Chapter 4 Reading ZARRAH BOOK COMPLETE ROMANTIC BY OUM HAIRAN.txt Arewa Novels

ZARRAH BOOK COMPLETE ROMANTIC BY OUM HAIRAN.txt

Author :  Fauziyya Tasi'u Umar Category :  Home Of Novels

Chapter   4 / 18

9K to 12K   out of 52.6K words

saboda an rainamin hankali...." Jin takun sawayen Mal Husaini yasata shigewa qarqashin gadon qarfen Inna tana kuka ya shigo dakin yana huci Yana cewa “kajimin mutane yan baqin ciki arziqi yazomin har gda Allah ya amsa addu'a ta Nima nakusa hutawa shine zakuyimin baqin ciki tabdi ai wlh baku isaba wannan aure me hanashi saidai mutuwa idan ma mutuwa zakiyi saidai ki mutu ja'irar yarinya kina tafe kamar ki karye saboda rama yo kika sake kika auri Wannan Dan gadon talaucin da ubansa tunda nasanshi da tàgiya daya nasanshi basai kin qwammace wannan makauniyar uwar taki barinki tayi ba"





Harya gama sababinsa ya fita Inna batace komai ba sai bayan ya fitane Asma'u ta fito tanata shassheqar kuka Inna tace “wai waye wannan ne daga zuwa Mal ya aminta dashi Babu binkice Babu komi?" Nan Asma'u ta yiwa Inna bayani Inna ta saki salati da sallalami tare da yiwa Allah kirari tace “naga takaina ni aminatu dama akan wannan kwasasshen mutumin Mal yacimin mutunci har Yana cimin alwashin aure Babu fashi aikuwa da fashi don baza'ayi wannan son zuciyar dani ba yaro shekara da shekaru Yana wahala Rana tsaka saboda son abin duniya Mal ya rufe ido yana cima mutane mutumci ai bake kadai ya haifaba yabasa wata Amma bake ba"




Dayin magariba kuwa saiga Kiran Sadiqu a qofar gdansu idanun Ma'u sun kumbura sunyi luhu² saboda kuka ta yafa mayafinta ta fito shima duk a hargitse yake yana ganinta ya riqo hannunta yace “Asma'u meye ne ke Shirin faruwa dazu Baffana yayimin kiran gaggawa naje yake fadamin Wai saqone daga Mal babuni Babu ke yayi miki miji hakanne da gaske Ma'u rabani zaayi dake?"
Kafin ta gama shassheqarta ta dago sukaji daga bayansu muryar Mal Yana cewa “eh hakanne babu Wai a ciki nama rabaku har abada indai nine mahaifin Asma'u to babukai Babu ita nayi Mata miji daidai da ita kaima kaje ka samu daidai dakai dama ai a rashin uwa ake uwar daki tunda uwa tazo kuwa dole uwar daki ta kauce soko kawai me hatimin talauci a goshi"




A sanyaye Sadiqu ya tsugunna gaban Mal Husaini yace “Kada kayimin haka Mal wlh idan ka hanani Asma'u kamar ka datsemin farin cikin rayuwa ne ka taimakeni kabarni da Asma'u nayi maka alqawarin Bata farin ciki fiye da Wanda kake hango Mata a Wanda kake Shirin aura Mata Mal baisan darajarta ba kamar yanda na San...."
Tsawa Mal Husaini ya buga Masa yace “kajimin yaro sakarai Shashasha aiyo wato Nima kana nufin kafini sanin darajar Asma'u ko to kaji in fada maka ba daraja ba ko alqabba ne Kai qarewar daraja Asma'u ba rabonka bace, kekuma munafuka na dawo kanki daga yau sai yau idan na qara ganinki da wannan faqirin yaron me riga daya saina Saba miki. Zaki shige gda kosai na karya qafafunki" a guje Asma'u ta fada gda tana kuka inda ta ishe Inna tana sallah fadawa tayi saman gadon qarfen Inna Mal Husaini ya biyota Yana cewa “wato Ni akeson a tozarta a garin nan a mayar dani sakaran uba da Bai Isa da gdansa ba ko to wlh baa isaba dole ne nasa doka abi ke Aminatu kin rainani Ina fada da babbar murya duk ranar dana qara ganin Ma'u da wani a Aseem ba sainaci mutuncinki wlh saikin gwammace baki sanni ba domin ranar ne zaki gane Nima namiji ne talauci ne yasani zama mace wawaye kawai masu qashin tsiya
[20/06 4:30 pm] Oum Hairan: *_ZARRAH_*



*_Oum Hairan_*


*_13-14_*





Tunda Asmah ta taji wannan hadi da mahaifinta ya shirya yi mata ta shiga  dimuwa da tashin hankali abubuwa suka jagule mata ta shiga  tsananin damuwa abubuwa duk suka rikice mata ta kasa gane ta Inda aka samu asalin barakar sosai take cikin qunci,
A bangaren Dr Aseem Shaheed jinsa yake  cikin walwala sabida ya samu yanda yakeso mahaifin  Asma'u sai ladabi yakeyi masa shima kuwa ya sakar masa kudi tunda ya fahimci kwadayi ne dabi'arsa tuni yasa aka fara gyarawa Mal Husaini gidansa tunma kafin a gama daidaita tsakaninsa da yartasa.
Itakuwa Innah tsallle tayi ta dire tace bada itaba bazaa taba yaudarar Sadiqu da itaba yaron tun asmah batasan kanta ba yakeyi mata wahala sai yanzu rana a tsaka wani yazo a dauki aure  a bashi wannan ai  rashin adalci ne, sosai Asmah ta samu goyon baya gurin Innah hakan ya dan  kwantar mata da hankali kadan.


Karatunta ta mayar da hankali tare da cin alwashin duk ranar da Dr Aseem ya kuskura yazo qofar gdansu saita tata masa asalin rashin mutunci, sati guda da zuwansu na farko tana kwance a dakin Innah abin duniya yayi mata zafi qarfi da yaji Yaya Mudam ya hana Sadiqu zuwa gurinta  saidai  su hadu dashi a burtsatse su tsaya suyi yar  hirarsu babban tashin  hankakinta yanda masoyin ya rame  yayi duhu da sun hadu sai ya fara yimata magiyar karta yarda a rabasu  a mafi yawan lokuta suna kuka suke  rabuwa duk da cewa Asmah bata gama gasqata mgnr auren ba,
Hakanan aketa gyaran gdansu ita  kuma tanaci gaba da zuwa makarantarta har tsayin watanni biyu sosai rayuwa ta fara canzawa a gdansu mal Husaini har buhun shinkafa yake  ajiyewa inda  itakuma a haukanta ta fara mantawa da aikin dake  tunkarota. Kwatsam ranar Wata alhamis sun dawo daga  tahfiz ita da Jiddarh Jiddarh ta biyo zata karbi wani text book.



Tun daga  nesa  ta hangi  wasu  manyan motocin alfarma a qofar gdansu guda hudu hakanan gabanta ya yanke ya fadi suka kalli  juna cikin sanyin jiki daidai lkcn da wasu  fararen dattijai suke fitowa daga  soron gdan nasu ta zubansu ido tanason ganesu amma ta kasa sai ajiyar zuciya kawai data suke ta rabasu ta wucce sudinma binta  sukayi da kallo.
Itadai ko arziqin gaisuwa basu samu ba tayi shigewarta gdan garama Jiddarh ta gaishesu suka shiga tabata abinda zata bata ta fito ita kuma ta dauko  buta  ta fito, mamakine ya cikata ganin matan  gdan nasu da yaransu Dijangala da Lantana a tsaye  cirko cirko to dake  ba shiri suka cika ba hakanan tayi shigewarta bandaki tanajinsu sunaja mata tsaki bata ko kallesu ba, fitowa tayi ta shige dakin Innah ta ishesu ita da mudam da Mal Husaini suna tattaunawa,
Kallonta mal Husaini yayi yace “nemi guri ki zauna duk na gama mgn da yan'uwanki kece kikeson ki bani matsala  kuma ke  dinma baki  isaba"


A gajiye ta nemi guri ta zauna Yaya mudam ya zabga mata harara ta sunkuyar da kanta Mal yaci gaba da cewa “dazu iyayen Aseem sunzo akan batun aurenki sun kawo kudin aurensu da sadaki sannan  sun nemi alfarmar ayi biki nan da Wata biyu dadai  nace  Wata biyar  nasa so munyi mgn dashi Aseem din yacemin babu komi zai dauki nauyin komai wannan tasa  da naga sauqi yazo na amince...."
Dagowa tayi da Sauri tace “Baffa Sadiqun fah...." Jitayi an buge mata baki ta dago da idanunta daya  kawo ruwa take ta fara tsiyayar da hawaye Mudam ya nunata da yatsa  yace “shegiya me qashin tsiya arziqi na kiranki tsiya na cewa nice taki  ana mgnr arziqi kina mgnr talauci ubanme Sadiqu zaici bare ya baki gayyar tsiya gayyar wahala....."


Dagansa hannu Baffa yayi yace “yo miye na bata bakinka abuda babu fashi  sai anyi  kawai kije ki fara shiri nanda watanni biyu zan daura muku aure kowa ta kama gabanta" miqewa sukayi zasu fita  cikin gunjin kuka  Asmah tace “Innah bazakice komai ba don  Allah kiyi wani abu...." Janyota Innah tayi jikinta tana Shafa bayanta sukayi ficewarsu sannan ne Innah tasamu  damar  mgn tace “to me zance Ma'un Innah kinji irin  diban  albarkar da Mal yayimin yau har yana cewa nice nake  zugaki kiqiyi masa biyayya, Asma'uh wannan lamari son zuciya ne saidai kawai Allah ya sakawa wanda  aka zalumta kiyi hqr kiyi biyayya insha Allah zakiga Ribar hakan a gaba"
Kwantar da kanta tayi a jikin Innah tace “wlh Innah badon  Allah Aseem yakeyin duk abinda yakeyi ba akwai manufa cikin lamarin nan Innah kada  kibari son zuciyar su Baffa ya salwantar min da rayuwarta......"



Rufe  mata baki tayi tace “Asmah kiyi hqr kuma kisa  kyakkyawar niyya a ranki  insha Allah Ribar abin zaki gani" sosai Innah ta rinqa yima Asmah nasiha hardai ta daina kukan ta koma  ta kwanta  lamo akan gadon Innah tanajin zafin abinda Baffa yayi mata shi bayama  jiye mata wulaqanci?
Ranar ko diban ruwa kasa zuwa tayi saboda zazzabin da yake  damunta




Washegari juma'a duk da batajin dadin jikinta haka ta shirya ta fita domin zuwa makarantar daga  yanayin takunta Indai kasanta zakasan akwai  abinda yake damunta, cikin saa tana zuwa gdansu Jiddarh ta ishe  ta shirya suka nufi makarantar a qafa suka tafi  domin dukkansu babu mai kudin Mota suna tafe ne tafiya irinta kurame babu me cewa wani, sunci rabin  tafiyar sukaji Mota a bayansu tanayi musu horn basu  tsayaba saidai kaucewa da sukayi suka bawa mai motar  hanya, zartasu yayi sannan  ya tsaya tare da kashe motar ya fito cikin shigarsa ta likitoci fuskarsa dauke da murmushin da shi daya  yasan ma'anarsa ya tako  inda  taja  ta tsaya tana qare  masa kallo batayi aune ba kawai saiji tayi ya sanya  hannunsa ya dago fuskarta ya dora  bakinsa saman kuncinta ya janye a hankali yana murmushi  yace “to ya kikaga salon wasan  namu?"



Takaici ne yasa batasan sanda  wasu  hawaye masu  zafi suka zubo mata ba murmushin fuskarsa ya fadada yace “tun yanzu? Haba  karki karaya da wuri mana aike jaruma ce  kin iya  rashin kunya zaki qwaci kanki dadin dadawa gashi kinyi saa  gyatumai kwadayayyu Allah ya baki kada  ki matsawa zuciyarki wajen tunanin abinda ya dace duk wani Abu da yake ya dace nayishi bayan iyaye shima masoyin na bogine  tunda ya siyarmin da soyayyar a farashi me arha dubu dari  da hamsin kacal kinga ko yanzu zaki iya  bambamce tazarar dake tsakaninmu koda yake banson  ma ki gane  yanzu ki bari sai can gaba saiki gane  lkcn da hakan zaibada show na gaske a lkcn ne wasan zai fara nanda 2 months yanzu sharar fage ce"..........

_Gareku yan'uwanmu na Niger kuma fah kuna  da damar  samun wannan littafan guda biyu idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_


*_Oum Hairan_*
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*




*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*





Littafin _*_ZARRAH* na kudine idan kinason zaki biya 200 ta _account dina_
__0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTBank_ _ko kati MTN ta whattsAp a wannan number 09013718241 ko VTU ta wannan number 09031307566._


_Gareku yan'uwanmu na Niger kuma fah kuna da damar samun wannan littafan guda biyu idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_



*_15-16_*



*_Last Free page_*




Sosai hawaye kibin kuncinta tana qara saita injin idonta akan Aseem kallo takeyi masa da yake bayyana tsantsar tsana dajin haushi da kuma tausayin kai tasan duk duniya ba kowane yaja mata wannan wulaqancin ba face Mal, numfashi ta sauke kawai ganin wankin hula na neman kaita dare ta juya ta canza hanya ta tafi tabarsa tsaye yana bin bayanta da kallo yana murmushin mugunta shikadai tasan abinda yake saqawa a zuciyarsa yarinyar ta gama lalacewa idan ta zama mallakinsa zai nuna mata iyakarta zai nuna mata duniya da bambamci.
Komawa yayi yatada motarsa ya tafi sai lkcn Jiddarh ta lura da cewa ashe Asmah ta jima dayi mata nisa tabita da sauri tana qwala mata kira bata tsaya ta saurareta ba sai a cikin makaranta suka hadu bayan an gama assembly suka tafi ajinsu Jiddarh ta dubi asmah tace “wato Allah idan yana sonka da arziqi sai ka zagi sarki a gaban fadawa yace gaisheshi kayi wlh Asmah a rayuwata na dade banga kyakkyawan namiji irin Aseem Ba kayy gsky kin dace, amma fah da alamun dan izzar masifa ne zakisha fama...."



Wani naushi da Asmah ta kaiwa Jiddarh a baki yasata gocewa tare da cewa “daga fadar gsky kuma Allah mijinki dan kyakkyawa dashi" malaminsu ne ya shigo hakan ya tilastawa Jiddah yin shiru ita dama Asmah bakinta ya kulle kalaman Aseem ne kawai sukeyi mata yawo a kwanya iyayenta matsiyata idan ta tuna wannan kalmar sai taji hawaye ya zubo mata to amma komai ya samu shamuwa watan bakwai yaja mata da mahaifinta baibi son zuciya ba da yanzu tana tare da masoyinta, da taji haka a ranta saita tuna yace da quarter million ya siye Sadiqunta.
Gabadaya duniya tayi mata zafi ji takeyi kamar tayita rusa kuka hakadai a dafe aka tashi suka tafi gda daqyar takai gidan saboda azabar masifar zazzabi da yake dirar mata tana zuwa ko uniform bata cire ba ta fara kwara amai bayan ta gama ta shige dakin innah ta kwanta tana mayar da numfashi




A kwance take amma duniyar juya mata takeyi itadai bata qara sanin komai da yake faruwa ba sai farkawa tayi ta ganta daure da robar ruwa a hannunta ta rinqa bin dakin da kallo daya da daya tanason tunano ko a ina take a hakan taji an turo qofar an shigo ta juyo da kanta idanunsa na kanta yana wani lumshesu kamar me jin bacci.
Guri ya samu ya zauna ya bude takardar hannunsa yayi rubuce rubucensa ya rufe ya sake dagowa yanzun kanta yana saman silling fasali yaja ya miqe daidai lkcn da Inna Azeezah qanwar Innah take shigowa suka gaisa har yana wani rusunawa tace “ya me jikin?" Kallon Asmah yayi yace “gatanan da sauqi yanzu ta farka da alamun jikin dakyau insha Allahu gobe ma zamu koma gida yasu Innah?"



“Alhmdllh" ta furta koma ta zauna tana hade kaya shikuma ya fice bai jima ba ya dawo da tarkacen ciye ciye ya ajiye Innah Azeeza nata godiya yayi murmushi yace “babu komai Innah yiwa kaine fatanmu dai ta samu lfy ai taji jiki sati biyu a kwance ga hidimar biki sai matsowa takeyi yanzu fah saura sati biyar" jinjina kai tayi tace “Allah yasadai ayi lfy a gama lfy"



Amsawa yayi da amin sannan yasa kai ya fice zuciyarsa najin haske yanajin nishadi yasan yagama saita saarsa Asmah zata gane kurenta tabbas zatasan ta shigo gonarsa da wannan tunanin ya tashi mota ya nufi gdansa yajima a mota kafin yayi qarfin halin fitowa yana ayyana ta yanda zai tunkari Mime da mgnr auren nasa bayan shi da kansa yayi mata alqawarin bazai taba hada matsayinta da wata ba balle aje ga batun aure.
Shahada yayi daya haura ya tunkari saman a kwance a parlourn saman ya isheta tana duba jarida ya nemi guri ya zauna ta ajiye jaridar tare da dagowa ta dubeshi sukayiwa juna murmushi ya shafa kansa yace “ya gda?" Miqewa tayi zaune tana yatsina tace “gashinan babu dadi kadaici ya dameni kaikuma ka daina samun lkc na na rasa meye yake daukenka hankali gareni" kawar dakai yayi ya shafa sumarsa yace “abubuwa ne sukayimin yawa 2 days dinnan inason samun zama dakema nakasa samun lkc” shiru tadan ratsa na dogon lkc can ya dago yace “Maryam Aure zanyi....." Wata zabura tayi ta miqe da sauri tace “me....me kace Aseem".......

[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*




*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*





Littafin _*_ZARRAH* na kudine idan kinason zaki biya 200 ta _account dina_
__0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTBank_ _ko kati MTN ta whattsAp a wannan number 09013718241 ko VTU ta wannan number 09031307566._


_Gareku yan'uwanmu na Niger kuma fah kuna da damar samun wannan littafan guda biyu idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_



*_17-18_*



Miqewa yayi yana shirin shiga daki ta riqoshi ta baya tace “wai da gaske kunne na yakeyi kaine kake fadawa Mimee zakayi aure Aseem da gaske hakane? Please tabbatar min domin nasan tudun dafawa" kama hannunta yayi ya zaunar da ita yana binta da kallo yace “ba kamar yanda kowanne aure yakw nawa yake ba Mimee idan kika tashi hankalinki ke kikaga dama da kanki zan Aure ne domin ramuwa da daukar fansa, idan baki manta ba nataba baki lbrn wata yarinya data mareni ta fasamin yatsa kwanakin baya, to itane zan aura, a zahirinta ba ajina bace kuma ba tsarata bace ni kaina inajin kunyar hadaka ta da ita ina qyaqqyaminta wlh don an daina cinikin bayi ne da siyo miki ita zanyi matsayin baiwa ki rinqa morarta




Dakatar dashi tayi da sauri tace “shut up Aseem banason yaudara da zalimci ni zaka wulaqanta ashe dsma abinda ake fadamin gsky ne Wayyoh Aseem meye nayi maka da zakayimin wannan sakayyar...." Rufenta baki yayi yana girgiza mata kai yace “kada ki kawo komai a ranki ba haka nake nufi ba har abada kece zabina kece burina kuma kece zuciyata wlh da gaske yarinyar nan don ke na aurota nasan zata taimaka miki




Sake dagansa hannu tayi ta miqe da gudu ta nufi dakinta ya bita da sauri daqyar ya samu ya shawo kanta bayan yayi mata manyan alqawura masu wuyar cikawa yana qara rantse mata baso bane zaisa ya auri Asmah kawai gayya ce to ganin yanda ya zage yana rarrashinta yasata sakin jiki amma duk da haka kishin mijinta yana cinta a ranta duk da tayi ammannar bai isa ya wulaqantata ba kodon soyayyar da mahaifiyarsa takeyi mata dole yabi umarnin uwarsa saboda haka ta yanke shawarar binsa ta qasa zata hadashi da hajiyansa tasanta sarai bata hada hanya da takala balle kuma ta bari a kawo mata yar matsiyatan qarshen zamani matsayin suruka da wannan tunanin suka fita ko a hanya aikin rarrashin mimee yakeyi suna shiga harabar gidan yaji gabansa yana faduwa so yayi ya juya amma INA ya makara yana daga Kansa ya hango hajiyansa saman bene ta zubawa motarsa ido dole tasashi fita yabi bayan Mimee data shige gdan a qofar falon sukayi karo da Hajja ta daukeshi da mari ya dafe gurin da tafukan hannunsa yanajin zugin marin saman jar fatarsa yana dagowa ta sake daukeshi da mari tana kumfar bakin cewa yanzu Aseem har kayi qwarin da zaka nemi aure batare da ka sanar dani ba saidai naji a wajen qannenka....."
Hawaye Mimee ta goge tace “ai dole bazai fada miki ba Hajja wai ya rasa dawa zai hadani kishi saida yar talakawa...." Dafe qirji

4 / 18