YAR HANNU BOOK COMPLETE NA ZEE MD.pdf

Author :  Zee MD Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   17 / 21

48K to 51K   out of 62.7K words

me zata ce mata wacce k'aryar zata
kuma yi mata a karo na biyu.....

Aysha tana shiga cikin soron gidan tafara sallama a hankali , muryar ta har rawa take
tana k'ara yin sallamar , jin ba'a amsa mata ba yasa tashiga tsakar gidan da duhu yafara
mamayewa , haka ta nufi cikin d'akin Gogal d'in wanda ta taga shi kad'aine a bud'e , nan ma
sallama tayi tana me raba idanuwa dan ta hango inda Gogal d'in take , da k'yar ta hangota a
kan sallaya tayi jigum tamkar wacce ma bata motsi , cikin sanyi murya Aysha ta furta
Subhanallah , daga bakin k'ofah ta tsaya tare da zubewa kan gwuiwowin ta tana sharar
Hawaye , Sunfi Minty 5 a haka kafin Gogal tafara magana " Aysha meyasa kika zab'i wannan
bak'ar rayuwar ? Meyasa kika canza halayyarki da nasanki tun asali da ita ? Aysha kin cuceni
da kika maida rayuwar ki a banza , kin zab'i siyar da mutuncin ki akan son kud'i da kuma kyale
k'yalen duniya , kin ci Amanata a matsayina na wacce nazamar miki uwa da uba , duk da ina
da laifi nayin sakaci har kika zama cikakkiyar *'Yar Hannu* , nakasa saka idanuwa akanki
nakasa bibiyar yadda kike mu'amala da kud'i , nabi son zuciya na dunga d'ora miki wasu
nauyikan namu , bandamu da irin kud'in da kike samu ba bandamu da irin yadda kike siyo
mana kayan Abinci ba , duk da kin yi min k'aryar cewa koyarwa kike a Makaran ta ake biyanki ,
amman ban bibiya na tabbatar da gaskiya ne ko kuma ba gaskiya ba , hawayen dake zuba a
fuskar ta ta goge kuma dai dai lokacin 'yan nefa suka kawo wuta , Aysha idanun ta akan Gogal
itama sai zubda hawaye take tanajin wata iriyar nadama na shigar ta , tabbas tayi nadama da
irin rayuwar da ta jefa kanta a ciki , kawai shashshekar kukan su ce ke tashi a cikin d'akin ,
Gogal ta dube ta tace inaso a karo na biyu kifad'amin gaskiyar abinda yasa kika zab'i irin
wannan rayuwar , kuma wallahi in har kika kuma yimin k'arya wlh bazan yafe miki ba , nan
Aysha tasa kuka tare da duban Gogal tace " zanfad'a miki wallahi amman dan Allah karki
tsaneni kuma karki koreni wlh bazan iya rayuwa ba mutuk'ar bana tare dake , runtse ido Gogal
tayi cike da tsawa tace " kifad'amin inajinki ,.......

Aysha tuni tashiga bawa Gogal labarin yadda akayi tafara bin maza , tunda ga kan
Fyad'en da Khalid yayi mata da kuma cikin da yashiga har ta zubar dashi da yadda Farouq yayi
mata shima , duk irin mazan da ta kula da kuma irin yadda take yi inzataje gun su bata b'oyewa
Gogal ba sai data gaya mata , .....
Gogal tuni tayi mutuwar zaune dan take tafara nuna Aysha da d'an yatsa tana k'ok'arin yin
magana , wani tarine ya turnik'e ta ta dafe k'irjin ta sannan ta daina motsi , da gudu Aysha ta
nufeta tana k'wallah k'ara " dan Allah Gogal ki yafemin wallahi natuba nadaina komai ,
rumgumo Gogal tayi ajikin ta wacce taji kamar bata motsi , da gudu ta ajiyeta ta fito tana neman
ruwa ta yayyafa mata , dayake a rud'e take kawai waje ta nufa tana kuka tare da neman
taimako , dai dai nan Hameed ya iso a motar sa yana ganin Aysha ta fito ko mayafi yasan ba
lafiya ba , ko tsayawa baiyi kashe motar ba ya fito da gudu ya nufota yana cewa " lafiya Aysha
meyafaru ? da sauri ta rik'o hannun sa tana fad'in " kataimaka min dan Allah kar Gogal ta Mutu

bazan iya zama a duniya ba indai babu ita , haka suka shiga cikin gidan a rud'e dan shima
ganin ta haka ba k'aramar rud'ewa yayi ba , ...

Koda yaga Gogal a shimfid'e tuni ya sab'eta a kafad'a yana cewa Aysha zo muje asibiti ,
tuni suka fito ta janyo hijab d'in ta suka fito tare , karo sukaci da Habu shima ya rufa musu baya
akasa Gogal a motar Hameed suka nufi Asibiti.......
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
🤒🤒


_NA_
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




*Alhamdulillah !*
*Alhamdulillah !!*
*Alhamdulillah !!!*



_Page._ 35


Jikin Gogal itama sanyi yayi tare da jin tausayin Aysha , ba komai ne yayi tasiri a
zuciyar Gogal ba yasa har tayi nadama sai Sakacin datake gani tayi akan kula da Ayshar ,
itakuma Aysha ba komai ne ya janyo mata haka ba face Rashin yadda da kaddara , da tunfarko
ta yi hak'uri da Abinda Khalid yayi mata da bata zama haka ba , duk da bayan Khalid ya yi mata
hakan kuma taso wannan yazama farko yazama k'arshe amman sai ga Farouq ya billo mata

shima , a haka zuciyar ta tashiga zugata akan cewar duk Namiji inyazo gunta to tabbas ba
soyayyar Allah yake mata ba sai dan surar jikin ta , tunda ganan tashiga bin zuciyar ta meyi
mata wannan hud'ubar , Allah yarabamu da sharrin Zuciya Ameen......

Gari nayi haske saiga Habu da kaya a hannun sa ya shigo d'akin d'auke da sallama ,
samun Gogal da yayi a zaune ba k'aramin dad'i yaji ba , dan yanajin tamkar Mahaifiyar sa
saboda gatan da ta nuna masa , nan suka gaisa tare da yi mata fatan samun lafiya me d'orewa
, ....
Kunu ya taho mata dashi tare da k'osai sai kuma kayan sawa kala biyu , sosai Gogal taji
dad'in ganin kunun tayi masa godiya tare da sanya masa albarka , Aysha tayi murmushi tace "
shine ni baka tahomin da waina me k'uli ba kawai ta Kakar ka kake ko ? inda sabo Aysha da
Habu sun saba tsokanar juna shiyasa Gogal tayi murmushi kawai batare da tace komai ba......
Dr. Hameed ne ya shigo cikin d'akin d'auke da sallama , amsawa Habu yayi tare da yi
masa sannu da shigowa , ganin yadda Aysha ke zaune tana bawa Gogal kunu tana sha cike da
kulawa , wani dad'i Hameed yaji ya ratsa shi dan da alama Gogal tadaina fushi da Ayshar , cike
da girma mawa yagaida Gogal tare da tambayar jikin ta , amsawa tayi cike da sakin fuska
sannan tashiga masa godiyar kulawar da yake bata , Hameed murmushi yayi yana satar kallon
Aysha wacce ta kauda kanta gefe tamkar bata gansa ba ......

Gogal ce tace " Sayyada baki gaida Dr ta ba kiyi masa godiya yana da mutunci , Aysha ta
jiyo ta gaida Hameed amsawa yayi shima yana me d'aure fuska tamkar bashi ba , Aysha bata
damu ba dan tasan dama dole Hameed zai tsaneta dan irin rayuwar datayi , Habu ne ya mik'e
tare da cewa bari yaje yadawo ..... Yana fita Hameed yace " Mama inaso dan Allah kidaina saka damuwa aranki , zuciyar ki
zata iya samun matsala a zo ana wani zancen ba wannan ba , Gogal tace " insha Allah zan
kiyaye daga yau nadaina saka komai arai , Cikin zuciyar Gogal kuwa tace " bazan daina
damuwa ba mutuk'ar ba Aysha tayi aure ba , amman indai tana gaba na to zan kasan ce cikin
damuwa , a fili kuma tashiga cewa Hameed " yau zaku bani sallama ko ? Hameed yayi
murmushi sannan yace " kibari sai nan da kwana biyu jikin naki ya kumayin kyau , Gogal tace "
banason zaman asibiti indai ba dole ba kuma jaga ai jikina yayi sauk'i sosai , Hameed yace
k'a'idar asibitin sa baya sallama akwana d'aya , dan haka tayi hak'uri zuwa gobe , badan taso
ba tace shikenan da yau da goben duk d'ayane , Aysha ita kanta so take a sallamesu dan
kawai ji tayi batason zama a inda Hameed d'in yake , wata kunyar sa takeji tare da nauyin sa
sannan yadda yake had'e mata rai sai take ganin tamkar tsanar ta yayi , ......

Wata Nurse ce tayi sallama cikin d'akin d'auke da Basket food a hannu , rissinawa tayi
tagaida Gogal tare da mik'awa Habeeb kwandon tace " gashi inji direban gidan ku yace abaka ,
ansa yayi batare da yace mata komai ba ita kuma ta fice....
Hameed ya dubi Aysha yace " ungo wannan ki d'ibar muku kuci sannan ki zubomin nawa ki
kawomin office , yana fad'in haka ya mik'e ya fita tare da cewa Gogal anjima zaidawo suyi
hira.....

Aysha bata tab'a kayan Abincin ba ta share tamkar bataji abinda yace mata ba kafin ya fita
, itama Gogal ba yunwa takeji ba sai dai kawai saboda Dr d'in , duban Aysha tayi tace " kiziba
masa abincin ki kai masa mana , Aysha ba musu tashiga bud'e kulolin Abincin , farfesun kaji ne
sai kuma farfesun kayan ciki daban , sai Shinkafa da miyar ganye wacce taji kifi wadatacce ,
sai kuma kunun gyada a cikin wani karamin flast , d'aukar filet tayi sannan ta dubi Gogal tace "
nifah bansan wanda zan zuba masa ba , Gogal tace "kawai ki d'auki kwandon Abincin kije
office d'in nasa sai kitambaye shi abinda yakeso aciki , Aysha badan taso ba ta mik'e ta d'auki
kwandon tafita ta nufi office d'in Hameed......

Tana shiga tayi sallama a hankali ta tsaya , Hameed yaji sallamar amman sai yayi kamar
baiji ba , ta dad'e a tsaye kafin yace " waye a tsaye ne in bazai shigoba ya koma , Aysha ta
shiga ciki sannan ta ajiye kwandon kayan abincin tashiga bud'ewa , bayan tagama bud'ewa
tace " mezan zuba maka daga ciki ? duban Abincin yayi sannan yace ki zubamin kunun gyad'a
sai ki zubamin farfesun kayan ciki , hakan tayi masa ta ajiye sannan ta juya zafa fita , Aysha
ya kira sunan ta cak ta tsaya zonan , a hankali ta tako tazo gurin dayake ta tsaya batare da
tace uffan ba , Hameed yace " meyafaru da Mama ta tashi taganki ? shuru Aysha tayi kamar
bazatayi magana ba sai kuma tashiga fad'a masa duk yadda sukayi da Gogal , Hameed ya saki
ajiyar zuciya sannan yace " ki godewa Allah da kika samu batayi dogon fushi dake ba , kuma
Allah yasa kinyi tuban gaske bazaki k'ara komawa ruwa ba , Aysha sosai taji rashin dad'i akan
kalmar sa na cewa wai Allah yasa tayi tuban gaske , Ameen tace masa ta juya tabar office d'in
nasa da sauri......


Haka suka yini a asibiti wannan abincin da aka kawo daga gidan su Hameed shi sukaci
har Habu ,.....

Hameed gida ya koma sai bayan Magriba yadawo asibitin , da kayan abinci yataho musu
sosai Gogal take godiya dan irin kulawar da yake basu har tayi yawa , wannan karon tun da
yashigo Aysha ta tsiri lazimi dan batason magana ta had'asu , tanajin sa shida Gogal sai hira
suke tamkar sun dad'e da sanin juna , nan take masa godiya akan nauyin ta da ya d'auka a
asibitin batare da an anshi ficikar suba , murmushi Hameed yayi sannan yace " Mama ai
asibitina ne kuma kinga ke Mama tace taya d'a dan yayi hidima da Mahaifiyar sa ace kuma sai
ta biya , Hawaye ne suka shiga zubowa a kuncin Gogal nan tashiga sama sa Albarka .......

*Bayan kwana biyu*

Tuni an sallami su sundawo gida , sosai Aysha take kulawa da Gogal tare da gujewa duk
wani b'acin ranta , Anan Aysha ta yanke maidawa da Alhaji Na Lamma mukullin gidan sa da
kuma motar sa , Gogal sosai tayi na'am da maganar Ayshar , ranar wata laraba da safe ta
shirya ita da Habu suka hau motar tare da tafiya da mukullin gidan dan maidawa Alhaji Na
Lamma , sai da suka fara zuwa gidan duk wasu kaya datasan natane a cikin gidan ta kwashe
ta fito dasu , Bayan ta gama kwashewa gida ta dawo dasu ta ajiye sannan suka nufi gidan Alhaji

Na Lamma.....

Gidan sa ba b'oyayye bane shiyasa basu sha wuya ba suka gano , suna zuwa Megadi ya
lek'o ya tambaye su su waye kuma wajen wa sukazo ? nan Aysha tace masa wajen Alhaji
sukazo suna son ganin sa , nan Megadi yace musu " Alhaji bashi da lafiya bazai iya fitowa ba
amman bari yayiwa yaron sa magana , nan yashiga cikin gida yayiwa Farouq magana akan
suna da bak'i , Farouq yace masa ya shigo dasu kawai , koda Aysha suka shigo Farouq yana
ganin ta ya mik'e dan mamakine ya kamasa , cikin zuciyar sa yake tambayar me Aysha tazo yi
gidan su kuma yanzu ? Aysha ta gaida Hajiyar Farouq sannan tace mata " dan Allah ko zan iya
ganin me gidan ? Hajiya tace " wacece ke baiwar Allah da kikeson ganin sa , Farouq yayi saurin
cewa " zaki iya ganin sa Aysha muje in muna miki d'akin sa , Aysha tabi bayan Farouq itama
Hajiyar mik'ewa tayi tabi bayan su....

Alhaji yana kwance gefen jikin sa baya motsi , sai dai fess jikin sa da alamar ana bashi
kulawa sosai , Suna zuwa Ya kafe Aysha da idanuwa bakin sa kuma yayi nauyi dan baya iya
magana sosai , take Aysha tasake jin tsoron duniya da dukkan abinda ke cikinta , tabbas me rai
baigama ganin halittar sa ba mutuk'ar ba mutuwa yayi ba , nan tashiga neman yafiyar Alhajin
akan barazanar da tayi masa san kawai ta mallaki gidan sa , ta kuma bashi mukullin gidan nasa
tare da na motar Farouq , kuma ta sheda musu tuntuni ta goge komai dayake wayar ta na
Abinda ta d'auka , Alhaji Na Lamma shima rok'on ta yayi tayafe masa duk da batajin wani abun
dayake fad'a , Farouq dama tuni ya tuba ya canza hali yanzu duk yadaina yawace yawacen
banza ya koma kula da dukiyar Mahaifin nasa , nan Shima Farouq yakuma rok'on yafiyar
Aysha sannan ta fito tabar musu gidan , Alhaji Na Lamma ya yagawa Farouq ya maidawa
Aysha komai ya bar mata halak malak , ......


Hameed yazo yayiwa Gogal sallama akan zai koma England sai nan da shekara zai
dawo , Gogal tanuna rashin jin dad'i na tafiyar sa , dan zuwa yanzu sosai sun shak'u da
Hameed kuma sosai yake bata kulawa , haka tayi masa fatan Alkairi tare da addu'ar kariya
daga sharrin duk kan abin k'i , Hameed sai dube dube yake kozaiga Aysha amman bai ganta
ba , gashi yakasa tambayar Gogal inda Ayshar taje , haka ya ajiyewa Gogal kud'i me yawa
sannan ya mik'e yana mata sallama , har k'ofar soro ta rakosa tana masa fatan ya sauka lafiya
, yana k'arasowa jikin motar sa ya fito da kayayyakin abinci da yasiya musu akaita shigar musu
dashi , yana shiga cikin motar zai tashe ta ya hango Aysha da Habu sun sauka a Napep , har
sukazo suka gitfa ta gaban sa bai tafi ba sai dayaga shigar su cikin gida ,.......

Koda Aysha tashiga gida da wannan kayan suka fara karo , daman tunda taga motar tasan
Hameed ne yazo amman ko kallon wajen da motar take batayi ba , duk wannan abun tanayine
dan ta nisan ta kanta da Hameed , tasan koda wasa ba aurar ta zaiyi ba tunda ta fad'a masa
asalin wace ce ita....

*Bayan kwana biyu*

Ruma sunyi waya da Aysha ta sheda mata sun tashi , nan tazo gidan da suka dawo kuma anan
Ruma take bawa Aysha labarin rabuwar

17 / 21