Author : Fauziyya Tasi'u Umar Category : Home Of Novels
Hajja tayi tace “na shiga uku ni Saratu yar talakawa Aseem ina ka samota me suka Baka suka sauya maka tunani ni zaka wulaqanta yanzu yaushe ma akayi aurenka da Maryam da har zaka tattagowa kanka aure kuma auren ma memakon kaci gaba sai kawai kaci baya to wallahi baka isaba dole ka hqr da wannan dan iskan auren naka ka zauna da matarka dana zaba maka"
Shidai tunda yayi qasa da Kansa bai dagoba sai yanzun yace “wlh Hajja ba haka bane kawai...." Buge masa baki tayi tace kawai Ubanka ka kiyayeni Aseem zanci ubanka wlh dama na lura shine yake daure maka gindi shi ko ubanme ya hanashi auren mace sama da dayan sai kai da quruciyarka zaka dorawa kanka wahala to indai na isa dole ka janye ban amince ba bakuma zan amince ba"
Juyawa tayi ta shige parlournta ta barshi tsaye itama Mimee tabi bayanta a sanyaye ya juya ya fice daga gdan yanajin zafin abinda Hajja tayi masa yanzu meye laifinsa don anyi masa ba daidai ba yayi shirin daukar fansa zaayi masa wata fassara ta dabam bandama abinsu shi meye zaici da wannan banzar yarinyar da bata isheshi kallo ba"
Da wannan tunanin ya nufi gdan Jabir yake fada masa abinda ke faruwa sosai shima Jabir ya jinjina abin ya dubesa yace “to kai tunda abin baiyi nisa ba ka hqr mana kasan dai halin Hajja shi kansa Dad hqr yakeyi da ita" girgiza kai yayi yayi murmushi yace “nifa babu abinda zaisa na janye akan qudurina saidai kowa yayi hqr kamar yanda nake haqurqurtar da zuciyata ta karbi auren idan na janye dama haka Asma'uh da nahaifiyarta sukeso farin ciki zasuyi nikuma ba burina suyi farin cikin ba saboda haka kawai aci gaba da tafiya a haka tunda Dad ya karba mgnr kowa ma kada ya karba" da wannan tunanin ya miqe ya nufi gdan Yayarsa Aseemah itace kadai me sauqin yanayi a wajenta yake tunanin samun mafita game da auren nasa yana zuwa ta tareshi da fara'a tana tsokanarsa nan yake zube mata abinda yake ransa sosai tayi murna ta tayashi fatan alkhairi yayi shiru kamar bazaice komai ba sannan ya dago yace.
“Banasonta Sister na rasa meye yasa na dage wajen Neman auren ta yar talakawa ce Allah ina qyaqqyamin kaina inajin kunyar nunata matsayin mata talauci yayi musu kanta nifa badon quduruna a kanta ba da tuni na hqr ko na samu nutsuwa"
Zubansa ido Aunty Aseemah tayi har saida ya rufe baki tayi ajiyar zuciya tare da murmushi tausayin Asmah yafi komai narkar da zuciyarsa duk da tasan cewa qarya Aseem yake yace bayasonta domin tasan zuciyarsa idan babu burbushin son babu abinda zai darsa masa son auren ta matsalar kafin ya aminta ya yarda yanasonta tasha wahala kawar dakai tayi tace “kaje kayita addu'a qila rabone tsakaninku kasan ba kowa ne yake da Baiwar gane abinda yakeso a qaramin lkc ba" sosai ta rinqa basa shawara wata yakan dauka wata kuma ya watsar da ita domin yasan bazai iyaba"
Baibar gdan ba sai bayan magrib ya nufi gdansa har lkcn Mimee bata dawo ba dakinsa ya shiga yayi wanka ya dawo ya kwanta a parlour ya kunna kallo.
**********
Tunda suka koma gda batada aiki sai tunani damuwa taqi damunta babban abinda yafi damunta shine yanda Sadiq ya manta da ita ko a hanya suka hadu sai ya kawar mata dakai koma ya buleta da qurar sabon lifan dinsa wannan Abu nayi mata ciwo gashi batada Wanda zata zauna tayi hira dashi taji dadi duk da zuwa yanzu sun daidaita da yan'uwanta so ta lura suma yan son zuciya ne har garama Dijangala ita ta fahimci akwai matsala tana tausayawa Asmah sosai musammam da taga kowa saurayinta yana zuwa gurinta suyi hira itakam Asmah Aseem tun ranar da aka sallamosu daga asibiti bai qara takowa gdansu ba saidai ya aiko Jabir duk ta rame abinka da mara jikin dama babu abinda kake gani sai dogon hancin da idanu duk rawar kannan da fitsarar Asmah tayi laqwas ko mgn wahala takeyi mata ana haka aka kawo lefen su Dija samarinsu sunyi qoqari sosai babu laifi a matsayinsu na talakawa kwana biyu tsakani aka kawo na Asmah ranar har wanda basa mgn dasu saida suka shigo ganin wannan lefe na al'ajabi
Lkcn bikin saura sati guda amma shiga shagalin biki itadai Asmah tunda aka fara bikin tana kwance a dakin da akayi musu na yaran gda batada aikin daya wucce kuka duk da fitsararta tasan haqqin Miji akan mace sosai yanzu indai ta bari aka daura auren nan shikenan ta zama nama duk yanda yaga dama haka zaiyi da ita? Hakan ba qaramin karyar mata da zuciya take ba ana saura kwana biyar tana gdan maqotansu tana kwance kasancewar ba Lfy ce ta isheta ba yaro ya shigo yace “wai ana kiran Asma'uh a waje" ajiyar zuciya tayi ta gyara kwanciya Jiddarh tace “ki tashi kije mana kinsan shima wannan dan Aiken ba qaunar jira yakeyi ba"
Tsaki tayi tace “kije kawai" sanin halinta ne yasata miqewa tace “bazakiyi mana buqulu ba yanzu haka kudin partyn aka kawo mana" Dija nayi mata dariya ta fice itadai bata tanka ba sai game da takeyi da wayar Hajar Matar gdan da suke yammatancinsu, da sauri sukaga Jiddarh ta nufo parlourn ta zauna tana Mayar da numfashi saida ta gama saita nutsuwarta tace “aikin babba ne Ma'uh yau me gayya me aiki ne yake tafe wlh yanacan saici mazu yakeyi kije yana jiranki" sosai taji qirjinta ya buga ta dago idanunta da suka kawo ruwa tace “don Allah kije kice masa bananan" zare ido tayi tace “ban isaba wlh ki tashi kawai kije" sharewa tayi ta koma tayi kwanciyarta daqyar tasheta shima saida Innah ta aiko da kanta sannan ta tashi tasa qaton hijjab dinta ta fito idanunta na fitar da ruwa ta nufi wajen ta jima tsaye kafin ya danna mata horn ta nufi inda motar take ya bude mata kamar taqi shiga sai kuma ta tuna maganganun Innah haka ta zauna ya mayar da qofarsa ya rufe ya juyo ya zuba mata ido tayi qasa da kanta tana wasa da yatsanta hawayenta na zuva saman santala santalan yatsunta,
Sun jima A haka kafin taji yaja Wata doguwar ajiyar zuciya ya furzar da iska yace “meye yayi saura?" Jan numfashi tayi me hade da majina kukan da take ta qoqarin hadiyewa ya qwace mata yayi saurin zubanta ido tare da kamo hannunta qirjinsa na bugawa da qarfi kukan yana masa kuda a kunne yace “ya....ya salam meye kuma na kukan?" Sake rushewa tayi da kuka gabadaya ya diririce baisan sanda ya hadata da jikinsa ba ya rungumeta sosai ta rintse idonta da qarfi ta sake qarawa kukanta sauti tace “nas....shiga ukuna wayyoh Innata ka sakeni don Allah banas....." Numfashinta taji yana qoqarin daukewa ta shidewa tayi saurin bude idonta tsoronta ya nunku jikinta ya dauki rawa tunda take bata taba ganin dan iskan bayyane irin Aseem ba Shikam babu abinda yakeyi sai tsotsar lips dinta daqyar ta hada qarfinta ta tureshi tana jan zuciya tare da sanya hijjab dinta ta rinqa dirzar bakinta tana kuka me taba zuciya tace “Allah ya isana mugu kwarto kawai......"
*_Oum Hairan_*
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*
*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*
_*19-20*_
Buda idanunsa yayi akanta yana mata wani kallo daya sanyata saukar da kanta qasa ta kama handle din motar zata bude yayi mata key ya tasheta ta dago da sauri ta kalleshi idanunsa nakan tuqin da yake amma hankalinsa na kanta cikin sanyin muryarta ta kuka tace “Ina zaka kaini?" Bai kulata ba kuma bai daina tuqin ba har saida suka isa wani gurin kwalliya ya bude motar ya fita bai jima ba ya fito ya bude mata yanayi mata kallon dake firgitata ta fito a sanyaye yayi gaba tana binsa a baya har suka shiga ciki ya samu guri ya zauna tana tsaye yana qare mata kallo har saida daya cikin ma'aikatan gurin tace “yallabai meye ake buqata?" Numfashi ya sauke ya nuna Asmah dake tsaye kamar dashe tanabin gurin da kallo ya yatsina fuska yace “wai Amarya ce wannan din so jibi zaa fara bikin zasuzo su biyar ayi musu kwalliya nawa ne zai isa?"
Nan sukayi masa bell ya biyasu ta shiga wani daki tace ta biyota sharewa tayi kamar bazata ba ta tsinkayo muryarsa ya daka mata tsawa jikinta na tsuma tabi bayanta suka shiga ciki kanta ta bude gashinta dake nade cikin dankwalin ya baje Matar tace “masha Allah Amarya angonki zai huta da gashi" itadai bata saurareta ba saima tagomashin harara data samu ta wucce ta dauko mata wasu turaruka ta bata tace “gashinan dukkanku Ku rinqa wanka dasu qamshi zai kama jikinku gobe kuzo da wuri ayi tsifa jibi ayi gyaran gashi jikinki zai dauki gyara sosai inajin gobe zamu fara"
Bata qarasa jin abinda take cewa ba tayi ficewarta, ganin fitowar natane yasa shi miqewa ya biyo bayanta ta tsaya jikin motar yana zuwa ya bude
Ya Shiga itama ta shiga yaja suka tafi sunyi nisa sosai ya magantu da cewa r“anar Friday akwai dinner da dare ki zama ready" shiru ce ta bashi amsa takaici ya cikashi a duniya yana baqin cikin yayi mgn a shareshi qwafa yayi dole ya gogewa yarinyar raini ya fahimci ta gama rainashi tun yanzun parking yayi a qofar gdan kafin ya gama tsayawa harta fice tabar masa ledar turarukan da aka basu ta shige gdan Hajar.
Qarin takaici ya cikashi ya cije lebe a fili yace meye take taqama dashi ne?" Bashi da me bashi amsa dole ya kira wani Yaro yabashi ledar turarukan da Wata qatuwar Leda da shi Kansa baisan meye a cikin ba Aunty Aseemah CE ta bashi tace yakaiwa Asmah juyawa yayi ya tafi zuciyarsa cunkushe da takaici koda ya shiga gda bai nemi Mimee ba itama bata nemeshi ba ya shige dakinsa ya kwanta ya rasa meye yasa idan Asmah tayi masa wulaqanci abin yake kasa gogewa a ransa a hankali yaja qwafa ya miqe ya watsa ruwa ya dauki wayarsa ya hau online kusan sati biyu kenan daya bata waya baitaba ganin ta a bude ba sai yau tunda ya hau ya bude kyakkyawan hotonta da tayi tana murmushi ido hakanan yake jin gabadaya lakar jikinsa na tsinkewa tunda yake da ita baitaba zubanta ido ya qurewa kyawunta kallo ba sai yau tabbas Allah yayi halitta a gurin shiyasa take shuka tsiyarta son ranta.
Agogo ya duba yaga goma harda kwata yaja fasali so yake yayi mata mgn amma ya rasa me zaice mata ya jima yana tunanin me zaici kafin dabara ta fado masa ya rubuta mata _“ki sauka haka dare yayi"_ iyakar abinda ya rubuta kenan bayan kamar minti uku ta duba batare data bashi amsa ba ta kashe datarta ta sauka hakanma baiyi masa ba yaso ace tayi mgn
Hakan bata samu ba ya lura yarinyar yar izza ce ta bala'i dole sai yayi shiri me kyau domin zama da ita sai an shirya, tsaki yayi kawai ya gyara kwanciyarsa washegari da wuri ya tashi ya fice saboda yanada abubuwan yi da yawa kuma yanaso a gama aikin bangaren da zata zauna a yau gashi dai yau yake son ya turawa da Mal Husaini kayan dakin su Dijah, ya manta da batun zuwansu gurin gyaran jiki sai wajen 1:30pm aka kirashi daga gurin ake fada masa mutum uku sunzo amma wacce sukazo tare jiya bata biyosu ba,
Takaici ya cikashi ya dauki wayarsa a fusace ya lalubo number ta ya danna kira yajita a kashe baqin ciki ya hadashi sosai ya miqe tsam daga inda yake zaune ya figi motarsa a guje ya nufi unguwar cikin saa kuwa ya tarar da mal Husaini a qofar gda suka gaisa nan yace ya shiga dakin zaure bari ya kira masa ita, da Kansa ya shiga ya fara qwalanta kira tanaji gabanta ya fadi don tasan bana Lfy bane ta fito a salube ya harareta yace “yar baqin ciki to kije Alh nason ganinki" kamar tace masa Mal bazani ba amma batada iko hakanan ta dauki mayafinta tasa ta dauki wayarta dake saman window ta fita.
Ta jima a zauren tabarshi tsaye sai faman duba Agogo yakeyi kafin tayi qarfin halin buda labulen tare dayin yar siririyar sallama itama saboda ta zama dole ne, ba kwalliya ce a fuskarta ba hakan ya matuqar burgeshi tunda yake da Asmah baitaba ganin ta da kwalliya ba. Ya shagala da kallonta kusan 15 minutes itakuma ta qosa da kallon ta dubesa a kaikace tace “zan iya tafiya?" Yanda tayi mgnr da muryarta me kama da me shirin yin kuka yasa shi zama a kusa da ita da Sauri wani gumi ya karyo masa ta goshi itakuma jin baida niyyar mgn yasata miqewa ta saita hanya zata fice yayi azamar riqo hannunta ba shidinba hatta ita saida taji wani shocking a gabbanta ta dago idonsu ya gauraya da juna sai wani lumshe fararen idanunsa yakeyi yana bude su akanta.
Hakan yasata qoqarin janye hannunta daga nasa maimakon hakan kawai saijinta tayi zaune a saman cinyarsa gabanta yabada wani rass abinka da matsoraciya gabadaya lkc guda ta hargitse shikam gogan qara gyara zamansa yayi hakan da yayi yasamu yanda yakeso manyan faffadan mazaunanta masu tudu suka danne masa burarsa da take ta qoqarin miqewa taimako daya Allah yayi masa yasa boxes daya kamashi kota miqe bazata nuna shi ba saidai yaji a jikinsa, sake sanya hannunsa yayi ya harde qugunta ya sanya su saitin Cikinta ya dora kansa saman kafadarta yana sauke mata wani huci me dumi da dumama yanayi.
Cikin dabara ta rinqa qoqarin zame jikinta yaqi bata dama har saida yaji ta soma shassheqar kuka sannan ya fahimci abinda yake shirin aikatawa ya sake ta ta zame a hankali ya kwanta saman kujerar three sitter din da yake kai tare da harde qafafunsa yana qoqarin aro kwarjini yasawa Kansa yace “meye ya hanaki zuwa gdan kwalliyar dana kaiki jiya?" Sunkuyar da kanta tayi har yanzu qirjinta lugude yakeyi itakam ta hadu da masifa wannan mutumin wanne irine me yake nufi da ita wanne salone wannan yake son zuwar mata dashi da yake Neman zarta girman kwanyarta a mizanin hankali.......
Ji tayi hannunsa na yawo a fuskarta ta dago da Sauri sukayi ido hudu yasa yatsansa
wasa da ruwan hawayenta yayi murmushin da yasa kuncinsa lomawa sajensa ya hadu da gumi ya kwanta luf a fuskarsa yace “Asma'uh Ma'un Innah Mara kunya fitsararriya wacce bata barin kowa idan tsautsayi yasa ya shiga gonarta am don Allah ki daina kuka kuka bai kamaci fuskar jaruma kamarki wacce ta shiryawa fito na fito da mutum kamata ba ki jira lkcn kuka na gaba lkcn da zaki gane shayi baikai matsayin ruwa ba domin shi ruwa haka ake buqatarsa shayi ko sai ansa masa Lipton da suger yake shawuwa, Kalmomin qarshe da nakeson sanar dake banson jayayya akan abinda yake hurumi na dole ne idan nasaki Abu kiyishi ko bakyaso kina nunamin jin dadinki kuma komai wahalarsa idan kin gama kiyimin godiya sannan koda wasa kada ki qara kashemin waya na kira ban sameki ba saboda banson shigowa wannan lungun talakawan dole ce take biyo dani am akwai sauran dokoki da sharruda na zama dani a matsayinki na baiwa don baki isa nayi miki kallon mata ba ke kanki kin sani zan baki jadawalin ayyukanki ranar da kika tare a gdana"
Shiru ce ta ratsa ta tsayin lkc har yanzu hawayen bai daina zuba a idonta ba yayi ajiyar zuciya ganin yanda ta lumshe manyan idanunta gashin idonta ya sauka saman kuncinta abin ya bashi nishadi bude bakinsa a saitin kunnenta yace “wannan dogon surutun ma da kika sani kiyimin gdy"
*_Oum Hairan_*
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_
_*Oum Hairan*_
_*21-22*_
Sake qoqarin shigar da ita yakeyi jikinsa ta sunkuya a hankali tanajin quncin abinda yakeyi mata A ranta tace “don Allah ka kyaleni na tafi jirana akayi...." Sunkuyawa yayi ya dora hannunsa a bakinta yace “da hakan ma ni meye yasa da nabaki umarnin kije kikaqi zuwa?" Yana mgnr yana dagota ta sake lumshe idonta yayi murmushi yace “ke jaruma ce kuma mara kunya tabbas saurin kuka bai kamaceki ba" Yana fadin haka ya juya ya fice yana cewa dole kibi abinda na gindaya miki idan kinqi kuma ki sake shigar da kanki sawarwarin wahala sakarya kawai"
Bayan tafiyarsa ta jima tsugune a gurin kafin ta tashi ta fice daga gdan ta nufi gdan hajar tana zuwa ta kwanta kanta yana juya mata abubuwan da suka faru suna dawo mata nan Hajar tazo ta sameta tana tambayarta meye yake faruwa ta miqe zaune tare da jan fasali tace “wai zai aureni ne matsayin baiwa Aunty Hajar wacce irin bauta ke a cikin aure bayan wacce duk wata mace takeyi a gdanta?" Shiru hajar tayi tana nazarin kalamin kafin tace “to Allah shi dai yasan karatun Kurma kedai kamar yanda Innah taketa fada miki kiyi hqr kuma kiyi biyayya Allah bazai barki banza ba zai kawo miki dauki a dukkannin lamuranki yanzun meye ya kawoshi?"
Goge hawayenta tayi tace “akan banje gyaran