YAR HANNU BOOK COMPLETE NA ZEE MD.pdf

Author :  Zee MD Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   7 / 21

18K to 21K   out of 62.7K words

na dare lokacin Gogal tayi bacci , Aysha na d'akin ta tana chat d'in
ta kamar yadda ta saba , jitayi ana buga musu gida da k'arfi tamkar za'acire k'yaure , mik'ewa
tayi ta ajiye wayar ta fito tsakar gida , d'akin Gogal ta lek'a har lokacin baccin ta take hankali
kwance , a hankali ta nufo soron gidan nasu tace " waye ? daga k'ofar gida taji ance " kibud'e
min inyaso zakiga waye bataji tsoro ko kad'an ba ta zare sakata , Farouq ne a tsaye shi kad'ai
yana wani huci tamkar zaki , duban juna suka shiga yi shida ita kafin yace " kishiga ki d'auko
min takardun gidan da Daddyna yabaki tare da mukullin mota ta yanzu yanzu , murmushi Aysha
tayi sannan tace " shine abinda ya aiko ka kenan ? Farouq cike da k'uluwa yace " shi ya aikoni
dan haka kije ki d'auko tunkafin jikin yagaya miki yanzu yanzu , Aysha tayi murmushi batare da
ta kuma cewa komai ba ta juya cikin gida , batafi minty 5 saigata d'auke da takardu da mukulli
tadawo , tana zuwa ta mik'a masa sannan ta d'auko masa katin shedar dazaije ya d'auki motar
a wajen gadi , tana gama bashi tace " gashinan zaka iya tafiya dan inason kulle gidan ,
murmushi Farouq yayi sannan yace " ashe dai kina da tsoro haka bansani ba ? kin samawa
kanki lafiya dan dayanzu kingayawa 'yan garinku , yana fama fad'in haka ya shige abinsa yayi
gaba , Aysha murmushi tayi sannan tace " yadda kazo ka anshi wannan abubuwan haka zaka
dawo dasu a yanzu basai gari ya waye ba , rufe gidan tayi ta koma cikin d'akin ta......


Wayarta ta d'auko ta bud'e data ta hau online , aikuwa taga Alhaji Na Lamma yana kai ,
murmushi tayi sannan tashiga cikin Videos tafara neman videon sa , tura masa tayi sannan a
k'asa tayi rubutu kamar haka :
_Ina so ka bud'e Video nan kagani yaka mata ace ansashi a Social Media dan wasu su d'au
style_...

Tana gama tura masa ta sauka gaba d'aya daga online d'in , batafi minty 5 da sauka ba
saiga kiran wayar Alhaji Na Lamma , kin d'auka tayi har sai da yayi mata kira biyar , Ana shidan
ne ta d'auka tana kaiwa kunne taji yana fad'in " dan Allah karkimin haka plss , kome kikeso
kifad'amin wallahi zanyi miki , in kikasa abun nan a Social media wallahi nashiga uku , ina da
surukai a 'Yaya ga matana suma ga kuma abokaina da kuma jama'ar gari dasu ke ganin

mutuncina , koda bata ga Alhaji ba amman tasan duk inda yake yana cikin tashin hankali , dan
yadda yake maganar kawai zakasan ba k'aramin kad'uwa yayi ba , muryar sa ta kuma ji yana
cewa " dan Allah kitaimaka plss mekikeso inyi miki ? Murmushi Aysha tayi sannan tace " inaso
ka kira wayar 'Dan ka yadawomin da duk abinda yazo ya karb'a yanzu , sannan kagaya masa
lallai yazo to ya durk'usa yabani hak'uri akan abinda yayimin , mutuk'ar hakan bata faru ba to
tabbas Videon ka gobe dashi za'a karya kumallo a Social media , dan ni bana shakkar dan
anganni a haka tunda daman sana'a tace , kit takashe wayar batare da tajira cewar saba.........






*Comment* plss



*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR* *HANNU*



_NA_
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*



_Page_. 12


A hankali Aysha ta d'aga k'afar ta tashige cikin gida , d'akin ta tashige kai tsaye ta
fad'a kan katifa tana nazarin magan ganun Jabir , a haka bacci yayi gaba da ita sai da safe ta
farka , wayar ta ta d'auka ta kunna aikuwa test tagani kala kala suna shigowa cikin wayar ta ,

bata tsaya bi takan suba ta mik'e ta nufi band'aki....

Bayan tayo wanka ta fito ta shirya sannan ta nufi d'akin Gogal , tana shiga tasa meta tana
shan kunu da k'osai , Gogal tace " sannu da tashi yau naga kin makara sosai , Aysha ta gaida
Gogal sannan ta matso tafara shan kunun itama tana fad'in " nifa Gogal gani nake tunda mun
samu gida gwanda yau mutashi daga unguwar nan , Gogal tayi jim sannan tace " nikam gani
nake wanda mu zauna anan saboda yadda kika fad'i gidan yayi mana girma , Aysha tace " haba
Gogal bawani girma da yayi mana zamu iya zama abin mu mu kad'ai , da sonake ma mutafi
harda Habu me shago ya dunga kulawa da gidan , nan Aysha ta shiga tsara Gogal har tasamu
ta amince nan da kwana biyu zasu koma sabon gidan....


Farouq tunda suka taho hanya yakasa yiwa Daddyn sa magana , sai da suka iso gida
sannan yadubi Daddyn nasa yace " Daddy yanzu ni a wacce motar zan dunga yawo kenan ?
Daddy yace " zansiya maka wata amman kayi hak'uri baza kasamu kamar taka ba sai dai
wacce bata kai taba , Farouq kad'an yarage baisa kuka ba taya shi dayake son ci gaba za
amaidashi baya , yanzu indai Abokansa suka ganshi da motar da bata kai tashi tsada ba ai
sunsamu abin yin gulma , tabbas zai koyawa Aysha hankali tunda duk itace sanadin hakan ,
Yana fita daga motar yayi b'angaren sa duk ransa a dagule.......

Hameed tunda ya koma k'asar America yakasa komai sai tunanin Aysha , daga ya rufe
idanun sa itace keyi masa gizo , tunda yadawo kwata kwata abokan aikin sa suka kasa gane
kansa , Aleeya budurwar sa wacce suke aiki tare babu irin tambayar da batayi masa ba akan
canzawar sa amman yace bakomi , kullum in yadawo daga wajen aiki bashi da burin daya wuce
ya keb'e kansa yana tunanin Aysha , abinda ke damunsa rashin sanin yaya take da kuma
rashin dabara dabaiyi ba ta anso number wayar ta , yanke shawara yayi na tahowa Nageria
kawai kozai samu sauk'i inya ganta.......


Tunda garin Allah ya waye Aysha taji batason yau ko soro ta lek'a , d'akin ta ta koma ta
kwanta tana danna wayar ta , kiran Alhaji Na Lamma ne ya shigo tana kallo amman tak'i
d'agawa , sai dayayi mata kira biyar amman tak'i d'agawa , daya ke datar ta a bud'e take sai
ganin test d'in sa tayi ya shigo ta whassp , nan ma ta bud'e tagani amman tak'i masa reply ,
Daga k'arshe ma ta kashe datar ta ta ajiye wayar tayi kwanciyar ta abinta , tana kwance taji
yaro ya shigo yana fad'in " wai ana kiran Babyn dad'i a waje , a zabure Aysha ta mik'e tana
fad'in " nashiga uku waye zai min wannan aika aika haka ? bata gama tsora ba sai dataji
muryar Gogal na fad'in " wace ce kuma Babyn dad'i agidan nan ? kaje kace banan gidan bane
kaji wannan suna haka mara amfani da ma'ana kuma , haka tai ta fad'a har yaron yafita , Aysha
jitayi jikin ta na rawa tamkar mazari da sauri ta d'auko hijab tasaka zata fito takuma jin yaron
yadawo yana fad'in " wai ance anan gidan take kuma tasan kanta , Aysha tayi saurin fitowa tana
fad'in " kai wannan wanne irin abune haka ? muje naga wanne d'an iska ne yake mana wannan
abu haka , Gogal itama ta fito tana fad'in " nima dai bari nazo naga waye me wannan aike haka
da bashi da mutunci , Aysha da sauri ta dakatar da Gogal tana fad'in " bari naje nagano ki koma

kawai basai kin fito ba ....


Aysha na fitowa waje taga Jabir tsaye ya hard'e cikin k'ananun kaya abinsa , yana ganin
fitowar ta ya fara wani shu'umin murmushi yana kallon ta , tana k'arasowa a fusace tace " wai
kai me kake nema a cikin rayuwa ta haka da kake damuna ? Jabir yayi murmushi sannan yace
" kan ki nake nema inaso ki anshi soyayya ta ki huta dani kawai , tsaki Aysha taja sannan tace "
idan kuma ban ansa ba fa ? Jabir ya matso gaf da jikin ta yace " in baki ansa ba kuma kin san
sauran zancen , dan duk duniya sai tasan wace ce ke , ta yadda kike shigar mutunci kina cin
zarafin hijab da nik'af , kina janyowa ana b'atawa masu irin wannan shigar taki suna , inaso
kisani zan fad'a miki hanyoyin da zaki bi dan bin umarnina ki zauna lafiya , Aysha tace " inaso
kasani ko kafita daga cikin rayuwata ko kuma insa afitar mun dakai , kuma soyayyace bazan
tab'a yin ta dakai ba saboda kaima ba soyayyar Allah zakayi min ba , murmushi Jabir yayi
sannan yace " kin tab'a gani anso karuwa soyayyar Allah ne ? ai tsakanin ka da ita kawai ka
murji jikin ta ka shige kabarta a wajen , ni bani da kud'in da zan biyaki in murji jikin ki amman
inaso ko taya ya sainayi amfani dake , Aysha tace " hakan ba k'aramin kuskure zakayi ba kuwa
a cikin rayuwar ka , tana gama magana ta juya zata tafi taji yace " Babyn dad'i ki saurari
tambayoyin da Kakarki zata miki akan wannan sunan , dan sai tasan komai game da rayuwar
da kikeyi har wannan motar da aka baki kika yi mata k'arya , Aysha duk da tanajin tsoro
amman haka ta dake bata nuna masa ba har ta shige cikin gida abinta..........




*In naga Comment inci gaba sannan in k'ara yawan typing*


_In kuma bakuyi ba intafi hutu sai bayan sallah ajini_


*'Yar* *Mutan Kanawa* _Ce_
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR* *HANNU*



_NA_
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨



*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*




_Page._ 14


Alhaji Na Lamma jikinsa har rawa yake wajen neman number Farouq , goge zufar
dake zubo masa yayi tare da danna kiran number Farouq , yana d'agawa yace " Daddy na
anso komai gani nama taho yanzu , Alhaji Na Lamma da sauri yace " maza ka juya ka koma
mata da dukkan abinda ka anso , Farouq a tsorace yace " what Daddy in koma mata dasu kace
fa ? Alhajin yace " Ae maza ka juya kamaida mata dasu nace , yana gama fad'ar haka ya
kashe wayar yayi cilli da ita kan kujera ya mik'e yana zagaye d'akin nasa , tambaya ya shiga
yiwa kansa " taya akayi wannan yarinyar ta shammace shi haka batare da yasani ba ? tabbas
duk yadda zaiyi sai ya raba ta da wannan video ko zai samu sukuni , mutuk'ar wannan video
yana tare da ita to zuciyar sa zata kasan ce cikin zullumi , haka yashiga kaikawo goge zufar
dake zubowa jikin sa , duk ac dake aiki a d'akin nasa sai yaji kamar ba su saboda zafin dayake
ji.........

Farouq juyawa yayi da kan motar yakoma gidan su Aysha , Farouq mamaki ne yakamashi
ta yadda akayi Daddyn nasa yace akoma mata da komai , yana tafe yana nazarin wane irin Abu
Aysha tayiwa Mahaifin nasa har ya sauko haka ? bai wani dad'e ba ya k'araso k'ofar gidan su
Aysha , yana zuwa ya fito daga motar ya zo k'ofar gidan yashiga bugu da k'arfi tamkar zai
karya musu k'aure , Aysha dama tana zaune tana jiran zuwan sa , tana jin yana wannan bugun
ta mik'e a hankali tayo hanyar soron gidan nasau , tana zuwa ta zare sakata tana duban
Farouq d'in , shima ita yake kallo cikin kwayar idon sa ta hango zallar tsanar ta , itama kuma
anata idon hakane dan ta tsani Farouq sosai , wurga mata takardun yayi tare da mukullun motar
ya juya zai tafi , Aysha tace " haka kake yiwa uwarka kenan inkaje bata abu ? a fusace Farouq
ya juyo tamkar d niyar marin Aysha wayar sa ta shiga ruri , dubawa yayi yaga sunan Daddyn sa
ya d'aga , yana d'agawa Alhaji Na Lamma yace " inaso kabata hak'uri akan abinda kayi mata
sannan in zaka bata hak'urin inaso ka rissina tamakar yadda kakeyimin , Farouq wani abu yaji
yatsaya masa a k'irjin sa tamakar ya had'iyi zuciya ya mutu , baice komai ba ya kashe wayar
yana duban Aysha yace " menayi miki haka kika zab'i kiyi min hukunci ta wannan hanyar ?
nabaki hak'uri akan abinda nayi miki nida abokaina amman kink'i saurarena , kuma ko a lokacin
da nayi miki wannan abu ai naji ba a cike kike ba , kinga daman ked'in *'Yar Hannu* ce ,
murmushi Aysha tayi sannan tace " kayi abinda Mahaifinka yace kayi yanzu katafi , kasan dare
ne yanzu hakan ba rana ba bare ka tsayar dani , Farouq ya rissina tamkar yadda mahaifinsa ya
umarce sa yabata hak'uri sannan ya shige yabar k'ofar gidan da tarin tsanar Aysha , da kallo

Aysha ta bishi tana murmushi sannan ta maida k'ofa ta rufe tayo cikin gida abinta......


Washe gari
Aysha tana tashi tagama had'a musu abin kari , Bayan sun karya tayi wanka ta fito sannan
tacewa Gogal " tanaso taje gidan da zasu koma d'in taga meye babu a ciki , Gogal tace " ai da
samo mana masu kura kikayi suka zo suka dib'i kayan inyaso basai mun nemi komai ba ,
Aysha tayi murmushi tana duban Gogal tace " ai wahala zasu sha masu kura Gogal sai dai
motar , amman bari naje dai nadawo sai muga yadda za'ayi , shigar ta ta tayi wacce tasa ba ta
rufe ko 'ina na jikin ta tafice daga cikin gidan....


Tayi nisa a tafiyar ta taji ance " Malama Aysha *'Yar* *Hannu* , ko bata waiwaya ba tasan
Jabir ne , dan yanzu kusan shine babbar matsalar ta a cikin rayuwa , duk inda tasa k'afa tasan
yana bibiyar ta amman dole tayi maganin sa tun kan dare yayi mata , wata dabara ce ta fad'o
mata kawai ta juyo tana murmushi tace " Malam Jabir manyan gari yakake ? Jabir cike da
mamaki yace " lafiya lau nake kema ina fatan hakan kike ? Murmushi tayi sannan tace " gashi
kuwa kagani , Jabir ganin Aysha ta saki jiki dashi yasa yafara tunanin ko barazanar da yayi
mata ce yasa taji tsoro , cike da jin shi wanine yace " ina zuwa haka manyan gari ? murmushi
Aysha tayi sannan tace " wata k'awa tace baban ta yarasu shine zanje mata gaisuwa , Jabir
yace " Ayya Allah yajik'ansa in kindawo anjima sai muyi magana ko ? Aysha tace " babu
damuwa sai nadawo d'in , Allah yadawo dake lafiya ya juya yabarta ta nufi titi tana dariyar
mugunta......


Gate hause d'in Alhaji Na Lamma Aysha ta nufa , tana zuwa tasamu me gadin gidan a
k'ofar gate a tsaye yana jin redio , tana zuwa tayi masa sallama ya amsa yana kallon ta tamkar
wanda yaga wata halittar daban , Aysha tace " inason shiga gidan nan dan zan duba wani abu ,
Megadin ya dube ta sama da k'asa sannan yace " baiwar Allah taya zanbarki ki shiga cikin gida
batare da nasanki ba ? kuma koda nasanki taya zan bud'e miki Alhalin Alhaji bai cemin in bud'e
miki ba ? d'age nik'af d'in Aysha tayi tana kallon sa sannan tace " kashiga ka gayawa Alhajin
kace me gidan ce tazo tanason suyi magana , mai maita wa Megadi ya shiga yi yana fad'in "
Me gidan ce tazo , haka ya

7 / 21