Chapter 3 Reading ZARRAH BOOK COMPLETE ROMANTIC BY OUM HAIRAN.txt Arewa Novels

ZARRAH BOOK COMPLETE ROMANTIC BY OUM HAIRAN.txt

Author :  Fauziyya Tasi'u Umar Category :  Home Of Novels

Chapter   3 / 18

6K to 9K   out of 52.6K words

shine komanta saiya zamana idan yasai da rake ko ya dauki tallan yalon bello yaje ya siyar ne yake samu yabasu abinda zasuci.
Ana hakane wata Ladi almajira tayiwa Inna tayin fita bara tunda dai Allah yasani batada mataimaki da farko Inna taqi abin Amma lkcn da Asma'u ta farayi mata mitar duk qawayenta sun tafi makarantar secondary ita tana gda saita farabin Ladi bara suna samo na batarwa a hakadai har suka Tara kudin makarantar lkcn har anci zango daya suka kaita Prime school dake Inna tun dacan Bata yarda yaranta sunyi makarantar gwamnati ba tace Babu karatu ita Kuma so take yaranta suyi karatu, daga lkcn da Asma'u ta fara zama budurwa saiya kasance idan sunje neman taimako mutanenmu sai suka fara nuna maitarsu akan yarinyar itakuma uwar tana nuna Mata aibin hakan musamman dake Asma'u tana zuwa islamiyyar dare, matsalar Asma'u daya ita tun tana qarama batada hqr Kuma Bata yafiya indai kayi Mata saita rama so da mutane suka fara gwada rashin imaninsu akan mahaifiyarta sai ta dauki gabarar duk Wanda yayi Mata ko waye a duniya saitayi Masa kalmarta daya itace “ka jira ZARRAH ta ranar da zan zama babbar likita zanyi fada da uban kowa a duniya Kuma zan nuna maka kaiba komai bane" yanzu haka zancen da nakeyi maka burinta na gab da cika domin kuwa takusa kammala secondary Wanda Innarta tafi shekara biyar tana adashin gata domin Asma'u ta wucce makarantar da zatayi karatunta na likitanci"




Murmushi Dr Aseem yayi yace “aikinka yana kyau Kuma meye yanayin ubanta da kudi sannan a wacce unguwa suke zaune?" Jinjina Kai Zahran yayi yace “wanda yayimin bayanin tarihinsu yace kirarin mahaifinta Mal Husaini idon cin naira indai kanada kudi to kanada cikakken mutumci a gurinsa idan kuwa baka dashi to kashinsa yafika daraja anan Tukuntawa gdansu yake shikuma babanta a sabuwar gandu majalissarsu take gefen rumfar wani me nama suna zaune idan ansiya suyi sudi aikinsu kenan"
Jinjina Kai Aseem yayi yace “ka gama magana inason kwadayayyen mutum saboda buri yana saurin cika Asmah ki jirayi zuwana burinki bazai taba cikaba zan rusanki duk wata walwala da farin ciki zaki rayu da qunci zan massheki baiwa a gdana saikin lashe tafin qafata da harshenki...... Dafashi Zahran yayi yace “tabani haushi dazu Amma da naji tarihinta sai tabani tausayi please ka hqr da daukar fansar nan kabarta don Allah akwai quruciya yarinya ce qarama fah....." Hannu ya Dora Masa a baki yace “karka qara bani hqr wlh bantaba tausayin wani Abu kamar yanda na tausayawa yarinyar nan ba Amma hakan bazai hanani daukar mataki akanta ba saita Raina kanta Kuma sai tasan tasa Wasa da Aseem Shaheed"...........



Vote
Comments
Share



*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*

_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*


_Bismillahir Rahamanir Rahim_


_Free Page 9-10_


*_Wattpad realfauzahtasiu_*

     Telegram
           👇
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

_____________________________
_____________________________



Tunda Asma'u ta koma gida take zumbure zumbure Matan gdan Babu Wanda ya kulata Inna kuwa ba ido ba balle tasan matsalar yartata haka tayi wanka tayi sallar azahar da La'asar ta zauna tsince wake bayan ta gama ta dora musu abinci tana girkin tana qunquni da haka ta gama ta zuba ta zauna tanaci bayan ta gama ta shirya ta tafi islamiyya sai shidda ta dawo lkcn uniform dinta ya jiqu ta wankeshi ta shanya sai lkcn ta jirge ta zauna tana bawa Inna lbrn abinda ya faru.
Sosai Inna ta nuna rashin jin dadinta da abinda yartata tayiwa Aseem tare da rufeta da fada daga baya ta dawo yimata nasiha to ta danji a lkcn ta miqe tayi sallah ta kwanta, washegari da wuri ta fice saboda so takeyi yau suje makarantar da wuri cikin saa ta tarar da Jidda ta shirya suka tafi suna tafe suna Hira Jidda tace.
“Nifa jiya kin kullemin Kai Asma'u waike bakida tsoro ne baki tsoron kada mutumin nan ya sanya yan sanda su kamaki?" Tsaki tayi tace “kuma saboda Ina tsoro saina bari yaci mutumcina na qyaleshi ko?"




Kada Kai Jiddah tayi tana Shirin yin magana wata mota tazo ta giftasu kawai sai sukaga taci burki a gabansu hankalin Asma baa kan motar yake ba har zasu gifta taji Jidda tace “mun shiga uku Asma'u mutumin jiya ne fah" da sauri ta kalli gurin suka hada ido ta galla masa harara ta qarawa tafiyarta sauri saboda Inna tace idan ta sake kulashi sai taci mutuncinta.
Murmushi yayi cike dajin tsanar yarinyar a qasan zuciyarsa yaja motarsa ya qara gaba ta gefenta ya wucce shuuu taja fasali tace “kaci arziqin Inna ta hanani kulaka wlh yauma dasai nayi maka rotse sakarai Wawa"





Duk da Aseem baiji abinda ta fada ba Amma ya fahimci dashi take murmushi yayi ya qara bawa motarsa wuta tabbas sai yayi maganin rashin kunyar yarinyar nan da take ganinta daidai dashi saiyabi ta kowacce hanya yaga ya koya Mata hankali saiya sanya Mata jin cewa Ashe ita ba kowa bace a rayuwarta tunaninsa yanzu ta inda zai fara gudanar da aikinsa kisan mummuqe yakeson yimata batare da wani ya gane qudurinsa ba yakeso ya baje tarihin rashin kunyar Asma'u,
Yana tuqi yana murmushi Yana maimata sunanta yanayin yanda ta harareshi dazun yana Masa gizo yanajin wani nishadi da Allah yasa yarinyar ta siyar Masa da qasar wasan dole akwai badaqala zai ganar da ita kurenta na shiga sharafin daba nataba. Koda yaje asibitin ya fara duba marasa lfyrsa bayan ya gama ya wucce nasa private hospital nanma yayi abinda zaiyi sannan ya shige office dinsa ya zauna yana juyi a kujerarsa cike da zumudin ganin yamma tayi Zahran ya gama aikinsa ya daukeshi suje su nemi mahaifin Asma'u kamar yanda ya tsara kafinnan Saida ya sake tura wani yaronsa yayi masa binciken tsaf inda anan ne yaron nasa Uzairu yake sanar dashi ai Mal Husaini yasa gdansa a kasuwa zaiyi auren yaransa uku sukuma iyayen zasu koma qauye da zama wacce bazataba Kuma tasan inda dare yayi mata.




Fiye da tunani Aseem yaji dadin wannan farin lbr aikuwa hudu da rabi suka fice daga asibitin suka nufi bakin kasuwar sabuwar gandu inda anan Mal Husaini yake zama Nan suka nemi a rakasu ofishin dillalan qasa akayi musu jagora sukaje suka gaisa Zahran yana nunawa Aseem Mal Husaini da yaketa maka hamma da hularsa ko Kari Babu bisa dukkan alamu yunwa yakeji.
Caraf kuwa Alh Bala dillali yace “Idon cin naira da alamun dai yau baa sammaka abin sawa a maqoshi ba ka fito" kamar me jiran kadan ya balle zance kamar Wanda ya qone a tsakiyar ka cewa yake “yo dama wadannan sakarkarun waye yanzu yake sammin abincin Lantana da Lamunde sunce sun daina cida qato Wai auren yayansu zasuyi Amina ce me tausayina take bane to itanma saidai idan wannan ja'irar yarinyar Ma'u batanan amma fir take hanawa tace ai ba Basu nakeyi ba kuma tana ganin lkcn da nake bawa Lamunde nikuma ganin suna fita bara nasan na annabi baya qarewa shiyasa bandamu da sammusu ba gashi anma kasa samun me siyan kangon can nawa bare na Dan murmure kafin bikin nan"




Jinjina Kai Aseem yayi Bala dillali ya dubesu yace “Alh Allah gida ko fili ko kango ko haya ake buqata?" Cire hularsa yayi ya maida hankalinsa ga Zahran Zahran ya gyara zama ya karkace yace “gda muke buqata ginin gargajiya anan Tukuntawa zamu zuba shanu da tumaki a ciki...." Yunqurowa Mal Husaini yayi Mal Bala ya dakatar dashi yace “toh ikon Allah kamar Kuma na nawa kuke buqata?" Kallon Aseem Zahran yayi Aseem da sai yanzu yaga samar mgn yace “ba qarami ba ba babba ba duk yanda kasuwa ta Kama munaso idan akwai a nuna Mana abune na urgent da muke buqatarsa tsakanin yau da sati biyu" duba Mal Bala yakai ga Mal Husaini da dama yake jiran abashi dama nan yayi kwance kwance yace “yo Alh Allah muje suga nawa Mana ko Allah zaisa a daidaita tunda qananun masu kudi sun kasa siye sunce zaici kudi wajen gyaransa




Tunda ya fara mgnr Aseem ya zuba Masa ido har ya gama murmushi Aseem yayi Wanda shikadai yasan dalilin murmushin nasa yace “ok muje mu gani idan yayi sai muyi ciniki Amma gsky muna buqatar gurin da wuri zamuyi aiki a ciki ne" Babu tunanin makomar iyalai Mal Husaini yace “Haba yaro abinda yake kasuwa ai ko yau kakeson abinka baka akayi indai ka biya nidai fatana Allah yasa gurin yayi maka fitinar zabba'u ta isheni yau ta debo wannan gobe ta kwaso wancan gara na auraddasu kawai na huta sauran kudin naci tsire dasu hhhh koba hakaba yaro..."
Sudai murmushi kawai sukayi suka nufi motar Mal Bala da Mal Husaini suka shiga baya Aseem da Zahran suna gaba a haka Mal Husaini yaketa basu kwatance suna amsawa har suka shiga unguwar tun daga farkonta suka fara Raina kansu asalin uguwar talakawa ce ko Ina kwatami ne yake gudu haka sukayita kutsawa lunguna har suka isa qofar wani tsohon gda ginin jar qasa dako arziqin yabe bai samu ba babu qofa a gidan sai labulan tampol da aka sanya domin sakaye gdan, tundaga qofar gdan Aseem ya qara Raina matsayin Asma'u tare da tsananin mamakin izzarta a matsayinta na wadda ta taso a wannan rubabbiyar unguwa a unguwar ma a gda mafi qasqanci domin shidai iyakar dubansa baiga gdan da yakai nasu Asma'u lalacewa ba a area.




Mal Husaini ne ya shiga ciki ya sanar da matansa cewa zaa shigo ganin gda me tankade ta tashi me dakama ta miqe sukayi daki Inna ce dama tana daki a zaune tana lazumi shigowa sukayi suna duba gdan a zahirin gdan Babu uwar da Aseem zaiyi dashi Amma da suka gama dubawa sai ya dubi Zahran yace masa “ina ganin kamar gurin zaiyi ai ko?" Sarai Zahran yasan me yake nufi shikuma sai yace “dadai an nemi Wanda yafi wannan gsky shanun zasu takura" dafashi yayi yace “kada ka damu fashe dakunan zaayi daki biyun nan kawai zaa bari saboda me gadi da abincin dabbobi" da wannan suka juya zasu fita suna Shirin fita kyawawan yammatan na sawo Kai Dijangala ce a gaba sai Zabba'u ita kuwa gwanar ta cake a qofar gda Laila sarkin soyayya ita da Sadiqun ta suna bawa fure ruwa ai suna fitowa tana dago Kai suka hada ido ba itaba shima Saida yaji gabansa ya fadi ya kasa dauke ido daga kanta dake dariya takeyi yanzun sabanin duk haduwar da sukeyi dashi yau saiyaga tayi wani haske tayi kyau kyawawan haqoranta ya zubawa ido da akayi musu kwalliya da siririyar wushirya.
Ganin fitowarsu daga gdansu yasata saurin tsuke fuska kamar ba itace take dariya ba ta kawar dakai daga kallon da sukewa juna ita da Aseem din, sosai Sadiqu ya lura da sauyin nata don haka ya dubeta.




Yace “ya akayine jarumar Mata?" Ajiyar numfashi tayi tace “meye ya kawoshi gdanmu?" Da rashin fahimta yace “wafa?" Duban Aseem tayi da ya juya baya jikin motarsa yana waya tace “wancan Mara mutumcin Mana shine fah mutumin da nake baka lbrn na fashewa qafa ko qarata ya kawo gda gurin Mal tab aikuwa zan daku shikuma zai ragargazu Dan wlh hayar tantiran hayin qwari zanyi su rugurgujeshi.
Dariya Sadiqu yakeyi Mata domin ya lura gabadayanta a tsorace take tsinkayo muryar Mal tayi Yana qwala Mata Kira “Ma'ulele ke Ma'u bakijina ne bakiga mutane ba dan qaniyarki irin tarbiyyar da gyatumarki tayi Miki kenan?" Sumsum ta nufi gurinsu duk a razane take a rusuna tace “ina yininku" Zahran ne da Mal Bala suka amsa shikuwa gogan kallonta kawai yakeyi Mal Bala yace “Mal nayi nayi dakai ka bani daya cikin yammatannan naka kaqi da tuni baba nakece maka ga Ma'u ma ta girma abinta" tsuke fuska Mal Husaini yayi yace “yo Banda abinka yaro ai sai yaro kaga wancan kafirin yaron da qaton Kai shine ya zamemin alaqaqai nayi nayi na rabasu sunqi rabuwa harma na hqr basa zanyi suje su qarata"
Dagowa Aseem yayi yace “wai itama wannan din taka ce Baba?" Murmushi yayi yana sosa qeya yace “wlh kagansu Nan kamar yar maraqan shanu haka akayita jeramin su harsu uku gasunan kansu daya ita wannan itace qaramarsu shekararta sha shidda sabodasu nema zan sayar da gdannan" Jinjina Kai yayi cikin jin dadi yana hango nasara yace “a aikuwa ba ayi haka ba kasai da gda baba kaida kake da Yaya Mata kabar gdanka kawai" da sauri ya dubeshi yace “inbar gda fah kace Alh waye zaiyimin auren yayan?" Murmushi Aseem yayi ya bude motarsa ya bude dashboard ya dauka raffers ta dari biyar biyar guda biyu ya bashi yace “karka damu baba ka riqe wannan gobe insha Allahu zan dawo ai kamarka kanada wadannan kyawawan yammatan ba abarka ka tozarta ba" sake miqa Masa wata reffer yayi yace a rabawa matan gdan wannan anan suka qyale Mal Husaini sake da baki da kudi a hannunsa suka dauki Mal Bala suka tafi a mota Aseem ya dubi Mal Bala yace “yarinyar nan data gaishemu ta fanshi mahaifinta indai zai bani auranta na rantse zanyi Masa komai da yake buqata na hidimar aurensu tun daga satin farko har ranar da zaa gama biki ka sameshi ka fada Masa idan ya amince har gdanma zan gyara Masa"..........
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*

_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*


_Bismillahir Rahamanir Rahim_


_Free Page 11-12_


*_Wattpad realfauzahtasiu_*

     Telegram
           👇
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

______________________________
______________________________




Tunda suka tafi sukabar Asma'u da sakakken baki kallon da Aseem yakeyi Mata ita da Sadiqu shine yafi Bata mamaki da Kuma dalilin zuwansu gdansu ganin ya damqawa Mal Husaini kudine yasata sake maida hankalinsu garesu amma sai taga ya dubeta yayi murmushi yaja motarsa sunbar Mal da kallon kudi cikin mamaki.
Mal Husaini na dagowa suka hada ido da Asma'u yayi saurin sanya kudin cikin hularsa tare da watsa Mata daquwa tayi saurin kawar dakai sukaci gaba da tsinkar furensu ita da Sadiqun ta Saida aka Kira magariba sukayi sallama ya nufi masallaci ita Kuma ta shiga gda ta dauki buta ta shige bayi ta Kama ruwa ta fito ta daura alwala daidai lkcn da taji Mal Husaini na cewa “ni Babu ruwana da inda Zaki Amina gdane saidashi zanyi dole kowacce ta nemi inda zata zauna kafin ayi bikin yarannan ku koma qauye ba Saida nace kada ku kuskura ku haifi Mata ba ku masu kunne qashi kuka haifesu ai gashinan basu kawo kudi ba sun kwamushe muku naku" cafkar kunnen Asma'u yayi yace “ja'ira da kanta tunna zuwa duniya saura naji kince wani Abu baki kamar gdan tsutsa tana tafe kamar allura" itadai tana samu ya sakar Mata kunne sumsum ta shige daki ta tayar da sallah tare da jan bakinta ta tsuke Abu daya ta iya tambaya shine meye ya kawo baqin gdansu? Inna tace Mata. Masu siyan gdansu ne daga haka tayi shiru da bakinta saboda batason subutar baki tasa tayi wata magana don Bata kuskura ta fadawa Inna tsiyar da tayiwa Aseem Shaheed ba.



Kwana Asma tayi tana tunanin dalilin da yasa Aseem yakeson siyan gdansu, a daren taci alwashin indai Allah ya hadasu gobe a hanyar makaranta sai taci mutuncinsa yanda zaiji bama ya sha'awar siyan gdan nasu, aikuwa tun asuba ta shirya taja ta zauna tana jiran lkc bakwai daidai ta fice daga gdansu ta nufi gdansu Jiddah suka dunguma suka tafi tana bawa jiddah labarin abinda ya faru jiya na zuwan Aseem gdansu a matsayin Wanda zaisai gdan zaiyi kiwon shanu"
Dariya sosai Jiddah tayi tace “kin gamu da qarfen qafa me wuyar kwancewa wato gayen nan ya shiryawa wasan so yake ya qure malejinki ya wulaqantaki Kinga idan ya siye gdanku ko haya ya baku ai babanku ya koma qarqashinsa balle ma tashinku zaiyi a wulaqance ya zuba shanu a gdan Kinga ya nuna Miki rayuwar shanunsa tafi taku muhimmanci. Nifa dama bangano Miki nasara a buga wasa da wannan mutumin ba da ganinsa kinsan yaci yatada Kai zai iya ramawa wulaqancin da zakiyi Masa ta duk inda yaso gara dai yan gujaru gujarun da muke tsokana Basu da yanda zasuyi damu sai tsaki sai harara"



Har sukaje makarantar Allah be hadasu dashi ba haka ta rinqa Allah Allah a tashi nanma Basu gamu ba taji haushi sosai so batada yanda zatayi dole ta hqr tana zuwa suka nufi islamiyya sai yamma suka dawo liqis dake laraba ce sunyi hadda a dakin zaure suka tarar da Mal Husaini da Mal Bala suna tattaunawa Mal Husaini sai dariya yakesu suka durqushe suka gaishesu da fara'a Mal Bala ya amsa inda Mal Husaini yace “Ina Ma'ulelena zonan dan qaniyarki" gabanta ya fadi tunda dama a tsorace take tana jiran abinda zaije ya dawo.
Matsawa tayi a darare ta zauna tana barin jiki don tasan ba wuya bane Mal ya maketa ba gyaran murya yayi yace “Ina kike Asma'ul Husnah?" Ajiyar zuciya tayi tace “gani Mal" Jinjina Kai yayi yace “yawwa Masha Allah dama wani umarnin gaggawa zan baki Kinga dai a yanda kuka taso a wahale a talauce to ke ki godewa Allah yasoki da arziqi yayi miki ludufi da ludufin da yakewa duk Wanda yaso cikin bayinsa jiya anzo ganin gida Ashe rabon aganki ne dan farin yaron nan Alhajin Birni eh wlh tallahi shine dai bayan sunga gda kinje kin gaishesu yagani yakeso harma yayimin alqawarin idan na bashi aurenki zai barmin gdana Kuma zaiyimin komai na auren Dijangala da Zabba'u keko yace ki cokali bashi buqata, kinji fah inda arziqi yake"




Tunda ya fara mgnr ta kafesa da ido cikin mugun tsoro da kaduwa ta gane waye yake nufi domin Zahran ba fari bane Aseem ne fari Anna sai tace “wa...waikace Mal Sadiqun fah?" Wata uwar harara ya buga Mata yace “Sadiqun0 ubanki yo ko Laminu ne uban Sadiqu ya dawo duniya ai bazai hanani cin wannan arziqin ba ke nifa bama shawara nake daku ba dagake har uwarki dama na dauka ke dake kin shafi zamani zakiba da hadin Kai to kema naga qwalluwar yar baqin ciki ce saboda haka tashi ware kauce karna makeki sauna kawai wadda arziqi ke binta tsiya ke dawo da ita baya"
Yana fadin haka ya miqe abinda yasata miqewa itama da gudu tayi cikin gdan tana rushewa da kuka tana cewa “wlh baa isaba bazaa taba cutata a hadani da wannan shegen azzalumin mutumin ba ai bani kadai aka Haifa a gdanba abashi wata Mana saini

3 / 18