Chapter 9 Reading ZARRAH BOOK COMPLETE ROMANTIC BY OUM HAIRAN.txt Arewa Novels

ZARRAH BOOK COMPLETE ROMANTIC BY OUM HAIRAN.txt

Author :  Fauziyya Tasi'u Umar Category :  Home Of Novels

Chapter   9 / 18

24K to 27K   out of 52.6K words

sanyi ya matsa jikin gadon da sauri ya janye bargon a razane ya zubanta ido bacci takeyi amma na wuya sanye take da qaramar rigar bacci iya gwiwa yaja fasali ya matsa ya zauna a gefen gadon yakai hannunsa saman goshinta yajishi zau yayi saurin gangarawa qirjinta yaji yanda zuciyarta ke bugawa da qarfi ya janye hannunsa a razane ya dagota jikinsa yana jijjigata sai yanzun ya lura ashe bama bacci takeyi ba suma tayi sake dagota yayi yana jijjigata ganin batamasan yanayi ba ya miqe da sauri da ya fita har yana tuntube ya nufi part din Mimee ya dauko key din motarsa ya sake fita da sauri yaje ya ciccibota yasata a mota.




Duk abinda akeyi a kan idon Naja'ah tana fadawa mimee sukayi qwafa tare shikam bai masan sunayi ba yaja motarsa a guje yana tuqi yana leqenta tsoronsa na nunkuwa yanda yaji zuciyarta tana bugawa da qarfi dakansa ya sunkuceta har dakin da yake tunanin ya dace yakaita ya fara dubata ajiyar zuciya ya sauke lkcn daya tabbatar tsabar zafin zazzabin ne yasa bugun zuciyarta ya qaru, ruwa ya jorner mata yasa mata allurai ya zauna ya zubawa fuskarta ido yanajin faduwar gaba ya rasa meye yasa duk sanda ya zubawa fuskar Ma'uh ido sai yaji gabansa yana faduwa sosai kyawunta yake daukar masa ido baya gajiya da kallon fuskarta musamman cikin watannin nan da tafara zuwa school ta waye tayi wani mayen kyau me daukar hankali jikinta ya qara murjewa dake tadan qara qiba sai qirjinta ya qara cika hips dinta da bombom dinta suka qara bajewa abin yana mugun birgeshi gashi nema takeyi tafi qarfinsa da idan zai tafi office yake fita da ita ya sauketa yanzun kuwa duk sanda zai fita idan yayi mata mgn sai tace batada lecture dole haka yake qyaleta da abin nata ma ya shahara kawai sai ta daina daga wayarsa ta daina bashi damar shiga part dinta koda kuwa ya shiga to bazai ganta ba tana dakinta ta kulle abinta.
Numfashi ya sauke ya dauki alluran ya daga rigarta ya saita inda zaiyi mata ya soka mata yanajin dumin jikinsa na hauhawa yanajin wani wahalallan yanayi da yake kasancewa a ciki duk lkcn daya matseta, daqyar ya koma ya zauna ya kifa kansa a saman cinyarsa yanajin yanayin yana qara zagaya ilahirin jikinsa a hankali ya gane ashe mugun feelings nata ne yake dawainiya dashi, bai bambamce hakan ba sai tsakanin shekaran jiya zuwa yau da bashi da gurin hutawa dake a baya da mimee ko banza idan yaso kota qarfi zai karbi haqqinsa to yanzun babu dama babu lafiya.



Miqewa yayi ya fara zagaya dakin zuciyarsa na ayyana masa abubuwa da dama yaja fasali tare da qaryata kansa a fili yace “habadai tama isa kenan so nake ta qara rainani ashe ma" da wannan yaji taja ajiyar zuciya ya matsa gabanta tayi miqa tare da salati yabi qirjinta da kallo yana hadiye wasu mugun yawu ya zauna da sauri yaci gaba da kallonta idanunsa na rikida, a hankali ta bude nata idon ta fara kallon dakin kafin ta sauke idanunta akansa, lumshe nasa yayi ta yunqura zata miqe zaune daidai lkcn daya bude nasa ya sake saukesu akanta.
Tashi yayi ya matsa gabanta ya taimaka mata ta tashi zaune batare da yayi furuci ba ya koma jikin basket din daya sanya aka kawo ya hado mata tea ya miqa mata ta kawar dakai ya zubanta idanunsa fuskarsa a daure da alamun babu wasa, kawar da kanta tayi ya zauna ya diba a cokalin yakai mata bakinta taso qin sha so amma yanda ya dage din yasata dole ta rinqa karbar tea din tanasha daqyar take hadiyarsa kamar ruwan magani, ta kawar dakai yafi sau goma yana qara matsanta tasha saboda magungunan da yakeson bata aikuwa daya cika matsawa wankeshi tayi da amai da sauri ya miqe ya riqota tanata kakarin aman yana dannanta qirjinta bayan ta gama ya shiga bathroom ya wanke jikinsa ya hadanta ruwa ya dawo sai yanzun ya samu damar mgn da cewa “kije kiyi wanka zakiji qarfin jikinki" itamma zafi takeji hakan yasa ta zuro qafafunta yabisu da kallo komanta me kyau ne sai tsabar iskanci da rashin kunya dake damunta koda yake alamu sun fara ta fara laushi,
Da azamar gaske ya tarota ta fado jikinsa sabida jirin daya debeta ya sunkuceta cak ya nufi bathroom din da ita ya mayar da qofar ya rufe ya ajeta ya fara qoqarin cirenta kayan ta riqe hannunsa da sauri a galabaice tace “kaje zanyi...." Bai tsaya saurarenta ba ya kama rigar ya zare tasa hannu ta rufe qirjinta ya zubanta ido yanajin wani lugudan zucci dana jiki hakanan ta qarfi yayi mata wankan tana kuka tana komai amma yaqi qyaleta yanayi yana bama idonsa abinci duk da bai cirenta pant ba amma shatin HQ dinta ya dauki hankalinsa matuqa har hannusa yakai ya shafa gurin sai kuma ya tuna wani abu kawai ya basar............


_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_



_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_



_*Fauziyyah Tasiu Umar*_


*ELEGANT ONLINE WTITERS*




_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_



_*35-36*_




Daukota yayi kamar wata bby ya fito da ita ya bude jakkar daya dauki mata ya bata doguwar riga ta zura ya zubanta ido kamar mai karantar wani abu sai kuma ya share ya juya ya nuhi waje ya jima ya dawo da magungunan ya dubeta ya debe kayan itadai ko kallon inda yake batayi tanaji ya sake fita da kayan ya dawo yace “zamu iya tafiya gda Allurai ne guda 12 zaayi miki daya kullum har zuwa lkcn da zaki warke"
Zaro ido tayi cikin firgici zatayi mgn ya fice yana cewa “ki fito ina jiranki" dole haka taja jiki ta fito ya budenta motar ta shiga yaja suka tafi, suna tafe yana sauraron wata waqa zahirinsa hankalinsa ba akan waqar yake ba abubuwa ne da yawa cunkushe a ransa yama rasa ta inane zai fara, wani guri ya biya ya tsaya ya fita ya siyo musu gasasshen nama ya dawo yaja motar suka tafi lkcn da suka isa gda 11:30pm yana budewa ta shige dakin.


Dakinta ta barshi tsaye yana binta da kallo jin da yayi ta mayar da qofar ta danna mata key yasashi jan fasali ya nufi kitchen ya bude freegde ya sanya mata kayan daya siyo a ciki ya nufi saman ya bude dakinsa da tsayin watanni bakwai din da tayi matsayin matarsa bai taba shigansa ba, mamaki ya cikashi ganin komai dake dakin tsaf kamar dama ana amfani dashi ya bude bayin shima ya ganshi tsaf dashi yaja numfashi yace “kowa da irin baiwarsa" komawa yayi ya zauna hakanan yaji yana sha'awar kwana a part din ya jima a zaune sannan ya tashi ya shigo bathroom din ya watso ruwa ya fito ya bude wardrobe din ya dauki sabon towel ya  budeshi a leda ya goge jikinsa.



Ya koma ya kwanta yanata tunanin ta inda zai farawa Asmah tabbas lkc yayi daya kamata ya fara neman haqqinsa na aure a gurinta itama kamar ko wacce mace zuwa yanzun idan yaci gaba da kawar mata dakai to cutuwa zai farayi, miqewa yayi kamar wanda aka tsikara ya bude qofar dakin nasa ya fito parlor harya kama handle din qofar zai murda sai kuma zuciyarsa ta fara ayyana masa yanzu kamar shi yaje yace zai nemi wani abu gurin wannan yarinyar yar rainin sense ai kawai gara ya bari ya samawa kansa wata hanyar.
Aminta yayi da shawarar zuciyarsa ya koma dakin nasa ya kwanta yanata matse matsen cinya feelings na damunsa amma girman kansa na bala'i ya hanashi samawa kansa maslaha, washegari tun asuba daya fita bai dawo part dinba to itama dake ba daidai takeba bata fitoba balle tasan meye yake faruwa a daddafe tayi sallah ta sake narkewa a gado tanajin yanayin zazzabin yana sake sauko mata.



Wajen 8:30am ya shigo cikin shirinsa na tafiya office ya bude dakin ya shiga ya isketa kwance kamar ruwa ya qarasa ya janye mata blanket din ya  zubanta ido gabadaya hankalinsa yana kan qirjinta baiyi tunanin idanunta biyu ba saida yaga ta bude idonta ya sosa qeya da yanayi na borin kunya yace “kinsha magungunan?" Lumshe idonta tayi ya juya ya fita ya hado mata tea ya dauko mata tarkacen daya siyo mata jiya duka babu wanda ta taba ya dawo ya taimaka mata ta tashi zanne ya rinqa bata a baki tanaci a hankali tana hawaye gabadaya sai yaji tausayinta ya qara mamaye zucciyarsa magunginan ya ballo ya bata tasha ya gyaranta kwanciya yace “zan sake sanya miki drip idan ya qare ki cire sannan kada ki zauna da yunwa kinji" dagowa tayi idanunta ya shiga cikin nasa yayi ajiyar zuciya shi kansa yanayin da yayi mata mgn dashi ya sanyashi jin wani yanayi na daban.
Juyawa yayi ya fita ya dauko drip din ya dawo ya sanya mata yanata zuba mata sannu ya fice tananan kwance bacci har ya fara daukarta taji an shigo part din nata saida gabanta ya fadi tayi tunanin Hajja ce aka bude qofar aka shigo ta sauke ajiyar zucciya ganin Jiddarh ce zama tayi kusa da ita tace “na shiga school najiki shiru inata kiran wayarki baa dauka ba qarshe wannan miskilin mijin naki ya daga yacemin bakida lfy shine hankalina yaqi kwanciya nace bari nazo naga jikin naki" lumshe idonta tayi batasan sanda hawaye ya zubonta ba tace “ina Innata kwana biyu idan na kira wayarta bata shiga" kallonta Jiddarh tayi tace “wai kina nufin baki sani ba ai bama ta qasar tana Saudia zaayi mata aikin ido" zaro ido asmah tayi ta yunqura zata miqe Jidda ta taimaka mata ta zauna tace “waye ya biya mata?" Harararta tayi tace “kinji ki toda wa kike tunani bayan mijinki"



Hawaye ne ya zubonta tace “shiyasa kullum yake qara samun damar cimin mutunci duk mgnr da tazo bakinsa ya fadamin uwarsa ma ta fadamin Jiddarh meye yasa Innah itama takeson zama irin Mal ne basa tunanin mutunci na da qimata a gdan aure kawai biyan buqatarsu suke dabbaqawa nikam wannan rayuwar bansonta zanso ace sun hqr da talaucinsu don mutumcinsu da qimata Jiddarh yaushe ne don Allah rana zatazo? Yaushe ne nima zanyi farin ciki a gdan mijina Jiddarh yaushe zan zama cikakkiyar mace me yancin zama da mijinta tayi hira tayi dariya suyi nishadi su bawa juna farin cikine, wlh a baya bana damuwa duk da cewar nasan cewa abin zai dameni wataran amma banyi tunanin zuwanshi a wannan lkcn ba Jiddarh babu irin kirsar da banayi domin na samu kan mijina amma na kasa samu harma takai na hqr na qyaleshi amma duk da haka bana tsira daga rashin albarkarsa na gaji Jiddarh na gaji gara na kauce na samu salama shima ya samu........"




Shigowar da sukaji anyi dakin ne yasasu dagowa suka kai dubansu inda ake shigowar Hajja ce take shigowa ita da wata mata gaban Asmah ya fadi taja hijjab da sauri tana shirin sanyawa tajita a baje a qasa bata gama tantance meye yake faruwa ba taji an rufeta da duka kamar saqon Allah aikuwa tuni ta fice daga hayyacinta Jiddarh ce tayi kukan kura ta angaje Hajja tace “kutmar Ubancan wannan wanne irin rashin mutunci ne ubanme tayi miki...?" Daidai lkcn Aseem ya shigo da mugun gudu ya hawo saman dan ko motarsa bai kashe ba saboda yanda Aunty Aseemah ta kirashi ta sanar dashi cewa Hajja zata kashe yar mutane Mimee ta shirya mata qarya da gaskiya"
Lkcn daya shiga ya tarar da Hajja tana zabura zata qara dukan Asmah Aunty Aseema da Jiddarh sun kakkare asmah dake kwance a qasa kamar gawa da gudu ya qarasa ya turesu ya dago Asmah da bakinta kanta da hancinta ke fitar da jini ya fara jijjigata fadi yake “Asma'uh! Asma'uh!! Ke Asma'uh Innanillahi wa inna ilaihirraji'un Hajjah kin kasheta meye wai Asma'uh ta tare muku ne kukeson ganin bayanta....." Miqewa yayi ya dorata a gado ya haura gadon da sauri da ruwa a hannunsa ya balle bottle din ya rinqa kwara mata yana kiran sunanta yana danna qirjinta a hargitse yana cewa “don Allah ki rufamin asiri kada ki mutu wlh bansan hakan zata faru ba da bazan fita ba" sake miqewa yayi ya fara zagaya dakin Aunty Aseema da Nasmah qanwarsa suna tsaye suna kallonsa itakam Hajjah murmushi tayi ta dubesa tace “badai ni zakaciwa mutumci ba na dauki yar aminiyata na baka kai kasan Maryam ba tsarar aurenka bace amma kayi mata wannan sakayyar da danyen jikinta kai kazama dan zaki ayu sarkin jaraba bazaka zauna kayi jinyarta ba ka taho gurin wannan shegiyar yarinya to wlh tallahi yau indai ni Zainab na haifeka saika saki wannan tsinannar yarinyar kafin ta qarasa shanyemin kai ka fara dukana akanta......"




Dago jajayen idanunsa yayi da suka qanqance maqwallatonsa sai motsi yakeyi abinka da farin mutum gabadaya jijiyoyinsa sun wani mimmiqe yayi mata wani mugun kallo da yasanya gabanta faduwa ya juya zai sunkuci matarsa tasha gabansa ya sake matsawa ta sake shan gabansa tace “bakaji abinda na fada maka bane Aseem ko sai naci ubanka......
Haurawa gadon yayi ya sunkuci asmah ya nufi qofa ta riqe rigarsa ya juyo yana qara rungume Asmah a qirjinsa yace “Ina sauke miki duk wani haqqinki na uwa dake kaina babu wanda na gaza so kema ki daina shiga lamarin gdana idan ba hakaba zan bawa duniya mamaki akan wannan yarinyar wlh zan iya batawa da kowa babu abinda ya shafeni domin banga abinda ta tare muku ba iyakar rigimar Asma'uh danine ko Maryam qarya take tace Asma'uh tayi mata wani abu Hajja kina yawan furtamin saina saki asmah na rantse da girman Allah idan kika matsamin zanyi miki biyayya zanyi abinda kikeso amma kisani bazata tafi ita kadai ba dole saida yar rakiya itama Maryam din zan yanka mata ticket inyaaso saiki bata guri a gdanki..........."




_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_


_*Oum Hairan*_


[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

*

_*37-38*_

Yana gama fadin haka bai jira cewar Hajjah ba ya fice da sauri ya nufi motarsa da Asmah yasata yana shirin shiga Jiddarh ta fito ita da Aunty Aseemah suka shiga yaja a guje suka fice Hajjah da Hajiya Kubura sai kallon kallo Nasmah ta tabe baki tace “ai dama tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka natsani mace me yawan kai qarar miji wlh yanzu me gari ya waya Allah da nice Bro Saina tarwatsa nutsuwar duk wanda ya tarwatsa tawa haba Hajja duba fa yanda kika illata yar mutane yanzu baki tsoron ta mutu?"
Tabe baki Hajjah tayi tace “shine me idan ta mutun aidai an rage mugun iri a bayan qasa irin jaraba irin maita sun qalace sun nace sun lashemin kuryar yarona kuma kuma sun dawo kanku dama kece nake gani me sauqi ashe kema kinbi sahu banzaye lusarai ke kinaga wannan rawar jelar ds yakeyi na banza ne ina ai dole na miqe na shiga sabara don qwato dana daga bakin kura"

Murmushi Nasmah tayi tace “kidai bada himma idan baki shiga ba ke ashigar dake karmami ni nayi nan aure ne dai Allah ya riga ya qullah abinsa kuma shi yaji ya gani ya dauko abarsa don yanaso so kawai ki koma gefe ki zama yar kallo zaihi maki sauqi"  tabe baki Hajja tayi ta cokalo kallabi gaba tace “zaiyi bayani ne shegen yaro saina hanashi sakewa da yarinyar nan ni bazan iya masifa ba" da wannan suka koma part din Mimee suka rinqa yimata famfo abin takaici wai uwa da suruka ne memakon su nema mata zaman lafiya sai tsiyar yanda zata hana abokiyar zamanta da mijinta kwanciyar hankali suke koya mata.
Sukam su Aseem daga gda bai zame ko inaba sai asibiti yayi mata dressing gurin da Hajja ta hadanta kai da wardrobe ya sake sanyanta drip ya nemi guri ya zube yana mayar da numfashi yace OMG Hajjah tana bani ciwon kai akan yarinyar nan wlh" dafashi Aseemah tayi tace “kayi qoqarin daidaita tsakaninka da matarka kaba wofi da tafi banza ajiyarsu idan har kuka samu fahimtar juna da Asmee zaka samu sauqin abubuwa" sosai yasan shawarinta gaske ne so amma tambayar da yake yiwa kansa ta ina zai fara daidaita kansa da asmah bayan tanayi masa kallon wani qaton Azzalumi wanda take addu'ar samun sanadin rabuwa dashi koda ta hanyar katsewar rayuwa ne?" Wata gajiyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace “hakane" kawai ya miqe binsa Jiddarh tayi tace “idan fita zakayi ka saukeni a bakin titi na koma makaranta yau zamu cike takardar practical" tsayawa yayi da mamaki lallai Asmah da gaske gaba takeyi dashi wato da yace idan lkcn practical dinsu yayi ta sanar dashi zai sama mata gurbi a hospital dinsa shine ta watsa zancensa a kwadon shara,

Jinjina kai yayi ya shiga motar Jiddarh ta shiga suka nufi makarantar dake private medicine school ce baisha wahala ba wajen yin duk abinda yayi niyyah aka bashi Asmah da Jiddarh zuwa asibitinsa yaji dadin hakan ya koma gidansa lkcn daya shiga mimee na daki taji shigowarsa amma jin barusar da mahaifiyarsa tayi yasa tayi qus har yayi wankansa ya sake fita bata fito ba
Tun tana jiran dawowarsa harta gaji ta fidda rai ta kwanta tana tunanin inda zatayi da Asmah itafah a tsarinta da yanda take kallon kanta ji takeyi wannan ai qasqanci ne ace mijinta bashi da lkcn ta saina wata banza a gefe to waima yaushe ne tayi saken da har mutane suka rigata gane mijinta yaudararta yayi da dadin baki yakece mata babu abinda zaiyi da wannan yarinyar ashe tuni ma yarinya ta gama da zucciyarsa koda yake sauqin da takeji da akace mayya ce lashe masa kurwar tayi yanzu burinta kawai ta warke ta bazama neman yanda zatayi ta batadda Asmah a cikin rayuwar mijinta.
Tana wannan tunanin wayarta tayi ring ta daga ganin number sace yasa gabanta faduwa ta koma ta zauna gabanta na faduwa har saida wayar ta katse sannan ta daga .yaja iska ya furzar  yace “ya jikin naki?" Ajiyar zuciya ta sauke meqarfi tace “uhm! Da sauqi ina ka shigane tun dazun nakeson ganinka" murmushi yayi yace “wai dayake jiya na kwana da Asmah so batada lfy ne shiyasa nakaita asibiti gashi mahaifiyarta bata qasar balle ta tayani jinyarta dole ni nake zaune da ita"



Mimee ji tayi kamar zuciyarta zata hantsilo tsabar tuquqin da

9 / 18