Chapter 2 Reading ZARRAH BOOK COMPLETE ROMANTIC BY OUM HAIRAN.txt Arewa Novels

ZARRAH BOOK COMPLETE ROMANTIC BY OUM HAIRAN.txt

Author :  Fauziyya Tasi'u Umar Category :  Home Of Novels

Chapter   2 / 18

3K to 6K   out of 52.6K words

akan cewa principal tace kada su fita da daidai su bari su tashi gabadaya,




Neman guri sukayi suka zauna kawai Jidda taga qawar tata na kuka Asma'u babu juriyar yunwa ko kadan tasan dalilin kukan don haka ta miqe da sauri ta nufi shagon me gadi ta siyo musu biscuits pure blues dan saba'in ta siyo musu lemo jarka daya sukaci Saida sukaji dama dama asmai ta dubeta tace “dama kinada kudi shine kikaqi ki siya Mana break?" Harararta Jiddah tayi tace “wanne kudi ke gareni kudin motarmu ne naga zaki mushe na taimaka na siyo Mana muka taba Kinga malama an gama fitowa kawai miqe mu yanki burtali"




Takaici ne ya hana Asma'u magana saboda tana cika magana zuciyarta fadowa zatayi haka suka rinqa dabawa a qafa gashi da nisa tsakanin unguwarsu da makarantar sosai suna tafe Jiddah nayi Mata hirar tura haushi taqi kulata sunzo daidai wani guri da ruwa yake taruwa kawai basuyi aune ba sukaji ruwan dagwalon kwata ya fallatso musu ya bata musu jiki musamman Asma'u da ruwan yafi batawa ta sunkuyar dakai ta kalli kanta tun daga sama har qasa ta dago kanta ta sauke akan motar da aka tayar ana Shirin tafiya zuciyarta na azalzala taga me motar yaja zai qara gaba ai batayi wata wata ba ta dauki wani dutse qato dake gefensu ta jefi motar akwaita da mahaukacin saiti kuwa ji kake taratsatsa glass din bayan 4matic din ya tarwatse hakan yasa me motar cin uban birki a fusace na kujerar me zaman banza ne ya fara fitowa daidai lkcn data nufo gurin itama tana fadin “ba iyanan naso ya tsaya ba sonayi ya ishe kan daqiqin dakejan motar yayi masa Ramin da jini zai hade da qwaqwalwar shege muga ta gadara da dagawa...." Sauke tafin hannunta tayi a fuskarta jin shu'umin Marin da aka dauketa dashi ta Jima dafe da kuncinta kafin tayi qarfin halin dagowa tana tuna Marin da Aseem Shaheed yayi Mata jiya kwatankwacin azabar da taji kenan aikuwa tabbas saita rama wannan koma uban waye ya daga hannu ya Mari fuskarta me daraja,
Idanunta ta rintse ta dage ta daukeshi da Marin da shima Saida ya dafe gurin kafin ya dago ta sake sauke Masa wani ta daga hannu zatayi na uku Wanda ya fara fitowar ya riqe hannunta da sauri jikinta na bari ta bude idonta daidai lkcn da Dr Aseem ya bude nasa shima tar a kanta lebensa datse da haqoransa ya saita injin idonsa akanta tare da sanya hannunsa ya zame hannun Zahran daga nata ya riqe na yan sakonni sannan ya saki Yana qara kallonta itama shi take kallo cike da mamaki da Kuma tsana.




Kafin yayi mgn tayi da cewa “au dama Kaine shaidanin daya batamin uniform dina lusari kawai kagani dai kaga irin aikina dama Saida na fada maka zamu sake haduwa gashi kuwa mun hadu ko banza zuciyata ta dan sauka daga radadin
Daka Bata sauna kawai ka dauka ana tabani aci bulus ne jiya kaci mutumcin mahaifiyata da tafi taka uwar don alamu sun nuna kaikam taka jefar dakai tayi wata me tsautsayin ta tsinta. Sannan yauma ka batani da ruwan kwata Kuma kayi tunanin wuccewa salin alin haba yaro kayi kadan ka taba ma'un Sadiqu ma'un Inna ka zauna lfy gashinan kayi ta glass din motarka Kuma dole aje akaiwa me gyara yaci kudi nidai nasan ko kaina ka siyar bazai gyara maka ba......
Tana maganar tana qasa qasa da hannunta ta sake daukan wani dutsen me nauyi tayi kamar zata wucce kawai ta sakar masa a babban yatsansa yakuwa yi qasa da sauri tare da sakin wata siririyar qara kafin Zahran ya Ankara ma'u takai a dari da sittin ba Zahran ba hatta Aseem da jini yake ambaliya a qafarsa Saida ya dago ya dubeta lkcn da take cewa su Corona virus aje ayi treating kafin mu sake haduwa na daujeta Wawa da kace bakaji.........




Vote
Comments
Share




*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*


_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*



_Bismillahir Rahamanur Rahim_



_Page 1-2_





*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*_Telegram Link_*
            👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7






____________________________
____________________________



_Farkon labari_

_1/3/2007_


Harabar gdan attajirin cike yake da mabarata maza da Mata yara da manya kowannensu yayi jungum jumgum Yana tsumayin fitowar Alhaji Qasim Wanda ya kasance shine mamallakin gdan Wanda ya kasance baya goya marayu jarumi Kuma adali me taimako da taimakon Allah da'ira da'ira almajiran sukayi kowa yana tattaunawa da abokin shawararsa inda a can nesa kadan da mutanen na hangi wata dattijuwar makauniya da wata yar kyakkyawar budurwa da shekarunta bazasu haura 17 ba sanye take da hijjab ruwan qasa Wanda dadewa da kodewa tasashi dole ya koma toka toka rigarta da zaninta ma gambal habaru ne ma'ana wari da wari tanada matsakaicin tsayi duk da kasancewarta a jigace Kuma a wahalce kallo daya zakayi Mata kasan alamu sun nuna tana tsananin ji da wannan mahaifiya tata fiye da tunanin Mai tunani.
Ba fara bace kallon farko zakace Mata baqa saboda dauda da rashin samun nutsuwar kula da Kai saidai idan ka qura Mata ido zaka gano cewa ba baqar bace kamar yanda idanu ya nuna a farko saboda roɗi roɗin hasken da zakake hangowa ta wasu bangarori na jikinta, tana da fasali da diri na bam mamaki Wanda a qananun shekarunta zakayi al'ajabin qirar da ilahi qadiran ala mayyasha'u yayi Mata so dake lamarin Allah yafi gaban misali da mamaki dole ka aje tunaninka ka Kama abinda ke gabanka.




“Asma'u! Asma'u!! key Asma'u!!! Tunanin me kikeyi ne dalla malama tun dazu Alh sai miqa Miki kudi yakeyi...." Abinda ya dawo da ita hayyacinta kenan ta durqusa har qasa ta karba ta bude baki cikin siririyar muryarta tace “mun gode baya goya marayu Allah ya tsare gabanka da bayanka ya hana maqiyanka ganinka sai bayan ka wucce Allah ya tare maka zafin hassadar maqiya da mahassada ta koma kansu....." hakanan ta rinqa jero addu'ar kamar yanda takanji Ummah tanayiwa duk wanda yayi musu ihsani.
Dadin addu'ar da Alh Qasim yaji tasashi qara zarar naira dubu goma ya sake miqa Mata kawai saita fashe da kuka bayan ta karba tayi masa godiya da fatan alkhairi, ya wucce ita Kuma ta dugungune kudaden ta tura a bra dinta ta Kama hannun Ummah tace “Ummah yau Allah ya dubemu ya amsa addu'ar ki ta jiya ya kawo Mana dauki dama tunda muka fito nake tunanin idan bamu samu sadakar Nan ba yau Ina muka Kama bamuda abinda zamuci ko na garin kwakin yau babu gashi gobe ance kar naje makaranta idan ban kawo kudin tearm ba, nikam Ummah badon kince na daina roqonki ba da sai nace kiyi hqr ki mayar dani makarantar gwabnati tunda na samu horon farko a ta kudin Ummah kudin sunyi yawa 14 thausand per team gashi babu mataimaki a gareki sai Allah da bayinsa zababbu...."
Lalubo bakin yar tata tayi tace “Asma'u komai kikaga ya faru da sanin Allah kada ki damu ba wayonmu ko dabararmu ke rayamu ba burina ko bana raye kiyi karatun bokon nan me zurfi kema kamar yanda kikekan na addini Asma'u burina ki zama likitan ciwona saboda na fara gajiya da wulaqancin da likitawa sukeyi Mana duk lkcn da ciwona ya tashi muka rasa mataimaki Asmah bani da tabbacin amfanar karatunki Amma inaso ki amfanar da al'ummah don Allah kada rudin duniya yasa kema kibi wancan sahun kinji?"




Jinjina Kai tayi cikin qoqarin sanyawa kanta dakiya da juriya nason cikawa mahaifiyarta burin data rayu dashi taqici taqi sha dominta ita kadai ta hana kanta sukuni dominta, da wannan tunanin ta Kama hannun Ummah ta miqar da ita suka fara fita daga harabar gdan suna tafe suna taba yar hirarsu tsakanin gdansu da gdan Alh Qasim tafiyace miqaqqa Amma haka ummah tace su tafi a qafa kawai don tsoron kada tayiwa kudin makarantar yar tata gibi ta shiga wani yanayi suna tafe suna Hira har sukaci Rabin tafiyar sannan suka tsaya saboda nishin da Asma'u taji mahaifiyar ta ta fara ta riqota da sauri ta zauna ta kwantar da ita a jikinta tace “Ummah kingani ko abinda nake gudu kenan shiyasa nace mu hau dan sahu naira dari zasu kaimu kikaqi....."
Mgnr ce ta maqale cikin tashin hankali ta rinqa jijjigata tana Kiran sunanta Amma Ina ta Suma nan fah Asma ta dora hannu aka ta kurma ihu tana cewa wayyoh Jama'a a taimakeni Ummana zata mutu don Allah kada ki bari ta mut...." Nandanan saiga mutane sun taru a gurin masu fifita nayi masu surutu nayi, itakuwa titi ta bazama ta fara tsayar da motoci da yawansu basa tsayawa wata mota tazo zata wucce tayi tsalle ta dira gabanta tare da rintse idonta take me motar yaci wani uban birki ji kake qiyyyyyy, abinda yaja hankalin kowa dake gurin kenan suka juyo domin ganin meye yake faruwa Asma da take tunanin ba a wannan duniyar take ba ta bude idonta daidai lkcn da taji an dauketa da wani gigitaccen mari daya sanyata durqushewa a qasa yace “banza mahaukaya zakizo kijamin masifa a banza......" Riqe qafarsa tayi da sauri tace “don girman Allah kada ka tafi ka taimakamin kada Ummah na ta mutu a titi kakaimu asibiti....." Dagota yayi kamar abin arziki ya qare Mata kallo sannan yayi watsi da ita tare da jan tsaki ya nufi inda Ummah take kwance ya leqa,




Tunaninta ya gama bata taimakonta zaiyi taga ya nuna Umman da yatsa yace “dama akan wannan tsumman kikeson kiyi asarar taki rayuwar sakarya kawai to meye yayiwa wannan yamusasshiyar tsohuwar saura ai bazata warke ba qarama ki lallaba taki rayuwar qila tayi Miki amfani a gaba farin magi duk ya kashe tsohuwa" durqushewa ta kumayi a qasa tana qoqarin yimasa magiya ya fincike qafarsa yace “stupid girl banida lkcn batawa akan wannan gawar...." Da wannan kalmar ya fada motarsa ta miqe tana me binsa da kallo tare da Jinjina Kai daidai lkcn Allah yakawo wani dan sahu wani mutum ya tareshi suka tarairayi Ummah suka sakata a ciki suka nufi Asibiti mafi kusa dasu da niyyar abata taimakon gaggawa kafin su tafi gda.
Suna zuwa aka tura Ummah aka shiga da ita ciki suka sanya mata ruwa kafin fitowar babban likita, bayan kamar shudewar awa guda sai gashinan dauke da files a hannunsa ya nufo dakin ta zuba Masa ido cike da wata muguwar tsana shima yana ganinta yaji gabansa ya fadi yayi saurin mazewa tare da juyawa ga daya gadon Yana duba mara lafiyar ya dauki file din yayi rubuce rubucensa ya juya zai fita tabisa da sauri tace “Dr Aseem wannan karon ba alfarma nake nema ba da kudina na kawo mahaifiyata asibitin nan domin a dubamin lfyrta qila taka uwar bata sallama farin cikinta domin nakaba shiyasa kake kallon iyaye Mata a banza koma dai menene kada ka manta ta haifeka ta raineka har zuwa yanzun Bata daina baka shawara ba inhar tana raye just aikin kudi kakeyi a biyaka kazo ka dubamin uwata nasan bakada ikon canza qaddarar Ubangiji Amma kayi wani Abu da zaisa naji a Raina bakada hannu wajen rushewar rayuwata wlh idan ka bari sakacinka ya kashemin mahaifiya sainayi shari'a dakai duk ranar da ZARRAH ta takai inda mahaifiyata ta bata darenta da ranarta domin ganin takai.........."





Wani murmushi yayi me kama dana rainin hankali ya matso gabanta ta matsa ya tsaya a inda yake yace “au kenan har jiran ranar ZARRAR ki kikeyi Kuma kinaji a ranki zaki sameta okay almajira kin birgeni da kika taro wasan dani saidai inaso ki sani bakikai na farashi dakeba ki bari ZARRAR taki takai tukun samu fara takun dake am bari kiji wani Abu daga kallonki naji na tsaneki saboda idanunki sun nuna bakida tarbiyya wannan dalilin yasa naji bazan taimakeki ba bazan taba taimakonki ba yarinya wannan asibitin nawane saboda haka na baki 10 minutes ki debe tsummar tsohuwarki a qara gaba kar a zubamin qwarqwata" hannu yasa aljihunsa ya zaro raffers ta dari biyar biyar ya jefa Mata yace “ga wannan idan ta mutu a sai geron sadaka" cafewa tayi ta saita tsaiwarta har ya juya zai tafi ta daga murya tace “Aseem Shaheed" juyowa yayi da sauri jin ta ambaci cikakken sunansa ta matsa gabansa ta keta raffers din gda hudu ta watsa masa tayi murmushi me hade da kuka tace “Sunana Asma'u Hussain ka rubutani cikin qaddarorin da zasu addabi rayuwarka wlh saina baka mamaki matsiyaci me taqama da kayan aro shashasha Wawa kada ka damu zamu sake haduwa a gaba wasan baa faraba"........




_Hmmmm Wasan baa fara ba correct Asma'u Dr Aseem a sake shiri_





*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*


_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*



_Bismillahir Rahamanir Rahim_



_Page 7-8_


*_Wattpad realfauzahtasiu_*


Telegram
👇
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7


_____________________________
_____________________________



Wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauke lkcn da yasa tisue yake tsane jinin tare da rufe ciwon sosai dutsen ya shigeshi hakance tasa Bai iya jan motar ba sai Zahran ne yaja Kai tsaye suka nufi Asibiti anan Zahran yayi masa dressing na ciwon.
Duk dagowar da Zahran zaiyi sai yaga shi yake kallo har ya gama Masa yace “angama Dr yau ka gamu da sharrin yayan talakawa narasa me muka tare musu sukejin haushinmu nasan da zaa Basu dama zasu iya kashemu su hut....” daga Masa hannu yayi a fusace jikinsa na yace “ka nemomin gdansu yarinyar nan a duk inda take a fadin garin Kano" da sauri Zahran ya Mike yace “in kasan gdansu me zakayi Mata" ya dade yana kallon Zahran kafin yayi murmushi ya miqe yace ya fara tafiya yana dingisa qafa yace.




“Nasan ba kowa bace ita face almajira mabaraciya yar jagoran makauniya so inason sanin asalinta need saboda nayi ramuwar gayya da hujja tabbas ko Ina yafe komai bazan yafe laifin fitarmin da jini a jikina ba hannun daya dauki dutse ya fasamin yatsa ya ciremin farce saiya goge takalmina" ficewa yayi ya shiga motarsa ya fuzgeta da mugun gudu ya nufi unguwarsu dake Shagari quarters yana parking ko rufe qofar baiyi ba ya nufi cikin gdan ya bude parlourn ya shiga Mimee matarsa dake zaune da cup a hannunta ta miqe da sauri da niyyar taroshi ganin Yana dingisa qafa yasata dafe qirji tace “Na shiga uku Life meye ya sameka a qafa?"
Kallonta kawai yayi ya wucce dakinsa ya fada gado yana huci kamar yaci Babu tunda yake Babu mahaluqin daya taba karambanin daga hannu ya mareshi har mari biyu a lkc daya da sauri ya miqe tare da kallon qafarsa cikin wani mugun quncin zuciya yake furta “Wacece ce ita meye take taqama dashi wacece ita!?" Yana mgnr ne da qaraji abinda yasa Mimee shigowa da sauri tace “lfy Life?" Iska ya furzar tare da cewa da ita “Asma'u Hussain wacece Asma da ta iya daga hannu ta mareni wacece ita data fitarmin da wani bangare na jikina?"




Duban qafarsa yayi tare da cewa “wlh saita gane kurenta saina koya Mata hankali saina wulaqantata ita da danginta gabadaya saina rusa Mata burikan rayuwarta" fuuuu ya shige bathroom Sarai Mimee tasan halinsa idan yanakan tsini bajin rarrashi yakeyi ba shiyasa batayi yunqurin rarrashinsa ba ta nemi guri ta zauna da tunanin meye ya hadosa da mace shida magana ma ko da maza ba damunsa tayi ba da har takaisu ga wannan tsamar tabbas bayan tiya akwai wata caca banza batakai zomo kasuwa.
Miqewa tayi ta fita ta hado masa abinci don tasan ba fitowa zaiyi ba yau an taba mazan fama Aseem rikici ne gabadayansa tunda ya dauki ragamar ramuwar Nan to gara tayi masa fatan nasara don idan ta cika mgn kanta fadan zai dawo. Zama yayi yana tsane jikinsa yace “meye wannan din?" Murmushi tayi tace “bansan zaka dawo da wuri ba jallop din taliya ce" zuba masa ta farayi ya karba Yana tauna abincin kamar Yana tauna magani ajiye flat din yayi ya miqe a gado tana kallonsa yanata qwafa ganin bazata iya ba ta miqe ta debe kayan ta fice dasu ta hada me aikinta dasu ita Kuma ta shige dakinta itama ta kwanta.




Wayarsa ya janyo ya kashe don yasan zaayita kiransa a hospital Kuma ba iya zuwa zaiyi ba yau gabadaya Asma'u ta Bata Masa lissafin ranar dole haka zata tafi a banza. Haka ya yini kwance saidai daganan ya juya nan sallah kadai ke tashinsa hudu da rabi na yamma Zahran ya kirashi yace “ya fito yanada lbr game da aikin daya sanyashi" miqewa yayi ya dauki rigarsa yasa ya dora hula ya fito a harabar gdan ya ishe Zahran ya qarasa fuskarsa kamar ta sa tsabar damuwa mota ya bude ya shiga suka dubi juna Zahran yace “Kamar yanda ka fada Sunanta Asma'u Hussain Babanta Mal Hussain talaka ne na qarshe domin kuwa tunda ya taso aikinsa Bai wucce dako da faskare ba mahaifiyarta Amina itace babbar Matar Mal Husaini sai sauran matan babanta su biyu Lamunde da Lantana su Hudune Yaya a gidansu Mudansir sai Zabba'u sai Dijangala sai ita qarama Asma'u wadda ake Kira da Ma'un Inna ko ace Ma'un Sadiqu autace a gdansu duk da kasancewar uwarta ba komai bace a gdan Amma hakan bai hanata samun gata daidai na talaka ba duk da kasancewar Babu abin sisi da Mal Husain yakewa yaran saidai suyi sana'a da iyayensu suyiwa kansu ita Inna da kake ji macece me qoqari gaya akan yayanta tayi qosai tayi aikatau gdan masu kudi tayi surfe tayi dakau sannan tayi wankau zamanin tanada idanunta har abincin siyarwa tayi duk da tanada ya mace Bata Dora Asma'u talla saidai Mudan da ita su dauka suje su siyar a bakin kasuwa a cewarta ita ya mace kadara ce me tsada Kuma abar farauta ce idan kayi wasarairai da ita kamar dawisu take inda yafi yalwal bishiyoyi da Ni'ima nan take fakewa tace zatayi rayuwa a cikinsa idan akayi rashin saa sai asamu mafarauta su kameta shikenan rayuwarta ta lalace:



Yarinya ce me qwazo tun tana qarama hakan yasa uwarta taci burin sai tayi karatu me zurfi lkcn da aka makantar da Inna lkcn Asma'u ta gama primary daganan abubuwa sukayita lalacewa dan abinda ake fita a Nemo na rainawa babu halin fita a nemoshi Nan suka shiga Ni yasu abinda zasuci ma yakan gagaresu akwai wani yaro Sadiqu da tun tasowar Asma'u yakeyi Mata wahala shine rakata makaranta

2 / 18