Author : Fauziyya Tasi'u Umar Category : Home Of Novels
jiki bane" harararta hajar tayi tace “ai dama saida aka fada miki baki gaji da zubar da hawaye bane shiyasa kikeqin daukar shawara kije kiyi abinda kikaga ya dace dake namiji ya aureka ma don qauna yaka qare bare wannan da ya aureki don gayya kada ki saita zamanki kije kina raba hali kishiyarki ta fahimci baraka tsakaninki da mijinki kigani in zakikai labari"
Sosai kalaman hajar ya kashe mata jiki tabbas wannan way din data dauka ba mafita bace gareta miqewa tayi ta zari hijjab dinta ta fice ta hau napep ta nufi gurin kwalliyar cikin saa taje angamawa kowa kawai aka hau yimata abinka da fata me kyau itan tafi kowa daukan kyau, hakanan bayan an gama suka tafi sai zuba qamshi sukeyi suna zuwa suka tarar ankawo kayan Dijangala da Rabi kayan sun gaji da haduwa kowa sai kodawa yakeyi.
Ko kallo basu isheta ba tayi shigewarta ta kwanta washegari aka shiga hidimar biki gadan² kowa yanata warkajami banda ita domin kuwa kowa daina kulawa tayi batada abokin hira sai wayarta itanma da taga zaa dameta take watsarwa tayi kwanciyarta a ranar ma saida sukakai ruwa rana kana ta yarda sukaje lalle da gyaran gashi yamma liss suka dawo juma'ah da safe aka kawo mata kayan dinner a wata qaramar akwati kayan sunyi kyau matuqa da yamma Aunty Aseemah ta turo aka dauketa bayan kwalliyar da sukaje akayi musu ta kuma gyarata tasa akayi mata shiri na musamman domin ita a ranta yanzun takejin qaninta yana aure domin wancan auren zabin mahaifiyarsu ne wannan kam duk da yana iqirarin bayaso tasan zabinsa ne.
Daganan aka daukesu qarfe Shidda sai gurin dinner din ashe shima gurin dinner din uku ya kama nasu shine na musamman tare kuma a lkc daya motansu ya tsaya aka bude masa ya fito itanma aka bude mata ta fito suka hade a tsakiya sauti me dadi yana tashi itadai banda hawaye babu abinda takeyi tasan daga gobe shikenan kashinta ya bushe a hannunsa, tana tafe tana layi har suka isa mazauni anan akayi kamu da duk wata bidi'a sannan aka fara gabatar da dinner din suna zaune zaman kurame babu me cewa wani qala tsakaninsu wayarsa tayi ring ya zaro a aljihunsa ya kara a kunnensa bataji abinda akace ba tadaiji yace “ok ganinan"
Miqewa yayi ya dubeta kamar zaiyi mgn kamar wanda ya tuna wani abu yayi gaba abinsa tabi bayansa da kallo take MC din ya fara babatun “toh amarya ya haka kika bari ango ya fice wasa bai qare ba?" Wasu hawayen baqin ciki suka zubo mata ta miqe itama da sauri ta nufi hanyar fita da sauri Jabir ya riqota yana girgiza mata kai ta watsa masa wani kallo da yasashi sakinta yace.
“Kiyi hqr kiran gaggawa ya samu a asibiti shiyasa" bata saurareshi ba ta hankadeshi ta fice wannan abu yabawa kowa haushi a gurin da mamaki kowa nata fadin albarkacin bakinsa itakam tana fita ta tsari napep ta fada masa inda zai kaita tana zuwa gda ta fada dakin Inna ta zube a jikinta ta rushe da kuka sosai hankalin Innah ya tashi daqyar ta samu tayi shiru ta lallabata ta fada mata meye ya faru, murmushi Inna tayi tace “banda abinki Ma'uh lfy ai tafi komai kada kisa wannan a ranki komai zakiyi kiduba girman Allah ki zauna da mijinki lfy ki fahimceshi kinji" sake kwanciya tayi jikin Inna tana sauke ajiyar zuciya tace “Innah wlh inajin tsoron mutumin nan bashida tausayi kuma ni nasan ba domin allah ya nacewa aurena ba"
Ajiyar zuciya Innah tayi taja bakinta ta tsuke tanaci gaba da shafa bayan Asmah, a haka bacci ya dauketa lkcn goma ta wucce daqyar Innah ta gyaranta kwanciya da taimakon Innah Azeezah a daren Jabir yake fada masa abinda ya faru baiji haushin kansa ba sai ita yayita kiran wayarta tasata a silent ya kira yakai sau uku bata dagaba dole ya hqr amma rainin yarinyar yanacin zuciyarsa ranar kwana yayi yana huci Mimee na kallonsa bata kulashi ba don ta fahimci a yan kwanakin bashi da fushin daya wucce Asmah sai wajen biyun dare sannan ya kwanta shima kiran wayar bai daina ba cikin saa kuwa ta daga cikin mayen bacci bai bari tayi mgn ba yace.
“Ke wacce irin mara tarbiyya ce da zaki jizgani a cikin abokaina kinsan su waye a gurin kuma kinsan dalilin da yasa na tashi nabar gurin ne shashasha sakarya mara tarbiyya....." Qit yaji ta kashe wayar ya miqe zaune da sauri yana kiran wayar yajita a kashe gabadaya yaja wani huci tare da cilli da wayar ya miqe kamar wanda aka tsikara ya zari mukulli sai kuma ya kalli agogo yaga uku saura wata ajiyar zuciya ya sauke ya koma ya zauna yana dafe kai yana mayar da numfashi a fili yace “saura 7 hours zakiyi bayani duk wani iskanci da kike ji dashi zaki saukeshi a gidan matsiyatan iyayenki" Komawa yayi ya kwanta
Tunda ta farka taga kiransa ta kasa sake rintsawa wai yar marasa tarbiyya ta jinjina kalmar nan tafi sau hamsin kafin ta sake kwanciya wannan wanne irin miji Allah ya zaba mata da wannan tunanin ta tashi kawai tayo alwala ta tayar da sallah ta jima tana roqon Allah ya cire mata jin ciwon kalaman Aseem a ranta ya sassauta mata zuciyarta ya bata ikon yi masa biyayya koda zata cutu matuqar bata sabawa shari'ah ba
Da safe kuwa kamar yanda suka tsara hakance ta faru qarfe goma masallacin dake kusa da gdan Mal Hussaini ya dinke maqil da dandazon al'ummah saida aka fara daura auren Rabi'ah da angonta Mansur sannan na Dijah da Khamal sai na Asma'uh da Dr Aseem Shaheed nan gurin ya dauki kabbara maroqa suka rinqa zubawa angwaye kirari a cikin gdan kowacce amarya murna takeyi amma banda Asmah da tayi laqwas ta lafe jikin gado idanunta na saman silling hawayenta tun daren jiya yaqi tsayawa dukkan wata kalmarsa babu me dadin da zata tuna tasata farin ciki a daidai wannan lkcn a ranta tanajin yanzu da bai rabata da Sadiq dinta ba da yanzu itama tanajin irin Happy din da yan'uwanta sukeji, itadai haka ta yini bata iya tsinanawa kanta komai ba sai kuka ko kwalliya taqiyi qarfe Hudu kuwa motocin daukanta sukazo lkcn daqyar Mal Hussaini yasata tayi wanka aikuwa tanajin ance ita akazo tafiya da ita ta rushe da kuka me dukan zuciya ta qanqame innarta tana mata magiyar kada ta bari a tafi da ita idan aka tafi da ita waye zaike yiwa Innah aikin gda,
Duk rashin tausayin Mudan ranar saida qanwar tasa tasashi kuka daqyar ya bambareta jikin Innah yasata a mota ya rufe tana kuka tana kiran sunansa shima hawaye yake sharewa hakan motocin suka daga suka dauki hanyar Shagari quarters horn sukayi aka bude musu get Aunty Aseemah ta bude musu bangaren amarya Asmah har zuwa lkcn shassheqar kuka takeyi sukuwa yan kawo amarya lalacewa sukayi a kallon wannan katafaren falo basu qarewa duniya kallo ba saida suka haura saman me dauke da madaidaicin falo da dakuna biyu sun bawa ido abinci sosai.
Dake ba yawane dasu ba kasancewar yace kada a wucce mutum biyar haka suka zaunarta a saman carpet din dake tsakiyar dakin jikin gadonta suka farayi mata sallama suka fice hatta Jiddarh ficewa tayi tabisu aka barta ita daya tanata aikin kukanta me ban tausayi, kusan awa uku tana zaune ita kadai tun biyar har tara sannan taji tsaiwar mota a harabar gidan qirjinta ya buga da qarfi ta koma ta sake lafewa dukan qirjinta na qaruwa daidai lkcn da taji an bude qofar an shigo an sake murda ta dakin an shigo qamshin turarensa ya daki hancinta ta sake narkewa inda shikuma ya tsaya akanta yana qare mata kallo, yafi 5 minutes yana kallonta kafin yayi wani murmushi yace “waike nan kin yarda amarya ce ke ko? Hmmm yarinya kinyi kuskure babba da kika yarda kika fado komata tabbas zaki fahimci bambamcin da kika kasa ganewa, am ba bata lkc nazo ba ga wannan ki taba nasan qila rabonki da nama tun sallah sorry karki damu da sai kin biya bana buqata kasancewar qyanqyaminki nakeji, abu daya da zan fadanki shine idan kin tashi kullum da safe kinada aiki a gdannan, ki shiga wancan part din ki gyarashi sosai sannan ki samawa matata abinda zataci am tanada qaramin ciki ne bata aikin komai saboda tanada matsalar mahaifa tana buqatar tausa kuma batason ta inji so duk sanda ta buqaci tausa kiyi mata har sai tace ya isa haka ina fatan kin gane?".................
_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_
_*Fauziyyah Tasiu Umar*_
_*23-24*_
Juyawa yayi ya fice daga dakin yaja qofar ya rufe ta miqe ta bude labule tana kallonsa ya bude dayan bangaren ya shiga ya mayar ya rufe taja fasali tare da ajiyar zuciya ta koma ta bude ledar gasasshiyar hanta ce da taji kayan lambu sai qamshin takeyi dayar ledar kuma kaza ce itama ta hadu taja fasali ta zauna da farko kamar kartaci zuciyarta ta raya mata garama taci rabonta ne idan bataci bama ba gwaninta zatayi ba.
Sake budewa tayi ta dauki hantar takai bakinta saida taci iyakar cinta ta kora da lemon ta miqe ta cire mayafinta ta shiga bathroom ta bata lkc tana kallon bayin tana mamakin irin tsaruwarsa kafin ta dauki sabon brush ta bude ta matsi man goge haqori ta wanke ta cire kayanta ta fara kokawa da shower ta hada ruwa tayi wanka ta fito ta shafa mai ta bude wadroop din ta dauko doguwar rigar bacci tasa ta karkade gadon ta haye taja bargo tayi kwanciyarta.
Baccinta tayi cikin kwanciyar hankali saboda gajiyar biki bata farka ba sai safiya ta tashi tayi wanka tayi sallah tana saman sallaya taji an taba qofar ta juya ta kalli qofar jin shiru baa qara tabawa ba yasata tunanin babu kowa taxi gaba da lazuminta sake taba qofar ne yasata miqewa tana tambayar “waye" ba ayi mgn ba ta bude qofar taja da baya da sauri Aseem ne tsaye cikin shirinsa na tafiya aiki da tarkacen laptop da takardu a hannunsa.
Qasa tayi cikin ladabi tace “ina kwana" Idanunsa ya dauke daga kanta ya juya ya fara tafiya saida ya kusa step din benen sannan yace “Mimee tana jiranki kije ki hada mata break" wani abune ya caki zuciyarta tana kallonsa ya fice hawaye suka sulalo mata na baqin ciki wannan baqin qasqanci da mahaifinta ya siya mata Allah wadarai dashi, komawa tayi ciki ta dauki wayarta da keta ring ganin number ya mudam tasan Innah keson mgn da ita ta kara a kunnenta a sanyaye, yanayin yanda tayi sallama ya tabbatarwa Innah ba qalau ba taja ajiyar zuciya tace “ya akayine ma'uh na?" Cikin kuka ta durqushe a qasa ta kwashe duk abinda Aseem din ya fada mata ta sanar da Innah Sosai Innah ta girgiza dajin wannan qasqanci da rayuwar Asma'uh ta tsinci kai a ciki amma a fili sai tace “duk a cikin ibada ne kiyi hqr zakiga ribarsa a gaba don Allah badon niba ki mayar da komi ya zama ba komi ba koda anyi abinda ya kamata ki kalla ki kawar dakai wataran sai labari"
Cikin mutuwar jiki tace “yanzu Innah yimata zanyi?" Murmushi Innah tayi tace “qwarai kuwa yi zakiyi domin Allah ai lalura ta kori komai kema wataran zata taimakeki" haka inna ta rinqa tausar Asmah hardai ta hqr ta saki ranta ta miqe ta dauki hijjab dinta ta nufi part din Mimee ta qwanqwasa aka bata izinin shiga ta bude ta shiga cikin nutsuwarta me tsayawa a rai tayi sallama, a qasan maqoshi mimee ta amsa tanajin wani kishi na taso mata duk yanda su Saimah sukazo suke koda kyawun matar yayan nasu ganin idonta sai taga tafi haka duk da kasancewar ba fara bace amma a sahun kyawu dole ta karbi lambar yabo.
Rusunawa tayi tace “Ina kwana Aunty...." Numfashi Mimee ta sauke tace “normal ina fatan Honey ya zayyana miki aikinki a gdannan ko?" Jinjina kai tayi Mimee tayi murmushi tace “ok sai a tashi a fara ina buqatar kunun tsamiya ne da qosan bread" miqewa tayi ta fara neman kitchen din ta nuna mata tace “ai basai kin wahala ba da part dinki da wannan duk iri daya ne bambamcin kawai a matsayi yake " duk da Asmah tasan mgn Mimee ta fada mata bata kula ba ta nufi kitchen din a hargitse yake gabadaya kayan sunyi qura ta jinjina kai ta lalubi tukunya ta dora ruwa ta rinqa bude kitchen cabinet din har allah yasa ta samu duk abinda take buqata ta hada ruwan kununta sannan ta debi surfaffen wake tasa masa ruwan zafi ya tashi ta hada tattasai da albasa da attaruhu da duk abinda tasan zata buqata ta wanke ta zuba a blander, a wannan lkcn ilimi ne kawai yake aiki bawai sani ba duk kayan aikin baqine a gurinta hakanan dai ta ganganda ta gama hada komai ta Jere a dinning din ta koma kitchen din ta fara gyaransa saida ta gyareshi tsaf ta wanke kayan da sukayi qura ta mayar dasu muhallinsu sannan ta fita parlor shima ta gyara tayi duk abinda ya dace sannan ta juya zata tafi taji Mimee dake zaune tana kallo tace “ki hau sama ki gyara masa dakinsa"
Tuni wani riqaqqen baqin ciki ya cika zuciyarta taji kamar tayi tafiyarta kalaman Innah ne kawai suka sata juyawa ta nufi saman ta bude dakin farko Allah kuwa ya taimaketa shi dinne ta shiga ta fara gyarawa saida ta gyareshi tsaf kayan da ya cire duk ta ninke tasa a kwandon zuba kayan wanki ta wanke bathroom ta fesa turare ta janyo ta fito ta rusuna gaban mimee tace “na gama" daganta kai kawai tayi ta juya tayi tafiyarta ta koma nata part din ta gyara ta nemawa kanta abinda zataci ta dawo ta zauna a parlor ta kunna kallo tana kallo tana karyawa bayan ta gama ta haura saman tayi wanka tayi kwanciyarta
Wayar tace ta dauki ruri ta daukota ta duba taja ajiyar zuciya Dijanta ce ta kara a kunnenta tayi sallama dijah ta amsa da sanyin murya tace “inanan inata tausayinki ance mazan da sukasan dadin mace sunfi rashin tausayi a daren farko Ma'uh nikam naci wuya ji nake kamar kar a qara" sarai ta gane inda ta dosa tayi dariya me qarfi tace “lallai inayi murna kice har Ali yaga Ali?" Ajiyar zuciya Dijah tayi tace “yanzu ke haka kuka kwana yana kallonki kina kallonsa duk irin maqudan kudadan daya kashe Allah bai fanshe ba?"
Numfashi taja tace “nifa banson gulmarki nan ina ruwanki tunda kedai anyi miki abinda kikeso" sanin hali yasa Dijah cewa “kekam kin fiya masifa daga na kiraki mu jajantawa juna zaki kama yimin fada to ai shikenan sai kiyita yi nidai nazama cikakkiyar mace yarinya ko iyanan alamu sun nuna nafiki" murmushi tayi tace “to meye na gorin abinnan da ba dambe ba kowacce mace ma tana zuwa gurin lkc dai igiya uku ke gareki nima itace dani saboda haka banga bambamcin ba".........
Kashe wayarta tayi ta gyara kwanciyarta tasha bacci sosai har wajen daya sannan ta tashi tayi sallah ta gyara gadonta ta nufi part din Mimee har yanzu tana kwance inda ta barta mamaki ya cika Asmah tayi mata sannu da gda ta dago ta kalleta saida gabanta ya fadi ganin irin kwalliyar da Asmah ta caba cikin wani tsadadden less dake cikin lefenta, sarai take kallon Asmah tun daga sama har qasa ta zubawa hips dinta ido tuni Asmah ta fahimci kallon qurillar da takeyi mata tayi qaramin murmushi a ranta tace “jira dai madam ba damuwata mijinki ba amma dole ne kisan nafi qarfin matsayin da kuka ajeni"
Dagowa tayi tace “me kike buqata?" Iska Mimee ta furzar ta qanqance ido tace “kewai bakisan matsayinki bane a gdannan? Waye ya baki damar kwalliya?" Dagowa tayi ta dubi mimee tace “wai dake naji sunanmu daya a duniya Matan Dr Aseem Shaheed shiyasa nabawa kaina yancin kwalliya a gdan mijina....."
Wata muguwar tsawa mimee ta daka mata tace “Ubanwa yace miki matsayinmu daya dake yar matsiyata? Ke mece a mata da har zaki hada kanki dani??" Abinda Asmah takeso kenan ta juya cikin salonta na iskanci tana kada mata mazaunai tace “In kinga dama ma ki kirani da tafi haka nidai inajin kaina matsayin matar Mijinki bawai isar ki ce tasa na qudurta yi miki wannan aikin da kuka bani ba not sister tausayinki ne a matsayinki na patient kuma naji mijina yace cikine dake zaki haifa mana sanyin idaniya" tsayawa tayi ta juyo tace.
“Bari kiji wani abu ko Maryam naso ko bataso Asma'uh ta Aseem Shaheed ce zabinsa ce sannan inayi ne don farin cikinsa tabbas zanyi komai indai zaisa mijina abin alfaharina Happy domin nasan zamusha mango harda gwanda ke har water milon zan yanka nabashi a baki....."
Dafe kuncinta tayi da sauri ta dago sukayi ido hudu da Aseem dake tsaye, ya hade rai sai huci yakeyi maimakon tayi qoqarin yin wani abu sai kawai ta shammaceshi ta fada jikinsa ta qanqameshi ta rushe da kuka, raunin Aseem kenan A duniya baya qaunar kuka a cikin kukanma ya rasa masifar da tasa indai Asmah zatayi kuka sai yafi dagansa hankali fiye da yanda kukan kowa yake dagansa.
Sake qanqameshi tayi tana tura masa nononta a qirjinsa tuni baisan sanda ya dagata ba cak ya nufi saman da ita Mimee na tsaye sake da baki tana kallon ikon Allah suna shiga ya ajiyeta saman resting chair ya fada bathroom ya sakarwa kansa ruwa a ransa yanajin zafin kukan da ta zauna tanata rerawa har wani qara sauti takeyi, badan ya gaji da wankan ba ya dauro towel ya fito yace “oh gud ki daina wannan kukan haka na fada miki banso ko?" Ajiyar zuciya ta rinqa jerawa ya tsugunna gabanta ya kamo hannunta yace “ki daina yi mata rashin kunya duk abinda zakiyi ya tsaya iyakar ni dana daukoki" miqewa tayi zata fice ya fincikota da qarfi ya hadata da bango ta saki qarawa hawayenta qarfi tanajin sanda yasa hannu ya shafa shatin inda ya maretan yace