimin fyad'e , Khalid yace " ayya sorry Baby kice mugun malami shine yafara yi mana hanya ,
nima kinsan Allah nine nafara yiwa yarinyar nan hanya , daga baya tasamu ciki nikuwa nayi
mata korar kare , dan a ganina taya za'ace daga kwanciya sau d'aya wai ciki yashiga ai tazo da
iskanci , sotake na aure ta ganin bata da wani asali gasu talakawa ba k'aruwa yasa na yi mata
fata fata muka rabu , Aysha jitayi in bata yi saurin fita daga motar Khalid ba to tana gab da
had'a masa jini da majina , shiyasa tayi saurin d'aukar kayan ta tace "muyi waya My dear , bata
jira cewar saba ta fice da sauri abinta , Khalid ko ajikin sa bai kawo komai ba sai ma bin
Mazaunan ta dayayi da kallo yana kuma wassafo dad'in daya sha ajikinta.......
Hameed yana zaune kamar ance masa ya kalli hanya ya hango Aysha ta nufo ta wajen
dayake , da sauri ya mik'e yana murza idanun sa itace dai ba gizo take masa ba , kwata kwata
Aysha bata kula da Hameed ba har tazo ta gifta ta gaban sa , haka yashiga binta batare da yayi
magana ba , sai datazo k'ofar gidan su lokacin Habu na zaune yanajin radio ta wuce shi yana
mata sannu da zuwa , da yauwa ta amsa ta shige ciki abinta shikuma Hameed yaja ya tsaya
gana yiwa Habu sallama.........
*Ina mutukar Son Comment d'inku Masoyana*
_Yin Comment shine ke k'ara mana k'aimin yin Typing_✍✍
*Saina jiku*
*'Yar Mutan Kanawa*
_Ce_
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
_NA_
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 24
Habu ya amsa sallamar Hameed yana duban sa , Hameed yace " Abokina dan
Allah inaso kamin magana da wacce ta shiga gidan nan , Habu ya dubi Hameed tabbas yaso
gane fuskar sa saboda yana yawan zuwa gun Aysha da dad'ewa lokacin suna wancan gidan ,
Habu ya nisa sannan yace " gaskiya yanzu ta dawo daga Makaranta nasan ba lallai ta fito
yanzu ba , sai dai ko kabari zuwa anjima in ta huta sai nayi mata magana , Hameed ya dubi
Habu sannan yace " nan ne gidan su kenan ? Habu yace ea.
Hameed yayi wata ajiyar zuciya kafin yace " nagode abokina xuwa anjima zan dawo nasan
lokacin ta huta , nan yayi wa Habu sallama ya juya cike da murna ya nufi gida , tabbas yau
yasan zai kwana cikin farin ciki na ganin wacce ya dawo Nageria domin ta , duk da yaso ace bai
baro k'ofar gidan ba har sai yaganta , amman gudan Habu yace masa bazata fito yanzu ba yasa
ya hak'ura , dan haka yanzu in anyi sallar Magriba zai shirya yaje gareta ya bayyana mata
abinda ke zuciyar sa.....
Aysha tana shiga tasamu Gogal na zaune tana kallo , bayan tayi mata sannu da gida ta
shige d'akin ta dan ta watsa ruwa , tunowa tayi da siyayyar da tayi a motar Khalid tayi sauri
d'aukar waya tashiga kiran sa , yana d'agawa yace mata " Babyna me kayan ruwa ya akayi kin
barni da tunaninki tunda kika tafi , wani murmushin takaici Aysha tayi jin sunan da yaki rata
dashi , cike da kasalalliyar Murya tace " My D nayi mantuwa a cikin motar ka , murmushi yayi
sannan yace " nima sai yanzu nagani dan haka ni mantuwar nan tamin dad'i dan ko bakomi na
sake dawowa na kalli kyakkyawar fuskar Mata ta , Wani abu Aysha taji ya tsirga mata a kwanyar
kanta , ada lokacin datake Ayshar ta sanda takeson Khalid indai yace mata matar sa har wani
dad'i takeji , amman a yanzu tamkar yasa mata dalmar wuta , dan ji tayi takuma tsanar sa a
ranta , shurun da yaji tayi shine yasa yace " naji kinyi shuru Aysha ko nayi laifi dan naki raki da
sunan Mata ta ? Da sauri Aysha tace " taya zanyi fushi naji ka kirani da kalmar da nadad'e ina
jiran ta daga bakin ka , duk a tunani na kawai muna abota ne amman bazaka iya auren mace
irina ba , Khalid ya zaro ido tamkar yana gaban Aysha yace " ni asuwa da zan k'i mace
kyakkyawa irinki , ina kallon kaina ne kawai a wanda basu isa ki aura ba saboda yanayin ki da
kuma irin gidan da kika fito , Murmushin mugunta Aysha tayi sannan tace " kadaina cewa haka
My D kasan shi so baruwan sa da haka , sai dai ina ganin in mukayi haka tamkar zamuci
amanar Ruma ne , Khalid yace " dan Allah kidaina saka wannan bagidajiyar a lissafi nifa
nafad'a miki ko sau d'aya ban tab'a son taba , kinsan manufa ta akan ta ki kwantar da hankalin
ki kawai kibani had'in kai , Aysha tace " karka damu Nawan nabaka , wani tsalle Khalid ya buga
kafin yace " ina nan hanya in anyi sallar isha'i nasan lokacin Ruma tazo ta tafi , Aysha tace "
shikenan sai kazo ta katse wayar sannan ta shiga wanka......
Tana fitowa takira Ruma a waya ta sheda mata ta dawo , bayan ta shirya cikin doguwar
riga ta nufo palor wajen Gogal....
Tana zama suka shiga hira take shedawa Gogal takusa daina koyarwa a Makaran ta ,
Gogal ta dube ta tace " kin sami mijin aure ne Aysha da zaki daina koyar wa ? Murmushi Aysha
tayi sannan tace " ina dai kan hanyar Samu sai ki kuma tayani da addu'a , Sallamar Ruma itace
ta katse su daha hirar su , shigowa tayi tasamu guri ta zauna tana gaida Gogal , ta amsa tare
da tambayar ta iyayen ta suna lafiya , Ruma tace "lafiya lau suke suna gaidake , hannun Ruma
Aysha taja suka tashi suka nufi cikin d'akin Ayshar......
Koda shigar su Ruma ta dubi Aysha tace " zakiyi mamaki jin cewar inason muyi magana
dake , Aysha ina da k'awaye sosai da wanda muke Sch d'aya da kuma wanda suke cikin Family
d'in mu , amman bantab'a jin soyayyar su araina ba kamar yadda lokaci d'aya naji soyayyarki ,
tun had'uwar mu naji kin shiga raina sosai tamkar wacce muka fito ciki d'aya , dan Allah Aysha
inaso kibani shawara akan Soyayyata da Khalid , tunsan da mukazo gidan nan naku nida shi
har yau ban kuma samun kan sa ba , kullum da irin uzirin da yake bani kwata kwata ko kirana
bayayi a waya , gashi in nakirashi nan ma sai ya katse yace aikine yayi masa yawa , kuma yau
d'in nan da safe Daddy ya tabba tar min da rashin zaman sa sosai a kasuwa , narasa me ke
damun Khalid kwata kwata da ya canza lokaci d'aya , hawaye ne suka taru a idanun Ruma ta
rik'e hannun Aysha tam taci gaba da magana " wallahi Aysha ina mutuk'ar k'aunar Khalid
shiyasa na damu ,