Author : Zee MD Category : Top Hausa Novels 2025
mata
da Reply na Hy My dear you'r welcome , Aysha tace " kozan iya magana dake in babu damuwa
? Leeemah tace " bawata damuwa Uwar ruwa ina jinki , sunan da Aysha ke amfani dashi shine
Uwar ruwa , Aysha tace wani aiki nakeso zakimin yaud'in nan inba damuwa ? Leeemah tace "
fad'i komai kikeso kan ki tsaye zanyi miki shi , Aysha tace yanzu dai kina wane gari dan inji ,
Leemah tace "Ina garin Kano unguwar Gadon k'aya , Aysha tace " gud inaso kimin wani aiki
anjima a Hotel d'in Taheer gate palace , Leemah tace angama Uwar Ruwa fad'i yadda aikin zai
kasance , Nan Aysha ta sheda mata tana so su had'u a Hotel d'in k'arfe hud'u da rabi dai dai ,
daga nan zatayi mata bayanin yadda zata yi aikin , take Leemah tayi Na'am nan suka gama
magana , Aysha kafin ta kashe datar ta ta kuma nemo Number Ruma ta tura mata voice d'in
muryar Khalid , wanda yake fad'in bason ta yake ba kawai saboda kud'in Mahaifin ta yake
kulata , amman da zarar ya aure ta yasamu kud'i to zai auri kalar matar da yakeso , harda
yadda yake cutar Mahaifin Rumar a kasuwa batare da yasani ba , duk voice d'in da sukayi sai
da Aysha ta turawa Ruma sannan a k'asa ta rubuta " ko zaki iya sheda wannan muryar waye ?
daga haka ta kashe datar ta ta sauka gaba d'aya daga kan Whaspp d'in ......
Wajen k'arfe Uku Aysha ta shirya cikin shigar ta ta kamala tafito , d'akin Gogal tashiga
tasa meta a zaune tana jan cazbi , durk'usawa Aysha tayi sannan tace " barka da wannan
lokacin Gogal ya jikin naki ? ba yabo ba fallasa Gogal tace jiki da sauk'i , Aysha tace "Allah
yak'ara miki lafiya da nisan kwana me amfani , Gogal bata amsa da Ameen d'in data saba ba
tayi shuru , Aysha takuma risinawa tace " ga Abinci can a kan Dinning nadafa miki ni zan wuce
makaranta , Gogal batare da ta dube ta ba tace " Allah ya kiyaye Aysha ta mik'e ta fita......
Koda ta fito sai da tagama dube duben ta bataga kowa ba sannan ta kama hanyar fita
bakin titi , wayar ta ta ciro tashiga kiran number Leeemah , tana d'agawa tace mata gatanan
tana shirin fitowa itama , nan Aysha ta kashe wayar sanan ta kira number Khalid , yana d'agawa
yace " Sweet yau kwata kwata kin ki bari naji muryarki dayawa , muna fara waya kike katsewa
kodai nayi laifine ? murmushi Aysha tayi sannan tace " babu laifin dakayi yau nayi busy ne sosai
, to Babyna ina fatan baki gaji da yawa ba dan kinsan yau zan danneki dayawa , Aysha wani
takaici taji ya kamata amman sai ta dake tace " bangaji ba My Baby kasan akan ka zan jure
komai , Khalid cike da murna yace " dama zakiyiwa Uncle d'inki dabara da munkwana tare
mufaran ta ran juna sosai , Aysha tace " karka damu zan gwada nagani ko zai barni , Khalid
har wani shauk'i yake yana ce mata shifa tun yanzu zai shirya dan ya matsu da yawa , itama
tace masa yanzu zata shirya taje takama musu d'akin tunda ya turo mata kud'in , nan sukayi
sallama Aysha tana duban wayar tana murmushin mugunta.....
Ruma wajen k'arfe uku ta d'auki wayar ta tana shiga Whaspp , sak'onni ne suka shiga
shigowa cikin wayar a ciki ta kuma ganin number da aka turo mata pic d'in Khalid , hannun ta
har rawa yake wajen bud'e sak'on taga me suka sake turo mata , tana bud'ewa taga Voice
guda uku ajere , tuni ta bud'e bayan ta karanta rubutun k'asa , Muryar Khalid tashiga ji yana bai
yana yadda yake shirya komai , jikin ta har tsuma yake tanajin wata iriyar tsanar Khalid , bayan
duk tagama ji ta mik'e da saurin ta ta nufi d'akin Mumyn ta , tana zuwa ta kunna mata Voice d'in
Muryar Khalid itama tashiga ji , bayan tagama ji ta kamo mata hotunan da aka turk mata tare
da sheda mata ance k'arfe Biyar taje Hotel d'in Taheer taganewa idon ta komai , nan Mumyn ta
tashiga salati tare da cewa bari takira Daddy ta sanar masa dan suma suje Hotel d'in dan
tabbatar wa , aikuwa koda suka sanar masa cewa yayi sutaho Hotel d'in su had'u acan dan
shima dama yagaji da abinda Khalid d'in keyi masa na rashin zuwa kasuwa , ashe ashe akwai
abinda ya taka shiyasa yake haka , .....
Tuni Ruma da Leeemah sun Bayyana a Hotel d'in Taheer , tana gama kama d'aki ta nemi
Number Ruma ta tura mata Room number d'akin , ciki suka shiga nan ta tsarawa Leeemah
komai yadda zata tafiyar dashi , basu dad'e da zuwa ba saiga Khalid ya iso sai faman zabga
k'amshi yake , akan idanun Ruma da iyayen ta ya fito daga motar batare da yagan suba ya nufi
Reception.........
*kumin Comment kuga ruwan Typing*✍
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 27
Washe gari tunda safe Aysha take shirya yadda Khalid zai shiga hannu , tunowa
tayi da jiya yace mata 2m .A account d'in sa kuma sunje shopping ta cinye masa 1m da dubu
d'ari uku , ya siya mata gold sark'a da kuma zobuna , yanzu in ta auna cikin Account d'in
Khalid saura dubu d'ari Bakwai , dole yanzu zata shirya cinye sauran canjin daya rage masa ,
dan bataso ko canji ta bar masa bare yaji dad'in cutar wasu agaba , tanaso ta maida shi talakan
k'arfi da yaji tunda dama motar dayake hawa ta gidan su Ruman ce Yake d'auka , wata dabara
ce ta fad'o mata da sauri ta d'auki waya zata kira Khalid , wata Number tagani ana kiranta da ita
, da kamar bazata d'aga ba sai kuma wata zuciyar tace d'aga kiji ko waye , d'agawa tayi tare da
yin shiru batayi magana ba , daga cikin wayar taji muryar Hameed yana fad'in Assalamu
Alaikum , muryar tasa tuni ta ratsa duk wani sassa na jikin ta , idanuwan ta ta lumshe sannan
tace " wa'alaikas salam , Hameed wata ajiyar zuciya yaja dan duk a tunaninsa baza ta d'aga
wayarsa ba amman sai gashi ta d'aga , My Angel dafatan kin tashi lafiya kuma ina fatan dai ba
bacci kike na tashe ki ba ? Murmushi Aysha tayi karo na farko a rayuwar ta dataji 'Da namiji ya
burgeta , kuma wannan shine karo na farko da aka tab'a kiran ta tare da tambayar ta tashi lafiya
, duk Namijin da zai kira ta sai dai yace mata A inah zasu had'u ko kuma yana Hotel kaza tazo
tasa mesa , baruwan su da tambayar lafiyar ta su dai kawai burunsu tazo su aikata Fasik'an ci
, karo na biyu dataji ta tsani zina dan bata da wata riba sai dai k'arshe ma ka had'u da tarin
dana sani , a hankali ta furta masa " natashi lafiya kaima ina fatan hakan daga gareka ,
Murmushi Hameed yayi har Aysha najiyo sautin yace " lafiya lau nima natashi sai dai zuciya ta
datake d'auke da farga da tarin k'alubale , Aysha ta d'an fito da ido a tsorace tamkar yana
gaban ta tace " wanne irin Fargaba da k'alu bale kuma ? murmushi yayi sannan yace " Zuciya
ta tana jiran amsar da zata samu daga gareki kinga kuwa dole na kasance cikin fargaba ,
Murmushi tayi sannan tace " kar kadamu komai zai zo da sauki kawai dai kajira lokacin yayi ,
Hameed yace " lokaci ya kusa tunda zuwa anjima zanji komai dan haka yau kisa aranki kina da
mara lafiya mai buk'atar tallafin ki , murmushi ta kuma yi tace " sai najika ta kashe wayar
batare da tajira yace mata wani abun ba , kallon wayar tayi tamkar me gano Hameed d'in aciki
tace " in na biye masa sai yaja zancen da hira har nazo na furta abinda zuciya ta bata yanke ba
, .......
Number Khalid ta nemo sannan ta shiga kiran sa , sai dai har ta katse bai d'auka ba ko
baya kusa da wayar ko kuma yana bacci , ajiye wayar tayi sannan tafito palor dan ganin ko
Gogal ta fito , bata gan ta ba hakan yasa ta shiga kitchen ta hau girka musu abinda zasuyi kari
dashi , Kunun gyad'a ta dama tare da soya musu dankalin turawa , tana gamawa ta d'auko ta
ajiye akan dinning sanna ta d'auki na Habu ta mik'a masa , koda ta shigo cikin d'akin ta ta koma
sannan ta fad'a wanka toilet , tana fito tasaka wasu riga da wando pakistan , rigar takawo mata
har gwiwa wandon kuma daga k'asa n sa ya d'an tsuke amman kayan sosai sunyi mata kyau ,
wani hijab d'an k'arami iya kafad'a ta d'auka ta zura tare da fito wajen Dinning , Ganin Gogal
tayi a zaune itama tana shan Kunun gyadar , tana zuwa ta gaida ta sannan tace " ai tund'azu na
fito naga baki fito ba , Gogal tace " natashi ne jikin nawa babu dad'i shiyasa , amman yanzu naji
sauk'i tunda gashi nafito ina karyawa , Aysha tace " kwana biyu ma ai bakizo munje ganin likita
ba , bari mugama karyawa yanzu sai muje kiga likita dan ciwo tun yana k'arami ake tarar sa ,
Gogal batayi musu ba dan tanason ganin likitan itama , Bayan sun kammala Gogal ta mik'e
zatayi wanka ta shirya su tafi , Aysha kuma ta shigs d'akin ta ta kuma gyara jikin ta tare da feso
turare sannan ta fito , zama tayi a palor jiran fitowar Gogal......
wayar ta ce ta shiga Ring ta d'auka dan ganin waye me kiran nata , Khalid tagani tayi
murmushin mugunta tare da d'agawa cike da kissa , Hy Babyna kankana uwar ruwa kinsan
har mafarkin ki nayi wallahi jiyan nan kin bani dad'i , kusan sumar dani kikai fa gaskiya ina
kwad'ayin ki yauma ki daure muhad'u , Aysha tayi wani murmushin mugunta sannan tace " kar
ka damu ai ni takace kuma kaima nawa ne komai kakeso zanyi maka , in ban faranta ranka ba
ran wazan faran ta My Dear ,, wani dad'ine ya kama Khalid tare da wani shauk'i , tabbas bazai
yi gangancin rabuwa da Aysha ba saboda ta ko'ina tagama had'uwa , katse masa tunani tayi
dacewa Babyna inason kamin wata alfarma dan nasan nafi k'arfin komai agurinka , Khalid
yace " inajinki Babyna fad'i kome kikeso indai ina dashi to zanbaki , Aysha tace " Wata Auntyna
ce tayi order kaya shine aka rik'e mata , yanzu haka sunce mata indai zasu sakar mata kaya to
dole sai ta turo musu da kud'i dubu d'ari shida da Hamsin , kuma kwata kwata kud'add'en
hannun ta basu kai hakan ba , shine tamin magana akan in nemo mata dan Allah zuwa lokacin
da zasu sakar mata kayan nata , Kayan 10M. tayi order da zarar ansakar mata kayan zata baka
kud'in , Khalid yayi d'an dum sannan yace " Babyna kinsan kwata kwata kud'in Account d'ina
yanzu saura dubu d'ari Bakwai , dama jiya na fad'a miki ko nawa ne aciki kuma kinga kinyi
siyayya a ciki , amman bakomai ai nima Auntyna kuma banaso ace Babyna tana damuwa ,
dan nasan indai ban baki ba wani zaki ce saki tambaya nikuma ina kishin hakan , nan Aysha
tashiga yiwa Khalid godiya tare da masa dad'in baki , tuni ya shagalce yaji ko 20M. Ta tambaya
zai bata tunda ta wuce haka a gunsa , dan shi yagama tsaida magana ita zai aura tunda ga
yadda ta sarrafashi jiya ta gama dashi , yayi sex da mata da yawa amman ba wacce ta iya
sarrafashi tamkar Aysha , gata Allah yayi mata baiwar ni'imah tamkar k'orama , a kasalan ce
yace " Babyna ki turomim account d'in da zan sa kud'in , Aysha ta amsa masa da zata turo
sannan tace " kawai ka turomin dubu d'ari Bakwai d'in sai in ciri dubu Hamsin d'in naje nakama
mana Hotel anjima , aikuwa ba musu Khalid na rawar jiki ya turawa Aysha duka dubu d'ari
bakwai d'in , koda Aysha taji kud'in sun shigo tayi wani murmushi sannan tace " taka ta k'are
Khalid sai wani kokacin , Aysha bazaka sake ganin koda tafukan hannun ta ba bare yakai ka da
ganin jikin ta , tasan yanzu bashi da ko ficika a account kuma yau zai zama tarihi a gidan su
Ruma , ....
Gogal ce ta fito suka fice harabar gidan , motar Aysha tashiga tare da bud'ewa Gogal ,
Gogal da k'yar ta yadda ta shiga saboda cewa tayi Aysha bata iya motar ba zataje ta yar da ita ,
Habu yana dariya yace " aikuwa ta iya sosai Gogal kishiga kawai Allah ya tsare sai kun dawo ,
Da Ameen Gogal ta amsa tana shiga sannan tace " kijanina hankali nidai , .........
Sorry kuyi hakuri
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
_NA_
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 30
Yana shiga ya kira number Aysha , tana d'agawa ya tambaye ta Room number
d'akin datake , nan ta fad'a masa ya kashe wayar ya nufi d'akin....
Tuni Aysha tashiga toilet yayin da Leeemah ita kuma ta haye gado tana lulleb'e jikin ta da
bargo , Khalid yana zuwa ya tura k'ofah dan ta sheda masa k'ofah a bud'e take kawai yashigo ,
koda ya shiga ganin Aysha akan gado kawai yafara cewa " wato Babyna har kingama shiryawa
ni kike jira ko ? da k'yar Leemah ta 'iya kwai kwayon muryar Aysha tace " haba Dear kawai
kataho nima a duk na zak'u kai kawai nake jira , dayake kanta na cikin bargo shiyasa baidamu
da canjin dayaji muryar ta tayi ba , tuni yahau cire kayan jikin tare da fad'in "Babyna ko tayin
cire kaya babu kin wani shige bargo , hayewa gadon shima yayi tare da shigewa cikin bargon
, dai dai lokacin su Ruma da iyayen ta suka banko k'ofar cikin d'akin , dayake ya manta bai rufo
shiyasa suka sameta a bud'e , shima kuma adai dai lokacin yaga fuskar Leeemah yabud'e
bargon cikin furgici , aikuwa idanun suka had'a da Alhaji Ashir da Mumyn Ruma da ita kanta
Ruman , da sauri Khalid ya rintsa idanu yana jiran yaga wai ko mafarki yake , sai dai jin Muryar
Alhaji Ashir ya tabbatar masa da ba mafarki yake ba idanun sa biyu , Alhaji Ashir yace "
Nagode wa Allah daya nunamin halinka tunkafin na had'a zuria dakai , duk cin amanar da kake
shirin yimin kuma naji komai , azzalumi macuci duk kud'adena dakasan ka d'iba kadawo min
dasu , nabaka nan da awa 24 in bahaka ba zansa a kullemin kai , samnan Mota ta dakake
yawo kana dibar matan bariki kuna yawon banza kabani mukullin abata na wuce da ita , Ruma
ta kallesa da mugun kallo tace " Mayaudari Munafiki Allah ya tsareni daga tarkon ka ta sanadin
Karuwar ka , ta kalli Leeemah tace " nagode miki da yadda kika farkar dani daga baccin
danake , kika cireni daga duhu zuwa haske kika rabani da auran Fasiki Macuci , ina miki fatan
shiriya daga wannan rayuwar da kika saka kanki kema , tana kaiwa nan ta fice daga